Header Ads
Showing 171001 words to 174000 words out of 227252 words

Chapter 58 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1415

Ads at the middle of Article

tayi su duka kafun tayi murmushi wanda iyakarsa fuska tausayin kanta da na Umma hadi da na kaninta kawai take ji tunowa da tayi da mahaifinta ko yana ina a halin yanzu Allah masani.
Numfashi ta ja mai tsayi har sai da Umma ta jiyo sautin sa juyowa tayi ta dube ta sosai.
"Lafiyarki kalau kike wannan doguwar ajiyar zuciyar?".
Ta fadi tana kara duban jikinta.
Gyaɗa kai tayi tana sake kokarin kakalo murmushi duk da kwallar da ke kawo mata farmaki a idanu.
"Ba komai kawai dai...Uhmm yawwa Umma zani gidan su Baseera".
Kallon tuhuma Umma ta shiga yi mata na dan lokaci kafun ta gyaɗa kai.
"Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutan gidan amma karki dade fa kin ga yamma ta fara yi".
Ansawa tayi da 'to' sannan ta dubi Mu'azzam da yayi kuri yana dubanta dakune masa fuska tayi cikin tsokana.
"Yah Mariya zan biki".
Ya fadi cikin sanyin murya zaro idanu tayi waje.
"Ni zaka bi caɓ! gaskiya a,a ba zan iya jigilar zuwa da kai ba ban son kaje gidan mutane kana yi musu rashin ji ka bar ni da jin kunya".
Ta fadi tana mai kama hanyar ficewa rau-rau yayi da idanu kamar zai yi kuka amma Umma ta hana shi ta shiga rarrashin sa.
Hafsat ce ta fito daga cikin daki fuskarta dauke da rashin walwala sai faman ya tsine fuska take yi kallo daya zakayi mata ka gane ramar da tayi ta ɗashe tayi fari sosai ga idanu duk sun zurma tayi firgai-firgai da ita.
Mariya dake koƙari ficewa ganin Hafsat ta fito ya sanyata tsayawa tana dubanta kafun ta dubi Umma cikin yanayi na tausayawa a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.
"Uhmm Hafsa ya jikin naki...".
Wata harara da ta maka mata shi ya sanyata saurin tsuke bakinta tana kau da kai zuciyarta take ji tana wani iri tuni ta fahimta har zuwa wannan lokacin ba abin da ya canza a Hafsat duk rashin lafiyar da take fama da ita kamar zata mutu amma bai sanya komai ya canza ba duban Umma tayi itama Umma ita take kallo mai cike da 'Allah ya kara' ta maka mata harara da sauri ta ja jiki zuciyarta na kunci.
"Munafukar banza sau nawa zance miki ki daina shiga lamarina ina ruwanki da rashin lafiya ta".
Furucin Hafsat kenan ta fadi da kyar kamar wacce akayi wa dole Mariya bata bi ta kanta ba illa karasa fita daga gidan cikin sauri da tayi.
*****
A hankali take tafiya zuciyarta ta mika ta can wani waje na daban kawai tafiya take ba tare da ta kula da inda take jefa kafa ba cikin wannan yanayin har ta isa bakin titi ta tsayar da mai Napep tana kokarin shiga wata bakar mota kirar 406 ta zo gilmawa ta gabanta kamar ance ta dago kai ta dubi motar wani irin faduwar gaba taji ya ziyarce ta da sauri ta runtse ido ta bude lokaci guda.
Shi din ne ba wani ba har ta mance yaushe rabon da ta ganni a idanuwanta tun lokacin da suka kusan kashe ta sai kuma ranar da ya zo wajan Hafsat abin yayi matukar bata mamaki yarda Huzaif ya kasance mai FUSKA BIYU a gareta yana bibiyarta yana ikirarin yana sonta sannan kuma yana son 'yar uwarta sosai taji lokaci guda ya fice mata a rai wani haushi da takaicin sa ya tsirga mata a rai domin ganin rainin wayo yake musu a tsakaninsu ya mai da su kamar wasu ball ya buga wannan ya buga wannan. 'Mtss.
Ta ja dogon tsaki dago kai tayi ta dubi mai Napep wanda shima ita yake kallo haushi ya sake turnuke ta ganin irin kallon da yake yi mata kamar ya ga wata bakuwar halitta.
"Tafi abin ka na fasa".
Ta fadi cikin haushi da takaici a rayuwarta ta ki jinin kallo shi kuwa kamar wani maye gabadaya ya juyo yana dubanta a hankali ta fara takawa tana barin wajan tana ji yana kiranta amma ko ta kansa ba ta sake bi ba.
Da sauri ta tari wani Napep din ta dane tana hango waccan sai faman dubanta yake yi har suka zo suka giftashi suna hada idanu ta galla masa harara gami da jan tsaki.
Tafiya sukayi sosai daidai wajan wani Mall ta hango motar Huzaif anyi Parking dinta daga dan gefe ta hango shi shida wata mace ya rike mata hannu sun tunkari cikin wajan zaro idanu waje tayi zuciyarta na harbawa da sauri-sauri kamar zata fallo daga cikin zuciyarta rintse idanu tayi zuciyarta na matsewa da wani irin bakin ciki tana tattama akan Huzaif anya kuwa son da yace yana yi mata na gaskiya ne an ya son gaske yake yi mata?
Girgiza kai ta shiga yi da sauri-sauri zuciyarta na mikata can baya lokacin da suka fara haduwa da yanayin da ya nuna mata ta tabbataa akwai alamar tambaya akansa bata san abin da ya shigar mata kai ba har ta yarda dashi bata san me yasa har ta saki da Huzaif ba sosai take ganin wautarta sai yanzu ta hango kuskuren da tayi har ta bashi fili a zuciyarta yake abin da ya ga dama aciki.
bata san sun wuce wajan ba sai da suka kai daidai wata hawa taji anyi sama da ita sannan tayi firgigin ta dawo hayyacinta ta shiga ware idanu gani tayi har sun shigo layin su Baseera wata irin ajiyar zuciya tayi mai karfi kafun ta runtse idanunta da wani irin yanayi a zuciyarta ta sanar da mai Napep daidai in da zai sauke ta.
Tana sauka ta bashi kudin sa ta dauki hanya domin karasawa gidan a bakin Get ta tsaya ta kwankwasa mai gadi ne ya leko ganin wacece ya saki murmushi ita ma murmushi tayi masa tana gaishe shi ya buɗe mata ta shiga a hankali take tafiya tana tunkarar kofar da zata shigar da ita cikin babbar falon haka kawai taji zuciyarta na kunci tana kuma bugawa cikin sauri-sauri a haka har ta isa bakin kofar ta rike Handle din haka kawai ta ji wata kasala da gajiya ta saukar mata sakin Handle din tayi ta dan ja baya tana ajjiyar numfashi tana mai lumshe idanu kamar mai jin barci a hankali ta sake kamawa idanuwarta a rufe ta tura gami da yin sallama muryar Mami da taji ta ansata ya sanya shiga ciki.
Zaune suke ita da Tareeq ya mike sosai kan kujera waya a hannunsa sai faman latsata yake yi Mami da ta ganta ta saki Murmushi kamar ko yaushi da sauri ta isa gareta ta durkusa ta na gaishe ta ansawa tayi kafun ta dube ta sosai.
"Ya jikin naki Mariya da fatan dai komai Normal ba abin da ke damun ki kuma?".
Gyaɗa kai tayi ganin Tareeq ya juyo da sauri yana dubanta suna hada idanu tayi kasa da kai shi kuwa har zuwa lokacin idanuwansa na kanta ajikinta take jin haka ana kallonta wani tunani ne ya fado mata kar Mami tace bata kyauta mata ba dago kai tayi a hankali ta dube shi.
"Ina yini Yah Tareeq".
Ta furta murya can kasar makoshi tana rawa bai ansa ta ba illah duban sosai da ya sake yi mata jin da yayi ance bata da lafiya kafun ya numfasa ya ansata ba yabo ba fallasa tare da yi mata ya jiki.
Haka kawai taji wani iri yanayin da ya ansa mata cikin izza da nuna rashin baiwa gaisuwar tata muhimmanci ji tayi zuciyarta wani iri duban Umma tayi tana faman yake.
"Umma Baseera na ciki kuwa?".
"Eh tana ciki yanzun nan ta tashi daga nan wai barci zata yi".
Murmushi Mariya tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk sai taji wani iri ganin yarda yake kallonta gabadaya taji kafafuwanta suna harɗewa kamar zata zube a kasa sauri ta kara don kar tayi abin kunya agaban wanda bai san ya kula mutane ba in an kula shi mtss ta ja tsaki ta dane sama abin ta har ta kai matakin sauka sannan ta juyawa da kanta kasa aiko sai idanuwansu suka sarke zaro idanu tayi sosai ganin har zuwa wannan lokacin yana kallon ta wani murmushi taga yayi na gefe kumatu tare da lumshe idanu da sauri ta kau da kai tana jin zuciyarta na bugawa cikin hanzari ta bar wajan.
Tana isa kofar dakin Baseera ta tsaya cak! tana mai da numfashi me Tareeq yake nufi da ita mai yasa yake yi mata haka me hakan ke nufi wannan kallon na meye yake yi mata ta lura dashi in dai ta zo gidan nan ta same shi gaban Umma ya dinga sha mata kamshi kenan amma in bata nan sai ya dinga jifanta da wani kallo dake faɗar mata da gaba ta rasa me yasa haka.
'me ya shafe ki dashi'
zuciyarta ta fadi mata da sauri ta daga kafunta alamun 'babu' ta tura dakin ta shiga ruf! ciki ta same ta waya a hannunta sai faman danne-danne take a waya da sauri ta karasa ba tare da Baseerar ta sani ba ta zaune gefenta tare da sanya dan yatsar ta daya ta ta sosa mata tsakiyar tafin kafarta wata irin razana da ihu Baseera tayi tana mai komawa can gefe ta cillar da wayar saman gado idanuwa a warwaje jikinta sai k'yarma yake yi Mariya ta kwashe da dariya kafun ta ce.
"Ke banza ni ce fa matsoraciya kawai".
Wata uwar harara Baseera ta cilla mata kafun ta ja wani numfashi mai nuna alamun ta firgita sosai.
"Allah ya isa wallahi ke kam an yi muguwa ai wannan sai kiyi ajalin mutum da tsoratarwa wallahi".
Ta fadi tana mai sankowa daga gadon tana isowa gareta ta zauna kallon sosai tayi mata kafun tayi murmushi.
"Baby din nan fa kyau kike karawa wallahi kamar wata sabuwar amarya meye sirrin ne ko dai...".
Sai kuma tayi shiru tana kyalkyalar dariya dubanta Mariya tayi cikin muryar mai rauni.
"Magana na zo muyi don Allah Baseera ki bani shawara".
Sosai Baseera ta shiga dubanta ganin yarda fuskarta ta nuna alamun damuwa gyaɗa kai ta shiga yi tana kokarin yin magana suka ji an turo kofa gabadayan su suka juya suka Fuskanci kofar Mariya ce ta zaro idanu kafun ta kau da kanta gefe.
"Yah Tareeq".
Cewar Baseera tana duban sa murmushi ya saki yana duban Mariya kafun ya dubi Baseera ya kashe mata ido daya dakune fuska tayi tana mai girgiza kai ba tare da ta bari Mariya ta ganta ba.


*_Kamala Minna_*😘😘😘
[9/23, 9:03 AM] DEENY MINNA🙋‍♂: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA TARA.




Sosai taji a jikinta kamar akwai abin da ke faruwa don haka ta dubi Baseera da taji ita ma tayi shiru tunda ta kira sunan Yah Tareeq dubanta tashiga yi ganin abin da take yi da idanu tana dakune fuska kamar wacce aka tursasa sai tayi abu ba tare da ta so ba.
Haka kawai taji gabanta yana faɗuwa dago kanta tayi gabadaya ta sauke wajan Tareeq wanda yake ta faman biyawa Baseera karatu ta hanyar idanu da hannu ganin Mariya ta dago kai da sauri ya wayance yana faman cin magani.
"wai shin me ya faru ne naji ihun ki?".
Ya fadi yana duban Baseera da tayi tsiru-tsiru gabanta na dokawa tsoronta daya kar Mariya ta gano abin da suke yi a tsakanin su akan ta ne susa keya tashiga yi kamar maras gaskiya tana faman yak'e.
"Bakomai Yah Tareeq".
Ta fadi tana mai duban Mariya wacce ta komar da kanta kasa tana nazarin yanayinsu tabbas akwai wani abu a boye a tsakaninsu wanda zuciyarta ta tabbatar mata akan ta suke komai haka kawai ta sha jinin jikinta.
"Uhmm Yah Tareeq..".
Da sauri ya juya har yana kokarin tuntube wajan fita nuni da Baseera tayi masa kamar Mariya ta gano su shi kuma abin da bai kauna kenan sam! Mariya ta gano halin da yake ciki a kanta.
Son ta yake yi amma ya rasa yarda zai yi ya fuskance ta ba yarda bai yi da Baseera tayi masa kamfe ba amma ta kekeshe kasa ta ki yarda ba abin da bata fada masa ba akan halin da Mariya take ciki amma ya ki amincewa giyar soyayya sai kwasar sa take yi amma ya kasa zuwa ya tunkari Mariyar.
Wani murmushi Baseera ta saki lokacin da ta hango Tareeq na kokarin bugar bango da sauri ta kalle shi shima kallon ta yayi yana dakune fuskarsa sannan ya fice daga cikin dakin..
"Mariya wai shin me ke faru ne naga duk jikin ki yayi sanyi haka".
Baseera ta katse shirun da yayi wa dakin ado.
A hankali Mariya ta dago da kanta ta dubi Baseera cikin yanayi na tuhuma sai da ta sha jinin jikin ta ganin irin kallon da Mariya take yi mata.
Murmushi Mariya ta saki na yak'e kafun ta nutsu fuskarta na komawa yarda take a shigowarta alamun damuwa.
"Sosai na kasa fahimtar komai, ban san ya zan fuskanci wannan lamarin ba".
Ta fadi tana mai tura laɓɓanta cikin bakinta fuskarta na kara bayyanar da tsantsanr damuwar da take ciki zuciyarta take ji tana kara matsewa da wani irin yanayi mai girman gaske haka kawai taji tana shakka akan ta fadiwa Baseera halin da take ciki a wannan lokacin.
Numfashi taja mai tsayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo cikin dakin na dan lokaci sannan ta tsaya cak! Ta juyo ta dubi Baseera da tayi shiru tana sauraron zuciyarta itama na ta fadan tsalle-tsalle da fargaban abin da take son kawowa Mariya din so take yi kawai fatanta ya tabbata Allah yasa maganar da Mariyar zata yi ya zo daidai da gaɓar da take so zata yi amfani da wannan damar domin samun abin da take bukata duk da zuciyarta na ta faman gargaɗinta ita akaran kanta jin wani iri take yi kan lamarin amma bata san ya za tayi ba.
Mikewa tayi ita ma Baseera tana takawa zuwa inda Mariya take tsaye jikinta na kara karyewa sosai zuciyarta na bugawa cikin wani mataki na rashin tsammani.
Dafa kafadar ta tayi tana mai ajiyar zuciya.
"Ban fahimce ki ba mai ke faruwa ne?".
Cewar Baseera cikin rashin abin cewa domin gabadaya ta shiga RUƊANI kawai jarumta ce take kokarin sanyawa kanta amma zuciyarta kamar zata faso tayo waje don fargaba.
"So nake yi ki bani shawara Baseera na gaji da wannan Bala'in gwanda na san abin yi tun kafin zuciyata ta buga na mace a banza a wofi".
Zaro idanu tayi sosai jin abin da take cewa da sauri ta kamo hannunta ta saka cikin nata tana dankewa da wani irin yanayi.
"A,a Mariya ki daina fadin haka wannan ba magana bace sam! komai da kika ga ya na faru dake ALKALAMIN ƘADDARAR ki ne a haka ki dauki komai a matsayin JARRABI a rayuwarki kar kiyi gangawar yanke hukunci ki bi komai a sannu karki ji zuciya ta kwashe ki ki zo kina dana sani".
Runtse idanu Mariya tayi tana jin zuciyarta na kara ya mutsewa da wani irin mataki tana mikata wani waje na daban buɗe idanunta tayi sosai kan Baseera wanda suka fara kaɗawa.
"Hmm Baseera kenan kin fi kowa sanin halin da nake ciki kin fi kowa sanin Bala'o'in da na shiga dole na nemi mafita tun wuri".
"Nasan da haka Mariya amma ki saurara ki yi tunani kafin ki yanke hukunci".
Sosai take dubanta karo na ba a dadi kallo ne wanda ya sanya Baseera shan jinin jikinta gani take yi kamar Mariya tuhumarta take bisa yanayin da ta lura yak'e ta shiga yi kafun Mariya ta kau da kai daga kallon da take mata ta ja wani numfashi mai tsayi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa.
"Wa ya dace na zaɓa a cikin su wa kike ganin shine INGANTACCE wanda ya dace da rayuwata?".
'An zo wajan'. Zuciyar Baseera ta fadi tana wani irin dogawa sosai zaka gane firgici a fuskarta idanuwanta a warwaje ta shiga motsa baki tana son yin magana amma ta rasa ta ina zata fara a hankali ta ja hannun Mariya suka koma bakin gadon suka zauna dukkaninsu sai faman ajiyar numfashi suke kamar wadanda suka yi aiki mai wahalar gaske suke zaman hutu.
"Kin fasa canza wani saurayin ne daga cikin UKU BALA'In naki?".
Baseera ta fadi tana faman sakin murmushin yake gabanta sai dokawa yake so take yi ta dauko gaɓar da zata sanar da Mariya komai amma tana fargaba da tsoro akan abin da zai je ya dawo bata san ya Mariya zata dauki lamarin ba bata san ya zata kalle ta ba anya kuwa ba zata ce ta fiye SON ZUCIYA da son kanta ba? Gyaɗa kai tayi.
"Duk mu ajje wannan maganar gefe Baseera na hakura da komai wallahi na mikawa Allah lamarina hukuncin sa kawai naƙe bukata a duk yarda ya zo zan anshe shi".
Jin abin da tace ya sanya Baseera dubanta sosai cikin sanya wa kai jarumta duk da dokawar da zuciyarta ke yi.
"Nikam nake ganin kamar ki canza zai fi miki lura da yanayin rigimar da kike ciki a yanzu in har kika zabi daya a cikin su kina ganin za a samu maslaha a tsakani kuwa... ko da yake hakan da kike gani shima ya dace tunda ba dukkansu zaki aura ba dole in kika zabi daya dole sauran su yi hakuri tun dake ba MATAR MUTUM UKU bace matar mutum daya ce namiji ne MIJIN MACE HUDU ba ma daya ba".
Tunda ta fara maganar take lura da ita sosai kamar akwai wani BOYAYYEN AL'AMARI da take boye mata haka kawai taji ba ta yarda da ita ba sosai take jin haka a jikinta.
"Uhmm shikenan tom...ko daya ke ke ma kin kawo shawara amma kuma yanzu in nace zan nemi wani daban me kike tsammanin zai faru?".
Murmushi tayi sosai wanda iyakarsa laɓɓan bakinta.
"Mazan ne ai ba wuya suke ba sai dai kice nagartarsu ce za ta yi wuya baki san wanda zai zo gareki ba akwai masuyi don Allah akwai kuma masu zuwa da wata manufa ta daban...".
Tayi shiru alamun maganar da take bata karasa ta ba numfashi ta ja kafun ta dubi Mariya tana kamo hannunta ta danke cikin nata.
"Mariya dama akwai maganar da nake so muyi dake don Allah amma ina so ki dube ni da idon basira kiyi mani kyankyawar fahimta don Allah ba a son raina zaki ji komai ba amma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads