Showing 54001 words to 57000 words out of 227252 words
Chapter 19 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
bacin rai ne a cikinta sosai da sosai ba ta san mai zata ce masa ba bata san wata irin amsa ya dace ta ba shi ba sosai ta fuskanci yana cikin yanayin bacin rai wanda ta rasa mai yasa hakan ya bayyana shin ko dai ya san Huzaif ne ko dai ya san wanene shi.
Tambayoyin da su dinga mata shawagi kenan cikin kwanya suna kara haifar mata da tashin hankali mai girman gaske.
"Dake fa nake Mariya kika yi shiru wanene waccan kin san shi ne?".
Sosai taji muryarsa ta kara buɗewa da sautin fushi a cikinta wani kaɗawa taji cikinta yayi ba ta taba zaton akwai ranar da za taji muryarsa haka ba bata taba zaton akwai ranar da zata ji magana irin haka mai dauke da daci a cikin ta ba girgiza kai ta shiga yi a hankali kafun ta kokarta jan numfashi.
"Ban san shi ba kawai dai...".
"Kawai dai me?".
Ya tare ta da sauri har lokacin muryarsa ba ta canza ta koma yarda ta santa ba.
Wani karfi taji ya zo mata cikin zuciya da sauri ta dago idanuwanta a rintse ta sauke su saitin Dr.Aqeel kafun ta juya ta kalli inda Huzaif yake tsaye har yanzu tana hango irin tashin hankalin da yake ciki.
"Gani nayi kamar yans cikin Matsala sosai naga haka a idanunsa shiyasa na ji ba dadi...".
Ba wai don ya yarda da maganar ta bane dari bisa dari domin zuciyarsa taki yarda da abin da yake gani jan numfashi yayi mai tauri yana kokari ajje maganar tata a zuciyarsa yana yarda da cewa ita ta hango tashin hankali game dashi ne shiyasa ta nuna jajantawa gareshi duban Huzaifa yayi daga inda yake tsaye yana hango tashin hankalin da yake ciki idanunsa sosai ya fuskanci wani abu cikin Maganar Mariya kuma zuciyarsa na karyata abin da yake zargi ba tare da yace da ita kala ba ya juya ya cigaba da tafiya jan numfashi tayi ita ma tana sake kallon Huzaif kafun ta kau da kai hadi da hadiye wani abu mai girma da ya tsaya mata a wuya ta daga kafafunta ta bi bayan Dr.Aqeel zuciyar cunkushe da abubuwa ma bambanta wanda ta kasa gane in da suka sanya gaba..
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA SHA TAKWAS.
*In ka rike mani za na rike maka ribar zama yarda da juna farin cikina zana sanar maka kai ka damu dani.*
--Usaini Danko
A hankali yake ajje komai na shi kan table din dake girke cikin kayataccen office din sa kallo daya zakayi masa ka gane hanzarin da yake yi cikin aikinsa gabadaya hankalin sa bai wajan abin da yake yi idanuwansa na wajan kofar office din ji yake yi ajikinsa akwai wanda zai shigo zuciyarsa tana sanar dashi hakan.
Bayan ya kammala komai a hankali ya fara takawa kan ƙafafuwansa don ji yake yi kamar abin da yake muradin gani kum zuciyarsa na sanar dashi tabbatarsa kamar ba zai tabbata ba gareshi sosai yake ganin tafiyar lokaci wanda yake hango kurewa a cikin sa duk dakika daya gani yake yi kamar tafiyar awa daya ce.
Wajan sakatariyarsa ya dosa yana faman jan numfashi.
"Sir Morning".
Abin da ta fadi kenan bayan ta dago kanta jin alamun mutum kusa da ita.
Hannu ya daga mata alamun amsawa kafun ya shiga waige-waige na yan dakiku sannan ya sauke idanuwansa akanta yana mai nisawa.
"Areefa ta shigo aiki yau kuwa?".
Mamaki taf! A fuskarsa take dubansa sosai take lura da canjin ogan nata tunda Areefa ta shigo cikin ma'aikatar nan gaɓadaya hankalinda da natsuwarsa suka karkata akanta ba ta san mai hakan ke nufi ba...ko da dai bai kamata tayi mamaki domin ta san waye Dr.Erena tuni ta diga masa ayar tambaya katotuwa.
Kaɗa idanu tayi kafun ta motsa tika-tikan laɓɓanta wanda suka sha jan jambaki sai faman kyalli suke yi.
"gaskiya bana zaton ta shigo don ban ji duriyar ta ba yau sam".
Ta karashe tana mai kafeshi da idanuwa sosai ta sosai kai taga ya shiga girgizawa yaka faman cizon laɓɓansa gami da haɗa hannayensa waje daya yana lankwasawa suna bada wani sauti mai zurfi.
A hankali ya fara taka kafafuwansa da sanyi a cikin su amma yarda yake tafiyar cikin hanzari bai bayyanar da haka din ba kofar fita daga sashi ya dosa yana faman hanzari cikin tafiyarsa cikin kankanin lokaci ya sauka daga benen zuwa tsakiyar cikin company din idanuwansa ya ware yana yawatawa cikin sashi da sashi na ko ina.
Ya jima cikin wannan yanayin kafun ya isa wajan daya daga cikin ma'aikatan da suke nan din ko wanne da bangaren sa kamar office.
"Mufeeda Please ko kin ga Areefa ta shigo yanzu?".
ya fadi har lokacin idanuwansa ba su tsaya waje daya ba.
Dago kanta tayi jikinta sanye da abaya kamar ko yaushe dubansa tayi da wani irin yanayi kafun ta kau da kanta sosai taji sunan da ya ambata ya shiga kuwwa cikin kwakwalwarta sosai take jin sunan yana haifar mata da wani irin yanayi mai girma gareta zuciyarta taji tana zaro mata wani labari mai girma da ta daɗe da binne shi a filin zuciyar ta ta sunan Areefa take ji kamar a mafarki abubuwa da yawa take ji a ranta game da sunan.
Nisawa tayi cikin wani irin yanayi mai girma kafun ta dago kanta ta sauke ga Dr.Erena wanda shi a wannan lokacin sam! hankalinsa baya kanta sai faman watsa idanuwansa yake yi cikin ko wani sashi na ma'aikatar har izuwa babbar kofar.
"Areefa".
Kamar daga sama taji bakinta na nanata sunan da wata irin murya mai zurfi da wasu abubuwa masu girman gaske.
"Ban san taba ban ma taba ganin ta ba!".
Muryarta da zurfi a cikinta tashiga fadin haka da alamun bacin rai tattare da ita musamman yanayin da fuskarta ta sauya lokaci guda bacin rai sosai ya samu masauki a ko wani sashi na filin zuciyarta da ruhinta.
sosai yaji sautin muryar Mufeeda akansa wanda tunda suke da ita bai taba jin tayi magana mai zafi haka ba sosai yake kallon ta cikin yanayi na mamaki kafun ya nisa.
"bakuwar da ta zo last week fa nake magana wacce kuke matsayi daya da ita".
Sosai yake yawatawa da idanunsa akanta yana kallon yarda komai nata ya sauya lokaci guda kai ya shiga gyaɗawa kafun ya juya ya doshi babban kofar da zata sadaka da reception din Company din.
Tsaye yayi hannayensa zube cikin aljihun bakar suit dinsa sai faman yawata idanuwansa yake yi ta in da zai hango can wajan Parking ya tsayar da ganinsa yana bin motocin wajan da idanunsa daya bayan daya bai dire a ko ina sai kan wata bakar marsandi wacce kallo daya zakayi mata ka gane sabuwa ce fil.
Ajiyar zuciya ya ajje hakan ya tabbatar masa da Areefa na cikin Company din nan amma kuma ya akayi bai ganta ba har sashinta ya duba nan ma bai ganta ba ya tambayi abokan aikin ta suma sunce ba su ganta ba mai hakan ke nufi?.
A hankali ya fara juyawa kan kafafuwansa domin koma cikin Company zuciyarsa cike da tunnain Areefa da dalilin da yasa bai ganta ba cikin Company kuma alamun ya nuna ta na ciki tunda ga motarta nan hakan ya tabbatar masa da zuwan ta da wannan tunanin ya koma ciki bai sake duban kowa ya hau matattakalar da za ta haura dashi zuwa sashin sa.
Mufeeda dake zaune tun dazu ta zabga tagumi tun da ya zo ya sanar da ita wacce yake nema ya fada mata sunan da yake cigiya shikenan taji ta komai nata ya canza sosai taji wani iri a jikinta har ma da zuciyarta sosai take jin wani abu mai nauyi mai dauke da bacin rai ya samu masauki a zuciyarta a hankali take ajje numfashi tana duban Dr.Erena zuciyarta na kara tabbatar mata da abin da take zargi.
Gyaɗa kai takeyi tana yatsine fuska gami da tura laɓɓanta cikin bakin sai da ta dauki lokaci mai tsayi a haka kafun ta ajje komai gefe ta cigaba da aikinta amma ta zuciyarta sai kawo mata abubuwa take yi wanda yake kokari addabatar ya hana ta aikinta.
Tana cikin kokawa da zuciyarta kamar daga sama taji sautin takalmi ya karaɗe cikin wajan gabanta ne ya buga ko ba a fadi mata ba tabbas ta gane ko wacece mai wannan tafiyar bata dago kanta ba sai dai aikin da take yi cikin Computer ta tsayar dashi cak! hannayenta ta janye daga madannan computer din ta hade su waje guda tana sarke su a hankali kafun ta dago kanta a daidai lokacin ita kuma ta karaso daidai wajan da take hannunta rike da jaka mai kalar Gold da wasu yan duwatse masu kyalli da akayi mata ado da su jikinta kananun kaya ne wando da riga sai abayar da ta daura a kai gaban rigar abuɗe yake ta yane kanta da gyalen abayar fuskar nan ta sha Make-up sosai hanyarta a kunnan ta sai faman sakin murmushi take yi da alamun wayar da take yi din tana jefa cikin nishaɗi.
Kuri Mufeeda tayi mata da ido tana saka dan guntun biron dake hannunta cikin bakinta rana jujjuyashi tana yawatawa da idanunta sosai akan Areefa da ta tsaya daidai saitinta bugun zuciyarra na karuwa sosai da sosai abin da take zargi ne take ganin tabbatarsa zuciyarsa na kara hasko mata abubuwa da dama da suke kara tabbatar mata da zarginta.
Yaa Allah!.
Abin da ta fadi kenan lokaci guda tana dafe kanta da taji yana sarawa runtse idanuwanta tayi sai sai da ta dauki sakann kafun ta buɗe su har zuwa lokacinAreefa na nan tsaye sai dai ta gama wayar ta sauke duban Mufeeda tayi wacce ita idanuwanta na kanta lokaci guda sua sarke a idanuwansu sosai suke kallon junansu wasu abubuwa ne masu girma suke wanzu a zuciyoyinsu sun dauki mintoci a haka kafun Mufeeda ta kau da idanuwanta gami da yin kasa da kai ita kuwa Areefa kafadun ta daga gami da nuna halin-ko-in-kula ta ƙyaɓe baki tana mai daga wa Mufeesa hannu ta raba ta ta wuce cikin takunta na musamman da duk lokacin da zata shigo cikin Company din take yin sa.
*******
Sosai hawaye ke kwaranyo zuwa saman fuskarta sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗi sosai take jin tashin hankali wanda ba ta tsammanin ba mai girma baɓe a rayuwarta ba ta san ya zata koyi rayuwa ba a yanzu bata san ya zata koyi rayuwa ba batare da wadannan dangin ran ba bata san ya zuciyarta zata koyi kewarsu ba sosai take jin abu mai girma na samun waje afilin zuciyarta yana zama duk jikin ta take jin yayi sanyi yana haifar mata da abubuwa masu girma da kara dagula mata lissafi ba ta san ya rayuwa zata kasance mata ba nan gaba ba ta san wata irin rayuwa zata buɗe ba a shafin duniyarta in ta bar wannan wajan.
Hannunta ta sa ta shafe hawayen da suke sake balle mata wasu na bin wasu hada kayan su take yi cikin yanayi wanda ita kan ta ba ta san ya zata fassara shi ra san dai akwai tashin hankali mai girma da zai zo mata ko ma tae ya zo mata ba ta san ya zata dauke shi ba ta san ya za ta ajje tashin hankalin nan a zuciyarta za ta bar su za tayi kewarsu ta tabbata dole ne su rabu rabuwa ta har abada wanda bata tsammanin za su sake hadu a duniyar nan domin da ma can matsayin su ba daya bane ta sani sam ba su dace da zama a inuwa daya ba har su shaku ta sani zuciyarta...zuciyarta ba tayi mata adalci ba ba ta yi mata daidai ba ta sani tayi sake sosai da ta bar zuciyarta ta shaku da mutanan da ta san tabbas su rabu ko tana so ko bata so domin duniyarsu ba daya bane suna da tazara mai girma a tsakaninsu akwai katanga mai girma da tayi musu SHAMAKI a tsakani yau ta ga ILLAR SABO a rayuwarta tabbas sabo shi ake yi wa kuka dole tayi jinyar zuciyarta wanda ba ta san ranar da zata warke ba daga ciwon da ya kamata mai girma wanda laifinta ne da tayi sake har ta bar zuciyarta da gangar jikinta sukayi saboda da wadannan mutanan masu ALHERI da YAƘANA.
"Mariya!".
Taji muryar Umma na ambaton ta cikin yanayi mai cike da rauni da kuma rarrashi.
Da sauri ta sanya hannunta ta shafe hawayen da suke saukar mata kafun ta kokarta janyo yaƙe muryarta na rawa ta ansa mata gami da juyowa ta na fuskantar ta kallon ta take da duk wani rauninta dake cikin zuciyarta tana jin yarsa ruhinta da gangar jikinta suke haifar mata da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa sosai take kallon Ummanta da yanayin da take ciki ta rame sosai sai dai kallo daya zaka yi mata kasan tana samun kulawa komai nata yayi normal duk wani abu dake damunta ya kau yanzu lafiya kalau take tana iya magana sosai cikin hankalinta ba tare da an samu matsala ba ko ya ya take sosai tayi wa Allah godiya da wannan ni'imar da yayi musu sosai take sake gode masa tafi kowa farinciki da wannan lamarin tafi kowa farin ciki da samun lafiyar Ummanta sosai take jin zuciyar na rage duk wani nauyi mai girma abu daya yake kara dakula mata lissafi in ta tuna shi Mahaifinta sosai take shiga tashin hankali mai girma sosai komai nata ke kara hargitsewa in ta tuna rashin matsaya da take dashi akam mahaifinta kullum cikin tunaninsa take ba ta san mai yasa ya tafi ya bar su ba a daidai lokacin da suke bukatarsa a filin duniyarsu ba ta san mai yasa ya bar su tsayin wannan lokacin ba bata san mai yasa ya dauki kafarsa ya bar su ba batare da ya sanar da su in da ya dosa ba sosai take shiga tashin hankali mai girma in ta tuna wannan lamarin.
Nisawa tayi kafun ta amsa kiran da Umman nata tayi mata.
"Ban san mai kike nufi da wannan kukan ba Mariya, Ban san mai kike so kuma ki daukowa kan ki ba, na lura sosai kike jin dadin zubda hawayenki baki san hakan yana matukar sanya ni cikin damuwa ba".
Shafe hawaye tayi sosai take jin maganganun Umma a zuciyarta sosai take fuskarta gaskiyar abin da Umma ta fadi sai dai bata san ya za tayi da abin da yake a zuciyarta ba sosai take jin rashin dadi ba ta san ya za tayi ta hana idanunta zubda hawaye ba.
"Umma Kiyi hakuri ban san ya zan yi in hana su zuba ba ne sosai take jin kewa a raina sosai nake jin rashin jin dadi a ko ina nawa saboda su mun shaku Umma suna da alheri sosai a duniyar su ban san yaushe za mu sake haduwa ba in muka rabu...".
Zuciyarta tayi rauni sosai muryarta ta karye hakan ya sanya ta yin shiru tana mai toshe bakin ta da taji kuka na shirin kufce mata.
"Yaushe zaki girma Mariya mai yasa kike abu kamar wata yarinyar da ke goye wa ya gaya miki kun rabu kenan har abada shin ce miki akayi daga nan lahira zaki tafi ba a duniyar zaki zauna ba to bari kiji mutum da mutum suna rabu sai su shafe shekaru masu yawa har su fiddo tsammanin sake hadƴwa amma cikin iko na Rabbi sai ki ga sun hadu har sun sake wata rayuwar a filin duniyarsu don haka ki daina YANKE TSAMMANI akan abin da bakin san yarda zai kasance ba Allah kawai za ki saka a lamarin ki ba fa rabu rigima a kayi ba balle ki ce tsakanin juna ba za a so sake haduwa ba ALHERI ne ya hada ku kuma kin san shi alheri a ko ina yake ba ya tafiya a banza".
Ba wai tana maganar nan ba ne don ta yarda ita akaran kan ta a,a kawai dai so take yi ta kwantarwa 'yar ta ta da hankali domin yanayin da taga ta dau lamarin mai gira a zuciyarta ko da yake tana da gaskiya zama lafiya aka ce yafi zama dan sarki zaman da akayi cikin aminci da mutunta juna dole a ji ba dadi wajan rabuwa ko zama da mutum kayi kullum kuna fada dole in za ku rabu kaji rashin dadi a ranka ta dani ita a akaran kanta abin da Mariya tayi ba ta ga laifin ta ba domin ta lura akwai sabo da shakuwa sosai a tsakaninta da likitocin asibitin tana kallon yarda suke mutunta ta da ahalin ta tana kallon yarda 'yar ta ta take ganin girman su da ba tare da raini ko wani abun kiba fiye da KWANA SITTI da tayi a asibitin nan kamar yarda taji likitan na fadi ta san dole ne su shaku sosai shakuwar da ba za su so rabuwa ba amma ba yarda za suyi rayuwa ta gaji haka aka rabu da mutum ma zuwa lahira kuma aka hakuri balle wannan a na cikin duniyar sai dai ace ba waje daya ake zaune ba.
Gyaɗa kai tayi cikin yanayi na tausayawa shiru ne mai dan tsayi ya ratsa cikin dakin ba abin da kake ji sai ajjiyar numfashin Mariya lokaci lokaci tana jan hanci da alamun kuka a ciki kawai daurewa take yi ba ta taba zaton za su rabu ba ba ta taba zaton magaɓar rabuwarsu a wata rana ba za ta tabbata kamar yarda Dr.Karami ke fada mata ashe da gaskiyar wannan ranar za ta zo filin duniyar su kowa ya kama gabansa ashe duk maganganun da yake mata masu shige da WASIYYA gaskiya ne amma ta kasa sanya hakan a zuciyarta taki yarda ta maganar tsa da take kallo a matsayin kanzon kurege bata san ruɗi da ya dauke ta ba bata san abin da ya shigar mata kai da zuciya ba ya hana ta hadda ce karatun Dr.Karami yanzu ga ranar ta zo ga cikin ta tsamo tsamo amma ta kasa yin komai sai nauyin zuciya da tashin hankalin da ta ke hangowa...
Sallamar da ta amsa kuwwa cikin dakin ne ta dakatar da ita daga zancen zuccin da take sosai taji wani irin bugun zuciyarta ya canza salo