Showing 63001 words to 66000 words out of 227252 words
Chapter 22 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
tsaya nan naji abin da Dadynki yace yanzu dai ke a ina kike kuma aji nawa kike...".
yarfar da hannu tayi tana mai yatsine fuska.
"wai fa ss-1 nake daga makarantar da muka baro da yake dadyna ma'aikaci ne sai aƙayi masa canji aka kawo sa nan garin shine zai canza min makaranta wai sai dai a mai dani js-3 ki ji fa don Allah ai wannan ci baya ne kamar ni kuma fa ina da kokari sosai da sosai...".
"Yaa Allah! Baseera wai don Allah bakin ki baya ciwo ne don Allah tsaya ki ja numfashi mana".
Mariya ta tare ta tana mai kama hannunta ta na zaunar wa kan kujerar da take zaune a kai.
"karki damu akan haka nima yanzu placement zan rubutu na tafi ss-1 kin ga kawai sai mu tafi tare...".
Wata irin zabura tayi tana dariya.
"da gaske ki ke don Allah to shikenan ma na hakura da fa balli na tayar nace ban yarda ba amma tun da kin ce haka zan zauna saboda ke my abokiya".
"Yaa Allah Baseera Oh My God wai ke don Allah yaushe zaki yi hankali ne Yaa Allah!".
Wata murya ce suka ji kamar daga sama tana fadin haka da sauri Baseera ta zabura tana dosar mutumin da yake tsaye nesa dasu hannayensa sarke a kirjinsa sai faman kallon su yake yi da yanayi na damuwa a fuskarsa.
"dadyna zo ka ga my new ƙawa wallahi mai kyau da ita ga ta da natsuwa irin ƙawar da kace nayi...".
Janyo ta yayi yana jan kunnan ta wata karamar kara ta saki.
"Dady Please don Allah ba zan sake ba".
"Ban san yaushe zaki girma ba Baseera ke ko gajiya ba kya yi da surutu haba mana! a ko ina sai kin nuna halin ki nikam zan ce ma na fasa saka ki a makarantar ba zan iya da rawar kan ki ba...".
"wayyo Allah dadyna Please for give me I'll never do that again".
Yanayin da ta marare ce taka langwashe murya ya sanya shi dungure mata kai yana murmushi halin Baseera sai ita duk yarda ta san zai sanya ka ki daukar hukunci akan ta ta sani.
"Zo mije ka ga my New Ƙawa please dadyna".
ta fadi tana jan hannunsa shi kuwa sai fizgewa yake yu amma taki dai nawa har sai da ya bi ta sannan ta daina magiya har zuwa lokaci Mariya na zaune idanuwanta akan su duk abin da suke yi tana kallo wani burgewa da sha'awa suke mata sosai da sosai taji Baseera da mahaifinta sun burgeta yarda suke kulawa da juna da nuna soyayya tausayin kanta take tana tuno nata mahaifin in da yana nan da shi ma haka zai nuna mata soyayya fiye ma da ta Baseera amma ina! hakan ya gagara ƙaddara ta rabata dashi rabuwar da ba ta san a wani hali yake ba ba ta san yaushe ne zai dawo duniyarsu ba su cigaba da rayuwa a tare a inuwa daya.
Tsiwar Baseera ce ta dawo da ita duniyar zahirin ta daga ta tunani nisawa tayi taja murmushi kafun ta dubi mahaifin Baseera da yake tsaya yana dubanta.
"Ina yini dady".
Mariya ta fadi cikin muryarta mai sanyi da girmamawa a ciki.
Sosai yaji ta burgeshi sosai yaji yana so su kulla ƙawance da yarsa ya lura akwai natsuwa da hankali a tattare da ita.
"lafiya yau ya hakuri da aku mai bakin magana".
Murmushi ta saki don ta fahimci in da ya dosa da maganar sa kasa tayi da kai tana mai amsa masa.
"Dadyna ka ga ba ta fada min sunanta ba amma ni na fada mata".
Baseera ta fadi tana mai duban Mariya da take kallonta fuskarta dauke da murmushi.
"Yaa Allah! ta ya ya za ta fada miki bayan kin cika mata kunne da surutu Allah yasa ma tace ba za tayi kawancen ba...".
"Dadyyy!".
Baseera ta fadi da rigima a muryarta kamar zata fashe da kuka duban Mariya tayi cikin yanayi na mararecewa.
"Please don Allah fada min sunanki kin ji in ba haka ba nace ba zan yi makarantar ba ma".
Yanayin da tayi maganar da gaske take hakan ya baiwa Mariya dariya ganin da gaske take.
"sunana Mariya Bello Gwada".
"woohh so Fastastic Nice Name".
Baseera ta fadi tana mai kambama sunan Mariya.
Ya tsine fuska Mariya tayi kamar wacce aka tsikarawa allura da sauri Baseera ta ware idanu alamun tsoro tashiga tambayar ta lafiya mai ke damunta?.
Girgiza kai tayi alamun bakomai amma ita kadai ta san abin da take ji tun da ta tashi yau take jin wani iri a jikinta kamar bata da lafiya lokaci-lokaci take jin cikin ta da mararta na murɗa mata sai taji kamar numfashinta zai dauke amma ba wanda ta fadawa haka sai dauriya da take yi taki bari kowa ya gane sai dai in ya motsa mata take cizon laɓɓanta har ya lafa.
Miƙewa tayi jin mararta ta daure sosai tana faman cizon laɓɓanta sosai Baseera ta lura da haka da sauri tayi wa mahaifinta nuni da abin da Mariya take yi da sauri shima ya ware idanuwansa sosai akan ta kafun ya dafa kafadarta.
"lafiya Mariya me ke damun ki ko baki da lafiya ne?".
haɗe jikinta tayi waje daya ji take yi kamar kayan cikin ta za su zubo kasa da sauri ta durkushe kasa tana mai sakin numfashi da sauri-sauri hakan da Alhaji Haruna ya gani ya sanya shi firgita kadan da sauri ya kamo ta sosai yana mai duddubata Baseera dake tsaye kuwa jikinta sai faman ɓari yake yi idanuwanta lokaci guda suka kaɗa sukayi jajir.
"Dady what is wrong?".
Muryarta a raunane kamar mai son fashewa da kuka.
"Mariyaaa!".
Muryar Dr.Karami da karaɗe wajan lokacin da ya fito daga office idanuwansa suka gane masa abin da ya sanya shi faduwar gaba idanuwansa a warwaje da sauri yayi jifa da ledar dake hannunsa ya tako cikin sassarfa kamo ta yayi sosai izuwa lokacin har ta fara ficewa daga hayyacinta hakan da ya gani ya kara tsora tashi da sauri ya dubi su Baseera da Mahaifinta cikin yanayi na tuhuma kafun ya kau da kansa cak! ya dauke ta yayi hanyar ficewa da ita daga wajan hakan da suka gani su ma sai suka rufa masa baya wajan da yayi Parking ya isa ya buɗe gidan baya ya sakata ya rufe kafun ya dawo gaba ya shige duk abin da yake yi cikin yanayi na tsoro da fargabar abin da zai je ya dawo key yayi mata kafun ya fizgeta ya bar harabar wajan suma Su Baseera motarsu suka hau suka rufa masa baya.
Wani clinic ya nufa da ita dake kusa da makarantar cikin sauri yayi parking ya zo ya sungume ta yayi ciki da ita ba wani bata lokaci aka amshe ta kayi emergency da ita sosai Dr.Karami ya shiga tashin hankali ba abin da yake tsoro illa wani abu ya samu Mariya bai san abin da zai ce da iyayenta ba bai san da wani ido zai kalle su ba bai san a me za su dauke shi ba fata yake yi Allah ya saukaka lamarin Allah yasa ba wani abu ne ya same ta ba.
Kafadarsa yaji an dafa hakan ya san yashi tsayawa cak! daga Safah da Marwa da yake faman yi a kofar dakin da aka shigar da Mariya da sauri ya juye ya dube shi shima shi yake kallo kafun ya kau da kai bai san shi ba bai ma taba ganinsa ba amma sosai zuciyarsa ke nazarin mutumin domin kuwa abun da yafaru da Mariya a wajan su ne yana zargin su komai ya faru da ita su ne sila numfashi yaja kafun ya sake dubansa.
"Mene ne hadinku da Mariya mai kuka mata?".
Abin da ya fadi kenan muryarsa da zurfi a cikinta yana faman haɗe fuska waje daya.
Sosai Alhaji Haruna yayi murmushi kafun ya bugi kafadar Dr.karami kadan.
"Haba mana abokina karka zarge mu da komai a kan yar uwarka ba abin da muka yi mata...".
"Ta ya kake so na yarda da maganarka...".
Kafun ya dire ya jiyo muryar Baseera cikin kuka tana cewa 'Ina Mariya?'.
Mamaki ne sosai ya cika sa ya shiga duban Baseera da alamun tambayoyi masu yawo sosai yake kallonta ko zai gane fuskarta amma ina bai ga alamun sanayya ba a tattare da ita kuma bai san taba balle yace yar uwar Mariya ce.
"ya kamata ka fahimci wani abu a kan Baseera ba mu da niyyar cutar da ita kamar yarda ka ganmu a yau mu ma haka a yau mu ka fara ganin ka Baseera Da Mariya cikin wannan lokaci suka hadu na kawo Baseera zan saka ta a wannan makarantar to a nan ta gano Mariya har take cewa dani tayi ƙawa shine fa na zo ganinta har mun gaisa ma sai naga ta shiga wannan halin Dan'uwa karka zargemu da komai wallahi zuciya daya muke tare da ku ba mu da niyyar cutarwa gareku don nasan illar haka".
Tun da ya fara magana Dr.Karami ke dubansa da idanunsa sosai ya fuskanci gaskiya a cikin kalaman sa sosai ya gane mutum ne mai kamal da hankali gami da natsuwa lokaci guda yaji kunyar abin da yayi domin kuwa Alhaji Haruna zai girme masa nesa ba kusa ba.
Murmushi yayi yana sosa keya kafun ya dubi Alhaji Haruna.
"Afuwan na tuhume ku akan abin da ban san ya yake ba kuyi hakuri Mariya amana ce a waje na dole in shiga yanayi in na ganta cikin wani hali".
"kana da gaskiya hakan yayi daidai yanzu dai wani hali take ciki".
Gƴaɗa kai yayi kafun ya nisa.
"sun shigar da ita ciki domin dubata...".
Bai kai ga karasawa ba likitan da ya shiga duba Mariya ya fito yana duban su kafun ya ba su hannun suyi musabaha yana mai duban su daya bayan daya har ya dire kallon sa ga Alhaji Haruna.
"Kai ne mahaifinta ko?".
Ya tambaya kafun ya dora.
"karka damu tana lafiya lokacin ta ne yayi nasu na mata kuma bata saba ba shiyasa ta shiga wannan hali amma Alhamdulillah muyi settling din komai yanzu haka ta samu barci nan da 30mint komai zai zama normal".
Hamdala sukayi su duka kafun Alhaji Haruna ya nisa.
"Muna godiya Doctor sosai da sosai Allah ya bata lafiya".
"Ameen.Yanzu dai zan muku last na magungunar da za a sai mata tana amfani dashi".
Gyaɗa kai sukayi Dr.Karami shi dai shiru yayi yana mamaki yarda Alhaji Haruna ya zage yana nuna shine Mahaifi gareta ba tare da nuna eh da gaske ba 'yar sa ba ne hakan yayi masa dadi a rai lokaci guda yaji mutumin na burgeshi sosai da sosai.
Ko da ya dawo daga duniyar tunani mamaki ne ya sake kashe shi ganin Alhaji Haruna yabi likita Office din sa sakato yayi da baki ya duban hanya kafun ya dawo da kallon sa wajan Baseera da ta zauna ta zabga tagumi hannu bibbiyu kamar wacce aka aikowa da mutuwar wani a dangin su duk bakin surutu ya mutu kamar ba ita ba ce aku a dazu.
"Ya sunanki?".
Dr.Karami ya fadi yana mai duban ta cikin yanayi na mamakin yanayin da ya ganta aciki kuma ya san duk a dalilin Mariya ne.
Ba ta an sashi ba illa kallo da ta yi masa tana mai sauke numfashi mai kwari sosai.
"C'mon Baby girl tell me your name...ko ba kya so ƙawancen da Mariya ne".
Ba tayi niyyar ansa shi ba amma jin abin da yace ya sanya ta sauri dubansa da murmushin yake.
"Please don Allah karka hana Mariya ƙawance dani sosai nake son ta a raina a lokaci guda naji ta burgeni kuma Dadyna ya na son ta ya yaba da hankalinta sosai da sosai".
"Oya C'mon tell Now".
Murmushi ta saki ganin yarda yayi mata cikin yanayi na wasa.
"Baseera Haruna Sa'eed".
Sosai yake dubanta yana tunanin in da ya san sunan mahaifinta sosai yake zaton ya san sunan amma ya manta a ina ne ya san haka gyaɗa kai yayi kafun ya nisa fuskarsa da murmushi.
"Masha Allah to naji na amince kuyi ƙawance But...akwai sharaɗi kafun amincewar...".
"Na yarda wallahi tell me".
Ta fadi cikin yanayi na zagwadi dubanta yake yi sosai, sosai ya lura i Baseera irin mutanan nan ne masu barkwanci da wasa da dariya a ko ina suke.
"ban da wasa in an fara karatu ina so ku hada kan ku waje gudu sosai nake so naji ana alfahari da ku a cikin makarantar nan".
"Promise".
Ta fadi tana mai dariya burin ta ya cika na samun ƙawa a lokaci daya daga zuwa makaranta.
"hala tana nan tana yi maka halin nata na surutu kamar aku".
Muryar Alhaji Haruna ta yanke musu hirar tasu Murmushi Dr.Karami yayi kafun ya dubi Baseera da ta cuno baki gaba alamun ba ta so abin da dady yayi mata ba.
"Yaa Allah! Ai ba za tayi ba tayi mani alkawari dainawa in kuma ta cigaba ba zan barta ta cigaba da ƙawance da Mariya ba".
"yawwa kayi mani daidai".
"kai dady".
Baseera ta fadi fuska a shagwaɓe har sai da ta basu dariya su duka.
"ku tashi mu shiga mu duba ta ko?".
Ya fadi yana mai dubansu ai kamar jira take cikin hanzari ta mike tayi hanyar shiga dakin har tana kokarin buge Dr.Ƙarami shi kam dariya abin ya bashi shikuwa dady dafe kai yayi kawai yana mai duban Dr.Karami yana mai masa nuna da ido yayi hakuri ba ta da hankali murmushi kawai ya yi yayi gaba.
Kwance suka tadda ita sai faman sharar barci take yi kallo daya zakayi mata ka gane ta ji jiki a dan lokacin don har fuskarta ta fada sosai Dr.karami yaji wani iri a ransa ganin yanayin da Mariya take ciki ji yake yi kamar ciwon da yake jikinta ya dauko ya mai doshi nashi jikin bai son abin da zai sake taba mata rayuwa bai son abu ko ya yake ya rikita Mariya sosai yake jin tausayin ta sosai yake jin wani iri game da ita duk lokacin da take cikin hali na damuwa sosai yayi KUDIRI a zuciyarsa da ruhinsa da izinin Allah sai ya canza mata rayuwa sai ta ji dadin rayuwa sai taji dadin yan uwa sai ya zame mata yan uwan da take kwadayi a rayuwarta sai yayi iya kokarin sa don ganin ta fuskanci rayuwar 'yanci duk wani kunci da damuwa sun bar duniyar ta sai dai bai san ta yaya zai yi wannan aikin ba bai san wacce hanya bace da zai bi amma dai zai yi iya bakin kokarin sa don ganin rayuwar Mariya ta zama normal like others.
Sai da suka shafe awa daya kafun Mariya ta farko sosai da sosai take duban su da idanuwanta da suke bude runtse idanu tayi ta shiga tunano abin da ya faru da ita wasu hawaye suka zubo mata a hankali ta ja numfashi kafun ta buɗe idanunwanta Baseera ta gani kusa da ita ta mai sakin mata murmushi ta sanya hannu ta dauke mata hawayen da suke zubo mata.
"Sannu ƙawata".
Ta fadi cikin yanayi na taushin murya da jajantawa.
Ba ta ansa ba sai duban Dr.karami da tayi da ya tallaɓe haɓa ya zuba mata manyan idanuwansa masu firgita mata tunani gyaɗa kai tayi tana masa kallon tambayar me ke faruwa mai ya kawo ni nan?.
Sosai ya gane abin da take nufi amma sai ya kau da kai domin bashi da bakin da zai iya cewa ga abin da ke faruwa da ita so yake yi sai sun koma gida komai a natse sannan sai suyi magana sosai da sosai.
"ina ke miki ciwo Mariya?".
Alhaji Haruna ya fadi cikin yanayi na tausayawa gyaɗa kai tayi alamun babu.
"Masha Allah haka ake so Allah ya kara lafiya ko Mariya"
Gyaɗa kai ta yi kawai sosai take hango karamin ci irin na wadannan mutanan daga haduwa amma sun yi mata abun da wasu nata suka gagara yi mata sun bata kulawa da duk lokacin su sun tausaya mata da halin da ta shiga sosai taji sun samu matsayi mai girma a zuciyarta sosai take hango martaba da karamci tattare da su bata da bakin da zata ce da su komai sai fatan alheri.
Ba su jima cikin asibitin ba bayan dube dube da likita ya sake yi mata ya tabbatar da ba komai ya ba su sallama domin tafiya gida a tare suka fita Baseera da Dady su ka hau mota daya ba don ta so ba don cewa tayi sai dai ta bi Mariya gidan su amma Dady yace tayi hakuri zai kai ta da kan sa zuwa da yamma suna cikin wannan yanayin ne Mariya dake tsaye jingine da motar Dr.karami tana kallon diramar da ake yi da Baseera sosai taji wani abu a kafarta yana bin ta da sauri ta duba.
"Yaa Allah! Jini".
Ta fadi muryarta da karamin sauti da sauri ta dubi wajan da suke tsaye tana duban su a daidai lokacin Baseera ta dubeta ganin yarda tayi da ido ya sanya tambayar ta ko lafiya nuni tayi mata da kafarta da sauri ta iso gareta tana dubawa to da yake zata girmewa Mariya a shekaru sai ya kasance ta gane abin da ke faruwa kuma dama dazu taji abin da likita ya fadi da sauri ta dubi Dady da Dr.karami.
"Dady muje da ita gida don Allah She need help please dady".
Yanayin da tayi maganar sai ya sanya su duban Mariya da sauri don ba su gane akan me take magana ba.
Da idanu tayi musu nuni tsaf! Su ka gane ita dai Mariya kanta na kasa cikin hanzari suka shiga motar su suka dauki hanya da yake ba nisa gidansu Baseera tafiya kadan sukayi suka isa Babban gida ne kallo daya zaka yi masa ka gane mai shi yana da rufin asiri sosai da sosai get ne babba mai ruwan blue sai ratsin gold da kayi masa Horn daya sukayi aka buɗe musu gabadaya suka shige ciki bayan sun yi Parking duk suka firfito ita dai Mariya duk a tsora ce take sai faman haɗe jikinta waje daya take yi da sauri Baseera ta kama ta sukayi cikin gidan a falo su ka tadda Hajiya Abida mahaifiyar Baseera babbar mace ce mai cikar kamala da mutunci sosai ta dubi Baseera fuskarta da tuhuma.
"ba dai har kun dawo ba ina dadyn naki yake?".
Tana magana ta na duban Mariya da take haɗe jikinta kanta a kasa duban Baseera tayi da kallon karin bayani.
"later please Momy".
Ta fadi tana zarcewa da Mariya in da dakin ta yake suna shiga ta zarce da ita Toilet duk wani abun bukata sai da ta tadanar mata kafun