Showing 6001 words to 9000 words out of 227252 words
Chapter 3 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
ta na ba da katin ganin likiti, ya dubeta.
"don Allah ku taimaka likita, haihuwa za tayi jini na ta zuba a jikinta".
dago kanta dake sunkuye tayi, tana dubansa cikin gilashin dake fuskarta.
"ka je ku shigo da ita, sannan kuma ku kawo katin da take zuwa awo dashi, domin ba za a taba ta ba, har sai an bada kati".
da mamaki ya shiga dubanta, ganin yarda ta nuna halin ko in kula akan lamarin. ji yayi kamar ya dauke ta da mari, amma ya kasa. da sauri ya juya zuciyarsa na zafi da radadi irin yanayin da ya ga Nurse sun nuna masa, da sauri ya isa wajan Napep, ya tarar Malam Bello, na kokarin fito da ita wacce a wannan lokaci kallo daya zaka yi mata, ka bawa zuciyarka amsa cewa ba ta da rai.
Cikin Asibitin yayi da ita tana rungume a hannunsa, mutane da yawa sun tsorota matuka da yanayin da suka ganta, suka shiga sallallami suna zaro idanu, Malam Bello, da ke rikice ya rasa ma in da zai yi da ita, sai faman zarya yake yi magana ma ta gagare shi, duk abin da yake da yawa Nurse na kallon sa, amma sai dai su ba banza ajiyarsa. ciki mutanan dake zaune a harabar asibitin wasu mata biyu suka iso gareshi,tare da taimaka masa, zuwa daya daga cikin dakin Asibitin. a daidai lokacin Nurse mai siyan da kati ta iso cikin dakin, tana duban Malam Bello. wanda gabadaya ya gama yin nisa da hayyacin sa. tambayarsa take, amma ya rasa bakin bata amsa, sai motsi yake yi da baki, daya daga cikin matan da suka taimaka masa ne ta dubi Nurse din.
"wannan ba fa shi ne mafita ba, ya kamata ko taimaka mata ki duba halin da wannan baiwar Allah take ciki, mana maganar kati duk ba shi da muhalli a halin da ake ciki, ceto ranta take bukata".
Kau da kai tayi, tana mai ya tsine fuska.
"ke ma kin san haka ba za ta taba yuwuwa ba, dole sai da katin ta na shaidar ta na zuwa ganin likita, sannan za a kula da ita".
Ta karashe maganar ta tana kokarin ficewa. da sauri dayar matar wacce da alamu haushi ya cikata, ta sha gabanta tana yi mata kallon na raina matsayin ki.
"wai ke kuwa kina da ita imani, baki san zafin da raɗaɗi bane a wajan haihuwa bane, ba ma haka ba, wannan fa yar uwarki ma cece, ya kamata ko don wannan matsayin da kuke daya ki taimaka mata".
Kallo uku ahu tayi mata, kafin ta gyara zaman gilashin fuskarta.
"karki jefe ni da wasu kalamai munana, karki ga laifi ne akan wannan lamarin, ke kanki sani, duk wata mace mai ciki in dai ta zo haihuwa sai an bukaci katin zuwa awonta, kafin a dubata...".
"wannan ba hujja mace malama".
Mai Napep ya katse mata maganar da take yi, cikin zafin rai ya dora da cewa.
"wannan maganganun da kike duk na banza wallahi, na lura ba ki da imani sam ke da wasu likitocin da kuke aiki, in har haka likitoci suke sam ba su yi ba a duniyar nan ko daya, ke ba zan musu kudin goro ba, dama komai na duniya akwai na gari akwai kuma bara gurbi, to ke ki na sahun bara gurbin wallahi".
Yanayin da yake maganar cikin zafin rai kamar zai rufeta da duka, ya fadar mata da gaba, nan ta shiga duban su daya bayan daya har takai ga Malam Bello, wanda idanuwansa gabadaya sun gama rinewa kamar wanda aka watsawa barkonon tsohuwa girgiza kai tayi gami da cewa daga dakin, adaidai lokacin Habeeba ta saki wani nishi wanda ya sanya gabadayansu suka dire akanta, numfashi take saki cikin wani irin wahalallan yanayi mai dauke da rashin hayyaci, idanuwanta a rufe amma hakan bai hana hawaye zubowa ba, Malam Bello ya isa gareta, gami da riko hannunta ya na ambatar sunanta, cikin murya mai taushi da tausayi, girgiza kai ya ga tana yi hawaye na kara balle mata, bakin sa na rawa ya shiga kokarin yin magana amma kamar wanda ka daurewa harshe maganar taki fitowa, ya shiga goge mata gumi dake ta faman tsantsafo mata a goshi. a daidai wannan lokaci wani dirkeken mutum, wanda da kallaeshi za ka gane babban likitane, yana gaba Nurse na biye dashi har ya iso inda Habeeba ke kwance, dubanta yayi sosai kafin ya komar da kallonsa izuwa wajan Malam Bello, wanda yake ta famam ajiyar zuciya.
"mai ya sa haka, mai yasa har kuka bari hakan ta kasance a gareta?".
ya fadi cikin murya mai nuna bacin rai. Girgiza kai ya shiga yi cikin rashin abin cewa, likita ya sake dubanta.
"ina katin ta wanda take zuwa ganin likita da awo dashi".
Nan ma girgiza kai yayi, alamun babu kenan.
Da sauri likitan ya dube shi cikin alamun zaro idanu waje, da madaukakin mamaki da kuma haushi.
"hakan da kuka yi sam bai da ce ba, ka ga yanzu kun haifar mata da matsala, domin duk wanda ya kalleta ya san tana cikin halin wahala, ya kamata kuke lura mace mai ciki tana bukatar taimako da kulawa da tattali, tun daga lokacin da ta samu ciki ya kamata ace tana zuwa Asibiti, a ko wani bayan sati uku tana ganin likita, hakan ne zai bata damar sanin halin da take ciki da abin dake cikin ta. kar ku ga laifin abinda wasu likitoci ke yi na rashin bada kulawa ga mai ciki, hakan na faruwa ne ta dalilin mai ciki da kum mijinta...".
"kayi hakuri likita don Allah, a bar zancen nan, ya kamata ace ku san abin yi akan wannan baiwar Allah, domin tana cikin hali mara dadi".
Daya daga cikin matan dake wajan ta fadi, cikin yanayi na rauni.
Murmushi likita yayi ,kafin ya shiga duban Habeeba, daga karshe ya umarce da su dauke ta domin zuwa dakin haihuwa, yana tsammanin haihuwar ce ta zo, cikin hanzari kuwa sukayi hakan. likitin ya kira Nurse uku, sukayi masa jagora domin kula da Habeeba, Malam Bello da sauran matan suka koma harabar Asibitin suka yi cirko-cirko, mai Napep nan yayi wa Malam Bello Sallama tare da fatan samun lafiya ga Habeeba ya tafi. ba tare da ya amshi ko sisin sa ba.
Sai da suka shafe mintina talatin, amma har zuwa lokacin ba alamun haihuwar za ta yiwu, tun likitar na tsammani har ya fara yanke tsammani. iya kokarin sa yayi amma bai kai ga ci ba, ga dai kan jariri a waje amma fitowarsa ya gagara, duk wani taimako yayi amma ina domin gabadaya jaririn ya cije ba alamun zai fito, dalilin kin buduwar kwankwason ta, yaki budewa balle jaririn ya fito, iya wahala Habeeba ta gamu da ita, shi kan sa jaririn wahala ta sheshi, ganin wanki hula na kokarin kai su dare, nan likiti ya fito ya ja hannun malam Bello, zuwa Office din sa, yayi masa bayani, ba karamar kaduwa yayi ba, nan likita yace in ya yarje ayi mata aiki, domin shine kadai mafita agareta, da ma jaririn domin kar azo ayi BIYU BABU.
Shiru yayi yana tunanin lamarin, ba wai aikin ne ba ya so ayi mata ba, a,a kudin aikin in da zai samo su, ita ce matsalar. domin kuwa a yanzu halin da ake ciki ko dubu biyu na sa takan sa ba shi da ita, balle wasu makudan kuɗaɗe da yake tsammanin za a nema a gareshi, numfashi ya ajje ya dubi likita wanda ya gama karantar halin da Malam Bello ya ke ciki.
"Likita ba wai ba zan iya sa hannu ba ne, a,a abin neman ne babu...".
Hannu likita ya daga masa, yana kokarin yin magana. kamar daga sama Nurse ta fado cikin office ta dubi likita.
"Sir ina tunani za ta iya haihuwa da kanta...".
Tun kafin ta dire, ya miki zumbur cikin hanzari, ya fice daga office din .Nurse ta biyo shi a baya tare da Malam Bello.
yana shiga dakin ya tadda sauran Nurse din akanta, yanayin da ya ganta da irin nishin da take saki ya kara sanya jin tausayinta, da sauri ya isa gareta, izuwa wannan lokacin kafaɗar jaririn ta yo waje, hakan ya tabbatar masa za ta iya haihuwar da kanta, a hankali ya fara kokarin janyo jaririn a hankali a hankali yake bi har ya zo matakin tsakiya, wato saitin cikin jaririn. a lokacin ta yi wani nishi mai dauke da wata hargitsattsiyar kara, wacce ta amsa kuwa gabadaya dakin. a sa'ilin da shi kuma jaririn ya fado duniya gabadaya. zubewa tayi daga kan gwuiwowinta numfashin ta na fita, cikin wani irin yanayi...
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
BABI NA UKU
Kuri likita yayi mata da idanu gabadaya hankalin sa da guntuwar natsuwar sa tana kan ta hannusa kuma yana mikawa nurses jaririn bayan ya yanke masa cibiya.
Abubuwa ne suka shiga yi masa dirkar mikiya a kwakwalwa zuciyarsa na ta tunano masa wasu abubuwa da baya fatan ace sun faru da wannan baiwar Allah ajiyar numfashi yayi gami da saurin duban Nurses da suma hankalinsu na kanta ganin halin da take ciki na rai kwakwai mutu kwakwai.
"maza kuje ku gyara jaririn sannan kuma ku dauko gado domin daukarta don na lura tayi matukar gajiya da galabaita".
Abin da likiti ya kokarta furtawa kenan cikin rashin tsammanin samun karfin daga laɓɓa har ya yi furuci gyaɗa kai yake yi yana gauraya kwayar idanuwansa cikin gurbin su laɓɓansa dake cikin bakin sa sai faman cizon su yake fuskarsa na kara bayyanar da rashin armashi da natsuwa.
Mikewa yayi cikin rashin kumaji duk wani azancin sa yana jin yarda yake kokarin kufce masa daurewa kawai yake yi yana yaki da batun da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ta sanar dashi ba zai so haka ba, ba ya faman haka ta kasance gyaɗa kai ya cigaba da yi kamar yana magana da wani ya ma rasa abin da ya dace yayi tunaninsa gabadaya ya wargaje sai akan abu daya wanda yake tsammmanin ba ɗa mai ido zai haifo ba.
Dawowar nurses ne ya dawo dashi daga duniyar fargaba da tsunduma ya shiga jan numfashi a hankali mai dauke da kayan tashin hankali
Ya dube su su duka yana mai kaɗa idanu yana mai yi musu nuni da ita nan suka shiga gyara mata jiki tamkar gawa haka suke sarrafa har suka kammala sannan suka daurata zaman gadon gami da gungurawa suka fice daga cikin dakin yana mai bin su da kallo numfashi ya ajje gami da jingina da jikin bango har zuwa lokacin zuciyarsa sai kokarin gasgata masa lamarin take wanda shi sam ba ya fatan hakan wuyar rigarsa ya gyara gami da jan jiki ya fice daga cikin dakin xan gefe ya hango Malam Bello tallabe da haba sai faman mazurai yake yi cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali kallo sosai likita ke bin sa da shi zuciyarsa na dauko tausayinsa tana jingina masa ta kowani bangare na sassan jikinsa sannu a hankali ya fara kokarin jan jiki ya isa gareshi amma sam bai san ya iso ba har sai da ya daf kafadarsa wata irin zabura yayi mai dauke da ajje wani gwauron numfashi idanuwansa fes kan likiti jikinsa yana rawa ya riko hannunsa.
"don Allah in har zaka yi furuci kayi wanda ba zai tafi da imanin zuciyata ba na rokeka".
yanayin da yake sakin furucin da kyar yasan ya jikin likita kara sanyi ya shiga gyada masa kai.
"ta haihu...".
shima ya fadi dakyar kamar wanda akayi wa dole idanuwansa na kan Malam Bello kamar yarda shi ma ya ke kallonsa zare hannunsa yayi saboda wani irin bugu da yaji ya kawo masa ziyara zuciya ya dubi Malam Bello.
"ina zuwa zan maka magana in an kammala gyara mata jiki sai ka zo ka ganta da baby ko".
ya karashe cikin sakin murmushin yaƙe bai jira amsawar Malam Bello ba ya ja jiki da sauri ya nufi dakin hutu da aka kai Habeeba ya tura ya shiga har yanzu dai jiya-i-yau da sauri ya isa gareta yana duban nurses da sukayi carko-carko da alamun yanayin da suka ganta ya tafi da yar guntuwar jarumtarta su hannunta ya kamo bayan ya dan rankwafa zuwa gareta hannun ya shiga juyawa yana mai kai dayan hannun nasa izuwa wuyanta yana taba alamun nemon motsin numfashi cak! ya tsaya kamar wanda aka cewa in yayi kwankwarar motsi ba zai ji sautin saukar numfashin nata ba gyada kai yake yi cikin raguwar faduwar gaba jin saitin kirjinta yana harbawa alamun da rai a jikinta har zuwa wannan lokaci ajje numfashi yayi mai karfi kafin ya miki ya shiga binciken ta sosai tsayin wani lokaci bayan ya kammala ya umurci Nurses akan su dauko masa kayan karin jini cikin sauri suka fice gami da daukowa ruwa ya fara sak mata gami da yin wasu allurai a cikin ruwan sannan ya juya inda ya juyo jaririn na kuka inda aka kwantar dashi kallonsa yayi sosai ɗa namiji ne fari tas dashi kyankyawa mai kama da uwarsa.
Barin wajan yayi, ya yi hanyar fita waje. A bakin kofa ya tadda Malam Bello tsaye ya na jiran fitowarsu, da hanzari ya isa gareshi dauke da fuskar murna sai faman tallar hakoransa yake yi kamar wanda aka baiwa sabuwar amarya amma in ka lura sosai zaka tabbatar da murmushin na yaƙe ne cikin kokarin dauko jarumta ya dorawa kansa ya isa gareshi shima da ya hango shi cikin hanzari ya baza masa idanu yana takowa a hankali kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki lura da yayi fuskar likita da murmushi sai faduwar gabarda take wa kirjinsa bugun kato ta fara saurarawa yashiga ajje numfashihar suka iso ga juna suna shakar numfashi Malam Bello ya sake ajje numfashi yana mai gyara zaman hular kansa ya shiga jiki na ɓari ya dubeshi.
"likita ka ja min rai wallahi, don Allah sanar dani halin da ake ciki, ko na samu raguwar bugun katon da zuciyata ke yi".
ya fadi yana kara kusanto shi kamar zai shige jikinsa idanuwansa fes akan sa.
zuciyar likita tayi matukar cilla cikin wani hali na ta rarrabi na rashin tabbas akan lamarin da yaji duniyar tunaninsa na shawagi dashi a ciki ya rasa mazaunan hankalisa sun ka sa zaman kalau ya tabbata zuciyarsa bata yi masa adalci ba in har ta dauko mata banzan tunanin nan wanda in har ya gasgatashi komai zai iya faruwa wani yake ya kinkimo ya daurawa fuskarsa tare da dafa kafadar Malam Bello.
"ta haihu lafiya an samu ɗa namiji ina tayaka murna...".
Sautin ihun da ya dauki cikin asibitin gabadaya shi ya daskarar da duk wani motsi na mutanan cikinsa ya tafi da furucin su likita da yayi mutuwar tsaye idanuwansa fes akan na malam Bello wanda shi ma kallo daya zakayi masa ka tabbatar zuciyarsa ta shiga halin tsoro matuka da ihun da ya karaɗe cikin asibitin da saurilikita ya juya ya yi dakin da Habeeba take ba wai don ya na da yakinin daga dakin ihun ya fito ba kawai zuciyarsa ce ta ja linzamin hankalinsa izuwa dakin ilai kuwa yana kokarin shiga suka ci karo da Nurses cikin yanayi na firgici da razana bakin ta na rawa ta shiga nuna masa cikin dakin da hannuamma sam ta kasa kokarin fadin wani abu da zai zarewa likita yarjewa kansa Habeeba ce tayi wannan ihun da hanzari ya fada cikin dakin malam Bello dake bin su a baya shima a daidai lokacin ya fado ciki.
Zaune take taɗe jikinta waje daya hannayenta cikin kunnuwanta sai faman zabga ihu take yi jikin ta na faman kyarma kamar wacce akayi wa tsinannan duka. kan ta su kayi gabadayan su malam Bello yana isa ya zauna kusa da ita yana mai kokarin janye hannayenta daga kunnuwanta yana mai dago habatar idanuwanta ya gani sun kaɗa sunyi jajir sai hawaye da suke kwaranyowa gabansa yayi mugun faduwa ganin irin halinda take ciki na rashin hayyaci juya wa yayi da sauri ya dubi likita bakin sa na rawa shima likitan idanuwansa na kanta domin abin da yake tsoro ne ya faru domin kuma ko tantama ba yayi ta samu matsala akan ta gau da kai yayi daga kallon da Malam Bello ke yi masa ya isa kusa da Habeeba ya kira sunanta amma ba ta amsa ba domin bata san ma yanayi ba sam! duban Malam Bello yayi cikin murya mai dauke da rauni.
"yi mata magana sanar da ita kai wanene".
da mamaki ya shiga duban likita jin abin da ya ce dashi gabadaya ya ji kansa na juyawa wasu lamura na tashin hankali yaji sun kawo masa hari ba shi ya mike yana nuna likita da hannu.
"ban gane zancen naka ba sam, taimaka kayi mani fashin baki, ta ya ya zaka ce na sanar da ita wanene ni, bayan nasan kuma mun san junanmu ba bakin fuskoki bane mu a tsakani don Allah likita ka fahimtar dani abin dake faruwa".
Ya karashe yana mutsuttsuka wuyar rigarsa yana mai cizon laɓɓansa ransa sai faman daci da fargaba yake yi domin yarda ya lura da canjin likita ya tabbata akwai matsala a tsakanin rayuwa matarsa kukan da jaririn ya saki ne ya sanya shi saurin juya inda ya juyo kukan da sauri ya kara kusa da gadon da jaririn yake kwance sai faman wuntsil-wuntsil yake yi da kafafuwansa hannunsa cikin bakinsa da alamu yinwa yake ji bai san halin da duniyar ta sa ta zo masa dashi ba hannu ya saka yadauki jaririn wanda yake nannaɗe ido ya zuba sa sosai yana ƙare masa kallo zuciyaraa da kasar ruhinsa sai hasaso masa abubuwa suke yi ma bambanta so da kaunar ɗan nasa yaji sun tsargar masa a jiki da jinin dake gudana ta ko ina a gareshi.
Hannu ya saka ya dauko jaririn kafin ya juya na kallon likitan.
"kace mani wani abu don Allah ko na samu saukin kunar rai da na zucci".
Idanuwa duk suka zuba masa ganin yarda yake magana cikin yanayi na wahalallan yanayi da rashin hayyaci.
Likita ya shiga gyaɗa kai kamar kadangare kafin ya nisa.
"ban san ya zan fara yi maka bayani ba amma dai zan ce maka