Showing 33001 words to 36000 words out of 227252 words
Chapter 12 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
da banza duk daya ne ta gani an aikaice akan ta anyi mata.
Hawayen da suka zubo mata ne ta sanya hannu ta dauke su sosai take gyaɗa kai ta na son yin magana amma ji tayi wani abu mai nauyi ya saukar mata a kirhi sosai take jin komai na rashin dadi na wanzuwa a gareta sosai take tuno rayuwar da tayi a makaranta da irin yarda ake korota dalilin rashin kuɗi sosai take tuno yarda ake mata gori a makaranta kowa ya gujeta ba ta da kawa ko daya domin ta fita zakka a cikin yaran makaranta kullum cikin rashin babu take ba ta ga watan da zai ya kare ba a ƙore ta ba ta ranar da zata zo har ta fadi ba a tuhume ta da rashin babu ba akan wani abun bukata a makaranta.
Kasa tayi da kai sosai take jin kuncin rayuwar da take yi sosai take hango ƙaddarar da take da wainiya da rayuwarta ita da ahalinta.
"Mariya!".
Sautin muryar Dr.Karami ta sauka cikin kunnuwanta wanda gabadaya ta mance ma da wanzuwan sa a wajan a dan razane ta dago da koɗaɗɗun idanuwanta ta sauke akan sa.
"karki ce da ni ba ki son karatu, karki ce dani maganar da nayi miki ne ta sanya ki kuka".
Kai ta shiga girgizawa sosai hawaye da sauka a kuncinta a hankali tashiga motsa laɓɓanta.
"ko daya ba ruwanka komai naka gaskiya ne mai kyau ne sai dai...".
Shiru tayi gami da yin kasa da kai sosai ya kafe da ido don ya gama fahimtar inda ta dosa da batun nata amma nauyi ya hanata fadi tausayinta sosai yake ji komai nata na rayuwa yake tausayawa.
"Karki damu Mariya nayi miki Alkawari...".
"Dr.Karami".
Sautin Muryar Dr.Aqeel ne ta katse masa maganarsa tsaye yake ya harɗe hannu a kirjisa fuskarsa kadaran kadahan gabadaya ke kallonsu sosai yake son fahimtar abin da zuciyarsa take sanar dashi sosai yake kallon yarda Mariya take kuka wanda sam bai da sauti sai na hawaye sosai ya fara jin wani iri a kasar ruhinsa da zuciya zargin Dr.Karami yake da shiga rayuwar Mariya ya kunsa mata wani abun wanda yasanya shiga damuwa sosai.
"na lura cikin yan kwanakin nan wani lamari ne yake tsakaninka da Mariya, in dai har za ku zauna tare bana taba ganinta ta tashi da dadin rai".
gabadayan su suka dubi Dr.Aqeel wanda shi kansa sai da ya tsargu sosai akan maganar da yayi duk sai yayi wani zuru zuru dashi yana faman yake.
Dr.Karami yayi murmushi domin ya rasa ina zai ajje zancen Dr.Aqeel bai fahimci in da ya saka gaba ba gabadaya tunaninsa ya tsaya akan zarginsa yake yi kenan da kuntata rayuwar Mariya? girgiza kai yayi kafin ya fara duban Mariya sannan ya dubi Dr.Aqeel.
"ce maka tayi ina takura mata hala?".
Sosai Dr.Aqeel yake nuna nadamarsa akan abin da yace ya san tabbas maganar da yayi ba ta da hurumin da za a ajjeta sosai ya shiga girgiza kai yana faman ajje yake kamar wanda aka baiea kyautar bazawara.
"Noo ba haka nake nufi ba".
Sosai su duka biyun suka kureshi da ita musamman Dr.Karami da ya fara hasaso wani abu da zuciyarsa ke sanar dashi amma yaki yarda da hakan mikewa yayi a hankali yana mai duban Mariya.
"ni zan tafi sai gobe kuma ki kula da kan ki sosai".
Gyaɗa kai kawai tayi alamun amsawa sai dai har ga Allah bata so tafiyarsa ba har a ranta tana jin dadin zama dashi amma ta lura Dr.Aqeel yana yi mata kanzagi akan hakan kamar ba ya so zaman da suke yi a tare tashi tayi tana duban Dr.Karami da yake yiwa Dr.Aqeel Sallama.
"Nagode sosai gobe Allah ya kiyaye hanya ya tsare".
ta na gama fadin haka ta gyarawa Mu'azzam kwanciya a kafadatar ta yi hanyar dakin da Ummanta take tana faman saka da warwara akan Dr.Aqeel gabadaya ta lura dashi ya fiye takura sosai duk da dai shi mai ALHERI ne amma wani lokacin abin da yake yi sam bai dace ba ya kamata ya san wani abu guda ba kowa ne zai iya daukar irin halin da yake nuna wa wanda zai san shi ba sai yaga kamar tsana ce kawai ko da ita a karan kanta ta fara dasa ayar tambaya akansa mafiya yawan lokaci in dai suna tare da Dr.Karami yana yi mata wasu abubuwa kamar natsana ita da Dr.Karami din ta rasa in ya dosa ta rasa menene nufin sa da hakan din.
Tsaki ta ja kamar harshenta zai tsinke ta karasa shiga dakin kwance ta sameta tana barci samun waje tayi ta zauna izuwa lokacin Mu'azzamn barci ya fara tafiya dashi sosai tashi tayi ta shimfiɗar dashi ta sannan ta samu gu ta zauna ta zabga tagumi ta fada duniyar tunanin mahaifinta wamda ba ta san a wani hali yake ba cikin duniyar rayuwarsa tun fitarsa kwanakin baya da yayi har yau ba alamun sa ta rasa ina ya tafi ta rasa mai yasa mahaifinta yayi mata haka ta ba so yayi misa da ita a kowani hali suka tsinci kansu tasani rashin abubuwa yana taka muhimmiyar rawa a duniyar rayuwarsu sai dai ba yarda za suyi ta sani rashin babu ne yasanya mahaifinta fita amma bai dace ace tsayin wannan kwanakin ba asan a inda yake ba har gida taje amma ta sami labarinsa ba sai ma rashin mutunci da Goggo Marka ta aikata mata da kuka ta baro gidan.
Sosai take jin faduwar gaba game da mahaifinta duk lokacin da take tunanin sa komai take ji bai mata dadi a rai ta rasa mai za tayi ta rasa mai ya dace tayi sosai kwakwalwarta ke caji wanda ita kanta ta san tunanin da take sanyawa kanta ya fi karfin kanta sai dai bata san mai za tayi ba komai a cakuɗe yake cikin duniyar rayuwarta.
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA SHA BIYU.
Sosai idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir kamar wanda aka watsawa garwashin wuta. Sosai yake jin wani zafi da zugi a kasar zuciyarsa sosai da sosai kirjinsa yana wani irin bugawa kamar zai rabe gida biyu numfashi yake ajje wa lokaci-lokaci mai tsananin zafi da zugi.
Shisha din dake girke a tsakanin kafafuwansa ya zubawa ido sosai kamar wanda yake son fahimtar wani abu game da ita a hankali ya kamo yar igiyar da ake amfani da ita ya kai bakinsa ya zuga tsayin sakanni talatin kafin ya zare daga bakinsa gami da sakin wani hayaki wanda ya turke masa fuska gabadaya ya kasance ba ka hango kansa ma sosai hayakin yake tuntulowa daga bakinsa da hancinsa sai da hayakin ya debi lokaci kafin ya tsagaita da tuntulowa sosai idanuwansa suka kaɗa har da yar guntuwar kwalla kwance a ciki.
Gyaɗa kai yake faman yi ba abin da yake yi masa shawagi a duniyar tunaninsa da zuciyarsa sai wani lamari da ya kasa gasgata shi ya rasa a ina zai ajje shi domin samun saukin raɗaɗin zuciya dana ruhi sosai yake jin nauyi a kirjinsa sosai komai ke kwance masa na tunani sosai yake jin abubuwan da suke addabarsa suna amsa kuwwa gami da sauti a kunnuwansa kirjinsa yake ji yana kara nauyi sosai numfashi ma dakyar yake samun ajjeshi.
A hankali ys ajje igiyar shisha din ya fara yinkurin mikewa wani irin nauyin kirji ya sake tokareshi daga hanzarin da ya so amfani dashi da sauri ya koma ya zauna ya na mai sakin numfashi da sauri-sauri kamar wanda aka sanyawa Oxgyen sosai yake jin bacin rai in ya tuna kalma guda da yanayin da take furtata akansa sosai yake jin ɗaci a ruhinsa akan duk kan wata kalma da ta fito daga bakinta sosai yake jin zafin tsakin da tayi masa a daidai wannan lokaci.
Mai yasa... Mai yasa mai dauki mataki tun a waccan lokacin ba, mai yasa ya bari damar ta subuce masa mai yasa yake kasa aiwatar da duk wani kudiri da ya daukarwa kansa in har yana kusa da ita ya rasa dalili.
Zancen da yake ta saƙawa kenan a kasar zuciyarsa sosai yake ganin tana yi masa kwarjini a idanuwa sosai yake kasa aiwatar da komai in yana gabanta.
Kai ya shiga girgizawa yana faman taunar laɓɓansa kamar su ne masu laifin sosai yake jin komai ya cushe masa sosai yake ganin kwanciyar hankalinsa na guje masa sosai komai ke shirin ƙwaɓe masa a rayuwa a dalilinta a matsayinta na kaskantaciya wacce bai dauka a bakin komai ba.
"Ni Huzaif ni ta wulakanta".
da sauri yake girgiza kai ya nasake furta.
"ya zama dole nasan abin yi zuciyata ba zata yafe mani ba sam! na lura da hakan".
Haka yake ta sakin zance kamar wani zararre tsayin lokaci kafin ya mike cikin karfi hali ya fada Toilet ruwa ya watsa wa kansa nan ya fito ya shirya domin ya lura in har yana zaune a waje daya komai zai iya hanashi sakat! musamman kan maganar yarinyar da yake ji a ransa ya tsana tsana mai tsanani.
*****
"Please Khairiyya!".
Ya fadi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareshi sosai yake jin zafi a zuciyarsa sosai yake jin ko ina na zuciyarsa na yayyagewa sosai kansa ke sara masa komai ya kwance masa sosai ya shiga tashin hankali mara yankewa wanda yake tsammanin zai iya tafiya da numfashin sa.
Sai da ya gama ja-in-ja da numfashin sa kafin ya daga laɓɓansa daƙyar.
"Ina cikin Matsala sosai da sosai na rasa ya zan yi komai yake kwance mani na tunani na komai zai iya faru ki taimaka ki zo".
A wannan karon muryarsa ta rage sauti sannan kuma tana rawa hannayensa duk biyun ya daura akan sa bayan ya sauke wyar daga kunnansa sosai yake jin tashin hankalin da ya tunkaro shi sosai yake jin bugun zuciyarsa na sauyawa daga kwanciya hankali zuwa akasinsa.
"ban san abin da ya sanya ni gamu da ita cikin duniyata ba, ban san abin da yasa ta shigo rayuwata ba ban san abin da yasa ranar ta zo mani a haka ba ban san mai yasa tsautsayin da nake gudu yake kokarin fado mani ba ban san gangancin da ya kai ni wannan ranar har hakan take dauko mani tashin hankali wanda ba zan iya dauka ba".
Gabadaya ya zube kan cafet din dake tsakar dakin yana faman sakin numfashi a hankali ji yake yi kamar gabadaya tashin hankalin duniya a kansa ya kare.
Marikin kofar da yaji an murza ne ya sanya shi saurin buɗe idanuwansa da suke rintse sosai yake kallonta da yanayin da ta shigo dashi kau da kai yayi gami da jan gudun tsaki wani haushi ne yaji ya tokare masa wuya ji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka sai yanzu yake dana sanin kiranta bai san dalilin da yasanya shi kiranta ba wani haushi yake ji a game da ita gabadaya yake ganin muninta da wani haushi nata yana tun karoshi mai da idanunsa yayi ya rufe.
Ita kuwa ganin irin Halin-ko-in-kula da ya nuna mata sai ta dauke kai tana mai jan tsaki a hankali ta fara taku har ta isa kan daya daga kujerun falon ta zauna kafin ta dube shi sosai kallo take masa na TUHUMA sosai take ganin sauyi gareshi sosai take ganin komai nashi ya sauya ba yarda ta san shi ba kyaɓe baki tayi kafin ta motsa laɓɓanta da suka sha Pink din jambaki.
"Huzaif".
Ta fadi a hankali tana kara kureshi da idanuwanta manya masu kalar madara sai faman kaɗa su take yi.
Bai motsa ba balle ta saka ran masawar sa sosai taji haushin haka amma bata nuna ma sai ma sake kiransa da tayi nan ma bai amsa mata ba hakan ya kara kular da ita a zafafe ta mike ta fara kokarin barin falon tana fadin.
"A rayuwa na kijin wulakanci zan iy daukar komai amma ban da wulakantawa kuma wannan zai zama karo na karshe wallahi!".
tana gama fadin haka ta rike murfin kofa tana kokarin murɗawa ta fice.
Huzaif da yake fama da zafin zuciya ya kokarta buɗe idanuwansa ya sauke akanta.
"Khairiyya".
ya fadi a raunane ita kanta sai da taji wani iri a jikinta a sanyaye ta saki kofar gami da juyowa ta dube shi tana harɗe hannayenta a kirji.
"Taimako nake bukata don Allah".
Da mamaki take dubansa tana juya maganar tasa akanta kafin ta yi taku uku sannan ta tsaya.
"Huzaif taimako fa kace?".
Kai ta shiga girgizawa tana faman sakin yaƙe.
"me ke damunka har kake neman taimako a duniyar nan?".
Ta sake fadi tana mai kafeshi da idanu sosai.
"Nima ban sani ba komai ya kwance mani kawai ji nake kamar bani ba...".
Da hanzari ta tare shi.
"Ban gane ba Huzaif?".
Tashi yayi daga kwancen da yake a hankali ya mike tsaya sosai yake kallon Khairiyya sosai yake hango zata iya taimaka masa sosi yake ganin ita kadaice zata iya yi masa komai da yake bukata.
Gyaɗa kai yayi kafin ya ciji laɓɓansa hannunta ya kamata ya fara kokarin ja da sauri ta fizge tana masa kallo mai dauke da TUHUMA shima kallonta yayi wani iri kafin ya sake jan hannun nata suka fice daga cikin falon.
******
Sosai ya zuba musu ido yana jin wani iri a gameda su gabadaya zuciyarsa ta ki yarda da su sosai gabansa yake faduwa ji yake kamar akwai mugun nufi a tattare da su sosai ruhinsa da zuciyaesa suke nuna masa shakka akansu idanuwansa sosai yake dubansu da su tun da yayi Parking a harabar asibitin ya tokare a jikin motarsa kira BMW yanayin su kawai yake kallo yake hango rashin gaskiya da kuma tashin hankali a tattare da su a hankali ya fara takunsa cikin natsuwa idanuwansa na kan su har izuwa lokacin kofar da zata sada shi da cikin asibitin ya dosa sai da ya zo daidai da su gabadayansu idanuwansu suka sarƙewa juna wani irin kallo suke duban junansu dashi kamar wanda suka san juna da jimawa zuciyoyinsu sai fama kawo musu wani lamura suke ma bambanta wanda su akaran kan su ba su na me nene ba.
Kau da kai Dr.Karami yayi da sauri yana gyara zaman niktayal din wuyarsa ya cigaba da takunsa ba tare da ya sake bi ta kan su ba har ya isa cikin asibitin.
Sannu a hankali ya fara takunsa yana ajje wa dakin su Mariya yanu fa yana kokarin sa kai itama ta sanyo kai zata yo waje kamar daga taji a kirjinsa da sauri cikin yanayi na firgici ta ja da baya tana mai zare idanu.
"Subhanallah!".
Ta fadi cikin tsanani kaɗuwa sosai take kallonsa shima idanuwansa na kanta sosai yaji wani irin Shock a ko ina na hanyar jininsa har sai da ya runtse idanuwansa domin ji yayi gabadaya kansa ya shiga juyawa kamar wanda wayar wuta ta zukar wa jini yayi low sosai
"Don Allah...".
Ta fadi tana mai rawar baki idanuwanta ta sauke su kasa sosai da sosai take jin ko ina na jikinta na sauri jininta yana kara gudu zuciyarta na kara sauti wajan bugawa.
Hannu ya daga mata yana mai sakar mata murmushi gami da lumshe idanuwansa sosai yake fuskartar natsuwar da take dashi sosai yake jin tana burgeshi duk da kananun shekarunta amma hankalinta na yanayin natsuwarta kamar mai shekaru sama da ashirin ko da yake duk wanda ya ganta ba zai taba bata haura shekaru sha biyar domin Mariya tana da tsayi da kuma kaurin jiki irin matan nan ne masu diri da cikar matantaka sosai ta ko wani fanni sosai jikinta yake bayyana irin baiwar kirar jikin da Allah ya bata ko ina na jikinta sosai ya cika sai dai ace yarinya ne a jikinta rintse idanuwansa yayi jin zuciyarsa na hasaso masa abubuwa ma bambanta da sauri ya zare tunani ya ajje gefe yana mai sauke numfashi.
"Yaa Allah! Mariya zaki fasa min kirji ko".
Ya fadi yana mai haɗe girarsa kamar gaske yanayin da ta dan razana ta dago kamt da sauri tana kallonsa lokaci guda idanuwanta sukayi rau-rau kamar za su zuvda hawaye.
"Don Allah...".
Da sauri ya kai dan yatsarsa bakinsa gami da furta.
"Shiit".
Yanayin yarda yayi salon sai ta saki baki tana kallonsa sosai taji ya burgeta da yanayin da murmushi ya sauka a fuskarsa ta tabbata wasa yake yi mata kasa tayi da kai ta dag laɓɓanta.
"Ban sani ba, ban san kana taho wa ba na rokeka...".
"Nace kiyi shiru mana!".
Ya fadi muryarsa da dan sauti a cikinta. Gyaɗa kai ta shiga yi tana kokarin giftashi ta wuce ya tae ta da cewa.
"Ina kike kokarin zuwa?".
Shiru tayi tama rasa mai za tae dashi sai juya faka din dake hannunta take mai dauke shara.
Sosai ya gane in da ta dosa amma so yake yi tayi magana da kanta amma ya lura magana ma wuya take mata
"koma ciki to tunda ba in da zaki".
Da sauri ta dago kanta tana kallonsa yanayin da taga ya ci mur ta san da gaske yake baki ta fara motsawa.
"Shara...".
Abin da ta fadi kenan ta tsuke bakinta ta sake yin kasa da kai tana cigaba da wasa da fakar dake hannunta gabadaya taji gajiya na saukar mata sosai ta matsu ta bar wajan amma ta lura Dr.Karami sai ya ga kafarta ta zubda ita kasa sannan zai rabu da ita.
"Ya jikin Umma?".
"Da sauki".
Abin da ta fadi kenan domin ta lura in dai yayi magana bata amsa ba hakan ne zai sanya ya hanata tafiya.
"Madallah! zaki iya tafiya".
Kamar wacce take jira da sauri ta fara jan jikinta har tana kokarin tuntuɓe sosai yake kallonta yana kallon yarda take ajje taukunta duk da dai cikin yanayin tsoro take amma hakan bai hana bayyanar da natsuwa a takunta ba sai da ya ga fitarta sannan ya numfasa ya karasa shiga dakin.
Tunda Mariya ta fice take gayyato natsuwa tana yafawa kanta sodai tsoro da kunyar Dr.Karami suke samun mazauni a zuciyarta sosai komai nashi yake burgeta sosai take jin wani iri in suna tare sosai zuciyarta ke natsuwa in suna tare amma a zahirince tsoro ne ke bayyyana a fuskarta ta rasa dalili ko da yake zata iya ajje hakan a matsayin Kwarjini da yake mata sosai musamman yanayinsa da cikar halintar mazanataka da yake dashi sosai take jin wani iri in tana gabansa sai ta raina kanta sai taga kamar dan tsako ne a gaban rakumi.
Har tasa inda za ta zubda sharar bata daina zancen zuci ba saura kadan ta afka cikin dan wajan da aka tanada don zubda shara ita kanta sai da taji