Showing 57001 words to 60000 words out of 227252 words
Chapter 20 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
sosai taji wasu katangun tashin hankali suna kokarin rikito mata akai wani kuka mai karfi taji yana kokarin kufce mata bakin ta na rawa ta shigo kokarin amsa musu amma hakan ya gagara da gudu tayi hanyar Toilet din dakin hannayenta rufe da bakin ta kuka sosai take jin yana taho mata ta na shiga ta mai da kofar ta rufe durkushewa tayi a tsakiyar Tiolet gami da sakin wani irin kuka mara sauti mai matukar taba zuciya da ruhi da duk wani mai jinsa.
Sosai Dr.Karami yaji gabanda ya buga yanayin da ya ga Mariya a ciki idanuwansa ya sauke kan Umma da tayi kasa da kai sosai take jin wani iri a zuciyarta raunin da ta gani game da 'yarta ya haifa mata da tausayi mai girma a zuciya ta sani 'yarta ta shaku da su sosai shakuwar da sai anyi dagaske kafun a rabu dole zuciyoyi su shiga halin damuwa dole gangar jiki su shiga hali na rashin jin dadi sosai da sosai.
Kallon kallo suka shiga yi tsakanin su Dr.Karami da Dr.Aqeel sosai suke jin wani iri a zuciyoyin su musamman Dr.Karami don ji yakeyi kamar ya falla da gudu ya bita ya rarrashe don ya san tabbas ba abin da yake damun ta sai maganar rabuwarsu ba tun yau ba ya lura sosai take nuna dauwa da tsoro duk ranar da ya yi mata maganar rabuwar su bai san abin zai yi tsanani haka ba ko d yake shi tashi zuciyar yanzu haka ciwo mai girma yake jin yana fama dashi jarumta ce kawai take hana shi bayyanar sirrin dake ransasosai yake kewar Mariya duk da dai a ransa ba ya tunanin rabuwa za suyi ba ya hangowa rabu sam-sam cikin wannan lamarin amma dai yau a wannan rana shi a karan kan sa yana jin ba dadi don ji yake yi kamar wanda ya tashi daga cuta saboda rashin kwarin jiki.
Duban Dr.Aqeel yayi wanda shi dai yanayin ya nuna akwai abin dake damun sa a ransa sosai da sosai fuskarsa ta nuna rashin walwala jikinsa yayi sanyi sosai idanuwansa sun kada kadan kamar mai son fashewa da kuka.
Ba tare da yayi masa magana ya doshi kofar Toilet yana kwankwasawa a hankali yana kiran sunanta sosai yake jiyo shasshekar kukanta wanda haka ba karamin taba masa zuciya yayi ba sosai yake jin tausayi da wani abu mai matukar girma suna wanzu a filin zuciyarsa a hankali ya cigaba da kwankwasa amma ko alamun za ta yi magana juyowa yayi ya kalle su suma shi suke kallo musamman Umma wanda ta gama karantar yanayin su su duka sosai take jin tausayinsu duk su ukun na samun waje a zuciyarta ji take ina ma tana da wata dama da zatayi amfani da ita domin fidda su cikin wannan yanayi amma ina! ta san ba ta dashi gyaɗa kai tayi tana kau da kai daga barin kallon Dr.Karami.
A hankali ya rike Handle kofar ya turo sai ya ganta abude take da sauri ya karasa turawa yana mai sanya ƙafafuwansa da yake ji kamar za su zubda shi kasa saboda raunin da ya ji sunyi sosai.
Durkushe ya hango ta hade jikinta waje daya sai faman jan numfashi take yi mai zafi sosai zuciyarta take jin tana wani irin harbawa kamar zata faso kirjin ta ta fito waje komai take ji yana kwance mata komai na cikin duniyar take ji yana sauya mata lokaci guda.
"Mariyaaa!".
Ya fadi muryarsa da wani irin rauni mai girma idanunwansa a kan ta a hankali ta shiga kokarin dago idanunta da suka kaɗa sosai sukayi jajir kamar wanda aka watsawa barkono wani irin bugu zuciyarsa tayi wanda hakan sai da ya sanya shi sanya hannu ya dafe kansa duniyar yaji tana juya masa lokaci guda kau da kansa yayi don ba zai iya kallon idanuwanta a yarda suke ba wasu abubuwa ne masu girma yake ji game da kallonta suna faru dashi a filin zuciyarsa.
"Ban san mai ya kike haka ba, ban san mai kike wahalar da kan ki haka ba, Haba mana Mariya mai yasa kike zurfafa lamarin nan haka rabuwarmu ai ba ta na nufin mun rabu har abada bane a,a muna nan tare a duniya daya har zuwa numfashinmu na karshe."
Ba ta san ya zata dauki maganar ta sa ba bata san ya zata daura su a MIZANIN HANKALI ba sosai take jin zuciyarta taki aminta da zancen sa sosai take jin kawai fadi yake yi domin ganin ta daina kuka rintse idanunta tayi kafun ta mike kan kafafuwanta cikin wani irin yanayi mai rauni.
"Ta ya ya kake so na anshi maganar ka ta ya ya ka ke so na gasgata abin da kake cewa bayan nasan dole mu rabu dole mu raba duniya bana zaton maganganunka za suyi tasira Yah Dr.Karami kawai ka fito fili kace mani yau ce rana ta karshe a duniyarmu da muka hadu yau ce rana ta karshe a garemu yau ne za mu rabu da juna...".
Wani irin nishi tayi kafun ta gyaɗa kai hawaye su zubo mata wanda Dr.Karami yake jin su kamar saukar ruwan zafi a jikinsa.
"Ban san ko zaka yi maki alkawaro ba sosai na yi sabo da kai a duniya ta ban sani ba ko za kayi mani adalci a duniyarka ka kasance dani mu ke mutunci ba zan taba mance alherin ka ba kai da sauran Al'umma sosai nake hango matsayin ka a matsayin dan uwa na jini ban da yan uwa so nake ka zama dan uwa gareni ka kasan ce mani dan uwa bayan Mu'azzam don Allah in kayi mani haka zan yarda kuma zan rike duk abin da kace mani in har ka rike mani abin da nace da kai".
Rintse idanu yayi sosai zuciyarsa da kwakwalwarsa yake jin suna wani shawagi dashi a wani mataki wanda bai taba jin kan sa a ciin sa bai san mai zai ce mata ba bai san wani kalamai zai yi amfani da su wajan yi mata magana ba abu daya ya sani shine ba zai iya rabuwa da ita ba zai so ace yarda take maganar nan shim ya fadi mata shima haka yake ji ransa kamar yarda take ji.
Nisawa yayi kafun ya kokarta dubanta yana sani murmushi mai karfin gaske.
"Na yarda tuni na yarjewa zuciya ta zan ci gaba da zama dake a duniyata har zuwa karshen numfshi ne na yarda na aminci da maganarki na rike miki alkawari ke ma ki rike mani kamar yardakika fadi".
Shafe hawayenta tayi kafun ta saki wani murmushi kamar yarda ta ga yanayi mata.
Alamu yayi mata da kai su fice daga Toilet din tana yatsine fuska alamun kyankyami kunya taji kai a kasa ta bi bayan sa zuciyarta na rake duk wani nauyi da ya tokare mata kirji tun lokacin da aka sanar da su sallamar su da akayi.
Bin su sukayi da kallo Umma ta dubi Mariya tana harararta kasa tayi da kai kafun ta dubi Dr.Aqeel wani kallo taga yana yi mata wanda sai da ya sanya gabanta bugawa da sauri tayi kasa da kai tana cizon laɓɓanta abubuwa da yawa suna rikita mata kwakwalwa a tsakanin Dr.Aqeel da Dr.Karami abubuwa da yawa take hangowa a tsakanin su wanda ta kasa gane menene iya tsayin tunaninta da tsayin lokacin da ta diba tana nazarin su ta kasa gane mai suke nufi da wasu abubuwa da ta lura suna yi mata....
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA SHA TARA.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'una mai nake shirin gani ni marka? Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!!."
Goggo Marka dake zaune bakin kofa tana kadin zarenta ta mike tana tafa hannaye tana fadin haka idanuwa warwaje lokacin da ta ji sallamar su Mariya jikin ta har ɓari yake yi ta shiga dubansu kamar wanda ta ga wani mugun abu.
Cak! Suka tsaya suma suna dubanta musamman Mariya da idanuwanta su kayo waje tana duban ta ganin yanayin da ta nuna juyawa tayi ta dubi Umma kafun ta sake mai da kallonta zuwa wajan Goggo Marka.
"Mariya Habeeba daga ina kuma haka?".
Ta fadi cikin yanayi na mamakin ganin su.
Suma mamaki ne ya cika musu zuciya sosai da sosai sun rasa abin yi gabakidayan su sai bin ta da kallo kawai suke yi suna faman gyaɗa kai a hankali Mariya ta ja jiki a sanyaye ta isa bakin kofar dakin su da yayi kaca-kaca kamar wani kudundubi kofar dakin su har an girgiɗe ta labulan kuwa an yi fata-fata dashi ta na hango tsakar dakin yarda ya zama kamar wajan wasan yara sosai taji ranta ya sosu matuka gaya tsaki ta ja kadan kafun ta ajje kayan da suke hannunta wani irin duba tayi wa Goggo Marka da tayi tsaye fuska cike da mamaki sosai Hafsi da ta fito da daurin kirji kai ba dan kwali gashin kan nan nata yayi wani kerere kamar dambun karangiya sai fama yawatawa da idanunta take tsakanin Umma da Mariya cikin yanayi na mamaki kallo daya zakayi mata ka gane a firgice ta fito daga cikin dakin barci ne a idonta.
Kau da kai Mariya tayi kafun ta isa in da Umma tayi tsaye kamar wacce aka dasa kallo daya zakayi wa fuskarta ka gane bacin ran dake kunshe a zuciyarta ansar Mu'azzam tayi ta goya sannan ta dubi Umma tana mai rike mata hannu suka baro wajan suka iso kofar dakin nan bari ta samu damar dan gyara wajan sannan ta dauko zani cikin kayansu ta shimfiɗa wa Umma ta zaunar da ita daga nan ta shiga dakin tsaye tayi tana bin sa da kallo wani haushi da takaici gami da tukukin bakin ciki suka cika mata zuciya sosai take ganin yarda dakin ya sauya gabadaya kamar dakin mahaukata kallo take tana tunanin ta ina ma zata fara gyaransa don ta san tabbas wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba haka kwafa tayi sannan ta fito daga cikin dakin Umma ta duba cikin yanayi na damuwa.
"Bari na siyo tsintsiya Umma domin wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba dole a gyara shi".
Gyada mata kai kawai tayi itama ba tare da ta sake cewa komai ba ta duba cikin kayan su gudan duba ta dauko cikin kudin da Dr.Aqeel ya bata ta fice daga cikin gidan bisa mamaki har yanzu suna nan ba su tafi ba baki ta saki tana duban su kafun ta taka ta isa wajan su.
"Uhmm wai har yanzu...".
sai kuma tayi shiru ba tare da ta karasa abin da tayi niyyar cewa ba ganin irin kallon da Dr.Karami yake yi mata na alamun tuhuma.
"ina zaki je kuma da wannan ranar daga dawowarku?".
Shiru tayi kamar ba za tayi magana ba can ta nisa.
"tsintsiya zan sayo dakin zan share yayi kura ne sosai da sosai ba zai zaunu ba".
ta karashe tana mai yatsine fuska kamar za tayi kuka sosai take jin wani iri a ranta ba ta so ta fito ta tadda su ba ba ta so a wanna lokacin ta sake saka su a idanuwanta ba ta so ace yarda ta baiwa zuciyarta hakurin kewarsu na dan lokacin nan suma sun yi hakan sun tafi ba za ta so wani sabon lamari ya sake afkuwa ba a nan wajan domin ba zata manta tsawon lokacin da suka shafe a nan wajan ba tun isowarsu ake abu daya sai da Umma tayi da gaske sannan suka shiga cikin gidan bayan sun yi sallama amma kuma abin mamaki ta fito ta tadda su.
"Bari naje na sayo Umma na jira na".
Ta fadi cikin yanayi na damuwa domin ba za iya tsayuwa tana kallon su ba sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗi ba ta jira cewarsu ba ta fara tafiya cikin yanayi na sanyi jiki sosai ko da ta isa shagon mai tazara kadan da gidan su makalewa tayi taki dawowa tana hango su ba ta ga alamun suna da niyya tafiya ba sam! ita kuma ba ta so su sake gamuwa a cikin halin da take ciki a yanzu so take ta bai wa zuciyarta hakuri so take ta fara koyon zaman kadaici tun yanzu don ta san tabbas dole wata rana su dau lokaci mai tsayi kafun su hadu kuma ya zame mata tilas ta yi abin da Ummanta ba za ta shiga damuwa ba dole ta kau duk wata damuwa a zuciyarta don ganin walwala ga Ummanta.
Numfashi taja kafun ta hango sun shiga motarsu ta lura sosai kamar sun damu da rashin dawowarta kuma ta san saboda su taki dawowa don haka suka yanke hukunci tafiya hakan yayi mata dadi sosai da sosai sai da taga sun fice daga layin su sannan ta tako cikin sarsarfa domin a tunanin ta kila su dawo.
*****
"Mun shiga uku".
Cewar Hafsi tana daura hannu akai idanuwa warwaje kafun ta sake jan numfashi mai dauke da tashin hankali.
"ki ka ce mani sun tafi kenan har abada ba za su dawo ba, amma kuma ga su sun dawo kuma kin ce mani Habeeba ta zama MAHAUKACIYA amma dube ta kalau ba alamun hauka a tare da ita".
Goggo Marka da ta yi zaman yan bori kofar daki ta zabga tagumi tana duban Habeeba da ɗan dake hannunta wasu katangun tashin hankali taji suna rigizo mata akai ji take yi duniyar na juya mata ba ta yi zaton haka zata faru ba bata taba kawo hakan akan ta ba ta yi zaton sun tafi kenan ko duriyar su ba za a sake ji ba a duniyar nan tuni ta saki jiki take shan sharafin ta ganin lokaci sai tafiya yake yi kuma ba su dawo ba hakan ya kara gasgata mata zatonta amma yau rana tsaka irin wanna mugun abu ya zo mata wani numfashi taja ta fesar kafun ta dubi Hafsi murya kasa-kasa domin bata so Habeeba ta ji maganganun da suke yi.
"tuni fa aka tabbatar mani da ta haukace ita da 'yar ta ta da mijin nata...".
Da sauri Hafsi ta katse ta.
"Injiwa ya fada miki to wallahi duk wanda ya fada miki hakan karya ne ki dube su fa su duka kalau suke ba abin da ke damun su".
Nisawa tayi ta kai hannunta ta na susar kanta.
"ina ganin mugun abu kenan da gaske Habeeba ba hauka tay...".
Sallamar da Mariya tayi ne ya katse musu hirar da suke yi sukayi wuri-wuri da ido alamun rashin gaskiya kallo daya tayi musu ta kau da kanta a jikinta take ji akwai maganar da suke yi wanda ya dangance su kunuwanta sun jiyo mata kalmar hauka da Goggo Marka take fadi a zancen hakan ya tabbatar mata da Ummanta suke yi wato hauka tayi kenan daukar ta suke a matsayin mahaukaciya wani kunci taji ya tokare mata kirji sosai taji ranta na ɓaci amma sai ta share su ta baiwa banza ajiyarsu ta isa in da Umma kenan zaune ta zabga tagumi da alamun ita ma ta ji hira da suke yi a kanta don idanunta har sun tara kwalla kadan.
Sauko da Mu'azzam tayi barci ya ke yi hankali kwance a haka ta mikawa Umma shi ba tare da tace da ita kala ba ta dauki tsintsiyar da ta sayo ta shiga dakin a hankali ta fara tattara kayan su waje daya ta na fitowa da su waje zuciyarta na kunci da bakin ciki sosai take jin tausayin kan su sosai take hango irin kalar zaman da za suyi a gidan nan duba da tayi da halin Goggo Marka yana nan yarda yake ba sauyawa tayi ba sai abin da ya ci uban na da sosai take ganin za su fuskanci yanayin rayuwa a gidan musamman yanzu da suka kasance su kadai ba mahaifinta wanda shi kadai suke samun sauki a wajan sa to yanzu baya nan Allah kadai yasan halin da za su shiga cikin wannan halin ta hau tsaftace dakin yayi kura sosai bayan ta kwashe komi ta samo ruwa ta yayyafa a dakin saboda ba simitin in tana sharewa kuma kura na tashi sosai a haka cikin jarumta ta kammala sharewa sannan ta fito ta barshi ya sha iska kayan su ta ajje su gefe domin sun yi datti sosai suna bukatar zama na musamman domin wanke su sai da ta zauna ta huta sannan ta sake fita ta sayo kayan wanki sabulu da omo ta zo ta ja ruwa sosai ta jika kayan duk abin da take yi akan idon Goggo Marka da Hafsi sai faman bin ta da kallo suke suna faman yatsine fuska kamar sun ga abin kyankyami..
*********
Satin su Mariya biyu da dawo gida izuwa lokacin mutanan unguwa da yawa sun san sun dawo ana ta zuwa musu barka da arzuki da kuma ya mai jiki a nan suke samun labari wajan mutanan gari wai ai Habeeba hauka cewa tayi ta shiga duniya tun da ta haihu cutar hauka ta same ta ba a san in da take ba Mariya da babanta kuma suma sun ba zama duniya ne neman ta tun da suka tafi ba labarin su.
Abin yayi matukar daurewa Umma da Mariya kai sosai suka ji a ransu bisa wannan mugun fata da akayi musu na halaka ko daya ke ba suyi mamaki ba tun da sun san halin wacce ta kulla musu wannan makircin kadan daga aikin ta.
Ba su ce da ita komai ba sai dai suka barta da Allah domin kuwa halinta yafi karfin su.
Kamar ko yaushe yau ma Mariya na goye da Mu'azzam tana dauraye musu kayansu domin tun da suka dawo ko tsinke ba ta bari Umma ta dauke komai ba ita take yi rainon Mu'azzam duk yana wajan ta tun da ba nono yake sha ba sai madara anyi anyi amma ina yaki kamawa ko ya kama ya fara sha sai ya saki dole ta kasance madara ake bashi.
"Mariya".
Ta jiyo muryar Umma ta na kiranta da sauri ta ajje wanki tana amsawa ta doshi dakin.
"Yawwa yar Albarka amshi nan maza ki je gidan kultum ki sayo mani tafarnuwa".
Da mamaki Mariya ta dubeta.
"Umma Tafarnuwa kuma, me zakiyi da ita?".
"Yaa Allah! Mariya kenan. ba fa wani abu bane zan yi da ita kawai kafafuwa na ne naji suna rikewa na san kuma sanyi ne ba wani abu ba shine fa zan yi amfani da ita".
dan tsuke fuska tayi