Header Ads
Showing 156001 words to 159000 words out of 227252 words

Chapter 53 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1414

Ads at the middle of Article

domin tabbatarwa idanunsa abin da ke faruwa numfashi ya sake ajjewa kafun yace.
"Mu je na gano ni dai zuciyata ba ta gasgata maganar taku ba bana tunanin haka zata faruwa domin tunda nake ban taba ganin kogin nan yaci mutum ba amma dai..."
Sai yayi shiru yana nazarin wani abu kafun ya sake dubansu yana mai cewa su je amma cikin su ba wanda ya motsa sai mazurai suke da mamaki yake kallon su ganin ba wanda ya motsa balle yace dashi wani abu.
"Magana nake yi daku fa cewa nayi muje ku nuna min ko?".
Nan ma ba wanda ya motsa sai dakuna fuska suke yi kamar za su fashe da kuka kamar wanda ba mazaje ba sosai Baffa ke mamakin halayensu na tsoro tun da yake haihuwa bai taba haihuwa 'ya'ya maza masu bakin tsoro kamar su ba ko don suna tsakiyar mata ne oho! shi wani lokacin abin mamaki yake bashi sannan kuma ya bashi takaici musamman in yayi lakari da har iyali suka ajje amma yarinta bata bar su ba.
Tsuke fuska yayi cikin yanayi na rashin wasa muryarsa da sauti mai nuna bacin rai ya shiga nuna su da hannu.
"ku wuce muje tun kafin ranku ya baci bana son sakarci kun ji ko".
duban juna sukayi kafin su ja jiki su fara tafiya wannan ya tura wannan wannan ma ya tura dan uwansa Baffa ya shiga bunkansa ya dauko sanda sannan ya sauya riga ya fito ya dubi surukan nasa dake tsaye cirko-cirko sannan ya juya ya tafi tun da suka fito daga sashin su yawancin matayen rugar suke bin su da kallo don sun tabbata ba lafiya tun da suka ga Baffa da kan sa.
Tafiya suke yi kamar wanda ba sa son zuwa Baffa na biye da su da sun tsaya sai ya daka musu tsawa cikin wannan yanayin suka tunkari kogin zuciyoyinsu suka fara lugudan bugu suka fara tirjiya kamar dabbar da ba ta son zuwa inda za a kaita ganin da Baffa yayi ba su da niyyar karasawa sai ya raɓa su ya wuce yana mai watsa musu kallon na raina muku wayo.
Tun daga nesa Baffa ya fara tsinkewa da lamarin hango abu da yayi bakin kogin ruwa sai wuce yake yi ta wajan amma ba alamun motsi bakinsa dauke da addu'o'in neman tsari ya tun kari wajan zuciyarsa na harbawa amma haka ya dake ya isa wajan ba karamin razana yayi ba sosai ganin mutum zube a kasa rabin sa a waje rabinsa a ruwa turkewa yayi daga nesa yayi nazarinsa sosai ya tabbatar da cewa 'eh' gawa ce dagaske domin ganin yarda fuskar ta kumbure sosai ba ma ka iya gane halintarsa ta asali da hanzari Baffa ya isa har zuwa lokacin zuciyarsa da bakinsa ba su daina karanto addu'o'i ba ya tsorata sosai tsoron da ya kusan sanya zuciyarsa firgici har ya fara shakkan zuwa wajan gawar domin bai san abin da ya faru da wannan mutumin ba bai san mai ya kashe shi ba sannan yana tsoron abin da zai je ya komo musamman a halin rayuwar da ake ciki na yanzu baka san hawa ba baka san sauka ba fada TARKO da zai kashe maka rayuwa shi kuwa ba zai so haka ba baya fatan rayuwarsa ta kare da tashin hankali wanda zai hana zuri'arsa samun nutsuwa suma sosai zuciyarsa take karanto masa shafi-shafi na matsalolin da zai iya fadawa amma duk da hakan zuciyar tasa ba tayi tasiri ba domin wani bangare na cikin ta yana kwadaita masa ribar TAIMAKO a rayuwa numfashi yaja mai karfi kafin ya hadiye wani yawu mai tauri ya juya ya dubi su Iro da suka kara yin nesa dashi suna hangensa daga nesa murmushi yayi duk da halin da yake ciki bai taba ganin matsorotar maza irin su ba.
Sai da ya kwashe mintina masu dan dama kafun ya karasa wajan gawar ya durkusa yana karewa fuskar kallo mai cike da suma kallo daya yayi masa ya gane babban mutum ne zuciyarsa yaji ta bugu lokacin da fuskar mutum tayi masa gizo da wata fuska da ya taba sani duk da dai ya manta a ina ya san ta amma fuskar tana yi masa kamanceciniya a hankali ya sanya hannu yana jayo shi daga cikin ruwan gabansa na cigaba da bugawa sosai gefen kogin ya ajje shi yana kare masa kallo zuciyarsa na ta nazarinsa kafun ya mike cikin yanayi na JARUMTA ya dubi su Iro da suka kara matsawa can nesa tun lokacin da suka ga ya fara kokarin fiddo da gawar da hannu yayi musu alamu su zo amma ba wanda ya motsa ganin in ya biye musu ba abin da zai yi hakan ya sanyashi takawa ya isa garesu.
"kuje ku taho mani da amalanken shanu yanzun nan ina jiran ku".
Duban sa sukayi cin rashin fahimta kafun Iro ya motsa laɓɓansa a dan tsora ce.
"Baffa Amma...".
Hannu ya daga masa cikin alamun yayi shiru.
"kuyi abin da nace muku kawai bana son jin komai".
Yanayin da yayi maganar rai bace ya sanya su jan jiki suka bar wajan da sauri domin yin abin da ya umurce su.
Nan ya tsaya yayi shiru abubuwa da yawa suna masa yawo akai zuciyarsa sai kai komo take yi akan lamarin nan sosai da sosai abin ya daure masa kai bai san yarda zai kwatanta lamarin ba bai san ya zai dauke shi a zuciyarsa ba sosai yake jin wani iri a jikinsa abin da bai taba faruwa dashi ba tun da yake a rugar nan tashi sama da shekaru ashirin kenan amma abun ya zo masa kamar almara numfashi yaja kafun ya ɗaga kai ya dubi gawar daga inda take kwance mamaki al'ajabi duk sun baibaye zuciyarsa.
Bai san me duniyar nan take so ta zama ba, bai san ya zamanin nan yake so ya zama ba, bai san me al'ummar nan ta wannan karnin suke so su zama ba, sosai yake tsoron duniyar nan a wannan zamanin sosai al'ummar cikinta suke firgita shi komai ya sauya tashin hankali an mai dashi kamar abin ado kisan kai abu mai sauki a yanzu kamar ran kiyashi zuciyarsa kuka take yi sosai in ya tuna al'ummar nan yarda suka ɓace a wannan zamani zai iya yuwuwa wannan bawan Allah kashe shi akayi ba tare da laifin sa ba kila yana da iyali a yanzu haka Allah kadai ya san matakin da suka kai na tashin hankali haka rayuwarsu zata dauwama kullum zuciyarsu na kuka tana kunci na rashin tabbacin inda yake...
Karar amalanken da yaji ne ya katse masa dogon tunanin da ya faɗa da sauri ya juya ya dube su sannan ya nisa.
"Meye yasa kuke abu ne kamar ba masu hankali ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba 'ya'yan musulmai ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba masu imani ba, mai yasa kuke abu kamar ba masu tausayi ba, mai yasa kuke gudun dan'uwan ku, ban san dalili ba? ko shakka bana yi duk da dai ban san waye wannan mutumin ba amma na tabbata yana da alaka da addinin musulunci ko ba ku da dangantakar komai da za ku iya taimakonsa dashi ya kamata ku dubi dangantakar addinin da kuka hada dashi shin ba kwa tunanin irin wannan lamarin ya faru da ku ko wani naku shin ba kwa tunanin ku faɗa halin rayuwa irin haka shin za ku so a bar ku cikin irin wannan mawuyacin halin ko wani dan uwa naku ya kamata ku sani duk zuciyar da bata taimako sannan bata tausayi to bata cika mai imani ba ya kamata ku sani shi wannan bawan ba shi ya saka kansa cikin wannan halin ba ina mai gargadin ku ku fidda tsoro a zuciyarku ku ajje komai na sakarci ku dauki hankali da natsuwa ku daurawa kan ku fisabillalahi yanzu in aka bar wannan mutumin a haka me kuke tsammanin zai faru dashi a amtsayin na matacce amma ba ayi masa suttura ba dabbobi ne da tsintsaye za su zo fa suna cin namansa wanda ba haka aka so ba ku kan ku na sani nan da dan wani lokaci in dai yana nan wajan wallahi ba za ku iya zuwa ba a yanzun ma kuna tsoronsa a haka ina ga kuma suffarsa ta fara canzawa ya kamata ku canza rayuwarku ku da zuciyoyinku tun wuri!".
Shiru sukayi suna jin abinda Baffa ke fadi lokaci guda jikkunansu sukayi sanyi zuciyoyinsu suka mika su wani mataki na daban wanda ba su san suna dashi ba sosai suka ji wani yanayi mai girma ya dalsu a zuciyoyin su tsoro da fargaba ya shige su sosai dangane da maganganun Baffa sai faman rauyasa kai suke bai ce da su komai ba ya fara kokarin karkata akalan amalaken yana kora shanayen ganin haka ya sanya su sauri zuwa suka anshe shi duban su yayi kafun ya kau da kai sosai yaji dadi a zuciyarsa ganin maganganunsa sun yi tasiri a garesu a hankali ya fara takawa suna biye dashi har suka isa wajan gawar hannu ya saka yana kokarin daukarsa duk da a zuciyarsa yana ji ba zai iya shi kadai ba amma bai so yayi musu magana so yake yi ya ga halin da suke ciki sannan da yanayin da suka shiga a game da maganar tasa bai gama tunaninsa ba yaji su a kusa dashi a tsaye suna faman bin gawar da kallo sannan suna bin shi shima da kallo kafun su saka hannu duk da zuciyoyinsu suna harbawa amma duk da hakan sai da suka raruma jarumta suka sakawa kansu suka taimaka suka saka gawar a amalanken kafun suka hawan suka fara kokarin kaɗa shanun amma ya tsayen dasu isa yayi wajan wata bishiyar dogon yaro ya sanya hannu ya katso reshe mai girma da yake bishiyar ba tsayi gareta ba sosai kuma shi dama mai tsayi ne zuwa yayi ya lullube gawar dashi kafun ya hau su ja su tafi zuciyar sa cike da tausayi da jin ƙai ga wannan gawar abubuwa sosai yaji suna yawo akansa da zuciyarsa.
A wannan yanayin suka shiga cikin rugar duk aka shiga bin su da kallo cike da yanayi na dan firgici a daidai saitin bunkarsa suka tsaya su Mariye duk sun fito daga bunkokin su sun yi tsarko-tsarko sai faman mazurai suke yi kamar wanda za ace musu kes! su kwasa da gudu.
"Taimaka mu shigar dashi daga ciki ko".
Ya fadi yana duban Iro da yake duban Baffa tun dazu yana son sanin abin da za ayi sun dauko gawa sun kawo gida bai san kuma abin da za ayi yanzu ba numfashi ya ja kafun ya dubi Ja'e sannan suka kama ba tare da sun buɗe gawar ba suka tattara har ganyen suka yi cikin Bunkar dashi ajje shi sukayi kan tabarmar dake shimfiɗe a tsakar bunkar duk suka saki ajiyar numfashi kafun Iro ya sake numfasawa a karo na biyu.
"Baffa yanzu me za ayi masa to?".
Murmushi yayi kafun ya shafa kasumbar fuskarsa wacce ta fara zama fara fat!.
"Kokari zamu yi mu yi masa suttura mu kai shiga gidan sa na gaskiya shi kadai ne gatar da za muyi masa".
Gyaɗa kai sukayi dukkannin su suna masu sakin ajiyar numfashi mai girman gaske.
"Amma Baffa kana ganin haka ya dace ba fa mu san shi ba, ba mu san daga ina yake ba kana ganin in muka yi haka ba wata matsalar?".
"Ja'e kenan yanzu ya kake so muyi in ba mu yi masa gatar kai shi gidansa ba in muka ce sai mun binciko wanene kasan lokacin da zamu dauka ba fa RAI gareshi ba, ba ma wannan ba yanzu in muka ce sai mun binciko yan uwansa ta ina zamu fara ba da wani haske ko tsani da za mu bi ya kai mu matakin da muke so lalube kawai muke a duhu hanya daya ce kawai muyi masaa suttura duk da dai ba mu san alkiblar da yake ba amma a zuciyata nayi amanna musulmi ne".
Da mamaki suka dube shi.
"Baffa kai ma dai da wata magana kake ai da ka kalli wannan zaka gane musulmi ne duk da dai ba a fuska ake rubutawa ba amma yanayin suffar mutum ma Allah na nuna yanayin sa da kuma zaton da za ayi masa na alkiblar da yake kalla".
Ficewa sukayi gabadayan su waje suka tadda matan rugar da tsirarin maza sun yi dandazo suna jiran fitowar su Baffa kallon su kawai yayi lokacin da ya fito ya san za ayi haka dama dole su ne mi ba'asi ta yarda suka ga an shigo da mutum wanda suka tabbatar ba kalau ba kuma suka ga sabon abu da ba a tabayi a rugar ba.
Cikin son fitar da su daga kokwanto nan Baffa ya shiga sanar da su abin dake faruwa ba karamar razana da tsoro suka nuna ba musamman matan masu tausayi wasu har da hawaye nan dai ya ja mazajen cikin su gefe duk da yawancin sauran sun fita kiwo ba sa nan musamman manyan 'ya'yan Baffa.
Nan dai suka ba shi goyan bayan akan shawarar da ya yanke nan cikin kankanin lokaci ka shiga kokarin suttur tashi Baffa da kan sa ya shiga yi masa wanka cikin wannan yanayin wani al'amari ya so daurewa Baffa kai koma yace ya daure masa ya sanya shi tsayawa akan abun da yake yi domin ya lura cikin gawar na dan motsawa kadan-kadan alamun numfashi da farko bai yarda ba ya dauka juyawar da yake yi masa na wakan yake motsa cikin nashi amma sai yaga akasin haka da sauri ya mai da komai gefe ya ajje yana kallon sarautar Allah.
Abu kamar wasa cikin hukuncin Allah sai ga motsin ya cigaba dayi har hannyensa sun fara motsawa nan da nan Baffa ya fita ya kira su Ja'e ya nuna musu abin da ke faruwa sosai suka nuna tu'ajibinsu.
"Baffa ko dai yana da rai ne bai mutu ba?".
Cewar Ja'e.
"Akwai alamun ran a jikin sa kasan mi yanzun kamata yayi mu taimaka masa tunda alamun ya nuna da ransa".
Cikin hanzari Ja'e ya mike yana duban Baffa.
"Bari na kira Malam Jaura Mai Magani Baffa".
Ba tare da ya jira ansar su ba ya fice jikinsa na ɓari dama ya matsu ya bar dakin domin gani yake kamar FATALWA ce ba wai sahihin mutum bane ya farko.
Ya jima kafin ya dawo tare da Malam Jauro din irin mutanan nan ne masu maganin gargaji na kauye kafaɗarsa rataye da jaka ta fata kallo daya zakayi masa kasan ya tsufa sosai fuskarsa duk ta tattare abin ka da bafulatanin mutum ba kauri sai tsawo ga wani gemu da ya ajje yayi masa tsiri a haɓa yayi fari tas! dashi.
Taimkon gangawa ya fara yi masa magani ya hada na sauyoyi ya murtsuke su kafun ya tsiyayi ruwan ya baiwa Baffa ya dura masa duk da izuwa wannan lokacin jikin nasa ya daina motsi hannu Baffa na k'yarma ya kai maganin saitin bakin sa yana mai furta Addu'ar neman dacewa ya shiga dura masa amma hakoran sunki buɗewa sai zubewa maganin yake yi a jikinsa ajjewa yayi gefe kafun ya sanya hannu ya buɗe bakin sosai wanda ya kunbure sosai jini duk ya taru masa laɓɓan nasa sun canza kala sunyi bakinkirin alamun mataccen jini a hankali yake dura masa wani na zubewa wani na wuce har ya gama ya mikewa Malam Jauro kokwan yana mai ajiyar numfashi kusan awa guda ana abu daya amma ko motsi bai sake yi ba amma Malam Jauro ya tabbatar musu da cewa yana da rai in Allah ya yarda zai tashi nan ya basu magunguna wanda za a dunga shafa masa da wanda za a dinga bashi na tsawon lokacin da zai farka domin ba karamar jika yayi ba jikinsa duk a kunbure yake ta ko ina sosai da sosai rigar jikinsa Baffa yayi kokarin cewa wacce gabadaya ta gama rine da jini.
Sosai Babba ya tsorata lokacin da ya gama cire masa rigar dak'yar wacce sai da ya yage ta ba dai ya fidda ita ta wuya ba saboda mannewa da tayi da ciwon dake jikin nasa hannunsa na dama da ya kumbura ya suntume Baffa ya kurawa ido sosai yana nazarin sa kafin wani lokaci ya gane harbi akayi wanda ya same shi a hannun nan ya shiga kwaɓa wani magani wanda Malam Jauro ya bashi ya shafe masa wajan dashi kafun dukkannin su su fice daga cikin dakin zuciyoyinsu cike da fargaba da yanayin da suka gan maras lafiyar a cikin in ba don Malam Jauro yace akwai numfashi ba ba su yarda ba musamman Ja'e da Iro wanda sukayi zaton kawai dama can a mace yake ganewa ne ba suyi ba suke ganin kamar motsi yake yi duk da wani ɓari na zuciyoyin su na sanar da su da sauran numfashin sa.
******
"Anya Baffa wanna mutumin zai tashi kuwa?".
Cewa Ja'e dake faman gasa masa jiki da tafasheshen ruwan magani wanda izuwa wannan lokacin jikin nasa ya sabe sannan kuma numfashin sa na fita a hankali.
Baffa wanda ya kure shi da ido tun dazu yana kallonsa yau kwana biyu kenan zuciyarsa na damuwa da lamarin mara lafiyar nan da ya tsinta sosai ya damu sosai yake son ya ga ya tashi kan kafadun sa yana so ya san ko waye shi yana son ya san wani abu game dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani lamari mai girma yana tattare da shi zuciyarsa da idanunwansa suna nazarin fuskarsa wanda har zuwa wannan lokaci bata dawo daidai ba ko idanun nasa bai iya buɗewa.
Numfashi ya ja kafun ya dube Ja'e.
"zan so ace ya tashi kan kafafuwan sa sosai nake bukatar haka ina so ya dawo duniyar nan ya cigaba da rayuwa sosai nake ji a jiki akwai wani al'amari da zai faru a game da wannan mutumin ko da dai ban san sa ba amma ina ji a jikina akwai wani abu a boye".
Shiru yayi yana duban Baffa jin abin da yake cewa wai akwai wani abu da yake zaton zai faru anya kuwa meye zai sanya kansa damuwa akan mutumin da bai san shi ba bai san daga ina yake ba...
Motsin shigowa haɗe da sallama da akayi ya tsinke musu zaren tunanin da suke yi Asiya ce ta shigo hannunta dauke da kwarya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads