Showing 144001 words to 147000 words out of 227252 words
Chapter 49 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
ta fice daga cikin dakin cike da tashin hankali mai tsananin girma da kokarin yayyaga zuciya da jiki baki daya kafafuwan kawai take dorawa a duk in da taji sun sauka har ta isa cikin falon ba kowa hakan ya sanyata ficewa da sauri hannayenta saman kirjinta idanuwanta sai lumshewa suke yi a hankali kamar wacce ke jin matsanancin barci haka ta isa bakin Get ko maigadi batayi wa magana ba ta buɗe kofar ta fice cikin hanzari hanya ta dauka sosai tana tafiya idanuwanta da wasu zafafan hawaye da suke ambaliya so take yi ta karya abin da kunnuwanta suka jiye mata so take yi ta karyata zuwanta gidan su Baseera a zahiran ce so take yi ta karyata kanta da kan ta ba taji wannan furucin ba so take yi ace ma a tashi duniyar baki daya ba tare da tabbatuwar wannan lamarin ba baza ta iya dauka ba zuciyarta baza ta iya daukar wannan lamarin ba ina! ba zata iya ba so take yi a tashi duniya so take yi a ce tashin alkiyama ne so take yi komai ya zama tarihi kamar ba ayi shi ba.
Wasu hawaye masu kokarin dauke fatar fuska suka sake balle mata zuciyarta take ji na kara kamawa da wuta ji take yi kamar narkewa take yi ji take yi kamar ba ita bace ji take yi kamar ba a halicce ta ba a filin duniyar nan.
Sam bata lura ta kai bakin titi ba har ta hau tsakiyarsa ihun mutane da Horn din motoci ya fargar da ita cikin razana zare idanu tayi waje ganin irin Go-Slow din da ta hada mutane wasu na ganin kamar bata da hankali wasu kam danna mata ashar kawai suke yi gaɓadaya ta firgice ta rasa ina zatayi hayaniyar mutane ya kara razana mata kwakwalwa hannu ta daura akai tana kokarin kurma ihu taji an ja hannunta anyi gefe da ita runtse idanu tayi jin wani irin Shock da ya ansa duk kan sassan jikinta da sauri ta buɗe idanuwanta buɗe baki tayi tana kokarin kurma ihu ganin wanda ke rike da ita da sauri ya sanya dan yatsarsa akan laɓɓansa fuskarsa ba wasa alamun tayi shiru tsit tayi amma har lokacin fuskarta da tashin hankali jikinta sai k'yarma yake yi fizge hannunta tayi tana faman ja da baya shi kuwa bin ta yake yi da kallo cikin tsananin mamaki da tu'ajibi hannayensa harɗe a kirjinsa ganin dai tana kokarin komawa kan titin da sauri ya fizgota ya ja ta kamar zata kifa can inda yayi parking din motarsa ya isa ya buɗe gidan gaba ya bata umarnin shiga amma taki sai faman tirjewa take yi tana faman wurga masa mugun kallo take yi kamar idanuwanta za su fado kasa.
Shi kan sa sai da ya ji gabansa ya fadi da kallon da Mariya take yi masa kallon da ya tabbatar akwai abin da yasa take yi masa shi kallo ne na tuhuma kallo ne kuma na ka yaudare ni kallo na kayi mani ba daidai ba.
"Please Mariya shiga daga ciki mana...".
Fizge kanta tayi tana kokarin raɓashi ta wuce batare da ta shiga motar ba amma ganin irin tsayuwar da yayi babu wasa ga wani girma taga yayi mata da kwarjini wani irin bugu taji gabanta yayi lokacin da taga rinannun idanuwansa ta kalle shi kallon da taga yana jifanta dashi da yanayin da taga kwayar idanuwansa na canzawa gabadaya ya firgita ta da sauri tayi kasa da kai.
"Muje nace".
Ya fadi da wata murya wacce ba wasa a cikinta dubansa ta sake yi cikin nuna son yin gardama amma yarda taga ya tsare gida sosai ya sanya jikinta mutuwa murus ta tokare bakin kofar ita bata shiga ba ita kuma ba ta wuce ba.
"Yaa Allah! Mariya kina da matsala sosai a rayuwarki kin fiye taurin kai".
Ya fadi yana dafe kansa da wani yanayi na damuwa kafun ya sake dubanta wacce ita ma a lokacin ta dago kanta ta watsa masa kallo.
"Nifa ba zan shiga ba kawai ka rabu dani kayi tafiyarka ba abin da ya dame ka dani ba abin da ya dame ka da yanayin da nake ciki don haka Leavea Alone Please".
Da mamaki yake dubanta jin maganar da take fadi wanda suka kusan tarwatsa masa kai amma sai ya maze cikin tsare gida sosai ya nuna rashin wasa.
"Kisan Allah ki shiga motar nan tun kafin raina ya baci don na lura sai na nuna miki kala irin taki sannan zamu zauna lafiya dake ban san abin da yake hawa miki kai ba ban san mai yasa gabadaya kike kokarin sanya kan ki cikin matsala har haka b...".
"Wannan ba damuwarka bace kawai ka rabu dani nayi tafiya...".
Ai ba ta kai ga dire zancenta ta ji ta saman set din motar baje numfashin da take ji na sauka akan fuskarta ne ya sanyata saurin dubansa kallonsa tayi shima ita yake kallo da matsanancin bacin rai sai faman huci yake yi tana jin yarda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri sosai take kallonsa ta kasa dauke idon ta kamar yarda shi yake kallonta da wani yanayi wanda ya shiga haifar mata da kasala mai tsanani gabadaya taji duk wani tashin hankali da take ji da bacin rai game dashi yana kaucewa a hankali wasu kibiyoyi take hangowa suna fitowa daga cikin idanuwansa suna sauka ana ta sosai taken jin zuciyarta na buɗewa da wani lamari mai giraman gaske kallon Dr.Karami take yi kamar bashi ba kallonsa take yi a wani mutum mai kwarjini da haiba gami da cikar zati wani kallo take jifansa dashi kamar tun da take bata taba ganin mai kyau da k'yan kallo kamar sa ba.
Hure mata idanu da yayi ne ya dawo da ita hayyacinta ba tare da yace da ita komai ba ya juya dayan barin na zaman direba ya shiga yayi wa motar ki har zuwa lokacin fuskar tashi ba alamun wasa sai ma kara tsare gida da yake yi ita kuwa gabadaya ta gama narkewa sai faman juyi take yi ta kasa zama sosai a kujerar da take duk yana kallon yanayin ta har ya yiwa motar Key ya cillata saman titi yana mai kara sautin wakar 'BECAUSE OF YOU' ta Amanda Mena dake tashi a cikin motar...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘😘
[9/3, 7:45 PM] DEENY MINNA🙋♂: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ARBA'IN.
Sosai take kai kawo cikin dakin gabadaya ta kasa zaune ta kasa tsaye tunda Dr.Karami ya zo ya ajje ta a kofar gida ya juya ya tafi ba tare da ya dubeta ba balle yace da ita k'ala hakan ba karamin taba mata zuciya yayi ba duk da tana jin wani iri a game dashi na bacin rai duk da ta san dai fushin da take yi dashi ba ta san ya yake ba amma ta tabbata halin ko in kula da ya nuna mata a yau yayi matukar sanyata cikin wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske sosai take jin zuciyarta da ruhinta suna faman kai kawo dauke da lamari mai matukar girma na tashin hankali.
Hannayenta ta daura bisa goshinta tana dafewa gabadaya take jin duniyar na sauyawa a gareta gabadaya take jin komai na kara cakuɗe mata sosai take jin lamarin da Baseera ta sanar mata ya samu gurbi mai girma a sassa na zuciyarta wanda sam ba kwanciyar hankali a cikin sa.
Numfashi take ja a hankali kafun ta ja jiki ta zauna bakin katifarta idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce aka zubawa barkono.
Bata san me zata yi ba, bata san mai ya dace tayi ba, ta tabbata lamarin nan zai iya narkar mata da zuciya har ma da gangar jiki sosai ta kasa gasgata abin da take ji a zuciyarta sosai take karyata kanta wanda bata san mai yasa haka ba ta tabbata zuwa yanzu ya kamata ta yarda da komai ta anshi komai a yarda ya zo sai dai kuma hanzarin da tayi ba gudu bane domin kuwa tana kallo kwaɗo yana shirin yi mata kafa kafar da take zaton in har yayi mata ita to komai ma ya rigaya ya gama faruwa.
Mikewa tayi cikin rashin kuzari tana faman sakin huci mai zafi da take jin sa tun daga kasar zuciyarta yake busowa bakin kofa ta tokare Umma da take kallo dake zaune tana gyarawa Mu'azzam riga gefe guda ta zauna tana mai duban su amma a badinance zuciyar ta can wani waje ta cilla ta mai nisan gaske tana gayyato abubuwa masu yawa tana ajje mata a filin zuciyar tata.
Umma ta lura da ita amma bata nuna ta ganta ba sosai take jin tausayin 'yarta ta a zuciyarta sosai yanayin da take ciki yake taɓa mata zuciya amma ta rasa ya za tayi ta rasa wani irin hali Mariya ta daukarwa kanta wanda ba a iya gane me ke faruwa da ita ba nisawa tayi bayan ta saki Mu'azzam yayi hanyar waje domin yin wasa ta dubi dakin su Goggo Marka kafun ta juya da hankalinta sosai kan Mariya da tayi tagumi da hannu daya idanuwanta akan Umma wanda sam ba ita kuma hankalin ta yake kai ba.
"Mariya".
Umma ta fadi murya a kasa cike da natsuwa da nuna rashin wasa kafun ta nisa ba tare da Mariya ta ansata ba.
"Ban san ya zan dubi lamarin ki ba, ban san a wani mizani zan ajje komai naki ba, amma sosai zuciyata ta cilla wani bigire mai girma akan yanayin ki. Kin boye abin da yake damunki kina kiɗin ki kina rawar ki ke da zuciyarki a tunanin ki hakan shine daidai ko?".
Girgiza kai tayi kafin ta nuna da hannu a lokacin Mariya ta dago idanuwanta ta na sauke su akan Umma kafin daga bisa ta kau da su.
"Ban san mai ya canza miki halin ki ba, ban san mai ya sauya miki rayuwa ba, nidai na san ba haka kike ba, ni dai na san ba wannan halin kika ta so dashi ba, amma lokaci guda kin sauya komai na ki ya canza kamar ba Mariya ba. Zuciyarki...ina Zargin Zuciyarki da kuma abin da ke cikinta don na tabbata akwai abin da ya shigar miki zuciya ya canza miki komai na ki na tabbatar da hakan a raina, amma ki kasa faɗi mani a matsayina na uwa gareki baki da wata shaƙiƙiya wacce ta dace ki kai wa kukan ki da neman mafita kamar ni baki da kowa ba ki da wanda zaki kai wa kukan ki kamar ni amma Mariya kin yi watsi da wannan damar wanda ita kadai ce hanya mafi dacewa dake a filin duniyarki".
Nisawa tayi kafin ta dubi in da take jin motsi a bayan ta Hafsat ce tsaye ta tokare bakin kofa ta zuba masu idanu kafin ta kau da kai gefe guda ita Umma nuna wa tayi kamar bata ganta ba Mariya dake zaune itama sun ga juna a tsakaninsu su zubdawa junansu kallo raini kafin Mariya ta kau da kai tana mai kokarin mikewa kan kafafuwanta.
Bata hanata b domin ta sani ganin Hafsat ne ya sakata mikewa ta shiga daki ita ma mikewa tayi ta bi bayanta.
Zuciyarta taji tana sanar da ita da ta fadi abin da ke cinta a rai amma tsoro da yarda Umma zata dauki lamarin ya hanata motsawa sai gyaɗa kai take yi kamar wata kadangaruwa Umma na binta da kallo.
"Ba zan takura miki ba domin bana son nima a takura min bana son takura ga kowa domin takurawa tana iya sawa kiyi mani karya ki fada min abin da bashi ne ba ni kuma ba zan so hakan ba na barki har zuwa lokacin da kikayi ra'ayi don kan ki".
"Ehem...Umma...".
Da sauri ta daga mata hannu ganin yarda ta fara kalato furucin da zatayi kamar wanda akayi wa dole ganin yanayin da Umma tayi ya sanya ta tsuke bakinta waje daya idanuwanta su tara kwalla kadan.
******
Kallonta yake yi da wani irin yanayi mai haifar masa da wani lamari mai girman gaske tun daga tushen zuciyarsa da ruhi yake jin yanayin gangar jikinsa da jijiyoyin jikinsa gami da ɓargo suna ansar wani sako mai girman gaske.
A hankali idanuwansa suka shiga lumshewa kamar wanda barci yaci karfinsa kafin ya sake buɗe su sosai akanta kafin ya kau da kai yana jan numfashi yana haɗiyeshi da kyar.
"Mariya...".
Kau da kai tayi daga kallon da take masa tun dazu mai cike da tuhuma da zargi kafin lokaci guda ta galla masa harara wacce ta sanya shi shanye abin da yayi niyar fadi.
Jikinta sosai ya ansa da yanayin muryar da yayi amfani da ita wajan ambaton ta amma bata bari hakan yayi tasiri a zahirin ta ba.
Juya tayi da zubar kowa gida zuciyarta da bugawa da yanayi na fargabar abin da zai je ya dawo ta san bata yiwa kanta adalci ba ita akaran kanta ta san haka amma bata san mai yasa komai take kasa saita shi ba ita da zuciyarta. Zuciyarta sosai take kara buɗewa da lamarin amma ita taki ba da kai bori ya hau numfashi take ja tana jin yarda kamshin turaren jikinsa ke bula ko wani sashi da lungu na cikin hancin ta yana haurawa cikinta yana hautsina mata kwanya da guntun tunanin da take ta kokawa dashi tun dazu.
Bata san shi ne ba da ba abin da zai sata fitowa har ta dubeshi har yayi kokarin kara rikita mata lissafi duk da tana kaunar sanyashi a idaniyarta amma kuma kuncin da take ji game dashi yafi garwashin wuta a gareta zafi.
" A tunani na ban yin tsammani na kai har haka a wajan laifi ba a wajan ki ko da yake ban yi mamaki ba tun da duniyarki ta kubuce ta daina tunanin wani mai kama dani komai sunana".
Numfashi taja gami da tsayawa daga takunta da take yi wanda take jin jikinta kamar yana narkewa yana watsewa a kasa juyawa tayi idanuwanta na sauka a nasa da wani irin yanayi wanda lokaci guda ya haifarwa da zuciyoyi biyu abu iri guda har ya kusan tona sirrin da yake a ko wani dayan su.
"kana kokarin daura min laifin da ban san dashi ba kana kokarin hukuntani akan abin da ban sani ba...".
"Ba magana bace wannan ya kamata ki daina yin ta kin ji ko!".
Ya fadi muryarsa da sauti a ciki yana takowa gareta sosai numfashin su yake dukan juna kafin Mariya ta kau da kai cikin kasalallan yanayi.
"Akan mi zaka ce ba magana bace kai ne dai kake raina ta amma ni abin da na fadi shine daidai!".
Ita ma ta fadi da zafi a muryarta kamar zata shako wuyarsa wani irin zafi da raɗaɗi take jin zuciyarta na haifarwa mai girman gaske. da mamaki yake dubanta jin yarda take masa magana murmushi yayi mai ciwo kafun ya kara kusanto ta.
"Mariya".
Ya kirata bata ansa shi ba illa dubansa da ta sake yi tana jan numfashi.
"Kace ban cancanta da na tsaya ina kula samari ba har su zama abokan rigima ta yanzu kai mai ya kawo ka nan har ka tsaya a nan kake magana dani har kake daga min murya kenan kai ma kana sahunsu?".
Runtse idanu yayi kafun ya buɗe su lokaci guda sun kaɗa sun yayi jajir.
Bai san ta wacce hanyar zai dubi Mariya ba bai san mai ya dace yayi mata ba da zata gane in da ya sanya gabansa take ganewa taki fahimtarshi shi kuma ya rasa gane ta ina zai bi domin fahimtar da ita komai bai koma ya sanar da ita bai san ta yaya zata fuskance shi ba yana tsoron abin da zai je ya dawo.
Takun da suka ji na takalmi ne duk ya dawo dasu daga dogon nazarin da su ka fada su duka dubanta suke yi da mamaki Baseera ce tsaye hannayenta sarke a juna fuskarta sanye da bakin glass No respect wanda ya hana tonuwar asirin yanayin da kwayar idanuwanta suke ciki amma daka kalleta zaka hango wani kwantaccen murmushi mai girman gaske a fuskarta ta a hankali ta shiga takowa har ta iso in da suke tsaye sai da tayi musu kallon tsaf! kafin tayi kasa da glass din tana duban Mariya wacce ita ma ita take kallon da wani yanayi wanda ba yabo ba fallasa.
Murmushi tayi mata kafun ta dubi Dr.Karami da yayi fakare yana kallonta kashe masa ido daya tayi wanda komai da tayi din akan idon Mariya ne hakan ya sanya ta juyar da idanunta jin yarda kirjinta ke ansa sautin bugu kamar zuciyarta zata faso kirji ta yo waje wani tukuki bakin ciki da takaici taji yana taso mata yana turkewa a makoshi numfashi ma daƙyar take jan sa idanuwanta lokaci guda sun kaɗa sun yayi jajir.
Motsa baki ta shiga yi kamar zata yi magana amma ina! ta kasa zuciyarta da take jin tayi nauyi kamar zata tarwatse ta hanata aiwatar da komai takun da taga Baseera nayi zuwa ga Dr.Karami yakara hargitse mata tunani da sauri ta fara ja da baya tana kokarin kwasa da gudu kuka ne take jin yana zuwa mata mai karfin gaske wanda ta tabbata in har ta cigaba da tsayuwa a wajan ba kuka kadai ne zata samu zarafin yi ba har zubewa akasa sumamiya sai tayi.
"Mariya".
Baseera tayi saurin kiranta ganin tana kokarin barin wajan ta juya tana takowa inda ta tsaya cak! fuskarta da murmushi kafaɗarta ta dafa kafun ta kure da idanu sosai.
"Uhmmm...".
Hannu ta daga mata a zafafe tana turen hannunta da ta daura mata kan kafada.
"Bana muraɗin jin komai daga gareki kin ji ko don Allah ki bar naji da abin dake damuna a zuciyata bana son karin wani Tension din a wannan lokaci...".
"ki daina fadin haka domin duk maganar da kikeyi karya ce kawai zalla a cikinta kuma bata kai zuciyarki ba ni nasan haka idanuwanki gashi nan kuma suna karya taki da kan su don haka Tell me the trut I don like joking Mariya in kuma ba zaki iya fadi ba ni zan fadi a yanzu nan ba sai kin bata min lokaci kin bata naki ba".
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi idanuwanta na kawo kwalla ji take yi kamar ta kurma ihu don takaici komai na Baseera haushi yake bata ta tsaneta tsana mai tsanani bata taba zaton zata tsani wani bawa a