Header Ads
Showing 114001 words to 117000 words out of 227252 words

Chapter 39 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1395

Ads at the middle of Article

a ranta lokaci yayi sosai take jin komai na dawo mata kamar yarda ya faru a shekarun bayan komai zuwa mata yake yi komai kallon sa take yi a yanzu yake faruwa ba TUNA BAYA bane runtse idanuwanta tayi zuciyarta da wani raɗaɗi da zugi ga wani bugu da take yi kamar zata faso kirji ta yo waje.
Zubewa tayi kan kujera ta mai jan numfashi wasu kwalla suka cika mata idanuwa hannun bibbiyu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa.
"Yaa Allah".
Ta furta cikin wani irin yanayi matsananci duniyar take ji tayi mata zafi da kunci komai take ji babu dadi a hankali ta kuma mikewa hannayenta goye a bayanta ta cigaba da safa da marwa so take yi ta tunano abin da ya dace tayi so take yi zuciyarta ta kawo mata wata satar ansa da za tayi mata amfani so take yi kwanyarta ta binciko mata wani abu mai girman gaske da ya dace ace shi ya kamata tayi.
Motsin kofar da taji ne ya sanyata saurin juyawa Areefa ce ta gani tana kokarin shigowa cak! ta tsayar da idanuwanta akan ta sosai take jin komai na sake dawowa mata kamar yanzu ya faru wani tunani taji ya zo mata a bazata runtse idanu tayi tana mai sake buɗe su akan Areefa gabatan taji yayi wani irin dokawa da abu mai girma.
'Anya kuwa?'
Ta fadi a can cikin ranta tana mai girgiza kai a daidai lokacin Areefa ta iso gareta tana mai dubanta.
"Ya dai Maama ko jikin ne?".
Ta fadi tana mai yawatawa da idanuwanta akanta.
Girgiza ka tayi alamun babu komai hannunta ta riko tana mai sarkewa cikin nata da wani irin yanayi mai girman gaske da sauri Areefa ta bude idanuwanta tana kallon cikin yanayi na alamun son sanin wani abu murmushi tayi mata kafun ta jata suka zauna waje daya suna fuskartar juna zuciyar Areefa sai kai kawo take yi so take yi ta san abin da ke faruwa domin ta hakiƙance yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ya tabbatar mata akwai matsala bata saba ganinta cikin wannan yanayin ba duk da boyewar da take yi na abin dake damunta amma ita a jikinta taji kamar akwai wani abu mara dadi dake shirin faruwa.
A hankali ta shiga motsa laɓɓanta idanuwanta akan Hajiya Layla da sai faman yak'e take yi kamar wacce akayi wa dole zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi na tashin hankali tsoro take ji tsoro mai girman gaske tana son tayi wa Areefa magana amma zuciyarta na gargadinta akan haka bata san ya zata dauki lamarin ba bata san ya zata fuskata ba tsoronta daya lamari ya maimaita kansa bata son haka bata son abin da zai sake dawowa a matsayin WAIWAYE sosai ta sani Areefa zata tashi hankalinta ita kuwa a filin duniyar nan abin da ta tsana kuma take gudunsa kamar shiga damuwar Areefa bata so ace ta sanadinta wani abu ya same ta so take yi ace har karshen rayuwarta ta dauwamar da Areefa cikin farinciki da muradan jin dadi amma Ta ya ya hakan zata kasance?.
'Bata sani ba'.
Zuciyarta ta fadi duban Areefa tayi akaro na ba a dadi wacce gabadaya ta gama shiga yanayi lokaci guda jikinta yayi sanyi sosai.
"Maama wai meke faruwa ne don Allah sosai naji gabana na faduwa fa don Allah fada min".
Ta fadi tana mai kara matse hannunta a na Hajiya Layla.
"Ban san ya zance miki ba, ban san ta ya ya zan fuskance ki ba, sosai nake jin rashin jindadi sosai zuciyata ke bugawa ina tsoron abin da zai je ya dawo, ba na son ace ta sanadina kin sake fadawa halin damuwa bana so nayi miki Waiwaye...".
"Maama!!!".
Areefa ta fadi da sauti mai girma a muryarta kafun ta sake motsa laɓɓanta kamar zata yi kuka.
"Don Allah mene ne? Ki fada min zuciyata sosai take bugawa Allah taba ki ji".
Ta karashe tana mai dago hannun Hajiya Layla tana kaiwa saitin inda take zaton zuciya na ajje.
"Areefa wani abu nake so na tambaye ki guda daya kwal! Amma kuma ban san yarda zaki dauki lamarin ba ban san da wacce fuska zaki anshe ni ba...".
"Kawai ki fadi koma mene ne zan dauke shi a yarda ya zo mani nayi miki alkawari".
Ta fadi da murmushi na kara karfin gwuiwa ga Hajiya Layla don ta lura da ita sosai yanayin ta ya sauya kamar da tsoro akan abin da take so tambayar ta akai.
"Zaki iya tuna ranar da muka dauko ki daga gidan marayu?".
Yanayin da take furta kalmomin da yarda bugun zuciyarta ke sauyawa ya sanya Areefa kureta da idanuwa kanta taji lokaci guda ya ansa wata kara mai girman gaske kirjinta yayi wani irin dokawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito a hankali ta ji duniyar na juya mata idanuwanta lokaci guda suka shiga lumshewa da wani irin tashin hankali mai girma wani CIWON RAI mai tsanani zafi da zugi taji ya ta so mata komai taji yana dawo mata kamar yanzu yake faruwa gabadaya numfashin ta ya dauke lokaci guda ta zube jikin Hajiya Layla ganin haka da ita kuma tayi ya sanyata kwala kara mai sautin sai da falon ya ansa gabadaya cikin tsananin firgici da razana tashiga girgizata tana ambatar sunanta amma ina Areefa tayi nisa cikin wata duniya mai cike da kwazazzaben tashin hankali da sanya zuciya ciwo.
Da gudu ta mike ta isa wajan Firjin dake girke cikin falon ta buɗe gorar ruwan EVA ta sungoma tana mai balle murfin tana isowa gareta ta tuntule mata akai aiko wani numfashi mai karfi ta ja har tana sarkewa da sauri Hajiya Layla ta durkushe idanuwanta na zubda hawaye masu zafi jikin ta ba abin da yake yi sai rawa laɓɓanta na kaɗawa.
"kiyi Hakuri Areefa ban so haka ba, abin da nake gudu kenan shiyasa na ki tambayar ki ban son abin da zai jefa rayuwarki a wani yanayi ban son na sake fama miki ciwon da ya jima a zuciyarki...".
Cikin wani irin yanayi Areefa ta daga mata hannu.
"Bakomai Maama wallahi ba komai karki damu tambaye ni abin da kike bukata na san ba wai zaki tambayeni bane don cutar dani".
Ta fadi da hawaye a idanuwanta zuciyarta na wani irin motsawa da ciwo mai tsananin gaske laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa komai taji ya sauya mata jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa.
Duban Hajiya Layla tayi wacce gabadaya ta gama rikicewa da tashin hankali ganin halin da Areefa ta shiga jikinta sai faman kaɗawa yake yi ta janyota jiki tana rungumewa.
"Kiyi Hakuri Areefa...".
"Ya isa haka Maama don Allah".
Shiru tayi jin abin da ta fadi dubanta take yi cikin wani irin yanayi na tausayawa zuciyarta na kara narkewa da kauna da tausayin Areefa.
"Shikenan na bari".
Hajiya Layla ta fadi da murmushin yake a fuskarta Kafun ta riko hannun Areefa sosai tana kwanta da kanta a kafadarta.
"Abu daya nake so ki fama min in har zaki iya tunawa Areefa kuma in har ba za ki kuma shiga yanayin nan da kika shiga yanzu ba kiyi man alkawari".
Gyaɗa kai tayi da murmushi a fuskarta tana mai kara kwantar da kanta a kafadar Hajiya Layla.
"NAYI ALKAWARI".
Shiru ne ya ratsa falon na yan mintina ba wanda ya sake magana a cikin su sai ajiyar zuciya kawai a hankali Hajiya Layla take shafar kan Areefa tana son yin magana amma zuciyarta na tsoratar da ita akan yin maganar domin bata san abin da zai faruwa ba sai dai kuma bata da zaɓi dole sai tayi tambayar domin ita kadai ce hanyar da take hango mafita a gareta da ita kan ta Areefa din.
"Bayan fita ta daga cikin Motar Dr.Erena shin gidan sa kuka tafi ko kun biya wani waje daban ne?".
Tsoro sosai ya bayyana a fuskarta lokacin da take maganar tana jin yarda jikin Areefa ya dauki rawa lokaci guda tana kankameta ajikinta sosai taji wani irin yanayi wanda bata san ya zata misaltashi ba game da Areefa lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi da tashin hankali.
"Areefa".
Ta kirata muryarta na rawa.
"Na'am Maama".
Ta ansa ta da son nuna ba komai amma yarda take ji a zuciyarta da ruhin ta kamar an dauko KASKO WUTA an juye mata haka take jin kirjin ta na wani azabar zafi runtse idanu tayi kafun ta motsa baki.
"Ba gidansa muka je ba wani daji muka nausa sosai ya kaini wani gida wanda shi kadai ne a wannan lokacin...".
Da hanzari Hajiya Layla ta dagata tana dubanta bakinta har rawa yake yi.
"Kenan ba gidan sa ya kai ki ba ko to gidan da kike ce kun je din waye a cikinsa?".
Runtse idanu ta sake yi idanuwanta na kawo kwalla.
"Haba mana Areefa karki yi kuka kin yi mani alkawari".
Hannu ta saka ta dauke hawayenta kafun ta shiga bata labrin abin da ya faru shekaru masu dama da suka shuɗe.
Kuka sosai Hajiya Layla take yi zuciyarta da ruhinta na zafi sosai ta rungumi Areefa ita ma da take kuka a hankali ta mike fuskata da murmushi mai tsananin ciwo.
"Shikenan Areefa ina so duk runtsi duk wuya karki sake daidai da rana daya Dr.Erena ya san nan gidan sannan ko yace yana so ya gana da iyayenki kice masa zakiyi shawara ki zo ki same ni don nasan nan da dan lokaci ya bukaci son ganin iyayenki domin neman auren ki auren da nake so ayi sa...".
"Maama".
"Shiru Areefa kiyi abin da nace kawai".
Daga nan ba wanda ya sake magana a cikin su Hajiya Layla sai safa da marwa take yi a tsakar dakin ita kuwa Areefa kwance tayi luf! tana jin yarda tsana da kiyayyar Dr.Erena ke kara samun masauki a filin zuciyarta KUDIRI tayi tare da Alkawari duk runtse sai taga bayan sa a filin duniyar nan..


*_KAMALA MINNA_*😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA BIYU


Zuciyarta take ji tana yi mata nauyi, da abu mai girman gaske. komai take ji yana zama kamar tarihi gani take yi kamar ba ta kwashe wadannan shekarun da suka bawa rayuwarta baya ba wai ita ce yau ta gama makaranta wai ita ce yau ake bikin kammala makarantar su, a matakin sakandire. gani komai take yi kamar ba gaske ba, gani takeyi tamkar mafarki ne take yin sa wanda a ko wani lokaci zata iya farkawa.
A hankali ta kai yan yatsunan Hannunta na dama zuwa bakinta tana cizawa, kamar zata zare su daga jikinta komai take ji yana tabbatuwa, komai take ji yana gasgatuwa, komai take ji yana zama zahiri ba badini ba. runtse idanuwanta tayi tana mai buɗewa ta shiga yawatawa da idanunta zuwa harabar makarantar dalibai birjin kowa sai murna yake yi da farinciki fuskokin su dauke da tsananin farin ciki mara gushewa.
'Yaa Allah'.
Ta furta cikin wani irin yanayi mai girman gaske zuciyarta take ji tana buɗewa sosai tana haifar mata da wani lamari mai girman gaske kwanyarta take ji ta shiga shawagi da ita cikin wata irin duniya na farinciki sosai take jin duk wata gaɓa ta jikinta tana ansa sakon da zuciya da ruhi suke miko musu na farin cikin da take ciki a yau din nan.
"Wayyo Allah na. Mariya gabadaya na gaji wallahi".
Muryar Baseera ce ta doki dodon kunnuwanta da sauri ta dago kai tana dubanta tana mai sakin yak'e gami da gyaɗa ma kai.
Kuri Baseera tayi mata da idanu kamar mai son gano wani abu daban a hankali ta shiga janye hannayenta data dafa kafadun Mariya idanuwan na kara yo waje da yanayi na damuwa ba bacin rai.
"Meye haka Mariya, me fuskarki ke kokarin nuna min ba dai zaki ce mani ba kya farin ciki da wannan ranar ba Yaa Allah!".
Ta karashe tana mai dafe kanta da take ji yana sara mata da wani irin yanayi mai girma da tashin hankali a cikinsa runtse idanu tayi kafun ta buɗe su kan Mariya da tayi shiru idanuwanta da wani yanayi na damuwa a ciki.
"Ban san me zan ce miki ba kuma Mariya, Shekaru fa tafiya suke yi kamar gudun ruwa a kogi ya kamata ace wannan shekarun da kika shafe kin canza komai a duniyarki, ki duba ki gani kin canza tsarin ki ya canza ke kan ki kin san komai game dake ya sauya sai dai abu daya...".
Tayi shiru tana jan numfashi mai dauke da damuwa mai girman gaske kau da kai tayi daga barin kallon Mariya ta juya kan dalibai dake ta fara'a da farin ciki.
"...Zuciyarki Mariya taki sauyawa, komai ya ki canzawa a cikinta kin ki baiwa rayuwarki damar kawo maki farin ciki a filin duniyarki Ban san mai ya sa ba?".
Sake kusantowa tayi gareta tana dafa kafadarta.
"ki na tunanin rayuwa zata yuwu a hakan kina tunanin wanan tsarin da ki daukar wa kan ki zai haifar miki da ɗa mai ido a rayuwarki ina! haka ba zai taba yuwuwa ba ya kamata ace kin sauya Mariya ki sauya rayuwarki!!!".
Ta karashe cikin murya mai amo da sauti tana rike kafadun ta tana girgizawa har sai da mafiya yawan dalibai suka dube su sosai.
Runtse idanu Mariya tayi tana mai toshe kunnuwanta da hannu bibbiyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir jikinta lokaci guda ya shiga rawa kamar wanda ruwa yayi mata duka sosai da sosai a hankali take duban Baseera da idanunta bakin ta na faman rawa kafin ta ciji laɓɓanta tana jin yarda zuciyarta ke matsewa a waje daya da girman damuwar da take ciki.
"Ban san ya zan yi ba Baseera, komai da komai duniyar ma gabadaya ta canza ban san haka duniyar take ba da ban so na shigo ta ba da na roki Allah ya barni a wata duniyar ba wannan ba zuciyarta ta gaji Baseera sosai zuciyata take zafi ban san meye maganinta ba kullum kullum komai kara rikice mani yake yi".
Ta karashe wasu zafafan hawaye na zubowa a fuskarta kafin ta sanya hannayenta ta dauke su.
"Mu tafi gida Baseera".
Mariya ta fadi tana mai shigar da hannun Baseera cikin nata tana jan ta ba tayi mata kardama ba haka tabi ta kamar rakumi da akala kawai binta take yi da idanu cikin wani irin yanayi zuciyarta sai faman dokawa take yi da lamarin Mariya bata san inda rayuwar Mariya ta dosa ba sosai komai da komai ya fita daban a rayuwarta tana matukar tausaya mata musamman yarda Kuruciyarta ta kasance da tashin hankali wanda ta rasa gane in da ya dosa a filin duniyar nan.
"Ba muyi Sallama da kowa ba Mariya hakan bai kyautu ba".
Baseera ta fadi cikin rashin abin yi tana faman jan numfashi.
Cak! ta tsaya Daga tafiyar da take yi kafun ta juyo ta dube Baseera suka fuskanci juna sosai idanuwansu na yawatawa a tsakani gyaɗa kai Mariya tayi kafun ta sake kallon filin makarantar da yarda dalibai suke kai komo.
"Ba abin da yayi saura da za mu tsaya muma kai kawo akan sa ban zan iya cigaba da zama bane na fi bukatar na je gida".
Kallon ta take yi da duk yanayin da take magana dashi da sam ba wani abun na a zo a gani murmushi take sakar mata na karfafa gwuiwa don bata so ta karyarwa da Mariya zuciya.
"Shikenan naji mu tafi gidan amma da kin bari Dadyna ya turo a dauke mu bari na kirasa".
Ta fadi tana mai zuge tsakarta domin dauko wayarta da sauri Mariya ta tare ta.
"Barshi ba sai kin kira shi ba kawai mu tafi domin a hanya zamu rabu gida zan wuce daga nan".
Ware idanu tayi kadan cike da mamaki.
"Ba zaki je gidan namu b...".
"Kawai dai zan zo amma yanzu na fi bukatar naje gida bana tattare da natsuwa a filin rayuwata".
Gyaɗa kai Baseera ta shiga yi kamar wata kadangaruwa a hankali ta fara taka kafafuwanta tana karasawa bakin titin dake kusa da Get din makarantar ta su.
Bata son ta matsawa rayuwar Mariya bata so ta fiye yi mata magama akan abin da ta san ba ranar karewarsa komai take gani a filin duniyar mariya sai kara rikicewa yake yi sosai take jin tausayinta a zuciyarta da ruhinta sosai ita a karan kanta tana jin rashin jindadi a rayuwar ta ba macen da ta dauko a matsayin yar uwa ba ƙawa ba kamar Mariya sosai take jin sashi na zuciya da gangar jikinta na sauyawa da duk wata damuwa ta Mariya.
Nisawa tayi kafun ta daga hannu tana mai tsaida mai Napep bayan ya tsaya ta kira Mariya dake can gefe guda ta zo su ka hau domin wucewa.
Ko a cikin Napep ba wanda ya yi magana kamar mutuwa ta gifta su cikin yan mintina kalilan suka isa layin su Baseera nan ta sauka ta biya mai Napep kudinsa har da na Mariya da zai kai ta gidan su.
"Mariya sai na zo ki gaida su Umma".
Gyaɗa mata kai tayi tana mai sakin yak'e nan mai Napep ya dau hanya domin isa da Mariya gida.
****
A hankali take takawa ko ina sasan jikin ta motsawa yakeyi sanye take da doguwar riga mai kalar baki da fari sa mayafin da tayafa kalar ja fuskarta da saukakkiyar kwalliya laɓɓanta sun yi jajir dalilin jan bakin da ta saka ja mai turuwa tun daga kofar gida take kallonsa da wani irin yanayi mai girman gaske tana faman sakin wani murmushi mai kayatarwa a haka har ta iso gareshi.
Jingine yake da motarsa ya harɗe hannayensa a kirjinsa idanuwansa kur! Akanta kamar ya ga sabuwar halitta a filin duniyar sa.
Sosai yaji gabansa yayi wani irin dokawa lokaci guda rintse idanuwansa yayi cikin tsananin tashin hankali mai girman gaske a hankali ya shiga buɗe su yana saukewa akan ta a daidai lokacin da ta iso gareshi cikin takun ta na jan hankali kusa dashi ta tsaya tana mai sanya hannunta guda tana dafa jikin motar sosai ta fuskance shi tana mai kaɗa idanuwanta cikin salon jan hankali.
"Uhmm Huzaif ai ban yi tunanin zaka zo ba".
Ta fadi tana mai kai hannayenta tana kara gyara zaman mayafin nata wanda a zahirin gaskiya ba wai tayi bane da sunan gyarawa a,a kawai tayi ne domin ta bayyanar da yarda rigar tayi matukar matse ta a kirji haka ya kara bayyanar da cikar kirjin nata na matashiyar budurwa mai ji da kanta.
Murmushin yake kawai yake saki kafun yaja numfashi.
"Eh wallahi amma... Nace ba...".
Sai kuma yayi shiru yana mai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads