Header Ads
Showing 123001 words to 126000 words out of 227252 words

Chapter 42 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1429

Ads at the middle of Article

da yake yi ba amarya aka bashi ba ya matsu yaje ya kanta.
Shi dai yaƙe kawai yake yi masa domin dai a daidai wannan lokaci. ya matsu ya ga jirkin su ya tashi ya sauka a kasarsa.
Bakwai da minti biyar jirginsu Dr.Karami ya daga zuwa najeriya.
********
Ya mutsa fuska tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk ta hada gumi a goshi hannunta face-face da kwabin fulawar Cake duban Umma tayi kamar za tayi kuka domin kuwa gabadaya take jin jikinta yayi sanyi da nauyi kamar wacce aka doddokewa kafadu lokaci-lokaci tana jin gabanta na faduwa wanda ta rasa dalilin haka tun da garin Allah ya waye a yau take jin ta a haka kwabin Cake din sai dakyar take yin sa jin Umma tace bazata yi mata ba ta gaji da son jikin da take yi sai kace mai laulayi.
"Don Allah Umma ki karasa min wallahi ba dadi nake ji ba a jikina".
Wani kallo ta watsa mata kafun ta dubi kwabin Cake din.
"Ai ke zan ga ranar da zaki daina son jikin nan naki wallahi kina mace amma ke gabadaya kamar wata mage ai ko mage ba zata nuna miki son jiki ba yarda ki kasan ruwa haka kike kuma ki karasa kwabin ki don ba yi maki zan yi ba ga dai yamma dai nan ta sako kai in kika bari har aka kira magrib wallahi ba zan tayaki aikin daren nan naki ba barci na zanyi".
Marere ce fuska tayi kamar zata fashe da kuka.
"Haba don Allah Umma daure ki karasa min...".
"Yaa Allah wai Mariya na tambayeki haka in kika yi aure zaki je kina wa mijin ki wannan SANGARTAR aiko tun wuri ki sauya don ba a san mace da nawa ba duk mace mai nawa sai kin same da kazanta da rashin sanin yarda zata kula da gidan auren ta".
"Naji Umma don Allah tausaya min Allah bana jin dadin jikina ne gabadaya yau din nan...".
"Sannu. ba rashin jin dadi ba kece General Hospital karewarta".
Umma ta fadi tana kokarin mikewa a daidai lokacin Mu'azzam yashigo da gudu ba in da ya dosa sai wajan kwabin Cake din ganin haka da Mariya ta yi ya sanyata saurin hanzarin cafko shi tana matse masa kunne.
"Sannu Biri sarkin barna wai kai don Allah Mu'azzam baka gani dai ka kyale sai ka bata ko to wallahi zan dinga dukan ka bar ganin Umma na goyan maka baya".
Turo baki yayi gaba kamar zai fashe da kuka Umma da ke tsaye ta shiga yi musu dariya.
"Yo cewa fa kikayi kin gaji ba sai ki barshi ya karasa miki ba ai sha yanzu magani yanzu ne Auta ba shi da jinkiri in dai wajan aiki ne yanzun nan zai yi sa yaro ba kiwa kenan".
Ware idanu Mariya tayi gami da tura baki gaba kamar zata rushe da kuka ta dubi Mu'azzam da yake kici-kicin kwace kansa ta tallake masa keya.
"Kai Umma wannan yaron naki ke kike goya masa baya kullum in zan yi kwabi sai ya nemi bata min bayan kuma in nayi duk shi yake cinye 'yar ribar".
"Kan ki ake ji miko min kwabin na karasa miki don na lura in na biye miki wannan kwabin sai ya dauko lalacewa".
Ai sai ta saki dariya da hanzari ta saki Mu'azzam ta dauki kwabin ta mikawa Umma da sauri ta shiga wake hannayenta cikin kwanon dake girke da ruwa a ciki.
Doguwar rikace a jikinta sai kallabi da ta daura kan ta dashi fuskarta fayau ba alamun kwalliya amma hakan bai hana sirrin kyanta fitowa sosai da sosai doguwar rigar ta anshe ta ta dan kamata kadan daga kugunta wanda yake cike sosai daga cikinta kuwa a matse yake kamar wacce bata cin abinci kirjinta ya cika sosai har yana kokarin rinjayarta saboda rashin ƙiɓarta doguwa ce amma ba can sosai ba jikinta kiran coca-cola ne.
A hankali ta warware dan kwalin kanta bayan ta matse daga kusa da Umma tufkanken gashin kanta ya baje sosai wanda yake ta faman sheki da daukar idanu a hankali ta shiga tattare shi a daidai lokacin wani kamshi mai dadin shaka ta ji ya doki hancinta da sauri ta ware idanu gami da kara buɗe hancin nata don sosai kamshin ya tafi da imaninta a daidai lokacin kuma wata murya wacce ta kusan narkar da Mariya kasa tayi Sallama wanda ya sanya gaban Mariya dokawa cikin wani irin yanayi mai razanarwa sumar tsaye tayi a daidai lokacin da ta daga fararen idanuwanta manya ta sauke su akan saitin mutumin dake tsaye cak! A kofar fuskarsa da wani irin yanayi idanuwansa dauke da wani kallon da ya sanya numfashinta kusan daukewa....


*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA BIYAR.


Numfashin ta take ji yana fizga kamar zai bar jikinta wani irin juwa da jiri taji tana kwasarta kamar zata watsar da ita kasa idanuwanta sun ya cak! waje ko juyawa ba sayi sosai take dubansa da kallo na mamaki da wani irin yanayi zuciyarta take ji tana bugawa da duk wani jan numfashin ta kamshin take ji yana dokar mata hancinta wani irin yanayi wanda ya haifarwa jikinta da wani irin kasalallan yanayi jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa kafafuwanta sai ƙarƙarwa suke yi suna kokarin zubda ita kasa.
Juyar da take ji tana wani irin juyawa da ita kamar wacce take samar gajimare runtse idanuwanta tayi a daidai lokacin da ta hango wasu abubuwa sun fito daga idanuwansa sun dire ana kamar saukar KIBIYAR AJALI lokaci guda zuciyata ta buga da wani irin yanayi mai girman gaske.
Sosai taji zuciyarta na buɗe a wani killataccen waje wanda ya jima kargame da katon kwado makullin sa ita kanta ba ta san inda ta jefashi ba sosai ta ji zuciyarta ta sauya bugu da wani al'amari mai girman gaske.
Ganin komai take yi tamkar a mafarki ba a zahiri ba ganin komai ta ke yi kamar ba a duniyar zahiri yake faruwa ba magudanan jinin jikinta take ji sun sauya a wani mataki wanda ita kanta ba zata ce gashi ba kwanyarta ta shiga kai kawo da wasu lamari masu yawan gaske wanda ta jima da binne su a zuciyarta.
A hankali take buɗe idanuwanta hancinta na sake dauko mata daddar kamshin sa wanda yayi matukar tasiri wajan juyar mata da duk wani kamshi da ta taba ji a filin duniyar nan.
Da sauri ta shiga warware dan-kwalin da ke kanta jikinta sai kyarma yake yi idanuwanta akansa har yanzu zuciyarta ba ta gama yarda da cewa shi ne ba sosai take ganin komai tamkar a mafarki dan yatsanta guda ta daga tana mai nuna shi bakinta na wani irin ɓari kamar wacce ruwan sama yayi wa dan banzan duka take rawar sanyi.
Shikam! mutuwar tsaye yayi zuciyarsa na bugawa da wani irin yanayi sosai yake yajin sa a sama duniyar na kai kawo dashi komai yake ji na kwanyarsa na wargajewa zuciyarsa na buɗe wani makeken fili tana dasa wata bishiya mai girman gaske wacce tayi rassa a lokaci guda duk ta mamaye kafatanin filin zuciyarsa.
Murmushi yake saki wanda shi akaran kasa bai san yanayi ba idanuwansa na juyawa da wani lamari mai girman gaske sosai idanuwansa suke bin Mariya da kallo kafun ya kau da kai cikin yanayin na bugun zuciyarsa da yake ji kamar zata tarwatse.
A hankali yashiga kokarin saita kansa yana jan numfashi mai taurin gaske kirjinsa yake ji yana nauyi sosai da wani abu mai girma gaske a hankali ya runtse idanuwansa.
"Yah Dr.Karami".
Mariya ta furta da wani irin sauti a muryarta wacce bata sam ma tana dashi ba bata san ta yi amfani dashi ba sosai take kallonsa sosai take jin jikinta na ansa wasu sakonni masu narkar mata da zuciya su hargitsa mata tunani.
Murmushi yayi kafun wani abu da ya tsaya masa azuciya ya wuce bayan ya haɗeshi dakyar.
Sautin muryarta da yaji yana ansa kuwwa a kunnuwansa hakan ba karamin narkar masa da jiki yayi ba gabadaya ji yayi sautin yana bin jikinsa yana ansa kuwwa a kwanyarsa da wani irin yanayi mai girman gaske.
"Mariya".
Ya fadi zuciyarsa na wani irin zillo kamar zata faso kirji ta yo waje.
"Yaa Allah Mariya wai da gaske kece?".
Ya sake fadi da wani murmushi mai kama da son fashewa da kuka idanuwansa naa kara narkewa da wani irin ruwa kamar na Rose tsakiyar kwayar idanunsa wani haske mai kama da na kibiya yake fitowa da sauri-sauri yana isa ga Mariya da ta gama narkewa cikin wani hali zuciyarta na wanzar da wani farinciki mara musaltuwa ji take yi kamar ta daka tsalle ta isa wajansa ta rungumeshu duniyar take ji tana sauyawa da duk wani hali da take ciki duniyar take ji tana kamfato mata wani farinciki tana ajje mata runtse idanu tayi jin abin da yace da sauri ta juya wajan da su Umma suke wayam! ta ga wajan ba kowa wata ajiyar zuciya tayi kafin taja kafa cikin sauri ko wani sashi na jikinta sai kaɗawa yake yi musamman kugunta da kirjinta. kafafuwanta kawai zaka kalla ka gane a harɗe suke tafiyar take yi amma ji take yi kamar zata kifa.
Fakare yayi da baki fuskarsa da wani kayataccen murmushi mai girman gaske idanuwansa kawai yake yawatawa akanta mamaki ne da tu'ajibi suka cika shi har yanzu zuciyarsa bata gasgata masa wai Mariya bace gani yake yi kamar wata halittace daban a tsaye a gabansa take yi masa magana gani yake yi kamar wata daban ce take tafiya a yanzu ba Mariya da yasani shekaru hudu baya ba komai ya sauya komai nata ya canza muryarta kirar jiki ta yanayin tafiyarta...
"Yaa Allah".
Ya furta yana kai hannayensa yana muttsuka idanuwansa da yake zaton karya suke yi masa gizo suke yi masa da wata mace ba Mariya ba zuciyarta na kara gasgatawa amma shi yaki AMANNA dan yatsarsa daya ya saka cikin baki yana cizawa da karfi jin zafin ya sanya shi sakin kara mai dan sauti.
"Ouchhh!!".
Ya furta yana yarfar dan yatsar nashi.
Ko da Mariya ta shiga dakin Umma na zaune tana karasa kwabin Cake din bango ta jingina dashi tana mai da numfashi da sauri-sauri idanuwanta a lumshe fuskarsa nayi mata yawo a idanuwanta murmushisa idanuwansa kai gabadaya ma fuskarsa take ganin tana kai kawo a cikin runtsantsun idanuwanta zuciyarta na wata irin harbawa da wani irin yanayi mai girman gaske numfashi ta ja kafun ta buɗe idanuwanta a saitin Umma da tayi mata fakare tana kallon Ikon Allah wai akace in kana da sauran numfashi kana DA SAURAN KALLO a filin duniyar nan mamaki ne ya cikata lokaci guda da taga canzawar Mariya yanayi da take kallon fuskarta da yanayin da jikin nata ya nuna wanda a tsayon lokaci mai yawa bata ga haka ba ta mance rabon da ta ga Mariya a haka bazama ta iya tunawa ba.
"Ke wai lafiyarki kuwa?".
Umma ta fadi tana mai tsuke fuska cike da mamakin Mariya tun lokacin da ta lura da shigowar Dr.Karami da yanayin da ta ga Mariya a ciki shiyasa ta zare jiki ta yo cikin dakin don ta lura tsaf! Mariya zata yi abin da zai tasa ta ji kunya a gabansa bata iya ƙewar mutum ba sam!
A duk lokacin da ta ga wani wanda suka jima ba su hadu ba ta dinga ɓarin jiki kenan amma na yau ya bambanta da sauran lokuta.
Wani murmushi mai kwari ne ya kufcewa Mariya kafun ta kai hannayenta tana toshe bakinta har zuwa lokacin jikinta bai daina ɓari ba.
"Yah Dr.Karami ne fa".
Uwar harara ta watsa mata kafin ta ja tsaki.
"Eh na san shine ai shiyasa na ga sai ɓarin jiki kike kamar wata sakarya ke a tunanin ki hakan da kikayi burgewa ce kina 'ya mace ki barin jiki ai sai ya dauke ki ba ki da natsuwa duk na ga abin da ya faru wanda sam bai dace ace ke a karan kan ki kike haka ba".
Zaro idanu waje tayi jin abin da Umma ta fadi da sauri ta sauya fuska alamun damuwa zame jiki tayi ta zauna kasa don jin kafafuwanta take yi kamar ba za su dauke ba.
"Au! zama kikayi ki bar shi a tsaye a tsakar gidan so kike yi ya lura da wautarki".
Runtse idanu tayi zuciyarta na wata irin harɓawa da sauri ta mike tana kokarin ficewa amma ta kasa sai kai kawo take yi tana susar kai Umma na lura da yanayin ta da sauri ta mike ta shiga kintsa dakin duk da ba wata gyara yake bukata ba komai tsaf yake hijab dinta ta dauko ta saka kafin ta dubi Mu'azzam da yake ta kasumar Cake sannan ta dubi Mariya.
"Ki dai kintsa ko".
Ta fadi fuskarta a daure kasa Mariya tayi da kai kafun ta gyara daurin dan kwallinta ta dauko hijab ta saka ita ma gabanta har lokacin bai daina bugawa ba fargaba kawai take yi ji takeyi kamar in ta fita ba zata ganshi ba gani take yi kamar a mafarki ne.
Numfashi ta ja kafun ta runtse idanu ta buɗe addu'a tayi domin samun sauki a zuciyarta.
A hankali taka ta fice daga cikin dakin kanta a kasa har yanzu yana nan tsaye harɗe da hannayesa a kirji dago kanta tayi ta dubesa idanuwansu suka sarƙewa waje daya lokaci guda zuciyoyinsu suka buga a tare da sauri tayi kasa da kai ganin wani murmushi da ya saki da ya kusan tafiya da imaninta.
"Sannu da zuwa Umma tace ka shigo daga ciki".
Ta fadi a wahale kafun ta juya tana kokarin komawa dakin.
"Bana son gaisuwar ai ni ba wajanki na zo ba".
Dr.Karami ya fadi da rashin wasa a muryarsa cak! ta tsaya da tafiyar da takeyi zuciyarta tayi mata wani wawan bugu ta runtse idanu kafun ta juyo cikin tsuke fuska da gayyato juriya ta ajjewa kanta zuciyarta na tuno mata da abin da ya faru na halin ko in kula da ya nuna a kanta tsayin shekaru sosai zuciyarta ta fara dauko laifinsa duk da dai bai taka kara ya karaya ba.
"Nima ai ba don halin ka na yi ba".
Ta fadi tana mai hanzarin barin wajan ta fada cikin dakin.
Murmushi yake saki yana mai nuna ta da hannu mamaki kamar ya kashe shi wai Mariya ce take magana haka ita ce tayi baki haka Mariyar da ya sani acan baya mai shiru-shiru magana ma wuya take yi mata wai ita ce da mai da masa da magana da yanayin fushi take yi dashi sai da ya gama shan sharafin mamakinsa sannan ya taka zuwa dakin a daidai lokacin ita kuma Mariya ta fito hannunta dauke da Jug na roba saura kadan suyi gware da sauri ta kauce ko kallonsa ba tayi ba fuskarta ba yabo ba fallasa yana kokarin mataa magana tayi masa wani kallo da ya sanyashi sauri sakin murmushi yana mai shigea dakin bakin sa dauke da sallama.
Bayansa tabi da kallo kafin ta ajje Jug din tayi hanyar waje kankara ta sayo ta zo ta hada masa lemo mai kayan kamshi da yake Umma na ajje kayan kamshi da kayan jinja saboda irin wannan yanayi na bako idon kunya sosai ta hada lemon sai kamshi yake yi sannan ta farfasa kankara ta saka a ciki sai da ta bashi kamar minti daya sannan ta dauka domin kai masa fuskarta a gimtse sai ka rantse bata taba yin dariya ba murya can kasar makoshi tayi sallama ta shiga idanuwansa kuwa na saitin kofar tana shiga da idanuwansa ta fara cin karo da sauri ta dauke kanta ta isa garesa ta ajje a gabansa ta mike wani plat ta dauko ta zubo masa Cake ta zo ta ajje masa duk kanta na kasa ta ki kallonsa amma shi duk motsinta na idonsa hanyar waje tayi tana kokarin fita.
"Mariya!".
Umma ta kira da wani sauti na tuhuma da sauri ta juyo ta dubeta alamu tayi mata da ido aiko sai ta kara tsuke fuska tana turo baki gaba ta gefen ido ta kalli Dr.Karami ya dauki Jug din lemon yana sha amma idanuwansa na kanta da sauri ta fice daga cikin dakin.
******
Duban Baseera tayi a dan hargitse idanuwanta ta bude su sosai kafun ta watsa mata wani kallo.
"Ke fa tsiyata dake wauta yasin daga fada miki magana kina kokarin canza mani manufa ta daban...".
Wayar dake hannun Baseera ta daura Ringing da sauri ta duba lokaci guda ta balle da dariya tana duban Mariya da tayi fakare da idanuwanta kallo daya zakayi mata ka gane ba cikin hayyacin take ba.
"Ke My Besty Mutumin ne fa yasin...".
Duka ta kai mata kafun ta mike tana kokarin ficewa a daidai lokacin ita kuma Baseera ta daga tana ansawa ganin Baseera na kokarin fita tayi sauri dauke wayar daga kunnanta.
"Billahillazi yana kofar gida ya biyo ki".
a firgice Mariya ta juya tana dubanta Baseera dake faman kwasar dariya idanuwanta a warwaje lokaci guda suka kaɗa kamar za tayi kuka.
"Yo ni mai ya dame shi dashi ai ba waje na ya zo ba...".
Da sauri Baseera ta mike tana katse wayar da dariya a bakinta.
"Yasin Karya kike daga gidan Umma yake yana nemanki Umma ta fada masa kika na nan yarinya kin gudu baki tsira bane bari ki ga".
Baseera ta mike tana zarar mayafinta tana kokarin fita waje ganin haka ya sanya Mariya saurin riketa.
"Ke fa ba hankali kika cika b ina kuma zaki kin san Allah ko kin je kin ce ina gidan ba zan fita ba domin kuwa ba abin da zan masa".
Tagumi Baseera tayi da hannu daya kafun ta saki wata dariya.
"Uhmm wai ma ni wallahi dariya kike bani mutumin nan yau satin sa kusan biyu yana zarya akan ki yana baki hakuri akan abin da yayi miki amma ke kamar wata dutse gabadaya kin kasa bashi lokacinki Mariya karki mance fa waye Dr.Karami karki mance lokacin da kika saka ni gaba akan baya kula ki ya manta dake amma yanzu dama ta samu kina kokarin sakinta".
Haushi ne ya turnuke Mariya tayi sauri ta fizge jikinta daga Baseera ta koma bakin gado ta zauna ta na mai zabga tagumi fuskar nan a haɗe kamar hadari da sauri Baseera ta iso gareta tana mai dafa mata kafada.
"Yi hakuri mutuniyar tashi don Allah muje bai da ace mutum kamar Dr.Karami kina yi masa haka ba...".
"Don Allah ki rabu dani Baseera karki saka raina ya bace

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads