Showing 117001 words to 120000 words out of 227252 words
Chapter 40 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
dubanta idanuwanta da ta kafe sa da su sosai yake hango wani irin yanayi da yake narkar masa da duk wani sashi na jikinsa bai san abin da ya hadashi da Hafsat ba bai san ya akayi ta shigo filin duniyarsa ba bai san ya aka yi har yake tsaye suna magana ba sosai zuciyarsa ta buga a duk lokacin da ya ga Hafsat a gabansa komai da yake kwanyarsa da zuciyarsa canzawa yake yi sosai yake jin filin duniyarsa na canzawa game da ita.
"Kayi magana mana Huzaif".
Ta fadi cikin salon kashe murya sai faman juya idanuwanta take yi a nasa.
"Uhmm ba komai wai dama cewa nayi Mariya ta dawo?".
Ya fadi cikin yanayi na ɗarɗar kamar wanda yayi laifi ake tuhumarsa.
Ware idanu tayi jin abinda ya fadi ta shiga tsuke fuska kamar biri da lemon tsami.
"Me kake nufi Huzaif me ya kawo Mariya a maganar mu meye kuma hadin ka da ita na dauko ba wata 'ya mace a filin rayuwar ka a yanzu kamar ni wacece Mariya kuma?".
Ta fadi cikin sauti kamar zata kai masa bugu kafun lokaci daya ta rikice da zubda hawaye tana shassheka.
Hakan ba karamin firgita Huzaif yayi ba da sauri ya shiga ba ta hakuri kamar zai yi mata sujjada jikinsa ba abin da yake sai ɓari da kakarwa a hankali ya zaro Hankicif a aljihunsa ya kai fuskarsa cikin rawar jiki yana dauke hawayen.
A daidai lokacin kuma Mai Napep yayi Parking Mariya da take ciki tana kokarin fitowa ta hango su wani irin bugu taji gabanta yayi kanta ya shiga juyawa kamar zata zube a kasa da sauri ta rike karfen kofar Napep din tana ambatar.
"Yaa Allah".
Komawa tayi ta zauna idanuwanta a runtse tana jin yarda zuciyarta ke yayyakewa da tashin hankali mai girman gaske ba ta san lamarin su ya kai har haka ba bata san cin amanar har ya kai haka ba ta lura So suke yi su ga bayanta so suke yi su kashe ta da ranta ba ta san sai yaushe zata daina ganin wannan bakin lamarin ba ba ta san sai yaushe duniyarta zata canza yanayi.
Sosai take cikin tashin hankali mai girma gaske mai kokarin raba ta da duk wani farin cikin da yayi saura a filin duniyar...ko da yake ba ma zata ce akwai farinciki a cikin duniyarta ba a yanzu domin ya jima da gushewa shekaru uku ana abu daya zuciyarta kullum cikin ciwo take sosai take hango yarda ALKALAMIN ƘADDARA yake juya duk wata rayuwarta a duk sakan ba ta tsammanin a cikin shekaru uku da suka bada baya daidai da rana daya ta samu farinciki bata tunanin a cikin shekaru uku da suka shuɗe daidai da minti daya tayi dariya wai ta farinciki ba ta san wacce irin rayuwa bace take yi a duniyar nan komai da komai nata na daban ne bata tsammanin a duniyar nan akwai mai rashin jindadi da kwanciyar hankali kamarta.
Numfashi ta ja mai karfi zuciyarta na dauko mata jarumta tana aza mata ta gaji ba zata iya cigaba da zubda hawaye akan mutanan da ba su san tana yi ba ba za ta kashe rayuwarta akan mutanan da ba su san darajar da kimarta ba ta daina damun kan ta ta daina sanya kaita a damuwa alkawari tayi daga yau ba wani daga cikin su da zai sake dasa mata ciwo a zuciya buɗe idanuwanta tayi a hankali ta saka hannayenta ta shafe kwallar da suka cicciko mata fitowa tayi daga cikin Napep ta dube mai Napep wanda yayi kuri yana kallonta ganin ta fito ya buɗe bakin sannan cikin yanayi na tausayawa don ya tabbata akwai abin da yake dawainiya da duniyar rayuwarta.
"Sai Hakuri yan mata lamarin duniya ne sai an din ga kai zuciya nesa".
Gyaɗa kai kawai tayi tana mai sakin yaƙe wanda take jin sa har cikin zuciyarta da sauri ta janyo hijabin jikinta ya dan rufe mata fuska cikin yanayi na hanzari ta doshi kofar gidan domin bata so ma su ganta balle wani cikinsu ya raina mata hankali...
"Mariya!".
Kamar daga sama ta jiyo sautin muryarsa ya ambace ta cak! Ta ji ta tsaya da tafiyar da take yi sosai ta ji sautin amon muryarsa ya ansa kuwwa a kunnuwanta da ma kwanyarta bakidaya a hankali ta dago kanta jin sautin takunsa yana karaso wa in da take kallo daya tayi masa da kai jin yarda zuciyarta ta harba da wani irin yanayi mai ciwo sosai.
"Uhmm...".
Da sauri ta dago kai gami da daga masa hannu lokaci guda idanuwanta suka kara rinewa fuskarta kamar hadari da yake kokarin zubda ruwa.
"Huzaif!".
Ta ambata cikin muryar gargadi kafun tayi masa wani irin duba wanda shi akaran kansa sai da yaji a jikinsa.
"kana tunanin a filin duniyar na akwai KALMA DAYA da zaka fadi na tsaya na saurareka akanta kana tunanin akwai lokacin da zan iya batawa akan ka".
Wani murmushi ta saki kafun ta juya ta dubi Hafsat dake tsaye jikin motarsa sai fama cika take yi tana batsewa.
"Bana tunanin akwai wani abu yayi saura a tsakanina da kai na fadi maka ba sau daya ba ba sau biyu bs hanyarmu ta rabu ba zamu sake haduwa ba har abada ya kama ta ka san da haka amma na lura so kake yi ka ture lamari kaki dauƙarsa da muhimmanci ka sani ba yarda za ayi kana tare da yar uwata sannan kace kana tare dani ta ya ya wannan lamarin zai kasance ina so ka sani ni da kai ba wata ALAƘA da za ta sake shiga tsakaninmu don haka na rokake da ka fice mani a rayuwa Huzaif na rokeka daga yau...".
Shiru tayi jin yarda zuciyarta tayi wani irin nauyi mai girman gaske kasa tayi da kanta tana jin yarda idanuwanta ke raɗaɗi da kokarin zubda kwalla da sauri ta bar wajan tana karasawa cikin gida.
Bin ta yayi da sauri yana kiranta amma ina sai ma ta kwasa da gudu ta fada cikin gidan cak! Ya tsaya bakin soron yana mai da numfashi da yake ji yana kai kawo kamar zai rabu da gangar jikinsa hannayensa duk biyu ya dafe kan sa da su ji yake yi duniyar gabadaya na juya masa da wani irin ta shin hankali mai girman gaske bai san abin da yasa Mariya take gudunsa ba bai san abin da yayi mata ba baya iya tuna komai komai yake ji yana sauya a filin duniyarsa daga kansa yayi ya dubi Hafsat da tayi masa kuri da idanu sai faman kumbure kumbure take yi cikin hanzari ta baro jikin motar ta tun karoshi kamar wacce zata kifa.
"Huzaif ni zaka ci wa zarafi ni zaka wulakanta a gaban waccen karamar yar duniyar ni zaka ketawa mutunci a gabanta to billahillazi baka isa ba zaka san ni kayi wa haka ka saurare ni".
Ta karashe tana mai jan tsaki kamar zata tsinke Harshenta.
"Hafsat mana! ki daina fadin haka ni ban ci miki mutunci ba sannan ban ci zarafin ki ba".
Wani kallo ta yi masa tana mai sake narkar da muryar cikin yanayi kamar mai son sakin kuka.
"Haba mana Huzaif ya za ace a gaban makiyiya ta zaka tsaya kana kulata ai sai ta rainani gaskiya ni karka sake in kuma ba haka komai zai iya faruwa".
"Naji shikenan ba za a kuma ba".
ko dubansa ba ta sake yi ba domin kuwa taji haushi matuka da yanayin da ta ga ya tsaya da Mariya a hankali ta ja kafafuwanta ta shige cikin gida shi kuwa Huzaif nan ta barshi tallaɓe da kai yana jin duniyar na juya masa ji yake komai na kwance masa a hankali ya ja jiki ya isa wajan motarsa ya shiga sai da ya shafe lokaci kafun yayi mata Key ya bar unguwar.
*******
Kallon da Umma ta watsa mata ne ya sanyata saurin yin kasa da kai tana kokarin shigewa daki ta dakatar da ita.
"Zo nan Mariya".
Duban Umma tayi ganin ba wasa a fuskarta ya sanyata dawowa da baya ta samu waje ta zauna.
"Baki ji ko Mariya, baki dai ji ko ni ban isa dake ba, ban isa nace miki bana son abu ba ko, ke kenan kullum abu daya kamar cin kwan makauniya dube ki don Allah kullum jiya i yau kowa na auki da kuzari amma ban dake kamar wata kazar mayu ban san ya zan yi dake ba ban san mai zan miki ba kuma ni dai a gaskiya na gaji da wannan lamarin naki na lura dai so kike yi ki kashe kan ki sannan hankalin zai kwanta in ba haka ba ta ya ya mutum sam shi a rayuwarsa ba zai dauki ƙaddara da jarabawa ba".
Yanayin da taji sautin Muryar Umma ya tabbatar mata yau dai ta kaita karshe duk hakurin Umma yau tayi mata fada tabbas abin ya kai intaha runtse idanuwanta tayi ta sani Umma ta dade cikin damuwa da ta ta damuwar ta sani sosai lamarin ta yake damun Umma sosai take gani a yanayinta tsayin lokacin da ta dauka cikin wannan halin ita ma haka ne ya kasance wasu hawaye taji sun zo mata.
"In kika sake kikayi mani kuka a nan wallahi sai na kwada miki Mariya don naga lamarin naki ba sauki sai abu ya ki ci yaki cinyewa haba mana maza ki tashi ki bani waje nikam tun kafin ki kai ni Bango ance mutum ya girma amma sam rayuwarsa ba ta sauya ba".
Da sauri ta dago idanuwanta da suka cika da kwalla ta sanya hannu ta dauke su.
"Uhmm Umma fa ba wani abu bane ba abin da kike zargi bane fa kawai bana jin dadin jiki nane kisan yau muka kammala komai na makaranta daga yaushi kenan".
Kuri tayi mata da idanu tana karantar yanayin ta ta san Mariya ba za tayi mata karya ba kuma in har bata manta ba kwanakin baya ta sanar da ita sun kusan kammala karatun nasu gyaɗa kai tayi tana mai sakin fuska sosai.
"Yo ai ke ce Mariya wani lokacin da kayan haushi kike wallahi sam ba a gane miki yarda kika san sahun keke ai shikenan Allah ya taimaka yasa anyi a sa'a kin ga yanzu dai burin naki ya fara ciki sai ki zage kuma ki cigaba da kokari kamar yarda kika saba".
Gyada kai tayi tana mai kalato murmushi tana daura a fuska mikewa tayi.
"Yawwa na mance dazu ma Yayan naki ya kira ni a waya".
Ras! Gaban ta ya fadk da sauri ta juyo ta dubi Umma cikin yanayi na tsoro.
"ya tambaya ina kike nace kina makarantar wai shi ne yace har yanzu baki kammala ba ne ya dauko tun wacce shekarar ai zaki gama".
Yaƙe tayi.
"Ke ma dai Umma tun yaushe nace miki mun gama kawai mun dau shekara daya mun kara domin koyan sana'o'i hannu ke fa nan na fada miki an buɗe makarantar koyan sana'a na fada miki kuma kika aminci amma yanzu kina nuna ba ki sani ba".
Dafe kai Umma tayi kafun ta dubi Mariya.
"Wai ni kam anya ban da cutar mantuwa kuwa Mariya haka fa mukayi da Yayan naki shekaran jiya wallahi yace an kawo sako nace a,a bayan kuma an kawo din".
Murmushi Mariya tayi.
"Akwai abin da kika sakawa ranki Umma".
"Ai komai ya faru kece sila mariya lamarin naki ne sosai ya firgita min rayuwa komai nawa sai a hankali...Allah dai ya kyauta kawai".
"Ameen Yaa Rabbi".
Mariya ta ansa tana mai shigewa daki zuciyarta da wani irin yanayi mai girman gaske ba abun da ke ansa kuwwa sai maganar Umma nacewa Dr.Karami ya kira wai har ya tambayeta abin ya daure mata kai in har bata manta ba yau kusan shekaru hudu kenan rabonta dashi duk zuwan da yake ba sa haduwa kullum cikin wasan buya suke a tsakanin su ta rasa dalilin da yasa haka ta rasa mai ya ke damun Dr.Karami komai nashi ya sauya tunda ya dauki kafarsa ya bar kasar nan shikenan kuma ya shafe babin ta da farko ta dauka laifinta amma daga baya kuma zuciyarta ta jima tana sanar da ita cewa kawai dai baya bukatar ta ne cikin duniyarsa shiyasa itama ta ajjeshi gefe kamar yarda Baseera ta bata shawara akan ta ajje lamarinsa gefe in ba haka ba damuwa dashi da take yi sosai zai taba mata rayuwa ba kadan ba.
A yanzu a daidai wannan lokacin komai take ji yana dawowa sabo fil! Ji take yi kamar yanzu komai ke faruwa ji take yi kamar yanzu ne suka hadu da Dr.Karami ji take yi kamar yanzu shakuwarsu ta wanzu a duniyar nan sosai take jin zuciyarta nayi mata tuni akan komai wani irin yanayi take jin jikin ta ya shiga komai take ji na canzawa numfashin ta take ji yana sauka a duk wata dakika da lamarin Dr.Karami sosai take jin bugun zuciyarta na sauyawa da duk wani lamarin Dr.Karami sosai take jin idanuwanta na bukatar ganinsa a daidai wannan lokacin sosai take jin zuciyarta da kwanyarta suna son tunaninsa.
Runtse idanuwanta tayi da karfin gaske tana mai kai hannunta saitin da take zaton nan zuciyarta take ajje a kirji sosai take jin bugunta na sauya komai ma da komai ji take yi ya sauya a lokaci guda.
Numfashi take ja a hankali har ta isa bakin katifarta ta baje tana mai duban saman dakin nasu zuciyarta sai zarya take yi da duk wani lamari da tunani na Dr.Karami lokaci guda taji wani murmshi ya subuce mata tuna rayuwarta tayi ita dashi a Asibiti...
"wato sabo 'yar taki tayi kwantai ba mai so an gama yawan ta zubar shine yanzu take bibiyar samarin Hafsi ko to wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa ko da bakar jaɓa take aiki ba ta isa ba tayi kadan mu zuba ni da ita shege ka fasa gata ga Hafsi nan ta cigaba da bibiyar samarin nata".
Kamar daga sama Mariya taji saukar kalaman a firgice ta mike tayo waje Goggo Marka ta hango tsaye ita da Hafsat sai faman cika take yi tana bacewa duban Umma tayi dake zaune tayi banza da su kamar ba da ita take yi ba.
Wani kallo Goggo Marka tayi mata kafun ta nuna ta da tsaya.
"ke dan hular ubanki shine saurayin na Hafsi kike kokarin kwacewa saboda ke kin yi kwantar ko to wallahi baki isa ba tun wuri ki fita daga harkar Hafsi in kuma ba haka na rantse miki da Allah sai kin sha mamaki na".
Fakare Mariya tayi mamaki ya cikata ga mari ga ansar jaka duk ba su isa ba ita batayi magana ba sai su ne za su zo suna gaya mata magana har sun manta waye Huzaif a wajanta har suke kokarin ci mata mutunci wani murmushi mai ciwo ya kufce mata ta dubi Hafsat da Goggo kafun da girgiza kai domin ita dai abin ta rasa ma gane kan sa wai kiri-kiri sai faman IHU BAYAN HARI suke yi gabadaya sun mance baya sun mance waye ita har da suke duban idanunta suna fadi mata haka ji tayi kamar ta buɗe baki ta mai da musu da martani amma ina ba zata iya ba domin sa tasan ran Umma in yayi dubu sai ya baci shirun shine mafi alheri a gareta da sauri ta juya ta koma cikin daki zuciyarta a cunkushe ji take yi kamar ta daura hannu akai ta kurma ihu don bakin ciki da takaici.
"FASHIN SAURAYI?".
Ta ambata cikin wani irin yanayi mai haifar mata da wani lamari mai girman gaske mamaki abin yake bata wani lokacin kuma ya bata bakin ciki da takaici bata ganin laifin kowa sai Huzaif tayi mamaki da canzawarsa tayi mamaki da lokaci guda soyayyar da yake nuna mata ta gani kashe ni ta sauya gabadaya kamar bai taba furta mata KALMAR SO ba a duniyar nan komai take gani kamar a Mafarki.
Nisawa tayi tana tuno lokacin baya yarda ya haukace akanta yana nuna yana son ta amma yanzu kamar bashi ba ta ga laifin Hafsi ba domin sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka kuma tayi alkawari ita da Huzaif har abada zata nuna masa ta fi karfin wulakanci da cin zarafi za ta nuna masa ita mace ce mai daraja da kima wacce ta san kanta ba irin matan da suke ɓarin jiki bane wajan kai kawo wajan saurayi ta daina damuwa dashi ta daina damuwa da bakin cikin da suke tura mata shi da Hafsat.
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA HUDU.
A firgice ya farka daga barcin da yake yi mai dauke da wani RIKITACCEN AL'AMARI wanda ya kusan sanya zuciyarsa da kwanyarsa daina aiki na wucin gadi sosai ya firgita da mafarkin barcin da yake jin sa kamar a zahiran ce ne ya faru ba wai a badinance ba.
Da sauri ya zuro santala santalar kafafuwansa da hutu ya gama yi musu ƙawa a hankali ya sanya takalmarsa da suke bakin gadon ajje masu matukar kyau da burgewa kallo daya zakayi musu ka gane na zallar fata ce.
Mikewa yayi kan kafafuwansa jikinsa sanye da Boxer wanda ya kawo masa har gwuiwa sai singilet mai kalar ash-colour wanda tayi matukar kama jikinsa ta bayyanar da cikar halittarsa ta mazantaka yana da damatsa da budadden kirji sosai mai dauke da kwantaciyar suma mai santsi kugunsa kuwa ba shi da fadi sosai ya dan tsuke kadan.
A hankali ya dauko jallabiyarsa mai ruwan jinin kare dake rataye ya sanyawa jikinsa wanda hakan ya kara haskakashi matuka Toilet ya nufa ya wanke baki sannan ya watsa ruwa sosai kafin ya fito ya shirya cikin Suit baka sosai ya gyara sajensa gami da tararren gashin kansa gyararre in ka gani sai ka rantse Shampoo ya saka masa amma ko kadan haka sufarsa take baka sidik sai sheki da take yi sosai ya ke kula da ita wajan gyara kwantattacen sajensa shima haka fuskarsa ta fito fes da ita manyan idanuwansa da dogon hanci gami da bakinsan dan madaidaici sun yi matukar tasira wajan kara ƙawata fuskar tashi.
Cikin hanzari ya gama shirye shiryensa kafin ya dauke Berifcase dinsa da sauran karikitan sa ya fice daga cikin dakin ya kulle can harabar gidan ya nufa in da motarsa take park-space tun kafin ya isa gareta ya danna mata Remove ta saki wani dan sauti tare