Showing 60001 words to 63000 words out of 227252 words
Chapter 21 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
alamun rashin son abin da Umma tace.
"kawai ki bari Yah Dr.Karami ya zo sai a fada masa ƙafarki na ciwo nasan zai baki magani ni kam ban yarda ki yi amfani da tafarnuwar nan ba tun da ba likita bane yace ki yi amfani da ita".
Murmushi tayi ta san halin Mariya sarai tun da ta warke a cutar nan in dai za tayi abu to tabbas sai taji daga bakin Dr.Karami tun da yana zuwa musu lokaci lokaci ya duba jikin Umma.
"Shikenan naji taimaka dai ki sayo mani na ajje in ya zo duk abin da ya ce dashi zan yi amfani".
Fuskar a dan tsuke ta amshi kudin ta ficewarta Umma na bin ta da ido murmushi a fuskarta sosai take jin kaunar 'yar ta ta a ranta sosai yanayin rayuwarta take burgeta da komai na ta godiya take yi wa Allah da ya bata 'ya kamilalliya mai natsuwa da sanin ya kamata duk da karancin shekarun ta hakan bai hana ta sanin ya kamata ba idanuwanta lokaci guda suka kawo kwalla.
"Ina ka shiga ne ina son ganin ka a duniyata ya Allah duk in da wannan bawan naka yake Allah ka tsareshi ka tsare masa rayuwarsa ya Allah ka karkato masa da hankali ya dawo gaban iyalansa suna matukar buƙatarsa".
A bayyane take zancen zuciyarta take ji tana yi mata zafi tun lokacin da ta tsinci labarin tafiyar mijinta shikenan komai ya kara jagule mata ta rasa ina zata sa kanta abubuwa da yawa sun rikita mata rayuwa ita ba dangi ba ita ba iyaye ba sannan gashi yanzu miji ba ta san a halin da yake ba sosai take godewa Allah da irin ƙaddarar da ta samun kan ta a ciki sosai take goɗewa Allah da irin jarabtar da ya jeho mata cikin rayuwarta.
Dauke hawayen ta sake yi tana mai gyaɗa kai ita kadai ta san abin da take ji a zuciyar ta da kasan ruhin ta sosai rayuwar duniyar nan ke tsorata ta sosai take tsorota da komai na duniyar nan baki dayan sa.
*******
Sosai zuciyarta ta buga lokacin da idanuwanta suka hango mata shi zaune saman motarsa ya tallaɓe haba kamar wanda aka aikowa da mutuwa cikin dangin sa runtse idanuwa tayi gani take kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin baki tana cizawa a hankali zafin da take ji yana ratsa ta ya tabbatar mata da gaske shi din ne ba wani ba.
Kallon sa take da duk wani yanayi da ta tsinci kanta sosai ta hango sauyin yanayi game dashi sosai ta hango canji a gareshi ba kamar kwanakin baya ba wani abu taji yana mata yawo a zuciya sosai take jin jikinta na sakin wani irin yanayi yana kaiwa ga kafafuwanta kamar ba za su dauki gangar jikin ta ba.
"Yaa Rabbi!".
Ta fadi tana mai kau da kanta tana gargaɗin zuciyarta da ta daina abin da take yi akan Huzaif...
"Mariyaaa!".
Kamar daga sama ta jiyo sautin amon muryarsa mai cike da wani irin yanayi wanda ba ta san yarda zata ce yake ba amma dai da alamun rauni a cikin ta dago kanta tayi ta hango ya sauko daga kan motarsa ya doso in da take da sauri ta juya za ta koma cikin gida domin ba zata iya tsayuwa dashi ba sosai take jin ta a wani mataki wanda ya canza mata komai nata yake yaki da natsuwarta yake haifar mata da abubuwa masu tsoratar mata da zuciya da gangar jiki.
"Don Allah...".
Tsak! ta tsaya ba tare da ta waigo ba jin abin da yace sosai taji wani abu a muryarsa wanda ya kara rikita mata zuciya da kwakwalwa.
"Ban san mai zance miki ba, ban san abin da ya dace na fada miki ba wanda zai canza komai da komai a idanuwanki".
Nisawa yayi yana mai dafe kansa da yaji yana wani irin juya masa kamar zai watsar dashi a kasa bai san abin da zai ce da ita ba bai san abin da ya dace yace da ita ba bai san ya akayi ya zo nan wajan ba bai san akan abin da kawo shi nan ba gashi dai ga Mariya amma shi a karan kan sa bai san mai zai ce mata ba.
Sosai ta gane inda ya dosa sosai ta fahimci akwai abin da ke addabar zuciyarsa.
"Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba...".
"Please Mariya mana".
Ya yi saurin katse ta jin abin da take fadi sosai ya ji wani iri a zuciyarsa.
"Ni ya dace na baki hakuri ni ne nayi miki laifi ni ne na aikata miki ba daidai ba afuwarki nake nema ba ban yi zaton kalamai na za su sanya ki ki tsane ni ba...ko da yake komai ya faru ni na jawa kai na don Allah kiyi hakuri".
Wani irin nauyi taji kanta yayi mata sosai taji rashin dacewa sosai taji kunya ta kamata ace mutum kamar Huzaif yake bata hakuri ta ya ya hankali zai dauka anya kuwa ba wata manufa a zuciyarsa anya kuwa zata yarda da maganarsa domin ita tun haduwarsu ta farko ta raina wa a zancin sa sosai ta gane bai iya lafuza ba...
"na san dole ki ji ba dadi a ranki amma duk da hakan ki daure ki yafe mani Mariya sosai da sosai na shiga tashin hankali a rayuwa tun haduwa dake na kasa sukuni komai nawa na rasa gane kan sa na sani kece...kece silar komai ya faru kuma na sani nine ban da gaskiya".
"Na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya ni dama ba kayi mani komai ba".
Sosai ta gaji da maganganunsa shiyasa ta katse masa hanzari da amsar bukatarsa.
Wata irin a jiyar zuciya yayi kafun ya dubeta da wani irin kallo.
"Na gode sosai Mariya".
Gyaɗa kai tayi kafun ta dago idanuwanta ta dube shi sosai taji gabanta ya fadi saboda wani irin kallo da taga yana yi mata sosai taji wani iri a ko ina nata da sauri tayi kasa da kai.
"So Fine Boy waye wannan yaro mai kyau dashi".
Ya fadi yana shafar kansa.
"Kanina ne".
Ta fadi a hankali sosai taji dadi da yabon da yayi wa Mu'azzam hakan ya kara rage haushin sa da take ji.
"Don Allah bani shi mana mu gaisa".
Ya fadi yana mai kasa da murya gami da mika mata hannu a hankali ta kwance Mu'azzam ba tare da komai ba ta mika masa wata irin runguma yayi masa gami da manna masa kiss a fuskarsa a daidai lokacin Mu'azzam ya buɗe idanuwansa yana kallon Huzaif murmushi yayi masa shima nan da nan ya wangale masa baki hakan ba karamin burge Huzaif yayi ba sosai ya shagala da kallonsa yana yi masa wasa har ya so mantawa da Mariya ma a wajan.
Sai da tayi gyarar murya sannan ya dago ya dube ta da murmushi a fuskarsa.
"Yana da kyau sosai ina son sa.
Ya sunansa?".
"Ibrahim amma Mu'azzam muke kiran sa".
"Nice Name sunan nashi ya dace dashi sosai, ya fi ki kyau fa".
Ya fadi da sigar zolaya
Dariya tayi kadan kafun ta mika masa hannu.
"kawo sa Umma ce ta aike mu fa?".
Ba musu ya mika mata shi
Kamar daga sama sai ga Hafsi tsaye akan su ta na duban su daya bayan daya a sheke Huzaif ya dube ta sannan ya dubi Mariya kau da kan ta tayi hakan da ta nuna sai ya karanci wani abu game da ita shima sai ya tsuke fuska kamar ba shi bane yake yiwa Mu'azzam wasa yanzu.
Tsaki ta ja ganin sun ba banza ajiyar ta tayi cikin gidan tana kunkuni.
"Sai anjima ma ko nagode".
Ta fadi tana juyawa da sauri ya tsaida ita yana mai sanya hannu cikin aljihunsa kudi ya zaro masu dan dama ya mika mata.
"Gashi ki sai wa Mu'azzam cakulat sannan don Allah in kin shiga ki gaida Umma".
Irin kallon da ya ga ta na yi masa ne mai cike da tuhuma da ban so abin da kayi mani ba duk sai ya tsargu jikin sa yayi sanyi duk sai ya ji ya rikice ya rasa ma mai zai yi.
Girgiza kai tayi kafun ta saki wani murmushi.
"Uhmm rike kudin ka na gode sosai".
Ta na fadin haka ta taka kafa da sauri ta bar wajan kallo ya bita dashi yana faman gyada kai kamar wani kadangare har takule a sabule ya mai da kudin sa aljihu ya jima a tsaye cikin nazari kafun ya ja kafarsa ya isa wajan motarsa ya bar unguwar cike da abubuwa masu girma da suka saka zuciyarsa nauyi.
Duk abin da yake yi Mariya na laɓe a zauren gidan da tashige tana kallonsa sosai taji ya bata tausayi sosai take jin wani irin abu game dashi a zuciyarta musamman yarda ya baiwa Mu'azzam kulawa duk sai taji duk wani kunci da take ji game dashi yana bacewa daga filin zuciyarta gyaɗa kai tayi ta kara sa cikin gidan ta sayo tafarnuwar ta fito a hankali take tafiya zuciyarta na ta kawo mata abubuwa masu yawa suna samun gurbin zama a kofar gida ta ja burki ta tsaya tana gyara goyon Mu'azzam.
Horn taji anyi mata a bayanta da sauri ta juya gabanta na faduwa duk a tunaninta Huzaif ne ya dawo amma sai ta ga akasin hakan Dr.Karami ne zaune cikin motarsa ya zuru kafafuwansa waje ya sauke gilas din yana kafe ta da idanu sai faman murmushi yake yi ita ma murmushi tayi tana mai yin kasa da kai.
A hankali ya mike kan kafafuwansa ya karasa fitowa ya kulle motar yana takowa zuwa gareta har lokacin kanta na kasa
"My Boy ya kake?".
Ya fadi yana taba Mu'azzam shi kuma sai faman zillo yake yi alamun yana so yaje wajan sa sosai suka saba tsakaninsu sosai Dr.karami yake son Mu'azzam in dai ya zo gidan to tabbas Mu'azzam na hannunsa har sai ya tashi tafiya.
"Ina yini".
Ta fadi kanta a kasa bai kula ta ba illa kokarin zare Mu'azzam da yake yi a bayan ta ganin haka ya sanya ta kwance shi.
Daukarsa yayi ya rungume shi yana mai manna masa kiss shikuwa sai faman Dariya yake yi.
"me kika fito yi waje tare dashi da ranar nan?".
"Umma ce ta aike ne sayan tafarnuwa".
Kallon hannunta yayi ba tare da ya ce da ita komai ba ya fara taka kafafuwan sa zuwa cikin gidan domin ba ai masa shamaki ba Umma ta bashi dama ya dinga shigowa duk lokacin da ya zo ya daina tsayawa a waje.
Mariya bin sa tayi a baya har suka isa cikin gidan bakin Kofa suka hango Hafsi baje tana cin awara tayi ɗaiɗai da kafafuwanta sai faman jan hanci take yi tana gumi alamun yaji yayi yawa ko kallon su ba tayi ba su ma ba su bi ta kan ta ba sukayi sallama dakin Umma su ka shiga bayan ta ba su izini.
Bayan sun gaisa nan Mariya ta shiga korawa Dr.karami bayani akan tafarnuwar da ta sayo wa Umma dariya yayi sosai kafun ya numfasa.
"Mariya iyayen tsari to ai ba wani abu bane tafarnuwa tana da amfani sosai a jikin mutum ba ta da illar komai ana so mutane suke amfani da ita sosai ko a cikin abinci ne domin magani ce kamar yarda kika ji Umma ta fadi don haka sai ki kyale tayi amfani da kayanta".
Dariya Umma tayi mata itama dariya tayi tana mikawa Umma tafarnuwar.
Shiru ne ya gifta tsakanin su na yan dakiku kafun Dr.Karami ya ja numfashi ya dubi Mariya sannan ya dubi Umma.
"Umma dama akwai maganar da nake so muyi game da Mariya akan karatun ta ya kamata ace ta koma makaranta zaman ta hakan ba zai yuwuwa ba ya kamata ace a yarda take da kuruciyar ta ace tana makaranta yanzu".
shiru Umma tayi tana gyaɗa kai sosai taji dadin maganar Dr.Karami domin tafi kowa son Mariya tayi karatu domin karatun Mariya abu ne mai muhimmanci a garesu dama al'umma baki daya sai dai WANI HANZARI ba gudu ba ba a nan gizo ke saƙar ba...
"Umma karki damu nasan abin da kike tunani wannan duk ba wani abun da zai gagara ba ne ni aka ran kai na nayi alkawari zan dauki nauyin karatun Mariya tun daga yanzu har zuwa lokacin da zata kammala shi".
Wani irin duban hanzari Umma tayi masa tana girgiza kai ba ta san wani irin mutum bane shi sosai ta fuskanci mutum ne shi mai yaƙana da alheri a rayuwarsa ba abin da ya hada su ba dangin iya babu na baba amma jibi yarda yake dawaniya da su tun daga lokacin da ta shiga matsalar cutar ta har zuwa wannan lokaci bai gajiya ba ga shi yanzu ya dauko wani gagarumin aiki wanda ya kamata ace su iyayenta ya dace ace duk sun yi sa.
rintse idanu tayi wasu hawaye suka zubo mata ganin hakan ya sanya Dr.Karami saurin dubanta.
"Don Allah Ki daina wannan kukan bai dace da ke ba sam! Addu'a ya kamata ace kin yi kawai Allah ya tabbatar da alheri".
"Hisham ban san da bakin da zan gode maka ba kayi mani komai na rayuwa ba tare da kasan su waye mu ba nagode sosai Allah ya saka maka da alheri ya cika maka burukan ka na alheri ya kare maka rayuwa da zuri'a" .
"Ameen Summa Ameen".
Ya fadi yana duban Mariya wacce tayi kasa da kai tana faman hawaye sosai ya ji ba dadi a ransa ba zai iya cigaba da zama yana ganin hawayen su ba don haka ya mike ya na mai ajje Mu'azzam.
"Zan tafi Sai gobe kuma in Allah ya kai mu zan zo domin yin abin da ya dace".
Ya na fadin haka ya fice daga cikin dakin ya bar su Mariya shanye da baki suna duban junansu...
*KAMALA MINNA*😎😎
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN.
Dubansa take yi da wani irin yanayi na na raina wayonka da azanicin ka kafun ta kau da kai tana mai sakin guntun tsaki ta nisa cikin yanayi na haushi.
"Ban san mai ya hau kan ba Dr.Erena sosai ka bani mamaki ban taba zaton kalaman nan za su iya fitowa ɗaga bakin ka ba ka dube ni up zuwa down ban yi maka kama da mai karamin tunani irin naka ba aiki na zo yi a wannan company ba zaman zance mara kan gado ba".
Ta karashe tana mikewa kan kafafuwanta fuskar dauke da tsananin bacin rai sai dai kuma acan kasar ruhinta da zuciyarta ba haka bane domin kuwa murna take har da tsalle-tsalle Dr.Erena ya kusan fadowa komarta abin da ta jima tana KUDIRI da muradin tabbatarsa kenan.
"Areef..".
Da sauri ta daga masa hannu kafun ta dauki jakarta dake ajje kan table din Office din nasa.
"Ya isa haka bana bukata ban so ka takura min, in kuma kace takura min zakayi wallahi yanzun nan zan rubuta maka takardar ajje aiki...".
Da sauri ya mike jin abin da take fadi jikinsa har ɓari yake yi ya iso inda take tsaye ya kafeta da idanunsa da suka gama tafiya a duniyar Areefa.
"No Please ba sai mun je wannan matakin ba...But Areefa ya kamata ki fahimce ni mana alkawari nayi miki komai kike so kuma ko me kike so ayi na miki alkawari...".
Da sauri ta watsa masa wani kallo wanda yake kara rikita masa lissafi kafun ta tsume fuska.
"Ban san ta ya zan maka bayani ka fuskanta ba Dr.Erena ban san da wani irin kalami zan yi amfani ka gane abin da nake nufi ba".
Tana gama fadin haka ta fara taka kafafun ta ta doshi kofar fita zuciyarta cike da abubuwa masu matukar yawa.
Shi kuwa shanye baki yayi yana kallonta har ta fice kafun ya ajje wani numfashi mai karfi ya koma ya zube kan daya daga kujerun Office din nasa.
******
*FIRST CLASS INTERNATIONAL SCHOOL GWADA*
Sosai farinciki ke wanzuwa a fuskarta tun lokacin da Dr.Karami ya danko ta daga gida zuwa haɗaɗɗiyar makarantar da ya zaba mata zata cigaba da karatun ta.
Zaune take zuciyarta falla da farinciki mara musaltuwa har da guntayen hawayen na farinciki duban Dr.Karami take cikin wani irin yanayi wanda ita kanta ta kasa tantacce matsayin da take ji ya samu a zuciyarta sosai take jin matsayi mai girma game dashi a filin zuciyarta sosai take jin komai na canzawa a duniyar rayuwarta a yau daya kadai sosai take hango mafarkinta zai tabbata na son karatu da ta jima tana rokon Allah ya bata damar da za tayi shi yau gashi Allah ya jeho mata Dr.Ƙarami mutumin da bata taba zaton za ta gan shi a duniyar mafarkin ta ba balle a zahiri amma gashi Allah ya kawo matashi ta hanyar da bata yi zato ko tsammani ba.
Numfashi ta ja kafun ta dago kai ta na kallon Office din da ta baro shi a ciki shi da shugaban makarantar suna zantawa.
Kamar daga sama taji an dafa mata kafaɗa da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada dago kanta tayi ta sauke kan wata matashiyar yarinya wacce a shekaru za suyi kai daya sai faman murmushi take sakar mata cikin yake ita ma Mariya ta sakar mata da martani.
"Sannu ko sunana Baseera Haruna Sa'eed ni sabuwar daliba ce da Dadyna ya kawoni yau ke ya sunanki".
Mariya da ta saki baki da idanuwa ta na kallon ikon Allah sai yanzu ta kyafta idanu kafun ta sake murmushi tana motsa laɓɓanta cikin mamaki da wannan kanzagi da zalaka na wannan yarinyar sai kace ta tambaye ta saki baki sai ratata zance take yi kamar an kunna rediyo ana sauraron shirin INDA RANKA.
"Karki damu haka nake shi kansa Dadyna aku yake ce mani wai na fiye surutu shiyasa yace kawai nafi dacewa na zama yar jarida".
'Kuma dai!'
Mariya ta fadi a zuciya tana tallaɓe haɓa kafun ta nisa.
"yo ai ni kin hanani ma cewa komai sai zuba kike yi dole dadynki yace dake Aku ke ba ki san ni ba nima ban sanki ba amma kin saki baki sai watso mani zancen ki ke kamar na tambaye ki".
Da sauri ta caɓe.
"Woohh ai na san ke ba mai cutar wa bace daga ganinki kina da kirki da natsuwa sosai da sosai domin dady yace in zan yi abokiya na samu mai natsuwa ba irina mai shegen surutu ba".
Dariya sosai Mariya take yi har tana rufe bakin ta mamaki take yi da halin Baseera sosai da sosai taji lokaci guda taji ta kwanta mata rai.
"to ni dai zancen ya