Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 227252 words

Chapter 16 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1377

Ads at the middle of Article

cikin kujerar da ya cusa kansa ya saki igiyar shisha tayi kasa hannayensa duk biyu ya cusa cikin cikakkinyar suman kansa yana cakuɗawa gami da yatsine fuska kamar zai fashe da kuka a hankali ya fara taka kafafuwansa yana yawatawa cikin dakin idanuwansa a rintse sosai kafin ya sake buɗe su ya sauke kan Mu'iz wanda shi ma idanuwansa na kansa.
Ba wanda ya sake kokarta cewa komai cikin su tsayin lokaci mai nisa iyakar nazarin Huzaif ya kasa samun abin da zai ce da Mu'iz wanda shi yake damunsa haka shima Mu'iz din yayi shiru ne domin jin abin da yake dawainiya da abokin nasa amma da alamun bashi da niyyar furta ko da kalma daya ce.
*****
"Sosai da sosai zan yi kewarki nan da yan kwanaki Mariya".
Dr.Karami ya fadi hankalinsa da idanuwansa na kan Mu'azzam dake hannunsa yana yi masa wasa shi kuwa sai bangale baki yake yi.
Wani iri bugu Mariya taji kirjinta yayi wanda hakan ya haifar da tsayuwar abin da take yi sosai taji numfashinta yana sama da kasa kamar zai fice daga jikinta bakinta ta dan buɗe kadan daga sunkuyen da take domin samun daidaituwar numfashi ji take kamar numfashin da take shaƙa ta hanci yayi kadan gareta a hankali take juya fida din Mu'azzam da take wankewa cikin ruwan dake girke gabanta. A hankali kalaman Dr.Karami taji suna haifar mata da wani irin yanayi gami da narkar mata da duk wani kuzari nata sosai ta fara jin wani gumi na keto mata daga cikin hanyoyin gashin dake jikin ta laɓɓanta ta tura cikin bakinta tana cizawa kadan-kadan jin furucin take kamar cikin duniyar mafarkinta jin su take kamar ba a zahiri ba ciza laɓɓanta da tayi hakan ya tabbatar mata da eh gaskiya ce tabbacciya.
"Ba ki so ko?".
Ya fadi jin shirun nata ya yi yawa kallonta yake yi da duk kan idanunsa yana ganin yanayin da ta shiga ya tabbatar masa da haka din.
A dan razane ta dago kai ta dube shi kafin ta mai da kanta kasa tana yawata hannayenta cikin ruwan dake gabanta a hankali take girgiza kai tana motsa laɓɓanta alamun tana son cewa wani abu amma ta kasa shima ya lura da hakan.
"kawai shikenan ma tun da ba kya son tafiya sai ki zauna ke ma ki zama ma'aikaciyar asibiti ".
Yanayin yarda yake ajje furucinsa fuskarsa dauke da murmushi zai tabbatar da tsokanar da yake yi mata.
A karo na biyu ta sake dago kanta a dan razane kafun ta ware idanuwanta kadan akansa .
"Uhmm...".
Sai kuma tayi shiru tana juya harshenta cikin bakinta idanuwanta akan Mu'azzam wanda shi izuwa wannan lokaci ita yake kallo.
"ko Bakya so?".
Ya sake fadi da muryarsa dauke da dariya sosai yana kallon yanayin da take shiga wanda hakan ba karamin burgeshi yake yi ba sosai ya fahimci sanyin hali da rashin son magana irin nata sosai yake ganin magana tana yi mata matukar wuya in suna tare amma kuma yanayin ta da yanayin da take furta komai nata ba karamin tafiya yake da zuciyarsa ba ga ta dai ba wata babbar mace bane amma yanayin da da salon da take komai sai ka rantse wata mace ce babba wacce ta baiwa shekaru talatin baya.
"Na fa gaji Malama in kin gama ki zo ki amshi Mu'azzam tun da na lura zaman nan din bai ishe ki ba".
Ya fadi cikin murya mai sauti yana mai kau da kai fuskarsa dauke da dariya amma yanayin muryar da yayi amfani da ita sai ka rantse bacin rai ne a cikinta.
Cikin hanzari ta mike jikinta har rawa yake yi zuciyarta na tsalle fuskarta lokaci guda tayi rauni sosai alamun ba ta so yanayin da ya nuna ba cizon laɓɓanta tayi muryarta a raunane.
"Uhmm yi hakuri".
Ta fadi dakyar tana mika hannu za ta amshi Mu'azzam gocewa yayi kafin ya juya ya kalle ta sosai yana murmushi.
"Kin fiye tsoro da yawa ban san dalili ba kina da shariya Mariya mai yasa ko ni ne...".
ware idanun da tayi akan sa ya sanya shi sauri yin shiru yana dariya kafin ya juya ya fara tafiya ba tare da ya bata Mu'azzam din ba.
Sosai take ware idanuwanta akansa tana kallon yarda yake ajje takunsa a duk takunsa daya tana jin yarda zuciyarta da ruhi gami da gangar jiki ke amsawa kamar ita yake takawa da takalmar kafafuwansa sau ciki masu kalar ruwan kasa sai daukar idanu sukeyi da yanayin kyalli kirar kamfanin Gucci rintse idanu tayi sosai gabadaya taji tana juyawa kamar wacce aka saka a majanjawa take walagigituwa da ita ta dauki dakiku masu yawa a wajan kafun ta ware idanuwanta sosai wanda har zafi-zafi taji su na yi mata gyaɗa kai tayi gami da zubda ruwan da ta gama wankin fidar Mu'azzam ta dauki karikitan ta fara takun kan kafafuwanta a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
Sosai tayi nisa cikin tunani kawai ajje kafafuwan ta take a duk in da taji sun sauka duk taku daya sai taji numfashin ta na janta tana kwato shi.
"Mariya".
Cak! ta tsaya kanta a kasa sosai taji muryar ta dakar mata kwanya gami da kara kawo mata wani abu na daban kuma zuciyarta lokaci guda ta buga.
Kwanaki kusan uku kenan rabon da taji ko da muryarsa ta rasa dalili a zuciyarta tajima tana nazari anya ba laifi tayi masa ba ya dauke kafafuwansa yake guje mata ya daina son saka ta a idanuwansa sosai take lura da wasu halaye nashi na daban masu tsauri wanda a iya zaman ta dashi ta fuskanci haka mutum ne shi mai saurin fushi ga zuciya abu kadan ne yake sanya shi janye jiki ga mutum.
Takun da taji nasa yana tunkaro ta hakan ya kara sautin bugun zuciyarta ta shiga kokawa da numfashin ta ta san shi mai alheri ne kuma ta gani sai dai ta rasa mai yasa cikin lokaci kalilan take jin wani irin abu game dashi sam bata so su kasance tare domin kuwa halayensa da yake amfani dasu sam ba su dace da ita ba sosai take jin ba dadi bata son mutum mai tsauri da sauri fushi akan abun da bai taka kara ya karya ba.
Ita dai a iyakar tsawon lokacin da suka dauka cikin asibitin nan daidai da rana daya ba ta tsammanin tayi abun da zai bata masa rai sai dai bata sani ba ko cikin rashin sani tayi masa ba daidai ba wanda sam bai kamata ace ya kama ta da laifi akan hakan ba.
"Mariya".
Ta ji ya sake kira wannan kiran sai dai ya bambanta dana farko domin taji muryarsa da wani irin sauti wanda ta kasa tattance shi.
A hankali ta fara motsa laɓɓanta tana kokawa da numfashinta da taji yana sarkewa.
"Na'am".
Sosai taji hucin numfashinsa a kusa da ita a dan tsorace ta ware idanuwanta da suke kasa kafafuwansa ta hanga sanye da takalma ash-colour sau ciki sai faman daukar idanu suke yi a hankali ta fara dauko idanunta tana bin sa da kallo tun daga kasa jikinsa sanye yake da suit Blue mai turuwa sai farar rigar dake ta ciki nektayal dinsa kalar ash-colour yarda takalminsa suke hannunsa duk biyu sanye suke cikin ajihun wandonsa saitin idanunsa ta sauke nata ganin sosai taji numfashin ta yayi sama da kasa ya koma daidai amma duk da hakan bai daina tsalle tsalle ba wani abu ne mai girman gaske take hangowa cikin idanunsa wanda tajima tana ganin hakan amma na yau ya bambanta sosai da sauran lokacin can baya kamar wacce ya rikewa idanu sam ta kasa daina kallonsa idanuwansa sarke da juna duk da nashi na cikin farin glass wanda ya kara ƙawata fuskar tashi duk da dai akwai rashin fara'a a cikinta.
"Uhmm...Dr.Aqeel...".
Hannu ya daga mata ya wanzar da wani murmushi mai zafi a zuciyar mai yinsa girgiza kai yake yi kamar wanda aka fada masa wata magana da bai yarda da ita ba har zuciyarsa.
"Bana bukatar jin komai Mariya na lura kin yasar dani daga duniyar ki sam-sam kin daina tuna ni a rayuwarki sosai ki ka zare ni daga cikin duniyar rayuwarki ban san dalili ba..Uhmm...ni dai na san ban yi laifi ba amma kuma naga an dauki fushi dani Me Ya Sa?".
Sosai take jin maganganunsa na haifar mata da wani irin yanayi mai wanzar da daci a zuciya sosai take jin haushin kalaman nashi ya fiye son kan sa da yawa ta lura da haka domin duk cikin kalamansa ba abin da ke yawarawa sai son kai ba ta san dalilin da yasa Dr.Aqeel yake yi mata haka ba bata san me yasa yake kokarin canza matsayin da ta samar masa a filin zuciyarta ba sosai take ganin girmansa domin kuwa bata ta ba manta alherin da ya saka mata a duniyar rayuwarta ba ita da makusantarta ba zata taba manta yarda ya dauke su ya kai su wani matsayi ba a lokacin da wasu suke kin su suke jifansu da wulakantaccen kallo sun mai da su marasa yanci da martaba a idanunsu shi ne yayi kokarin ganin an daina kallon su haka ta sanadinsa komai ya wanzu amma ba ta san me yasa yake kokarin canza komai nasa ba cikin kankanin lokaci wanda ko da wasa ba ta taba zaton hakan ba a filin zuciyarta.
Nisawa tayi gami da sanya hannunta guda tana dafe goshinta sosai take jin kanta na sarawa da duk wasu kalamai nashi sosai take jin rashin jindadin haka bata so zuciyarta ta canza mata matsayin Dr.Aqeel sosai da sosai take kallonsa a matsayin da take kallon Dr.Karami...
Rintse idanu tayi wani abu mai girma taji ya danne mata zuciya yana kokarin karyata zancen da take yi a yanzu.
Yaa Allah!
Ta fadi a can kasan makoshinta wanda take jin sa yana wani irin bauri-bauri.
"Ban san a wani matsayi kika ajje ni ba sosai da sosai nake ganin kin canza matsayin da nake dashi a idanunki da zuciyarki a can baya Me Ya Sa?".
Ya sake fadi cikin wata irin murya wacce ta sanya Mariya saurin girgiza kai sosai take hango rashin adalci a furucinsa sosai take hango rashin dacewar hukuncin da yake yankewa a kanta sam! hakan bai dace ba ya kamata ace ya yi mata duba natsanake kuma ya ajje komai nasa na tunani a MIZANIN HANKALI kafun ya yanke mata hukunci sosai take ganin tsaurin hukuncin nasa wanda ta tabbata bai dace da ita ba.
Gyaɗa kai ta cigaba da yi tana tura laɓɓanta duk biyun cikin bakin ta.
"Dr.Aqeel bana zaton abin da kake fadi haka yake, bana zaton akwai adalci a wannan hukuncin da kake yankewa akaina. Ya kamata ace kayi nazarin komai sosai kake da matsayi na musamman a zuciyata ba zan manta alheri ba domin kuwa in har na mance alheri hakika na zama BUTULU wanda ba zan so haka ba".
Yanayin da take furta duk kalma daya a furucinta tana faman rintse ido zai tabbatar maka da sosai take jin wani abu mai girma a zuciyarta wanda ba komai ya haifar da haka ba sai yarda lokaci guda take kallon mutumin da bata yi zato ba zai sauya daga yarda ta sansa a can baya.
"Yaa Rabb!".
Abin da ya fadi kenan yana mai ware idanuwansa akanta sosai yake kallon yarda laɓɓanta ke motsawa kalamai masu taushi suna fesowa daga bakinta yana kallon yarda take cijewa da raunin da yake kawo mata hari amma sai tayi amfani da jarumar zuciyarta wajan fadi masa abin da take ganin shi ne ya dace sosai da sosai.
Gyaɗa kai yake yi yana faman yawatawa idanunwa a fuskarta dake fuskartarsa amma idanuwanta a dan kulle kadai wanda zara-zaran gashin idanunwan nata ya hana ya gane yanayin da kwayar idanuwan nata suke.
Shirun taji yayi yawa har kafafuwanta na kokarin kasa daukar gangar jikinta a hankali ta dago idanuwanta ta sauke su fes akansa batare da ko ɗar! ba yanayin kallon da ta gani yanayi mata ya kara rura wutar bugun zuciyarta amma taki bari hakan yayi tasiri a zahirance cikin karfin hali ta fara motsa laɓɓanta.
"Ban san abin da yasa kake kokarin daura min laifin da ban san dashi ba. Ban san abin da yasa kake kokarin canza komai ba. Kai kan ka kasani dole na damu da kai amma kuma kai na lura gabadaya ka sauya daga in da na san ka ban san dalili ba...Uhmm in laifi nayi maka kayi hakuri".
Ta karashe fuskartar da wani murmushi wanda ita a karan kanta ba ta san yarda akayi ya samu gurbin zama a fuskar ta ta ba.
Ta fara gajiya da tsayuwar da take yi ta lura sam! shi gajiya bata fara rauni a kafafuwansa ba a hankali ta fara taku akan kafafuwanta da take jin su kamar na roba ne suke kokarin narkewa amma karfin zuciyar da tayi amfani dashi ya hana hakan tabbatuwa.
"Zuciyata...".
Muryar Dr.Aqeel taji ta saki ihu da fadin haka wanda hakan ba karamin sakata cikin wani yanayi yayi ba matuka!
Cak! Ta tsaya da takun da take yi lokaci guda taji wani irin abu mai kama da ruwa yana bin sassan jikinta yana haifar mata da wata irin kasala mai kokarin zubda ita kasa a hankali taja jiki ta isa kofar dakin da suke ta dafa ta sosai take jin duniyarta na juyawa da sauri-sauri kamar zata watsar da ita wani waje mai nisan gaske.
Nisawa yayi yana kallon irin halin da ta shiga duk da jarumtar da ta sakawa kanta amma hakan bai hana wanzar da halin da ta faɗa ba nisawa yayi gami da cigaba da furucin nasa.
"Sosai take tausayin ki sosai take son ta ga kina cikin farinciki mai armashi...".
Nisawa yayi wanda hakan ya sanya Mariya sakin Gwauron numfashi ta ciza laɓɓanta.
"Nasan da haka da dadewa shiyasa na baka matsayi mai girma a zuciyata kamar yarda kake fadi mani matsayina a gareka".
Ta fadi tana mai yawatawa da hannunta saman kirjinta da take jin yana bugu kadan-kadan.
Da sauri ta ja kafafuwanta ta fada cikin dakin bayan ta sakar masa wani yaƙe wanda take zaton wai murmushi ne tayi masa wanda ta karyata hakan.
Sosai ya shiga gyada kai yana bin kofar da kallon kafun ya daga hannayensa duk biyun ya dafe kan sa da su yana mai faman juya kwayar idanunsa gami da ciza laɓɓansa.
Bai san abin da yake kokarin faruwa dashi ba. Bai san mai yake koƙarin saka shi cikin wani hali ba sosai yake ji a ransa akwai abin da ke shirin faruwa dashi a zuciyarsa zuciyarsa ta jima tana sanar dashi amma ya kasa gasgata haka ya dauki hakan a matsayin hauka irin ta zuciya mai kwashe kwashe bai san mai yasa yarinyar nan tunaninta yake wahalar masa da zuciya ba sosai yake kokarin yakice komai amma hakan ya gagara ganin haka yake a matsayin wauta na zuciya sosai yake ganin rashin hankalinta sosai yake son kin amsa komai da take yi domin kuwa rashin dacewar haka ya ke gani a filin rayuwar duniyarsa.
Ya kaucewa ganinta ko zai samu sassaci akan komai ya gujewa haduwarsu domin ko zuciyarsa zata daina yi masa wannan labarin kanzon kurege da kullum take masa ya daina wanzuwa in da take ne a tunaninsa haduwarsu ne ke haifar da haka ashe ba hakan bane domin kuwa rashin haduwarsu hakan ya kara rura wutar abin da zuciyarsa take kokawar kawo masa filin rayuwarsa wanda sam ya ki amincewa da haka wanda ita kuma zuciyarsa ta hakikanace abin da take sanar dashi dole ya yarda dashi domin kuwa shi kadaine zai sassauta masa komai na filin zuciyar tasa dama filin rayuwarsa gabadaya...
Girgiza kai yake yina faman karyata zuciyarsa a hankali ya fara jan kafafuwansa da yake jin sun masa nauyi sosai, yana barin wajan domin ya lura zuciyarsa so take ta haukata shi da abin da yake zaton ba zai taba tabbatuwa ba har gaban abada...
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.


*Ita gobarar zuciya ruwa ba zai kashe ba, so ne ginshikin halinta. ba kowa ke sani ba*
--ISA AYAGI😘


BABI NA GOMA SHA BAKWAI.
Abu mai girma taji ya zo mata wuya ya tsaya cak! Numfashi ma da kyar ta ke jansa don ji take kamar zata shiɗe a hankali ta kai hannayenta duk biyun ta dafe kanta da take ji yana kokarin tawatsewa sosai take jin kirjinta na buga a duk sakan sai take hango tashin hankalin da ta gan shi a ciki sosai take hango yanayin fuskarsa mai dauke da kayan damuwa masu girma sosai.
Sosai take jin wani abu mai kalar tausayi yana saukar mata a wani sashi na zuciya yana haifar mata da wani yanayi mai sanya kasala da sanya wani wani ciwo mai girma.
Ba ta san ya zata yi ba, ba ta san me take ji game dashi ba, ba ta san mai zuciyarta ke kokarin yi gareta ba, ba ta san mai yasa tunanin wannan mutumin yake kokarin samun waje a filin zuciyarta ba, ba ta san mai yasa komai ke kokarin wargaje mata da tunaninsa sa ba ta tsane shi bana ta son ko ganin fuskarsa a filin rayuwar duniyarta sosai take jin ɗaci da bauri a zuciyarta duk lokacin da ko sunansa taji sai taji kamar ta kurma ihu amma a halin yanzu wani irin yanayi take ji game dashi sosai KUDIRI da tayi akansa a zuciyarta taji yana kokarin rushewa sosai taji bangarori na sashin zuciyarta sun kasu kashi biyu suna faman tamka muhawara wanda hakan ba karamin sanya ta tashin hankali yayi ba wanda ita kanta ba ta san mai ya dace tayi ba, ba ta san mai ya dace tayi akan wannan lamarin na zuciya ba.
A hankali take sauke hannayenta daga kanta idanuwanta take rintsewa tana buɗewa a hankali gani take yi komai da yake faruwa da ita a yau kamar mafarki ne ba gaskiya ba za ta so ace a cikin barci ne komai ke faru da ita za ta so ace ba a zahiri bane za ta so ace kamar tatsuniyar kanzon kurege ne wannan lamarin.
Sosai take jin wani sashi na filin zuciyarta na halittar wani abu mai girma wanda yake kara tsuke mata da zuciya a duk sakan sosai take jin jikinta na samun wasu abubuwa da su ka danganci zuciyarta sosai take jin duk wani sashi na jikin ta na

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads