Showing 168001 words to 171000 words out of 227252 words
Chapter 57 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
da gudawa ko da yake irin wannan bala'in da take ciki komai ma zata iya zama numfashi ta ja tana zama bakin katifar da Mariya take zaune tayi mata kuri da idanu sai faman yake take yi wanda sam bai mata kyau ba.
"Kin gama fushin da ni kenan kin ga dama kin zo".
Cewar Mariya tana hararar Baseera da jikinta ya gama yin sanyi da Al'amarin Mariya sai faman gyaɗa kai take yi zuciyarta na tsananta bugu kafun tayi kokarin kirkiro yaƙe ita ma ta yi mata.
"Ban san me yasa har yanzu Baseera ki ka kasa daidai ta komai ba dama fa a hannun ki take amma kin kasa amfani da ita duk wannan abun dake faruwa ke ce kike da mafita amma kin ki amfani da ita ban san me yasa ba?".
Ta karashe tana janyo hannun Mariya ta damke a nata nan da nan sai ga hawaye a idanuwansu su duka numfashi suke saki a hankali Mariya sosai take jin wani iri a zuciyarta ana cewa tana da mafita a hannu amma ita ta ka sa gane a ina mafitar take a gareta komai ta kasa tunani akan sa kwanyarta a tsaye take cak! tana babbakewa bata da wani kuzari ko jarumtar yin wani tunani.
"ki yi kokari don Allah ki samarwa kanki farin ciki da kwanciyar hankali har da muma mu sa mu don Allah".
Baki ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai da ta runtse idanu kafin ta buɗe su da ƙyar ta daga laɓɓanta.
"Ban san me zan yi ba Mariya sosai na kasa yin komai bana so wani abu ya sake hadani da su Umma tace wai zabi na gareni har da mafita kamar yarda ke ma kika ce amma na kasa tuna haka bana tunanin haka zai yuwu".
"Mariya ke ki da wannan damar sai dai kin kasa amfani da ita ya kama ta ace kin fidda daya daga cikin su ina tunanin haka shi ne kawai mafita a garek...".
Da sauri ta fizge hannunta tana ja da baya kamar wacce aka doɗanawa garwashin wuta duban Baseera take yi cikin wani irin yanayi idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir sai faman hirji take yi tana jan numfashi yana kokarin kwace mata kai ta ke girgizawa a hankali tana mai runtse idanunta kafun ta kai hannunta daidai kirjinta ta dafe da karfin tsiya.
"Ba zan iya ba Baseera bana son su na tsane su".
"Zaki iya Mariya za ki iya ki na son su baki tsane su ba ni na san haka daurewa zaki yi don Allah".
Bude idanunta tayi da sauri tana duban Baseera kafun lokaci guda ta kifa kanta kan katifar tana faman nishi dakyar kamar wacce aka shake a makoshi....
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘😘
[9/17, 8:28 PM] DEENY MINNA🙋♂: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.
Abu kamar wasa Mariya zuciyarta da kwanyarta sai kuwwa suke mata mai sauti akan batutuwan Umma da Baseera sosai take jin lamarin ya fara samun karbuwa a gareta zuciyarta na ta kokarin bata dama tayi abin da suke bukata amma ta rasa ta yarda zata fara domin kuwa wani bangare na zuciyarta sai safa da marwa yake yi wajan yanke hukunci kan lamarin.
Numfashi ta ja kafun tayi shiru tana mai tallaɓe haɓarta kamar daga sama ta jiyo kuwwa daga waje da ihu shiru tayi tana sauraron kafun daga bisa ni tayi hanyar fita tsakar gidan Umma ta hango tsaye tana kallon ikon Allah Goggo Marka ce ta turmushe Hafsat sai faman jibga take yi kamar ta samu jaka daga ita sai dan fatari a kugu zanin ya fadi Mariya da take kallon ikon Allah bata san lokacin da dariya ta kusan kufce mata ba duban Umma tayi cikin yanayi na mamaki abin da tunda take a rayuwarta bata taba gani ba shine yau yake faruwa tabbas in da sauran numfashin ka a duniya kana DA SAURAN KALLO.
"Umma me ke faruwa ne hak...?".
Da sauri Umma ta daga mata hannu ba tare da tayi mata magana ba idanuwanta na kan Goggo Marka da ta zage sai jibgar Hafsat take yi kamar Allah ya aikota sai faman numfashi take ita kuwa Hafsat sai zunduma ihu take yi tana kokarin kwace kanta.
"Umma zata kashe fa bai kama ta ki bar ta tai ta dukan ta b...".
Sake daga mata hannu tayi a karo na biyu ta juyo ta dube ta fuskar ta da yanayin bacin rai sosai da sosai kafun ta hadiye wani yawu mai tauri mai nuna a wuya take.
"Yo meye na ki a ciki ta kashe ta mana wa tayi wa jikarta ce komai tayi mata wallahi ko a jikina".
Nan da nan Mariya tayi rau-rau da idanu tana duban Umma jin abin da tace.
"Haba mana Umma mai yasa zaki ce haka? kina kallo fa irin dukan da take yi mata bai kamata ba...".
"A wajan ki ne kike ganin bai kamata ba Mariya..tun dazu nake jin haniyar su ina zaune a nan daga cikin dakin su ban tanka ba sai da naji Goggo na zunduma mata zagi kamar wata wacce ta kirkiri maguzanci shine fa na tashi domin bata hakuri in laifi Hafsat tayi mata amma sai ta hada dani tana tsine min har da iyayena take anbata har tana cewa in har ni ba shegiya bace na fice na ba su waje".
Umma ta karashe tana dauke hawayen fuskarta da suke ta faman zuba kafun ta sake nisawa cike da bacin rai.
"ko ni shegiya ce wallahi dole in bar su in dai ina da zuciya balle kuma uwa da uba akwai su ban hanaki ba zaki iya zuwa ki cece ta domin 'yar uwarki ce ta jini amma ni kam wallahi a,a haram shan giya gidan liman".
Ta karashe tana karasawa wajan da take wankin kayanta ta cigaba da yi sai faman ajiyar zuciya take da wani irin yanayi na takaici zagin da Goggo tayi mata tun da take a rayuwarta ko kwatankwacinsa ba a taba yi mata ba.
Jikin Mariya yayi sanyi sosai tausayin Hafsat take sannan kuma maganganun da Umma ta faɗa mata suna ci mata zuciya sosai taji ranta ya baci tun da taga Umma na hawaye ta tabbata yau an kaita bango numfashi ta ja mai tattare da bacin rai kafun ta dubi Umma wacce take faman dirza kayan wankin kallo daya zakayi mata ka gane sauke haushinta take a jikin kayan da saurin Mariya ta isa gareta ta riko hannunta dago idanuwanta tayi wanda sukayi face-face da hawaye sun kaɗa sun yi jajir sosai hannu ta saka ta na goge mata su.
"Haba Umma me yasa kike zubda hawayenki akan Goggo ya kamata ki saba ba yau bane ta saba yi miki haka...".
"Na san ba yau bane amma abin da tayi mani yau na tabbata zai ji ma a zuciyata bai gogu ba duk abin da take yi mani ina hakuri amma yau HAKURINA ya kare ta kai ni bango amma ba komai Allah na nan ai zai yi mani sakayya".
Ta karashe tana rike hannun Mariya da take goge mata hawaye da su juyawa sukayi su duka suna kallon Goggo Marka wacce ta dago a wannan lokacin tana faman sakin numfashi kamar wacce tayi gudun faffalaki.
"Ni zaki tozarta ni zaki ciwa mutunci ni zaki kwancewa zani a kasuwa to wallahi ba ki isa ba kin yi kadan a yau din nan sai kin koma wajan uwarki ba za ki ja min abin kunya ba a gidan nan haka kawai ina zaman zama na zaki dauko mani ALAƘAƘAI ba garai babu dalili ban san hawa ba kawai sai naji sauka ai da sake wallahi ba a gidan nan ba".
Abin da Goggo Marka ta shiga fadi kenan tana faman haki kamar wacce Numfashinta ke gardama sai faman nuna Hafsat take yi wacce ke kwance idanuwanta sun kada sunyi jajir sai zubda ruwan hawaye suke yi tana faman nishi domin ta daku iya dakuwa
Duka ta sake kai mata cikin rashin tsammani ta doke mata baki lokaci guda ya fara zubda jini kafun ta shureta da kafa ta wuce bayan ta tsintsine mata tayi hanyar dakinta sai faman zage-zage take yi.
Su dai su Umma kasake sukayi gabadaya ta rikita su sun rasa mai Hafsat tayi mata har haka ta duke ta duka mai ansa sun duka haka ko barawo akayi wa wannan dukan sai ya san ya daku a hankali Mariya ta kalli Umma tana faman gyada kai kallon ta Umma tayi ta kau da kai don ta san abin da take nufi a hankali Mariya ta ja jiki zuwa in da Hafsat take bakinta sai zubda jini yake yi idanuwanta na zubda hawaye kallonta tayi kafun ta kau da kai jin zuciyar na tunano mata da kiyayyar da Hafsat ke mata tana jin wani iri da bacin rai amma haka ta daure kawai ta dago ta tana mai zare mata dankwalin kanta tana goge mata fuska da jinin dake zuba a jikinta.
"Sannu ko Hafsat me kika yi wa Goggo haka har take dukan ki abin da bai taba faruwa ba?".
Ta tambaye ta tana mikar da ita kan kafafuwanta ita kuma sai faman cizon laɓɓa take yi saboda tsananin ciwo da jikinta ya kama yi lokaci guda.
"Uban ki tayi min hegiya tsohuwar munafuka in baki sake ta kin bar wajan nan ba in na zo wallahi sai na hada dake".
Kamar daga sama suka tsinkayo muryar Goggo Marka na fadin haka da sauri Mariya ta ja baya tana mazurai.
"Shaggu na kurya masu gansa kuka a idanu ina ruwan ki da ita kinibabba me ya shafe ki da abin da tayi min in ban da kuturun kinibibi irin na ruwarki shine zaki zo kina tambayar ta".
Da hanzari ta ja jiki ta bar wajan tana kallon yarda Goggo Marka ke faman watsa mata banzan kallo kafun ta juya wajan Hafsat dake tsaye kikam.
"ke kuma zo ki shige tun kafun nazo wajan nan na karya miki shaggun kafafuwan nan naki bakar munafuka kawai".
Kikam tayi ko motsi ba tayi ba sai faman zunburo baki take yi gaba wanda ya fara tasawa.
"dake fa nake ko ki zo ki shige ko kuma ki fice daga cikin gidan nan".
A hankali ta fara dingisa kafar da tayi mata tsami sosai ta tunkari dakin tana zuwa Goggo Marka ta dungure mata kai tare da hankaɗa ta cikin daki kafun ta juyo ta dubi su Umma tana jan katon zaki.
"Tsofaffin munafukai kawai ta Allah ba taku ba".
Murmushin takaici Umma ta saki kafun ta ja hannun Mariya su shiga cikin dakin su rai a matukar bace.
*****
Tafe take kanta a kasa kamar wata maras gaskiya Hijab din ma sakko dashi tayi zuwa fuskarta yarda ba kowa yake gane waye ba hannunta rike da ledar kayan cefanar Cake a hankali take tafiya kamar wacce bata son taba kasa.
Kamar daga sama taji yo Horn din mota da sauri ta dago kai kafun ta shiga ja da baya duk a tunanin ta kan hanya take ake mata horn amma sai ta ga akasin haka motar a tsaye take gefe guda amma sai danna horn ake yi haka da ta gani ya sanyata tunanin ba da ita ake ba da saurin ta shiga waige-waige don ganin da wanda ake amma ba kowa a hanyar sai tsirarun mutane kuma kowa harkar gabansa yake yi koman da kanta kasa tayi ta cigaba da tafiya amma gabanta sai dokawa yake yi domin tunaninta ya bata da ita ake yi hakan ya sanyata kara saurin tafiyar da take yi daidai kwanar da zata shigar da ita kofar gidan su ta ga Motar ta shawo gabanta da gudu cikin tsananin firgici tayi gefe tare da sakin kara mai sautin kayan hannunta duk suka zube kasa don duk a tunanin ta markaɗe ta motar za tayi amma sai taga akasin haka buɗe idanuwanta tayi da suke runtse ta sauke akan motar ganin ana kokarin buɗewa gabanta ne ya yanke ya fadi ganin waye a cikin motar yake kokarin fitowa haɗe fuska ta kare yi ta durkasa kasa tana hada kayanta gabanta sai dokawa yake yi da wani irin yanayi gabadaya jikinta bari yake yi lokaci guda idanuwanta suka kada sukayi jajir duk ta rikice kayan nata ta kasa hada su hannunta karkarwa yake yi kawai.
Daddaɗar kamshin turare ne ya daki hancinta lokaci guda ta ja numfashi mai tsayi gami da runtse idanuwa sosai taji a jikinta kallonta yake yi a hankali taji ana ansar ledar dake hannunta cikin rashin kuzari ta saki ledar ba tare da wata gardama ba a hankali ya shiga tattare kayan ya ajje su gefe idanuwansa gabadaya ya sauke akanta yana kare mata kallo kafun lokaci guda ya ja numfashi mai tsayi zuciyarsa na mika shi wani mataki na daban mai cike da abubuwa muhimmai akan Mariya.
Mika hannu yayi kamar zai kamo nata hannun da sauri ta mike tana ja da baya idanuwanta cikin nashi suka sarke gabanta ya cigaba da bugawa a wani mataki wanda yake rikita mata tunanin gabadaya ta rikice sai faman rawar jiki take yi zuciyarta taji tana mikata wani sashi na daban mai kokarin canza mata duk wani tunaninta memorinta taji yana kokarin goge haddar da tayi runtse idanu tayi jin wani abu mai kama da kibiya mai tsanin haske ya kufto daga fuskar Dr.Karami mai tattare da lallausar murmushi ta tunkarota kafun lokaci guda ta buɗe idanun nata haske ya mamaye fuskarta wani numfashi ta ja mai karfi kamar zata shiɗe.
"Ban san me zan ce miki ba Mariya amma ki sani zuciyata tana matakin da take kokarin tarwatsewa da son ki na azabtu na wahalu lokaci mai tsayi wanda nayi tsammanin rayuwata ta kare ke nan duk a kan ki son ki Mariya sosai zuciyata ta kasa sarrafa kanta a dalilin sonki komai...komai nawa ya canza sosai da sosai duk dalilinki ki dube ni Mariya ni mai son ki ne so na hakika ki daure don Allah karki baiwa zuciyata kunya".
Wani irin dokawa zuciyarta tayi wanda har sautin ita kanta sai da ta ji ya bayyana idanuwanta a rufe jin ta take yi zuciyarta na mikata wani mataki da bata tajin taje ba sosai taji kamar kan gajimare take yawo maganganun Dr.Karami suka shiga sauti a cikin kwanyarta mai kara zuciyarta da ruhinta taji suna buɗewa da wani irin yanayi suna ansar sakon Dr.Ƙarami gabadaya taji komai nata kamar sabo komai ya goge sabbin abubuwa taji suna shigarta ta ko ina sake damke idanuwanta tayi kafun ta bude su ta sauke akan sa wani irin kwarjini da haifa take hangowa saman fuskarsa suna kara narkar mata da zuciya cikin wani mataki wanda ba zata iya sarrafa kanta ba.
Durkusawa tayi ta kamo hannayen ledan kayanta ta mike sosai kan kafafuwanta da taji suna lauyewa suna kokarin zubda ita kasa kokarin motsawa tayi tana ɗaga kafar guda daya da taji tayi mata nauyi sosai runtse idanu ta sake yi kafun ta tura laɓɓanta duka cikin baki a hankali ta shiga takawa idanuwanta na kara lumshewa gabadaya garin taga yana juya mata ji take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata MARIYA ce ba ita ba tana ji yana kiran sunanta muryarsa na dakar mata zuciya da kwanya suna kara rikitata amma ta kasa katabus tafiya kawai take yi bugun zuciyarta na kara tsananta sosai a cikin wannan yanayin taji ta cikin soron gidan su lokacin guda ta karasa shiga ta zube tana mai jan wani numfashi mai tsayi dumin hawayen da suka zubo mata ya sanyata buɗe idanu a razane duk a tunanin ta ya biyo ta amma sai ta ga akasin haka bata goge hawayen ba illa wani kuka ta taji ya zo mata tun daga zuciya da ruhi da gangar jiki kukan take yi mara sauti sai faman shassheka take yi kamar wacce numfashin ta zai dauke...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[9/22, 9:13 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.
Cikin kwana biyun da tayi bayan haduwarta da Dr.Karami gabadaya ta gama rikiciwa ta rasa mai ke yi mata dadi a rayuwarta zuciyarta sai faman zillo take akan lamarin sa ta rasa ma me za tayi.
A hankali take kokarin saita kanta da samo mafitan da take ganin ya dace da ita sosai take hana idanuwanta barci tana kai kukan ta wajan Allah domin ya zaba mata abin da yafi zama alheri a rayuwarta baki daya.
Sosai zuciyarta ke matsewa sosai take jin nauyin da zuciyarta ke yi yana raguwa a hankali sosai take jin ya kamata ace izuwa wannan lokaci ta sarara wa kanta da rayuwarta sosai take jin lokaci yayi da ya kamata ta kawo karshen komai.
Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zai yuwu ba ta san ya za tayi ba sosai zuciyarta ta karkata zuwa ga Dr.Karami yawancin barci in tana yin sa duk shi take hangowa amma bata jin za ta iya aurensa.
Amma kuma bata san dalili ba in maganar aure tafi karkata ga Dr.Aqeel tana son Dr.Karami shima Dr.Aqeel tana jin son sa sosai a ranta ba kadan ba sai dai fili mai yawa Dr.Karami ya mamaye mata.
Haka rayuwarta tayi ta tafiya har tsayin wata daya amma har lokacin bata yanke hukunci ba ta rasa wanda zata tunkaro ta fada masa halin da take ciki domin samun mafita tana tsoron sanar da Umma domin yanzu duk ta ja baya ta bata dama ita akaran kanta tayi abin da ya dace Baseera kuma har zuwa wannan lokaci taki yarda su hadu domin bata son ta zo mata da wani lamarin na daban bata so ta zaba mata abin da ba shi zuciyarta take so ba
Haka dai ta cigaba da dakon wannan lamarin har da karshe ta yanke zuwa gidan su Baseera domin ita kadai ce k'awa shakikiya da take ganin ya dace ta san matsalar kuma ta bata shawarar da take ganin ya dace.
Sanye take cikin daguwar riga mai kalar baki da ratsin ja kadan ta sanya jan gyale tayi rolling din shi a kanta sosai ya fito mata da kyanta duk da ba wata kwalliya ba ce ta a zo agani tayi amma tayi matukar kyau takalmi flat ta saka a kafarta sannan ta fito tsakar gida ta tadda Umma zaune ita da Mu'azzam duban su