Header Ads
Showing 165001 words to 168000 words out of 227252 words

Chapter 56 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1416

Ads at the middle of Article

kara kamawa da wuta yake yi ya kasa yin wani tunani ma na kirki ko zai samu mafita.
Ya jima tsaye a wajan kafun ya yanke hukuncin barin wajan domin ya tabbata ba fitowa za tayi ba shikuma ba iya shiga gidan zai yi ba domin kuwa gabadaya bai son su hadu da Umma kwata-kwata.
Yana kokarin shiga motarsa ya hango Mu'azzam ya fito da gudu yana waige da alamun biyo shi akayi da sauri ya dakata yana mai da kofar ya rufe kamar daga sama ya hangota ta tunkaro kofar fitowa tana ta faman kiran Mu'azzam amma ina sai kara wutar gudun sa yake yi wata irin mutuwar tsaye yayi ganinta ta canza sai yaga ta kara masa kyau da haske sai dai ta kara ramewa sosai harɗe hannayensa yayi a jikinsa kirjinsa da yake faman dokawa da sauri-sauri a daidai lokacin Mu'azzam ya iso gareshi ya kankame shi yana neman ya ceceshi amma shi ina fuskarsa da komai nasa na kan Mariya a daidai lokacin ita kuma ta dube she wata irin razana tayi kafun idanuwanta su yo waje sosai da sauri ta juya ta fada cikin gida cikin wani irin hali mai ciwo a zuciya.
Ya shafe lokaci kafun ya ja wani gwauron numfashi mai sauti ya durkusa ya dafa kafadar Mu'azzam yana kallon sa abin mamaki fuskar Mariya yake ganin tana yi masa gizo tana mai sakin tattausar murmushi a gareshi sai da Mu'azzam ya taba masa fuska sannan ya dawo hayyacinsa yana dubansa kafun ya ce dashi.
"Me kayi aka biyo ka da gudu haka hala rashin ji kayi ko?".
Juyawa yayi ya kalli kofar gidan kafun ya dubi Dr.Karami da ya kureshi da idanu.
"Yah Mariya ce ke kuka a daki shine na fadawa Umma kuma ta hanata kukan to shine don Umma ta shiga bandaki shine ta biyo ne don ina ce mata mai kukan banza".
Dariya Dr.Karami yayi amma cikin zuciyarsa ji yayi wani zafi na kawo masa farki sosai tashin hankalinsa na daduwa kalmar 'kuka' da yaji Mu'azzam ya ambata tana yi ita Mariyan sake daga kai yayi ya dubi kofar gidan yaji kamar ya mike ya fada cikin gidan ya lallashe ta.
"je kace ina kiranta".
Ya fadi yana dubansa cikin idanu shima Mu'azzam din dubansa yake kafun ya shiga girgiza kai.
"a,a dukana za tayi kuma ko an aika ta zo ba ta fitowa kullum".
"Me yasa?".
Ya fadi bugun kirjinsa na sauyawa da sauri-sauri
Girgiza kai yayi kafun ya sake kallon kofar gidan.
"nima ban sani ba kawai dai kullum a daki take zama ba ta fitowa ko Umma bata tayawa aiki".
Runtse idanunsa yayi jin wani abu ya tokare masa zuciya kafun ya sake fadin.
"Ba ta da lafiya ne".
"Tunda ta dawo daga asibiti shikenan ina ganin kila bata ji sauki bane".
Mikewa yayi ya saka hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi masu auki ya mikawa Mu'azzam girgiza kai yayi alamun ba zai ansa ba sai da yayi dakyar sannan ya ansa.
"kace ina gaida Umma da Ita Mariyar kaji yi maza ka koma gida ba wanda zai dakeka".
Da gudu kuwa ya juya yayi gida shikuwa jin gina yayi da mota yana faman mai da numfashi sosai yake jin zuciyarsa wani iri jin halin da Mariya take ciki ji yake kamar ya kakkare mata damuwar ya dawo da ita kansa ya sani har da laifinsa wajan sanyata ko wani hali ta fada yana da kamasho in da ya san haka rayuwar zatayi musu inda ya san ALKALAMIN KADDARA haka zai rubuto musu wannan rayuwar da bai yi SAKE wajan bayyana mata yana son ta ba da ya furta mata tun lokacin da yake ganin bata cancanta ba ya san komai daren dadewa zata koyi son shi kuma zata ajje kalmar so da ya fadi mata tun lokacin baya har zuwa lokacin da za ta gane meye SO.
Da wannan kuncin zuciyar ya shiga motarsa ya bar kofar gidan kwanyarsa sai wuta take kokarin kamawa da ita gabadaya ya rasa me ke masa dadi a rayuwarsa dole ya san abin yi dole ya fuskarci wannan kalubalin dole ya nemi mafita a gareshi.
********
Tana zaune ta na aikin Cake wanda ya zama yanzu ita ce take yinsa Mariya ta zama abin da ta zama sosai lamarin na Mariya ke sha mata kai ta rasa mai ke damun 'yarta ta yau kusan wata guda kenan tun da aka sallamota daga asibita ta rasa gane kanta kullum cikin kuka take kullum cikin damuwa bata da aikin yi sai kuka abin na taba mata zuciya tayi faɗan tayi rarrashin amma bata sauya zani ba har ta zurawa sarautar Allah ido ta sani suna cikin yanayi na rayuwa duk yarda ta zo musu dole su anshe ta duk wani abun dake faruwa dasu na dadi da rashin sa ALKALAMIN ƘADDARAR su ce a haka ba yarda za suyi...
Tunanin ta ya katse lokaci guda da hanzari ta dawo hayyacinta jin an kwaso da gudu anyo waje gabanta ya yanke ya fadi daga idanuwanta tayi cikin fargaba da tsoro duk a tunaninta Mariya ce amma sai taga akasin haka Hafsat ce ta fito da gudu daga dakin Goggo Marka ta zube tana ta faman amai da kakari kamar wacce zata amayar da 'yan hanjin cikin ta amai take yi wanda ba komai a cikinsa sai ruwa da majina sosai ta rike cikinta tana faman nishi tana murkususu kamar wacce akayiwa dukan shan gishiri.
Da sauri Umma ta zare hannunta cikin kwabin da take yi ta dauraye hannayenta ta mike kan kafafuwan ta da sauri ta karasa inda Hafsat take wacce ta gama galabaita rikota tayi tana mata sannu gabadaya jikinta ya saki sai faman nishi take yi kamar wacce rai ke kokarin ficewa daga jikinta sosai Umma ta tauyasa mata ganin irin halin da take ciki lokaci guda duk ta zurma kamar wacce take amai da guda.
Ruwa ta debo ta bata ta dauraye bakinta sannan ta wanke mata fuska ta taimaka mata ta mike ta raka ta daki ta kwantar kafun ta dubeta ganin ba kowa a dakin.
"Dama baki da lafiya ne ina Goggo din take?".
Banza tayi da ita jin yarda cikinta da kasar mararta ke kartawa da wani irin azababben ciwo kamar yan hanjinta zasu zazzage sai faman juyi take tana cizon laɓɓanta idanuwanta a runtse sosai zuciyar Umma ta karyewa da yanayin da ta ganta a ciki sai faman sannu take mata jin ta kasa bata ansar tambayar da tayi mata sai da ta jima a tsaye ganin Hafsat ta lafa da murkususun ya sanyata juyawa tana kokarin fita har ta daga labule sai ga Goggo Marka ta sanyo kai ita da sauri ta ja baya Goggo Marka ta shiga dubanta da wani irin yanayi na tuhuma kafun ta leka cikin dakin ta hango Hafsat a kwance sake dubanta tayi.
"Lafiya me ya shigo dake dakina".
Ta fadi cikin tsawa tsawa da nuna bacin rai
"A,a Hafsat naga ta fito tana ta kalaya amai shine na taimaka mata ban san bata da lafiya ba".
"Ba ta lafiya fa ? Kika ce injiwa ya fada miki lafiyarta kalau sai dai in wani abu taci yake tayar mata da zuciya har ya kaita ga amai"..
Yanayin da take maganar kawai zaka kalla ka gane bata da gaskiya da sauri ta shigo dakin har tana bangaje Umma kayan da suke hannunta gabadaya suka watse Umma tabi kayan da kallo lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi ganin kulin maganguna har su mataccen ƙadangare da sauri ta ja da baya ita ma Goggo Marka kayan tabi da kallo kafun ta dubi Umma a dan tsora ce ta shiga tattare kayan tana cewa.
"to ki fita mana ko kin tsaya kina kare min kallo ko da kwai wani abu ne?".
Tana magana jikin ta na rawa da sauri Umma ta fice daga cikin dakin gabanta na kara tsananta faduwa sai sunayen Allah take kira sosai zuciyarta ta shiga zargin abin da tagani fata take yi Allah yasa hakan kar ya tabbata kar dai ace wani abun Goggo Marka take aikatawa domin sosai ta ji a jikinta akwai wani abu a boye dangane da abin da ta gani a yanzu ta jima tsaye a kofar dakinta tana tunani kafun ta isa wajan aikin da take yi gabadaya taji ya kuma sure mata kwasar kayan tayi ta fada cikin dakinta...


*_Kamala Minna_*😘😘😘
[9/17, 8:26 PM] DEENY MINNA🙋‍♂: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA SHIDA.


Zuciyarta zafi take sosai kwanyarta sai kokarin kamawa da wuta take yi ta rasa komai nata mai armashi ta rasa duniyar guntun farin cikinta dake rayuwarta sosai take cikin yanayin kunci zuciyarta sai faman yayyagewa take yi da girman tashin hankalin da take ciki kuka ya daina samun gurbi a idanuwanta HAWAYEN ZUCIYA su ma kan su sun dai samun gurbin zuba komai ya kafe komai ya daina samun numfashi mai kwari daga gareta ba ta san ya zata kwatanta wannan lamarin ba bata san ya zata dauke shi ba bata san mai yasa duniyarta take kokarin yamutsewa ba koma tace ta ya mutse ALKALAMIN KADDARA yayi rubutu mai tsauri akanta bata yi tsammanin rayuwarta zata kare a haka ba farin ciki babu shima kwanciyar hankali babu komai da komai babu kawai dai...
Wani irin kartawa zuciyarta tayi da hanzari ta mike daga kwancen da take tana sanya hannayenta duk biyu tana dafewa idanuwanta a runtse kamar wacce ake sokawa karfe mai tsanani jar wuta a jikinsa numfashi take da kyar tana jin kirjinta na kara tsananta bugawa mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman cizon laɓɓa kamar zata fizge su daga mazauninsu.
Kai kawo ta shiga yi cikin dakin a hankali tana duban su Umma da suke barcinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba sosai take tausayin kanta sosai take ganin kamar ita kadai ce a filin duniyar nan take cikin tashin hankali gani take kamar ita kadai ne so yake bugawa yadda ransa ke so kamar wata ball bata san ya zata dauki AL'AMARIN SO ba a filin rayuwarta bata san ya zata kwatanta bala'in da fada ba A DALILIN SO ba tana shakka akan cewa so yana da dadi gaskiya ba za ta amince da haka ba so guba ne ba komai ba.
Haka tai ta safa da marwa a tsakar dakin har zuwa wani lokaci mai tsayi cikin DUHUN DARE ba tare da ko yaya ne barci ya so kama ta ba in aka ce ma barci zai zo wajan ta zata karya ta domin kuwa ita a karan kanta ta manta yaushe rabonta da yin barci mai ansa suna barci...
"Ke Mariya wai lafiyarki kalau kuwa?".
Kamar daga sama taji muryar Umma a dan razane ta juya ta dube ta zaune ta hangi Umma ta kafeta da idanu kafun ta cigaba da fadin.
"Ke yanzu fisabilillahi kina ganin haka ya dace miki Mariya kina zaton wannan abin da kike yi shi ne zai zame miki mafita a filin duniyarki bana zaton haka wannan damuwar da kike shiga ba karamar matsala zata jefa ki ba ke ko fada ba zakiyi wa kanki ba yaushe ki ka farfaɗo daga ciwo wa yayi zaton ma za ki sake WATA RAYUWA a duniyar nan".
Rausayar da kai tashiga yi cikin rashin abin cewa ta sani duk maganganun da Umma take fadi akanta gaskiya ne amma ita bata san ya zata koyi duk wannan abubuwan ba zuciyarta sosai da sosai take zafi sosai take cikin tashin hankali wanda ba ta san ya zata kwatanta shi ba.
"Zo ki zauna muyi magana".
Cewar Umma cikin Muryar rarrashi da tausayin 'yar tata a hankali Mariya ta ja jiki ta isa kusa da ita ta zauna kafun ta dago ido ta dubi Umma jikinta ya shiga rawa kamar wata mai jin sanyi.
"Umma ina cikin bala'i ban san ya zan kwatanta shi ba bana zaton na shigo duniyar nan a nasara bana tunanin akwai wata rayuwa da zan yi har karshen numfashi na bayan wannan...".
Sosai tausayin ta ya kara rikita zuciyar Umma nan da nan ƙwalla suka tarun mata a ido bata bari Mariya ta gani ba domin kuwa ita ta san halin da take ciki akan duk matsalolinta amma bata nuna mata ba ta son abin da zai kara dagula mata lissafi dakatar da ita tayi.
"ki daina fadin haka Mariya na sha fada miki duk abin da ki ke ganin yana faruwa da baya dama tun fil'azal ALKALAMIN KADDARA ya zana masa haka a KUDINSA don haka Mariya ke daina cewa ke ce kika fi kowa rashin rabo a duniyar nan ke taki matsalar kika sani in da zaki ga na wani zaki sha mamaki zaki ce ke ba komai bane ya same ki godiya zakiyi wa Allah duk wannan abubuwan suna cikin KUDIN JARABAWARKI...".
"Sauki fa kika ce Umma?"..
Mariya ta fadi da wani irin yanayi mai karya zuciyar mai sauraronta kafun ta ja numfashi tana tura laɓɓanta cikin baki.
"bana tunanin haka bana zaton akwai wanda ya kai ni rashin nasara a filin duniyar nan...".
Da sauri Umma ta rufe mata baki muryarta na karyewa kamar mai son fashewa da kuka.
"A,a Mariya ki daina yawan batun nan zaki iya yin saɓo Allah zai yi fushi dake ki dinga tunanin bayanki ki dinga tuna wanda ya fiki Mariya akwai wanda yafi ki da yawa su zaki duba domin ki tabbatar da cewa ke rayuwarki ma a haka akwai farin ciki shin kina tunani kuwa akan wanda suke faɗowa duniyar ba tare da komai ba ba uwa ba uba ba dangi shin bakya tunanin irin rayuwar da suke yi shin kina tunanin in suka shiga matsala akwai wanda yake rarrashin su ke ki godewa Allah kina da masu duba ki har su ji ƙan ki Mariya rayuwar nan da kike gani ba wai farin ciki bane a cikinta ba wani nishadi a cikinta duk wanda kika ji yace duniyar nan akwai dadi to ki tabbatar auren sa duniyar tayi ki sani duniyar nan ba wai zama ake yi na dindindin ba komai dake faruwa jarabawa ce akwai ranar da komai zai sauya kuma zai canza...".
"zuwa yaushe Umma zuwa yaushe kike tunanin rayuwa zata sauya bana tunanin haka bana tunanin rayuwa zata sake buɗe mana wani shafi bacin wannan ki duba tun da na ta so rayuwa take juya mana baya rashin gata rashin Uba rashin kwanciyar hankali komai ma Umma babu a rayuwar mu ta yaya kike zaton zan yi farin ciki?".
Maganar take yi cikin rashin hayyaci muryarta na kara buɗewa bakinta sai rawa yake yi Umma kallonta kawai take yi tana faman gyaɗa kai hawaye sai bin kumatunta suke yi bata san ya zata kwatanta wannan al'amarin ba ita gabadaya komai ya kwance mata komai ya kara dagule mata numfashi ta ja mai karfe kafun ta hadiye wani yawu mai tauri ta sake duban Mariya bayan ta dauke hawayen da suke faman zubo mata gabanta yana todakawa so take yi tayi magana amma tana tsoron yarda komai zai watse in batayi wasa ba amma ana ta tunanin ita ce kawai hanyar mafita a garesu.
"Mariya mai zai hana ki zabi daya a cikin su tun da abin da ya kasance haka duk wannan kai ruwa ranar da ake yi bana tunanin zaki iya zama matar su su duka mace bata auren namiji sama da daya maza ne suke da wannan damar ta aure mace sama da daya kokari zakiyi ki baiwa zuciyarki juriya da hakuri ki runtse idanu ki zabi daya a cikin su".
Galala Mariya tayi da baki tana kallon Umma da wani irin yanayi gabanta na tsananta bugawa kafun wata dariya ta kwace mata kamar wata sabuwar kamu sosai take duban Umma wasu hawaye na zubo mata da take jin su kamar garwashin wuta suna saukar mata a fuska laɓɓanta ta ciza sosai har sai da taji zafi ya ziyarce ta kafun ta sake su.
"Zabi kuma Umma? bana tunanin cikin UKU BALA'I zan iya daukarwa kai na daya gaskiya bana tunanin a filin duniyar nan ko zan rasa mai so na zan iya daukar wani a cikin su bana son su su dukan na hakura da su domin kuwa komai ya faru dani a dalilin su ne duk wata bakar rayuwa da wahalar ta da na shiga a dalilin su ne ba su da tausayi ba su da imani sam a zuciyarsu suna son kan su da yawa in da suna jin tausayina wallahi ba za su yi mani haka ba Umma WASU MAZAN san kan su kwai suka sani da burinsu da suke fatan cimmawa akan abinda suke so ba ruwan su da abin da zai faru in dai ba akan su ba ne".
"A,a Mariya ki daina fadin haka duk ba mafita bane mafitar kenan ki zabi daya a cikin su dolen su ne su kyale ki tun da ba dukan su zaki hada ki aura ba miji daya a ka sani mace na aura a al'adance haka a addinance".
Wani murmushi mai ciwo ta saki.
"Bana tunanin zan iya daukar daya daga cikin su...nifa Umma na dawo daga rakiyar su a rayuwa ta ba zan sake kokarin faɗawa matsalar rayuwa A DALILIN ƊA NAMIJI ba an yi na farko ba za a sake yin na biyu ba na gwanmace in zauna haka ba aure har na karashe rayuwa ta...".
"Ya isa haka Mariya nace miki ya isa haka abin naki yana neman zama rashin hankali kuma kina nuna nufin don wannan abin ya faru dake shikenan kuma kin yanke rahama a rayuwarki kenan butulci zaki yi wa Allah to tun wuri ki san abin yi domin ba zan lamunci wannan shirman naki ba".
Tana gama fadin haka ta koma ta kwanta hakan ba karamin tashin hankali ya saka Mariya ba duban Umma take yi da mamaki zuciyarta sai faman bugawa take yi sosai take jin wani iri maganganun Umma sai tsananta sauti suke yi a cikin kanta runtse idanu tayi tana daura hannayenta saman kirji tana jin yarda yake bugawa cikin wani irin yanayi sake buɗe idanu tayi ta kalli Umma wacce tayi shiru ta san ba barci take yi ba sosai ta lura ranta ya dan sosu kin amincewa da tayi da maganar ta gyaɗa kai tayi kafun ta zabga tagumi hannun bibbiyu.
******
Tunda Baseera ta shigo take kallonta da wani irin yanayi na tausayawa ganin yarda Mariya ta fige ta kanjame kamar wata mai amai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads