Showing 129001 words to 132000 words out of 227252 words
Chapter 44 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
nisa a sonka, na jima ina sanar da ita cewa ba mu dace ba amma bata ga hakan ba ta nuna min so ba ruwansa da haka, Dr.Erena naji ma ina son ka so mai tsanani sosai nayi zaton za ka gane in da na dosa amma ina sam hankalin ka bai kai nan ba maganar gaskiya ina son ka kai ne namiji na farko a filin duniyar nan da zuciya ta tayi amanna dashi a fannin so ban san ya zan kwatanta maka ba amma ka sani ina son ka so mai ansa suna so".
Zabura yayi daga kan kujerar da yake zaune idanuwansa cike da tulin mamakin maganganun Mufeeda hannu ya shiga nuna ta dashi yana jan numfashi kafun ya saki wata dariya wacce ta kaɗa 'yan hanjin Mufeeda sosai lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi runtse idanu tayi wasu hawaye suka zubo ta kasar Glass din da ke fuskarta kafin ta shiga haɗe hannayenta waje daya tana Rolling din su.
"You Love Me? For God Sake! Mufeeda kina cikin hayyacin ki kuwa kin san waye Dr.Erena kuwa da kike daukar wa kan ki wahalar son sa to maganar gaskiya ba zan boye miki ba bana tunanin zan iya zama nayi soyayya dake bake ba ma hatta WATA MACE daban bayan Areefa bana zaton ko kallon arzuki zan iya yi mataa ya kamata ki san wani abu mace bata gabana mace daya na taba so kuma nake burin zama da ita ita ce Areefa ita ma ban san ya akayi zuciyata ta kamu da son ta ba a RANA DAYA ba zato ba tsammani naji KIBIYAR AJALI ta son ta ta cakar min zuciya wanda har zuwa wannan lokaci na kasa zareta sai kara lumewa take yi cikin zuciyata da duk wani gurbi na cikin ta".
Dubansa take yi da duk idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir fuskarta har tana canza kala izuwa ja sosai take jin duniyar nayi juya mata da duk wasu kalaman Dr.Erena da take jin su kamar saukar garwashin wuta.
Numfashi take ja da take jin sa kamar ta na jan barkono izuwa kanta dama cikin ta sosai take jin duk wani sashi na jikinta na narkewa kamar zata watse a kasa dan yatsanta daya ta kai baki tana cizawa domin tabbatar da abin da yake faruwa da ita gaskiyane ba a mafarki bane yau ta kara tabbatar wa da maganar hausawa na cewa SON MASO WANI koshin wahala ne ta tabbatar da yau Dr.Erena baya tare da ita At All baya gayyatarta a filin duniyarsa bai ma san tana yi ba.
"Na lura da abin da kika zo dashi akan Areefa duk kishi ne kina tunanin son da nake yi mata zai bari na dauki abin da ki ka zo mani dashi a gaske to ko da kuwa gaske ne ba zan dauka ba Areefa mace ce da nake so so mai garman gaske wanda bana zaton a filin duniyar nan akwai macen da zan iya yiwa ko da kwatar son ne don haka fice mani daga cikin Office".
Ya fadi yana mai yi mata nuni da hannu fuskarsa a murtuke kamar bakin hadarin da ya gangamo yake kokarin zubda ruwa.
"Dr.Erena MENE NE LAIFIN ZUCIYA don ta nuna so da kulawa akan abin da take so bana zaton son da nake yi maka zaka yi masa fatan KARKON KIFI ka sani so nake yi maka son da ban taba yi wa wani ɗa namiji ba a filin duniyar nan ya kamata ace ka girmama son da nake yi maka ka dauke shi da daraja ka killace shi a zuciyarka a wani fili ko ya ya ne...".
"Are U At Of Your Sense Mufeeda kina da hankali kuwa wacce irin magana ce haka kike fadi wani irin hauka ne haka ina so dole ne nace bana yi na ce bana sonki leave alone mana".
Murmushi ta saki mai ciwo kafun ta zare Glass din dake fuskarta idanuwanta da suke rine suka bayyana sosai take duban Dr.Erena da yake mata kallon wulakanci da raini laɓɓanta ta ciza.
"Karka yi tunanin don na furta kalmar so a gareka zai baka lasisin wulakanta ni, karka yi tunanin don buɗe baki na sauke aji na da daraja ta ta 'ya mace za ka wulakanta ni ka sani ba aibu bane san nan ba zubda mutunci bane don mace ta buɗe bakinta ta fadiwa ɗa namiji tana son sa ba san nan haka ba yana baiwa ɗa namiji dama bane don ya wulaƙanta 'ya mace don ta nuna tana ta son sa ba duk macen da zata iya buɗe baki tana cewa namiji tana son sa ba abin kunya bane kuma ba abin a wulakanta ta bane domin tayani don ceto kanta da halin da zata fada ka san wannan Dr.Erena karka yi tunanin son da na nuna ina yi akan ka zai baka damar tozartani ka wulakanta ni daraja da martaba ta tana nan ba abin da ya ragu sannan ko a duniyar masoya na san nayi abin kwarai wanda da yawan mata ba sa yi sannan kuma kamar yarda mata suke tsoro halin da ka nuna min da tozarci da wulakanci don kawai na nuna ina son ka ba laifi na bane laifin zuciya tane wacce ba ƙashi gareta ba".
Dubanta ya sake yi a wulakance domin sosai zuciyarsa tayi zafi da kalamanta motsa baki ya shiga yi yana kokarin magana ta daga masa hanni.
"Ba sai ka daka min tsawa koka koreni kamar wata mara 'yanci kai ba yanzu zan bar maka Office din ka".
Tana fadin haka tayi hanyar fita daga Office har ta rike Handle din ta juyo ta dube shi sosai kafun ta kau da kai tare da ficewa daga cikin office din tana kokari hau benen da zai kai ta kasa ita kuma Areefa na sako kai saura kadan suyi gware nan suka shiga kallon kallo a tsakanin juna su fuskar Mufeeda cike da kunci da bakin ciki kallon Areefa take yi da wani irin yanayi kafun ta kau da kai gami da jan tsaki ta wuce ita dai Areefa bin ta take yi da kallo ganin yanayin da take ciki kamar akwai abin da take damun ta musamman idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir kafaɗarta ta daga cikin nuna halin ko in kula kafin ta isa ta tura kofar cikin Office din.
Tsaye ta same shi yana kai kawo hannayensa goye a bayan sa motsin shigowar tane ya sanya shi tsayawa yana jan numfashi fuskarsa a daure kamar hadari.
A hankali ta isa ta zauna tana mai daura kafa daya kan daya bakinta dauke da cingum tana faman taunawa idanuwanta akan Dr.Erena kallon sa take yi da wani irin yanayi mai haifar mata da ɗaci a zuciyarta sosai take dubansa da damuwar da take fuskarsa a ranta take fata dama ya dauwama a haka yaƙe ta saki kafun ta kaɗa idanuwanta.
"Me ke faruwa ne Dr.Erena?".
Sai a lokacin yaja numfashi mai girma ya na huci gami da runtse idanuwansa dubanta yayi kafun ya ja kujera ya zauna.
"Wannan mai kalar haukar ne za tayi mani akunyanci bata san na fita da duk tashencin ta ba".
Cikin rashin fahimta ta yatsine fuska cikin son karin bayani.
"Wai fa zuwa tayi tana sakin wasu banzayen kalamai kafun daga karshe ta dire da cewa wai ni take so ki ji fa wata wauta da kalar hauka".
Fakare tayi tana kallonsa tana karantar yanayin sa mamaki ya cikata ta yarda Mufeeda ta iya jefa kanta son wannan mugun mutumin mara tausayi da imani ita kam bata ga abin so a jikinsa ba bata ga abin burgewa a gareshi ba har da Mufeeda zata zo tana fada masa tana son sa har ya samu damar ci mata mutunci ya wulakanta ta ko da yake kila kudin da yake dashi ya ruɗeta in kuwa haka ne Mufeeda bata yi wa kanta adalci ba da tayi sake ta fada motar kwadayi ta dire a tashar wulakanci da cin mutunci.
"Ni ban ga abin ta da jijiyoyin wuya ba don tace tana son ka ai ta dace ace kai ma ka anshi son da take yi maka duk macen da zata iya zuwa ta ce tana son ka ai bata cancanci wulakanci da tozaryawa ba duk da dai ku mafiyawancin maza haka kuke in har kuka ga mace ta mutu akan son ku shikenan kun samu hanyar wulakanta ta da cin zarafin ta iri-iri".
Murmushi yayi lokaci guda kafun ya motsa laɓɓansa.
"Bana tunani haka zata kasance tsakani na da ke Areefa so daya nake yi kuma akan ki yake bana zaton akwai wata mace da zan so bayan ki akan ki na fara so kuma akan ki zan gama so ki san wannan".
"Uhmm haka dai kace aiku dama haka kuke maza akan mace akwai iya dadin baki musamman in duniya na yi muku biyayya ba abin da ba za kuyi wa mace ba".
"Areefa na lura kamar kina goyon bayan Mufeeda da ne ko baki jidadin abin da nayi mata ba".
"Ko daya wallahi amma dai ka sani mace mace ce ko min lalacewarta don haka ka kula mace ba yar wulakanci bane ita mai daraja ce da kima duk da dai wasun mazan ba su dauki mace a bakin komai ba sun mai da ita kamar riga lokacin da suke ra'ayin ta za su saka ta da sun gama kuma su cire su ajje ita da banza duk daya".
Mikewa tayi tana mai daukar jakarta ta dubi Dr.Erena da ya saki baki yana ta faman murmushi idanuwansa akanta kafun ya mike shima.
"Ya haka Areefa ina zaki daga zuwanki kuma Please ki zauna mana akwai maganar da nake so muyi dake mai muhimmanci ce".
"At this Time bana tunanin zan iya zama kuma ina da abin yi gaskiya".
"Please mana Areefa".
Juya idanu tayi kafun ta dube shi cikin gyaɗa kai ganin haka ya sanya shi komawa ya zauna yana mata nuni da ta zauna ita ma ba musu ta zauna yana ma kallonta kallo na sosai da sosai kafun ya ja mumfashi.
"Areefa maganar gaskiya ya kamata ace kin ce wani abu akan alakar dake tsakaninmu ya kamata ace kin motsa motsawarki kawai nake buƙata a yanzu".
Ci rashi bawa zancen nashi muhimmanci ta dubeshi kafun ta motsa laɓɓanta cikin ɗacin zuciya.
"Ina jin ka me kake nufi?".
Sai da ya sosai ƙeyarsa kafun ya saki murmushi na sosai da sosai.
"Maganar aure mana ya kamata ace mun tsayar da magana a wannan lokacin...".
Da sauri ta daga masa hannu tana mikewa kan kafafuwanta zuciyarta take ji tayi wani bugawa da tashin hankali mai girman gaske jin zantukan nashi take yi kamar saukar aradu ƙwanyarta taji tana juya a hankali ta dube shi.
"Please ka bari za muyi waya in na koma gida kaji komai zai yi settling a cikin kan kanin lokaci".
Tana gama fadin haka ta fice daga Office din cikin sauri kamar wacce zata kifa haka take ji komai taji lokaci guda ya canza mata da tashin hankali mai girma kunnuwanta take ji ba za su iya daukar kalamansa ba masu dauke da kunci da bakin ciki tafiya take yi har ta sauka kasa ta isa in da sashin ta yake komai ta kammala a hanzari ta zare key din motarta ta fice daga cikin reception din tun kafin ta isa in da motar ta take tayi mata key ta buɗe baya ta isa ta shige ta haɗe kanta da sitiyari tana mai da numfashi a hankali kanta take ji yana sarawa da karfin tsiya kamar zai rabe gida biyu sai da ta shafe lokaci mai tsayi kafin ta yiwa mota key ta fizge ta cilla ta saman titi ta shiga zabga gudu kamar wacce zata tashi sama burin ta kawai ta ganta a gida ko ta samu tayi saita kanta sosai take jin tashin hankali na tunkaro ta sosai take jin ranta na kara baci duk lokacin da suka hadu da Dr.Erena don dole kawai take zama dashi da umarnin Hajiya Layla.
*********
Tun da ya doso Muhabbir Coffee yake jin gabansa na yankewa yana faduwa lokaci lokaci hakan na karuwa sosai yaji a jikinsa akwai abin da ke kokarin faruwa dashi.
Parking yayi bayan yashiga wajan yayi oda din duk abin da yake bukata ka kawo masa a hankali yake kai Coffee bakin sa yana kurba har zuwa lokacin jikinsa bai daina sanar dashi wani abu dake kokarin faruwa dashi ba tun yana daukar lamarin da sauki har yaji zuciyarsa tana kara azalzalarsa da yabar wajan A hankali ya mike ya dauki wayarsa da key din sa bayan ya biya kudin abin da yayi oda ya doshi in da motarsa take ajje ya bude ya shiga ya zauna bayan kulle yana kokarin yi mata key yaji an dorasa masa bakin bindiga ta bayan kansa zare idanu yayi a firgice yana kallon mutane biyun da suke bayansa zaune ta glass din gaban motar.
"ja motar muje".
Daya daga cikin su yace dashi murya a buɗe gabadaya kamar saukar markaɗe.
Jikin rawa ya shiga yi jin abin da suka ce dashi ware ido yayi yana kokarin juyawa ya dube su laɓɓansa na motsi daya daga cikinsu ya daka masa tsawa cak! ya tsaya da maganar da yake kokarin yi jikin sa na ƙyarma sai faman ambaton sunan Allah yakeyi.
A hankali yayi wa motarki bayan ya yi ribas ya fice daga cikin wajan. In ba wai kasan abin da yake faru a cikin motar ba ba zaka iya cewa komai ba dubin gabadaya glass din motar mai duhu kuma a zuge yake.
Suna fita daga cikin wajan suka shiga nuna masa hanyar da zai bi a hankali a hankali suke tafiyar har suka fara ficewa daga cikin gari nan Alhaji Abdulwahaab ya kara ruɗewa ganin suna tun karar daji da sauri yayi kokarin taka burki amma jin bindiga a keyarsa ya sanya shi kara wuta cikin hanzari jikinsa na rawa domin ya tabbatar wadannan mutanan barayi ne ko kuma yan satar mutane.
Daji sosai suka yanka sai da yashiga cikinsa sosai sannan suka ce yayi parking a hanzarce yayi sannan ya juya yana kokarin kallon su daya daga cikin su ya buga masa kan bingida a gefen fuska wanda hakan ya sanya shi sakin kara gami da yin lif! jikin kujera kamar wani mara lafiya wajan da suka dokar masa lokaci daya ya fara fiddo jini.
Gabadayan suka buɗe suka fito dayan su ya ja kofar gaban ya buɗe ya fizgo Alhaji Abdulwahaab zuwa waje ya baje akasa kansa na buguwa da gefen motar wata irin kara ya saki gami da ambaton sunan Allah numfashi kawai yake ja a hankali gabadaya ya gama shiga tashin hankali mai tsanani dagowa yayi cikin matsanancin yanayi yana duban su ganin su yake yi suna kasuwa bibbiyu idanuwansa suna lumshewa a hankali yana buɗe su bai ankaraba ya sake ji an kai masa wani wawan naushi a fuska an daki goshinsa da kan bindiga nan ya baje a sume bai sake sanin in da kan sa yake ba.
Duban juna sukayi suna masu sakin wata mahaukaciyar dariya kafin su tafa hannayensu a hankali suka fara tafiya suna ficewa daga wajan shikuwa Alhaji Abdulwahaab bai ma san in da kan sa yake ba.
Ya dauki lokaci mai tsayi can wajan magrib sanyin yamma ya kaɗashi ya farka a wahale yana kokarin buɗe idanuwansa amma jin su yake yi kamar ba a jikinsa suke ba dafe kan sa yayi sosai yana mai kara runtse idanuwansa lokaci daya ya buɗe su duhun daren da ya fara shigowa shi ya an karar dashi da sauri ya tashi zaune ya juya yaga motarsa hannu ya saka ciki Aljihu wayarsa yaji da sauri ya zaro yana dubawa 6:50pm shida da minti hamsin ya gani a hankali ya shiga kokarin tashi amma tsamin da jikinsa yayi ya hana shi kokarin da yake yi rarrafawa yayi har ya isa wajan motar ya dafata sannan ya mike yana faman cizon laɓɓansa buɗe motar yayi ya shiga a hankali yana faman numfarfashi yakeyi zama yayi sosai yana jin yarda bayansa ke amsawa da ciwo mai tsanani cikin dauriya yayi wa motar key Allah ya taimake shi ta ta shi ajiyar numfashi yayi mai karfi a hankali ya shiga yin ribas har ya juya hanyar da zata fiddo shi daga cikin daji.
Sosai ya fita daga cikin daji ya shiga gari daidai wani Super-Market ya tsaya ya daga kansa sama daidai wani shago da yake zaton clinic ne haka kuwa akayi KAMALA CLINIC ya ga an rubuta da dan hanzarin sa ya buɗe ya fito ya doshi wajan bayan yayi sallama ya shiga nan ya yi musu bayanin abin dake faruwa wani daga cikin ma'aikatar wajan ne ya zo yayi masa komai da ya dace har da allurai sai daya sha
Kafun ya fito ya dauki hanya zuwa gida zuciyarsa cunkushe da godiyar Allah da lamarin ya tsaya a haka ba tare da sunyi masa wata illa sosai ba.
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA SHIDA.
Juyi kawai yake yi saman faffaɗar gadonsa da ya kusan cinye rabin dakin numfashi yake ja a hankali zuciyarsa na wani irin kartawa.
A hankali ya mike yana kai kawo a tsakiyar dakin gumi mai tsananin zafi sai tsantsafo masa yake yi a goshi lokaci-lokaci yake runtse idanuwansa ba abin da yake hangowa sai Huzaif da ya rike hannun Mariya sosai yaji zuciyarsa na zafi da zugi wani katon abu mai nauyi yaji ya zo masa zuciya ya tsaya cak!.
Bai san abin dake damun sa ba a daidai wannan lokacin zuciyarsa sosai take son firgita masa tunani game da Mariya sosai yake jin wani fili mai girma ya buɗe a zuciyarsa ba abin dake yada zango a cikin sa sai lamarin Mariya sosai yake hangowa a ranar da ya fara ganinta bayan shekaru hudu da suka shuɗe ba tare da ya sanyata a idanuwansa ba.
Runtse idanuwansa ya sake yi a karo na ba adadi kafin ya shiga taka kafafuwansa a hankali yana mai isa toilet din sa ruwa ya watsa domin ko zai samu sa'ida a zuciyarsa dama gangar jikinsa gabadaya.
Yana cikin goge sumar kansa da shawul wayarsa dake yashe gefen gadonsa ta dau Ringing ya tsine fuska yayi kafin ya dubi wayar cikin halin-ko-in-kula yana mai jan guntun tsaki sai