Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 227252 words

Chapter 23 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1383

Ads at the middle of Article

ta nuna mata duk yarda zata yi sannan ta fito ta bar ta a Toilet din ma'ajiyar kayan ta ta nufa ta buɗe wata doguwar riga ta fiddo gami da wani hijabi mai kalar pink da ratsin kalloli daban daban wanda suka karawa hijabin kyau sosai bakin kafcecen gadon ta ta ajje su sanna ta zauna ta na mai zabga tagumi mintina goma Mariya ta shafe a toilat kafun ta fito tana raɓe-raɓe kamar mara gaskiya da sauri Baseera ta mike ta isa wajanta.
"dafatan kin yi yarda nace ko?".
Gyaɗa mata kai tayi domin wata irin kunya ce taji ta lullubet sai sunne kai take yi kasa.
"Uhmm Karki damu kin ji ko Mariya ba abin da zai sa me ki in Allah ya yarda".
Kai kawai take gyaɗa mata a haka har ta taimaka mata ta kara gyara jikinta bata kayan da ta dauko mata ta saka da kanta ta gyara mata fuska ta baɗe mata jiki da wani lafiyayyan turare mai sanyin kamshi.
Suna cikin kwalliyar ne Hajiya Abida ta shigo fuskarta dauke da murmushi tana duban Baseera.
"dakyau Auta ta kin kyauta da wannan taimakon da kikayi dadyn ku ya fada min komai dake faruwa".
Murmushi Baseera tayi ita kuma Mariya kasa tayi da kai don kunya.
"'Yawwa Mariya kisan mi yanzu lokaci ne da ya kamata ki kula da kan ki sosai ban da wasan banza ko kule-kule kuma don Allah karki sake ki kasance mai yawan zama cikin maza ke 'ya mace yanzu girma ya kamaki dole kiyi taka tsantsan da rayuwarki domin abu kalilan zai ruguza miki rayuwa ba fata ake ba amma tunatarwa na da dadi in Allah ya yarda Allah zai kare muku rayuwa da sauran 'ya'ya mata masu wannan lokacin Allah ya tsare muku rayuwa ku duka kin ji 'ya ta Mariya".
Sosai Mami tayi mata nasiha da tsoratarwa akan abin da zai rugaza mata rayuwa ba karamin dadi Mariya taji ba ta shiga mata godiya nan aka kawo mata abinci Mami ta saka ta gaba sai da ta ci sannan suka hada mata goma ta arzuki su ka rakota har falo in da Dr.Karami yake zaune da Alhaji Haruna ba karamin bugawa gaban Dr.karami yayi ba ganin Mariya ta sauya lokaci daya kamar ba ita ba ya shiga cizon laɓɓansa don tabbatar da Mariya ce ba wata ba wani murmushi ya sakar mata kafun ya mike bayan yayi wa su Alhaji Haruna godiya da karamci da sukayi musu har wajan mota suka rakosu nan Baseera ta sanar da Mariya anjima da yamma in sun taso islamiyya zata zo gidan su a haka sukayi sallama suka tafi zuciyoyin su fal da farin ciki mara musaltuwa.
Tun da suka baro gidansu Baseera ba wanda yayi magana a tsakaninsu Mariya sosai ta haɗe jikinta waje daya kirjinta taji yana bugawa a hankali ba abin da ke yi mata yawo akai sai abin da ya faru da ita da kuma irin maganganun da taji Mami na fada mata wanda ta tabbatar haka abin yake rintse idanu tayi ganin abin take yi kamar almara kamar cikin mafarki ba gaske.
A bangaren Dr.karami shima mamaki ne ya cika shi ko da yake in yayi duba da yanayin ta lokacin ta yayi a matsayin sa na likita zan iya gane haka wanda ma ba su kai shekarunta ba ma sun yi balle ita da yake zaton za tayi 16years.
Da wannan tunanin da zuciyoyin su suke suka isa gida daidai kofar Gidan yayi Parking tsayuwar motar ne ya dawo da Mariya duniyarta da sauri ta dago kai dubi bangaren Dr.Karami da sauri tayi kasa da kai domin ita yake kallo a hankali ta sanya hannu ta buɗe kofar ta fice kamar daga sama idanuwanta suka hango mata abin da ya kusan sanyata sakin fitsari Huzaif ta hango zaune saman motarsa ya haɗe kansa da gwuiwarsa bisa alamu ya jima a wajan zaune da sauri ta juya ta dubi Dr.karami wani irin kallo ta ga yanayi mata mai cike da tuhuma sosai ta hango wani irin yanayi mai kama da bacin rai a fuskarsa kasa tayi da kai da sauri ta fara taka kafafunta wanda take jin su kamar za su narke sosai take jin kanta na wani irin juyawa kamar zai dare gida biyu duk taku daya in tayi sai ta ja numfashin ta da taji yana barazanar daukewa ba ta kai ga shig gida ba taji kugin tsayuwar mota da sauri ta juyo Dr.Aqeel ta hango yana fitowa daga ciki motarsa idanuwansa akan ta sosai ta firgita ganin wani kallo da shima yake yi mata wanda bata san da me zata fassara shi ba a ranta ta furta.
"Yaa Allah! me ke shirin faruwa da ni ne?".
Ai ba ta san lokacin da ta ja kafa tayi cikin gida ba sai faman haki take yi ba ta tsaya ko ina ba sai cikin dakin Umma ta baje kan katifar dake yashe cikin dakin sai faman sakin hirji take yi gabanta na faman bugu kamar zai tarwatse komai taji yana juya mata Umma da ke zaune ta shiga dubanta da mamaki da farko ba tayi zaton Mariya ba ce sai da ta kalleta sosai domin kayan da ke jikinta ba ta san ta da su ba tana kokarin yin magana ta tsinkayi sallamar Dr.Karami da sauri Mariya ta kara dunkulewa waje daya tana cusa kanta cikin hijabin dake jikinta gabanta na kara tsananta bugawa.
Ko ta kan ta bai bi ba Umma kawai yayi wa bayani abin da ya faru mamaki sosai taji nan ta shiga yi masa godiya amma shi ina hankalinsa na kan Mariya wani kallo yake watsa mata ta gefen ido kafun ya dubi Umma muryarsa da sanyi.
"Umma na mance shaf! in Allah ya kai mu gobe zan koma can wajan aikina domin hutun da na dauka ya kare ina muka fatan alheri sai na dawo".
yana gama fadin haka ya mike saman kafafuwansa Umma kuwa sai faman sheka masa addu'a take yi da neman tsari.
A haka ya fita ba tare da ya dubi Mariya ba baya ya ajje wa Umma bandir din kudi masu yawan gaske duk da zuciyarsa sai a zalzalar sa take yi
ita kam Mariya ba a maganarta domin lokacin da taji abin da ya fadi ba ta san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba wasu katangun tashin hankali suka rikito mata akai lokaci guda taji wani zazzabi na shirin rufe ta gabadaya ta kasa motsi jikinta gabadaya taji ya canza kamar ba na ta ba komai taji ya sauya mata a kankani lokaci tsoronta daya Allah yasa ba fushi yayi da ita ba ya yanke mata wannan danyen hukuncin mai barazanar tafiya da numfashim ta kuka take yi na zuciya idanuwanta sai zubda hawaye suke yi sosai take hango tashin hankalin da za ta shiga in ba Dr.karami ta dade a wannan yanayin kafun wani mugun barci yayi awon gaba da ita ya je fata wata duniya mai dauke da Dr.Karami wanda ta kasa tantace ta mene ne sannan ta kasa gane wata irin rayuwa ce suke yi sosai ta hango tashin hankali mutane uku take hangowa ko wanne kuma ita ya dosa da abu mai girma wanda ta kasa gane mene ne?




*KAMALA MINNA*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA DAYA.


Tun ranar da Dr.Aqeel ya dauki kafarsa ya bar kasa najeriya shikenan natsuwar zuciya da ruhi suka gagari duniyar Mariya sosai ta shiga tashin hankali mara musaltuwa bata taba zaton zata yi k'ewarsa har haka ba bata zaton zuciyarta da gangar jikinta za su kasa sukuni har haka ba tayi kuka, kukan wanda take zaton zai rage mata raɗaɗi zuciya amma hakan bai yuwuwa ba sosai ta raya darurruka masu yawa cikin yanayi na damuwa da takomshin saƙar zuciya.
Sosai takoma shiru-shiru magana ta za me mata wani aiki kato a duniyarta ba ta san ya kayi ta batawa ran mutumin da ya jikanta a rayuwa ba ba ta san mai yasa tayi gangancin haka ba bata san mai yasa a ranar da za su rabu ta barshi sa tukwuicin bacin rai ta sani da fushin ta ya bar kasan nan ta sani dole ya shiga cikin yanayi na bacin rai duk a dalilin ta ina zata gan shi ta bashi hakuri a ina zata ganshi ko ba a zahiri ta wanke laifin da ta yi masa ta sani sosai yayi mata nisa nisan da ba ta da damar da zata je in da yake har karshen rayuwarta in bashi ne ya dawo ba ya tadda ita tunanin ya ta'allaka ne a yarda za t rayu dashi a zuciyarta wanda ba ta san adadin lokacin da zai dauka kafun ya dawo ba sosai take hango gangancin da tayi na bata damar da ta samu.
Haka ta cigaba da rayuwa cikin wannan yanayi da tunanin Dr.Karami lokaci mai tsayi cikin duniyarta haka ta cigaba da zuwa makaranta tana karatu da tunanin Dr.Karami a ranta da ruhi dama duniyarta baki daya.
Mutum daya ce take samun damar da take zama tana zantawa da ita har ta rage mata damuwar dake addabar zuciyarta sosai Baseera ta taka muhimmiyar rawa a duniyar Mariya sosai take nuna mata rashin dacewa ga halin da ta je fa kanta duk yarda zatayi don ganin ta rage mata tunanin abin dake dawainiya da Mariya tana yi sosai take hanata zaman shiru kulli-yau min in dai basu da lesson to tabbas zaka same su zaune waje guda suna bitar karatun su domin Baseera ta hakikance haka ne kawai zai rage abubuwa da yawa a duniyar Mariya da suka addabe ta.
A bangare guda kuma Dr.Aqeel da Huzaif suma sosai suke saka ta cikin halin rashin kwanciyar hankali domin ta hakikance a ta dalilinsu komai ya faru da ita tsakaninta da Dr.Karami sosai take jin tashin hankali a duk lokacin da suka kwaso jiki suka zo gareta bata san abin da suke nufi da ita ba sosai take ganin suna takura mata domin kuwa laifin komai da komai da ya faru akan su ta daura su ne silar faruwar komai.
Ko dai dai in tayi duba ta wani fannin duk wanda ya zo a tsakaninsu tana kula su hakan kuma na kara tuna mata da Dr.Karami tana ba su lokaci sosai da sosai domin Dr.Aqeel ba abin yadawa bane shima ya taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarta sosai da sosai ba za ta yi masa halin dan'adam ba mai mai da alheri zuwa akasin sa.
Haka shima Huzaif duk da tabon da yayi mata a zuciya hakan bai sa ta watsar dashi tun da ya nuna nadamarsa akan abin da yayi amma kuma ba hakan bane ya sanya ta tsayawa dashi har ta bashi lokacin ta illa soyayya da yake nunawa kaninta Mu'azzam soyayya ce mai girma a tsakaninsu gami da shakuwa sosai da sosai yake bashi kulawa yake tattalin sa kamar dan'uwansa na jini hakan ba karamar rawa ya taka ba har Huzaif ya samu matsayi a filin zuciyarta.
ba ta san wata irin ƙaddara bace take yawo da ita a duniyarta a duk lokacin da ta tuno abubuwa da suke ta faruwa da ita a filin rayuwarta sosai take hango tashin hankali mai girma nan gaba duk ranar da Dr.Karami ya duro kasar nan.
*****
"Nikam ina ganin Bariki 'ya duk idanuwanta sun gama buɗewa tana kallon mutane ɗai-ɗai kamar tsararrakin ta ni ban san wani tsohon makiri bane da wannan danyen aiki in ban da son sani da kalan-dangi da neman mai da yariya karamar yar duniya me nene haka kullum yarinya kenan da tsukanken wando da guntun hijabi tana zarya a hanya kowa ni kare da doki suna kare mata kallo".
Goggo Marka ce take fadin haka tana tafa hannu a daidai lokacin da Mariya ta dawo daga makaranta jikinta sanye da Uniform riga da wando sai hijabi wanda iyakarsa kirjinta.
Tun da Mariya tafara daukar kafarta zuwa makaranta tun daga wannan rana Goggo Marka take debe mata albarka akan cewa iskanci kawai da duniyanci ya sanya aka saka ta makarantar yahudawa yarinya sai kara girma take yi tana buɗewa kowa ni namiji sai kallon ta yake yana haɗiyar yawu.
Ba karamin tashin hankali Mariya tashiga ba a ranar da taji mugun nufin da Goggo Marka ke jfanta dashi tayi kuka kuka mai amsa sunansa kuka Umma ita kanta tayi bakin ciki mai girma sosai zuciyarta tashiga tashin hankali jin mugun nufin da ake jefar 'yarta da shi a ranar ta so ta hana Mariya zuwa makarantar amma zuciyarta ta hanata tana mai gargaɗin ta akan sabawa alkawari da kuma rashin baiwa Dr.karami muhimmancin abin da yayi musu na alheri sosai tayi duba akan ilmi tasan ilmi na da matukar muhimmanci a duniyar rayuwar 'yarta sosai karatun da tayi zai taimaka mata a fannoni masu yawa a wannan zamanin da ake ba wai ita kadai Mariya ba har da su iyayenta da al'umma a duk ranar da ta zama wani abu a filin duniyar nan a dalilin karatu tasan za suyi alfahari da ita sosai da sosai.
Ta sani dole ne ta jajirce sannan ta kau da kunnuwanta ga sauraron duk wani mugun furuci da za a fada mata ita da 'yarta dole ta rarrashi zuciyarta dole ne ta cigaba da yi ma 'yarta addu'a sannan ta kara mata karfin gwuiwa ta nuna mata amfanin karatu a duniyarta da su iyayenta dama Al'umma gabadaya ita dai fatanta a kullum Mariya ta tsare rayuwarta da martaba gami da darajarta ta dage wajan karatu sosai da sosai duk wuyarsa da wahalarsa zata ga amfaninsa nan gaba sosai da sosai domin a yarda suke yanzu karatunta zai matukar taimaka masu nan gaba sannan ta kara tunatar da ita cewa ta dube su da rayuwar da suke yi ta tabbata in da sunyi karatu a zamaninsu ba a za su fuskanci kalubalin rayuwa har haka ba ko ma za su fuska to ba zai yi tsauri haka sosai da sosai ba.
Huɗubar Umma sosai ya samu waje a filin zuciyar Mariya ta ajje waje na musamman.
Sosai take jin tausayin iyayenta na kara samun fili mai girma a zuciyarta da ruhinta sosai take hango irin rayuwar da suke gudanarwa tana hasashe kafun zuwanta duniyar nan ta sani sun fuskanci KALUBALE sosai da sosai in tayi duba da yarda auren iyayen nata ya kasance a yarda take samun labari sosai suka shiga tashin hankali kafun tabbatar auren iko na Allah ne kawai yayi aiki a tsakanin iyayensu har suka bar su suka auri junansu.
Domin sosai ake fuskarta matsala tsakanin Fulani iyayen Habeeba da manoma iyayen Bello sosai rashin jituwa ke tsakaninsu amma sai Allah ya kulla soyayya mai girma tsakanin 'ya'yansu wanda haka sam bai yi musu dadi ba su iyayen musamman ta bangaren iyayen Habeeba domin AKAN SO da take yi wa Bello ta zabi kin bin iyayenta domin da rigima tayi rigima abu yaki ci yaki cinyewa sosai suka fara kokarin haɗe kayan su domin canza mazauni nan Habeeba tayi tsalle ta dire ta nuna ita ina ba za ta bi su ba komai za suyi mata kuwa tana tare da Bello gani take in aka raba ta dashi to tabbas zata iya rasa rayuwarta sosai iyayenta sukayi fushi da ita har ya kai ba sa yi mata magana ganin da sukayi da gaske take sannan da ban baki da mutane suke ba su hakan ya sanya su barwa Habeeba auranta akan kuma komai yasa me ta kar ta sake ta tako kafa in da suke domin kuwa duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka a ranar da aka daura auren Habeeba da Bello a ranar iyayenta suka bar garin Gwada gabadaya zuciyoyin su cike da abubuwa marasa dadi su yi KUDIRI a ran su ba za su sake takowa zuwa wannan garin ba har gaban abada.
A lokacin da akayi auren Bello mahaifiyarsa bata raye mahaifinsa ne kawai yake duniya sai matarsa Marka wanda tun lokacin ita ce take rura wutar komai domin sam bata kaunar auren ta tsani Bello da uwarsa domin a tunaninta shi ne ɗa namiji a gidan kuma shi ne magaji ita kuwa 'yarta daya Zainabu wanda suke kira da Abulle Abulle macece mai hakuri bata biyo halin mahaifiyarta ba domin sosai take bakin cikin duk abin da taga mahaifiyar ta ta nayi wa su Bello Abulle ta riga Bello Aure domin tun tana shekaru sha biyar aka auren da ita tun da tayi auren bata taba haihuwa ba har akayi bikin Bello lokacin da Bello shima ya tare a nan gidan su sun jima kafun ita ma Habeeba ta samu ciki wannan rashin samun ciki sai ya buɗe wa Goggo Marka katon filin tsula rashin mutunci ga Habeeba tana mai aibata ta wai juya ce bata haihuwa kila ta gama yawon bin mazan ta acan rugarsu ta gama zubda kwayayen haihuwarta a layi wajan tallar su ta gado shine aka likawa Bello sosai take jin bakin ciki da takaici sosai ta so yin dana sanin auren Bello amma in ta tuna irin HALACCI da yayi mata ya nuna mata so da kauna ya tattale ta ya za me mata MIJIN MARAINIYA sai taji a ranta za ta iya zama dashi da ko wani irin hali ne ko da kuwa Goggo Marka za ta dinga yankar naman jikinta ta miya dashi.
Ba karamin tashin hankali Habeeba ta fuskanta ba a tsayin shekaru biyu da tayi a gidan auranta sosai duk hakurin ta da kai zuciya nesa hakan bai hana ta shiga matsananciyar damawu ba duk da bata gayawa Bello abin da ke faruwa tun ba ya ganewa har ya zo ya na fuskanta ya yi bakinciki ya nuna bacin ransa amma mahaifinsa ya dinga ba shi hakuri akan kar ya damu wata rana sai labari.
A na cikin wannn tataburzar ciki ya bayyana jikin Abulle Innalillahi wa inna ilaihir raji'una.
Ina wuta Goggo Marka ta saka Habeeba nan fa ta sake bude sabon shafin gori da aibatawa bakaken maganun kuwa ba a magana a lokacin Habeeba ta ga tashin hankalin da bata yi tsammani ba domin kuwa Goggo Marka zuwa tayi da kanta tun cikin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads