Header Ads
Showing 150001 words to 153000 words out of 227252 words

Chapter 51 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1394

Ads at the middle of Article

masa baya illa Goggo Marka da Hafsat dake tsaye suna duban su da wani irin yanayi da nuna halin-ko-in-kula ga lamarin Umma kuwa cikin gida ta koma ta dauko mayafinta ta yo waje ko kafin ta iso ba wanda ta tadda nan ta jin gina da bango tana faman ajiyar numfashi mai zafi kafin ta rintse idanuwanta ta buɗe su.
"Allah ga bayinka kai ka san abin da yake damun su a filin duniyar nan kayi musu maganinsa".
Tana gama fadin haka ta juya cikin gida cikin yanayi na rashin tabbas din 'yar ta ta domin kuwa ta san ko sun kaita asibiti sai dai su dawo da ita domin tuni ta tabbbatar Mariya ta shuri burji rai yayi halinsa.


*_Ina bukatar ra'ayoyinku Makaranta da duk wani masoyina na labarin nan kafin muje ga cigaba ina so duk ku antayo min wani tsokaci game da labarin da ya danganci sharawa ko gyara_*
*_KAMALA MINNA_*😍😍😍
[9/6, 1:59 PM] DEENY MINNA🙋‍♂: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA DAYA.




Saura kadan Hafsat ta bangaje Umma lokacin da ta karasa cikin gidan. domin a soro ta tadda ita, tana faman leken duk abin da ke faruwa.
Dubanta tayi kafin ta girgiza kai, ta wuce ta cikin yanayi na kunci da bakin cikin halin-ko-in-kula da halin ƙi da suke nunawa ga 'yarta musamman Hafsat da ƙiri-ƙiri ba kunya ba tsoron Allah take fitowa fili ta fadi mugun nufi akan Mariya da wannan tunanin ta isa ciki gidan.
zaune ta hango Goggo Marka kofar dakinta tana faman ɓarar gyaɗa tana tauna tana wakar barmana coge ganin Umma ta shigo ya sanyata yin shuri tana dubanta.
"Ai kawai aje a sanar da jama'a da Malam Nata'ala, domin yin jana'izarta tunda an shuri burji".
Wani tuƙoƙine da bakin ciki ya tokarewa Umma wuya lokaci guda a rana daya yau taji bazata iya shanye wannan cin zarafin da cin fuska da ake yi mata ita da 'yarta ba dubanta tayi ƙwalla cike da idanu.
"ai ƙaddarar mutuwa tana kan kowa kuma wanda ya mutu da da yanzu duk ba hanzari sukayi ba wajan barin duniya".
Wani uban ashar Goggo Marka ta danno kafin ta miƙe jikinta har ɓari yake yi saboda tsabar masifa kamar jira take yi tayi mici-mici da idanu zanin jikinta har yana kokarin kwancewa ta watsar da gyaɗar dake hannunta.
"Ni kike fadiwa haka Habeeba eh lallai duk mai sauran rai a duniyar nan yana DA SAURAN KALLO ke har kin yi bakin da zaki yaɓa mani magana ke har kin isa".
Ta shiga sababi har ta isa gare ta tana dungure mata goshi a daidai lokacin Hafsat ta iso cikin gidan jin hayaniyar Goggo Marka ganin abin da ke faruwa ya sanyata hanzarin karasowa tana duban Umma uku ahu tana faman yatsine fuska kafin ta ja dogon tsaki kamar harshenta zai tsinke ta ja hannun Goggo Marka suka bar wajan tana mai fadin.
"yo ana tara kartan mazaje ba dole mutuwa tayi hanzarin zuwa ba tunda jaraba da masifa ta cika zuciya ko wani kare da doki nata ne mu dai Allah ya tsare mu da kamayamaya kar ajona mana mu tafi wajan likita yayi ta aunamu kamar yadi".
Mamaki ne ya cika Umma jin furucin da 'yar cikinta kamar Hafsat take fadi mata duk da dai bashi ne karon farko ba da ta fara dubanta tana mata izgilanci da kalamanta amma taji maganar yau sosai har kokwan ranta girgiza kai kawai tayi ta ja kafafuwanta da taji suna kokarin gagarar daukarta ta shiga cikin daki cike da tashin hankali mara yankewa abun ya zame mata GOMA DA ASHIRIN a filin duniyarta.
*******
Kai kawo kawai suke yi a Reception ɗin asibitin gabadaya hankalin su a tashe yake in ka zare Dr.Karami da yafi kowa fidda tsammani dafatan samun Mariya a yarda ya dauko ya saka a mota ya tukota zuwa asibiti ba tare da ta yi ko da motsin ba hakan ya kara hautsina masa tunanin kwanya ya firgita masa duk wani fata da burin da yake dashi akanta yayi dana sani da takaici kuma akan abin da yayi na rashin bayyanar da abin dake zuciyarsa tun kafin lokaci ya kure masa sannan ya ga bakin kansa akan yarda komai ya hautsine komai ya dakule duk a gabansa ba tare da yayi wani fata ko yinkurin yin wani abu ba ya sani Mariya zata tsane shi tsana mai tsanani a filin duniyar nan dalilin kin bata dama da yayi abin ya zame masa goma da ashirin ya tabbata har da zancen Baseera ya so kashe ta yasani zata dauke shi a wani dan ta'adda makashin rai cikin wahala ba tare da cuta ko samun matsala ba.
Bai san ya lamarin zai zo masa ba amma ya tabbata sai yafi kowa shan kashi a cikin su dole ya fuskanci kalubale mai tsaurin gaske dole ya fara tanadar makaman yaki domin guntule duk wani abu da zai kawo masa hari na kalubalen da zai fuskanta.
Numfashi yake ajjewa a hankali kamar wanda ranshi yaso barin jikinsa daga baya ya tsaya kuma yake mai da numfashi duban su yake yi daya bayan daya yana ajjewa kowannen su kallo na irin yarda yake jin kowannan su a zuciyarsa da Dr.Aqeel suka hada ido ya jefa masa kallon takaici kafin ya kau da kai lokaci guda cike da bugawar zuciya.
Motsin buɗe kofar da akayi ne ta dakin da aka kargame Mariya a ciki ya sanya dukkaninsu mikewa kan kafafuwansu cikin hanzari da firgici na rashin abinda za a zo dashi a matsayin sakamako a junansu.
Dr.Karami ya fara tarar likitan da ya fito yana faman sharce gumi kafin ya dubesu su duka da yanayi na rauni na sosai.
"Kai ne Dan'uwanta?".
Likita ya fadi yana mai duban Dr.Karami da ya iso gareshi a hargitse kamar mahaukacin da ya balle daga gidan mahaukata.
Gyaɗa kai ya shiga yi yana faman nishi kamar wanda akayi wa dole.
Sosai likitan ke dubansa yana son gane tashin hankalin da yake ciki bai gama yanke hukunci ba yaji an kwala masa kira kamar daga sama da sauri ya juya Nurse din da suka shiga tare ne ta yafito shi da dan razana a fuskarta da sauri ya juya cikin sassarfa yana kokarin tura kofar Dr.Karami ya sanyo kai shima zai shigo amma sai likitan ya dakatar dashi ta hanyar yi masa kallo gami da girgiza kai sa'annan ya mai da kofar ya rufe.
Dr.Karami ji yayi kamar ya kurma ihu inda yana da raunin zuciya ba abin da zai hanani shi rushewa da kuka domin yanayin da yake jin zuciyarsa ahalin yanzu yafi komai ciwo ji yake yi zuciyar kamar ba tashi ba ba abin da yake yawo a ciki illa wani irin tausayi da mahaukacin son Mariya ji yake yi kamar ya kwato duk wata cuta da take kokarin kashe masa ita ya dawo da ita jikinsa ko zai samu burinsa da fatansa ya tabbata a filin duniyar nan haɗe kai sa yayi da bango yana faman numfashi kamar wanda yayi gudun ceton rai ko da yake za a iya kiran hakan da gudun ceton rai don yarda yake wassafa abin kamar tashin alkiyama yake kallo duk wani tashin hankali da yanke tsammanin farin ciki ya tabbata akansa a daidai wannan lokacin.
Ji kawai yayi kafafuwansa na kokarin kasa daukarsa bai san lokacin da ya sulale zuwa kasa ba ya zauna kamar wani kayan wanki idanuwansa yaji suna wani yaji-yaji zuciyarsa na zafi da raɗaɗi a hankali ya fara ambaton sunan Allah a bakinsa yana faman sakin huci mai zafi.
Shigar likita cikin dakin ya tadda Nurse gaban na'urar da take tafiyar da yanayin wanzuwan numfashin mara lafiya da sauri ya isa wajan ganin numfashin da ya samu ya kwato da kai da taimakon Allah yana kokarin kufcewa aka karo na ba adadi da sauri ya isa wajan yana duban na'urar kafin ya sauke dubansa kan Mariya dake kwance sambal wacce bata da mara da gawa ga Oxgyen da yake kargame a hancinta a hankali ya kai hannunsa saitin makoshinta da kirjinta yana tabawa komai yaji ya sauya ba a yarda ya barshi ba idanu ya zaro kafin ya sake duban na'urar wacce take nuni da numfashin yana kara samun ragwanta da sauri ya zaro abin auna mara lafiya ya jona mata a kirji kafin ya soka abin a kunnuwansa lokaci guda ya zare ya isa ga na'urar yana tabe tabensa tun yana yanke tsammanin samuwar komai har ya fara firgita da yanayin numfashin da sauri ya isa ga Mariya yana dubanta ita kanta Nurse din abin ya fara fidda mata da tunani daga kai da sauri ta iso wajan tana duban likitan kafin tayi wani yinkuri wanda take fatan samun daidaituwar komai likitan ta kalla wanda ya gama firgita sosai a hankali takai hannayenta saman kirjin Mariya ta shiga dannawa da sauri-sauri a daidai lokacin Na'urar tayi dan kara tafiyar numfashin ya fara canzawa cikin yanayi na farfadowa daga suman da yayi hakan da Nurse din ta ga ya bata daman saurin cigaba da danna kirjin Mariya kamar zata burmasshi ita da gadon shi kuwa likitan gaban Na'urar ya isa ya shiga dube-dube yana kokarin saita komai.
Lokaci mai tsayi suka dauka suna abu daya gabadaya sun gama hada gumi da fidda tsammani da fata akan Maryia domin tafiyar numfashin ma yaki gaba yaki baya iya kokarin su sun yi amma abun ya ci tura lokaci guda fuskar Nurse din tayi rauni kamar wanda zata fashe da kuka danna kirjin Mariya take yi zuciyarta na kara karyewa da rauni mai girman gaske hawaye lokaci guda suka shiga zubo mata ba ta bi takan su ba illa kokarin na ganin ta ceto numfashin wannan baiwar Allah a hankali ita kanta numfashin nata da kirjinta su fara sauyawa da bugu ganin numfashin ya fara yin kasa ta tabbata yayi kadan gabadaya sai dai wata amma ba Mariya ba kokari ta kara kalatowa da jarumta ta shiga dannan kirjin Mariya tana duban Likita da komai yake shirin wargaje masa kamar ƙyafta idanu Na'urar ta saki wani sauti lokaci guda numfashin ya shiga tafiya da sauri-sauri yana cike gurbin da bai kai ba lokaci guda ya dawo yarda ake so Mariya dake yashe Nurse na danna mata kirji wani yin kuri tayi kamar wacce aka bugo kasan gadon tayo sama sannan ta koma ta sake yin wani yinkurin kafin nan ta koma da sauri Nurse ta shiga rirrike ta.
Gwauron ajiyar numfashi likita yayi yana dauke gumin da ya tsatsafo masa a fuska kafun ya iso ga Mariya da take ta faman jan numfashi ta hanyar Oxgyen dubanta ya shiga yi kafun wani lokaci yayi kokarin ganin komai ya daidaita duban Nurse yayi tare da yi mata jinjina ganin yarda tayi firgai-firgai da ita kamar wacce ta kwato kanta daga bakin kura.
Ya jima yana bakin kokarinsa kafun ya saita komai sannan ya fice daga cikin dakin.
Da hanzari Dr.Karami ya mike daga yashen da yake gefen guda yana faman cizon laɓɓa kamar mace mai nakuɗa sosai yake duban likitan cikin yanayi na tabbacin abin da zai fada masa mai dadin ji ne ko sauraro sosai tsoro da firgici su ka bayyana a idanuwansa kirjinsa da zuciyarsa sautin bugunsu yana ansa wa cikin gangar jikinsa ruhinsa kuwa ji yake yi kamar ya shuri burji ya bar jikinsa ya zama matacce.
Sai da ya gama firgicinsa yana ta faman jan numfashi magana yake so yayi amma ya kasa sai haɗe hannayensa yake yi waje guda yana matsewa yana faman mazari kamar wanda ake kaɗawa gangi shi kansa likitan tsayawa kallonsa yayi sosai ya fuskanci akwai wata alaƙa mai karfi tsakaninsa da Maras lafiyar wanda hakan ya kasa boyuwa a gareshi.
"Doctor don Allah...".
Furucin da Baseera take kokarin yi kenan lokacin da ta hango fitowar likita gabadaya ta gama firgicewa sai faman jan numafshi take yi bakinta na ɓari ta hadiyi yawu mai tauri kafin taja fasali ta sake dubansa tana goge hawayen da suke ta faman ambaliya a fuskarta.
"Karka ce mani ta mutu domin kuwa ba wai ita kadai ta mutu a filin duniyar nan ba akwai rayuka masu muhimmanci a duniyarta da za su salwanta wanda kuma har dani bana tunanin zan iya juri da yin TAWAKKALI in Mariya ta zarce in da ba a dawowa domin na tabbata ba zata yafe mani ba na tabbata ina da laifi mai girma wanda na san zuciyarta ta kunsa kuma ba zaya yafen ba...".
Nishi tayi tana faman hade hannayenta waje daya alamun roko kafun ta dubi Dr.karami da ya runtse idanu kana hango yarda kirjinsa ke dokawa kau da kai tayi tana kara jin zuciyarta na karye da tsananin tashin hankali mai girman gaske.
"Karka ce mani ba zan sake jin sautin Muryarta ba karka ce mani ba zan sake cigaba da rayuwa da ita a filin duniyar nan ba don Allah Doctor kace wani abu".
Dubansu yake yi daya bayan daya har da su Dr.Aqeel da Huzaif da suke ta faman kokawa da numfarfashinsu tashin hankalin su na daduwa gabadaya sun gama firgicewa sun gama yanke tsammani da numfashin Mariya a doron duniyar nan.
Nisawa yayi kafun ya dubi Baseera dake ta faman rusar kuka.
"Ki tsaurara kalaman ki kamar ba 'yar musulma ba ko Mariya mutuwa tayi bai kamata ace kina irin wannan maganganun ba dole ki saka tawakkali a zuciyarki dole ki anshi ko wacce irin ƙaddara ce ta faɗo duniyarki...".
"Ya isa haka Doctor".
Dr.Karami ya tare shi yana faman jan numfashi ya buɗe idanuwansa akan sa sosai sun kaɗa sunyi jajir jijiyon kansa duk sun fito sunyi ruɗu ruɗu.
"Ya kamata kayi abin da zai kawo kwanciyar hankali da natsuwa a garemu duk wani dogon turanci ba zai tsayar da kalamin da kake cewa bai dace ba abu daya zaka fadi wanda duk zai kau da rashin hayyacin da muke ciki".
Magana yake amma da ka kalle shi zaka gane akwai dauriya da juriya a zuciyarsa amma in ba don haka ba da tuni ya zube akasa a hankali ya shiga lumshe idanuwansa ya na matsawa jikin bango ji yayi kafafuwansa na kokarin zubda shi kasa jingina yayi da bangon zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri.
"Ban san wa zan fuskanta ba".
Likitan ya fadi yana dubansu domin gabadaya sun gama rikita shi da rashin hayyacinsu.
Dr.Aqeel ya tako gareshi da hanzari ya roko hannunsa sosai.
"Fada min ni ne makusancinta me ke damun ta...".
Wani haushi ne da zafin zuciyata ya turnuke Baseera jin abin da Dr.Aqeel yake fadi dubansa take yi da idanuwanta duba na raina hankalinka cizon laɓɓanta tayi kafin ta kara dubansa sosai.
"Mukusanci fa kace?...".
Ta fadi tana dariyar da ta fi kuka ciwo kafin ta sake cewa.
"kawai cewa zakayi kana cikin yan ta'addan da ke kokarin salwantar mata da rayuwa".
Da sauri ta dubi likita.
"Don Allah na rokeka karka saurare shi kar kace dashi komai game da Mariya domin ba amfanin da zai iyayi akanta illa ya kara turbudata cikin tashin hankali duk da sun yi ajalinta".
"Doctor Please Rabu da su don Allah ni ne mai kaunar ta nine masoyinta na asali...".
"Karya kake yi..wai don Allah me kuke son mai da ita ne ta shuri burjin ma ba za ku daina hauka kuna saka mata bala'i ba".
Baseera ta sake katse Huzaif da ya iso shima yana cewa wani abu.
"Yaa Allah wai anya kuwa kalau kuke anya kuwa ba kune kuka saka zuciyar baiwar Allah nan take kokarin bugawa ba haba mana menene haka kuke yi gabadaya kun rikita ni na rasa wajan da zan duba na fuskance shi".
"Doctor ni zaka fuskanta".
Kamar daga sama suka tsinkayo muryar Dr.Karami cin sauti mai ansa amo sosai da sosai a hankali ya fara takowa da wani irin yanayi tattare dashi karkasahinsa da mazantakar da yake tattare da ita jarumta da zuciyarsa ta gayyato masa duk ya ajje su saman fusakarsa lokaci guda duk wata kwalla da take kokarin samun gurbi a idanuwansa ya haɗiye su yanayin takunsa da sautin da takalmarsa ke bayarwa ya sanya likitan dubansa duba na sosai da sosai zuciyarsa ta yarje masa da cewa wannan shine makusancinta na kut da kut.
Gaban likitan ya zo ya tsaya sosai kan kafafuwansa duk da raunin da suke kawo masa hakan ya jajir ce yana jin yarda yake tsoro da kuma fargabar ansar abin da likitan zai sanar dashi zuciyarsa narkewa take yi da tashin hankali wani fili mai girma da ya jima da gina shi ya ajje Mariya a ciki ji yake yi yana kara buɗewa da wani yanayi na so mai girma sai yau sai yanzu a daidai wannan lokaci ya ya gama AMANNA akan son da yake yi wa Mariya sai yau ya gasgata da gaske yana sonta so mai ansa suna so sosai yake jin zuciyarta ta gama ajje GURBIN SO ako wani sashi da fanni na cikin ta ya yarda ya kuma amince son Mariya A JININSA YAKE a jikinsa yake son Mariya shine farincikin rayuwarsa son Mariya ya gama tafiya da duk wani imaninsa na filin duniyarsa.
Likitan da yake can kasa da Dr.Karami ya dago kai ya ajje idanuwansa akan nasa sosai yake hango wani lamari mai girman gaske lamarin da a lokaci guda ya ba shi suna da SO sone aciki son wanda son yake tsammani ita ce akwance ita ce wacce aka kawo bata da lafiya...
"Ni ne makusancinta ni ne dan'uwanta ne ni komai nata a filin duniyarta ni ne farincikin rayuwarta ni ne...".
Kau da kai yayi da sauri jin zuciyarsa na kokarin harbawa da wani irin so mai girma ba ya tunanin zai iya daukar abin da likitan zai fadi a wannan lokaci yana tsoron yace masa da gaske ta mutu yana tsoron yace masa AN KASHE SO don ya tabbata son sa za aka kashe farin cikinsa zai kare a filin duniyarsa Mariyaaa ce.
"Akan wani dalilin zaka dauki wannan lamarin ka jingina wa kanka a matsayinka na wanda bai san WACECE ITA ba akan mi zaka ce kai ne makusancinta akan me zaka ce kai ne kafi kowa kusanci da ita".
Dr.Aqeel yake fadin haka a zafafe yanayin sa kawai zaka kalla ka gane danyen so da yake ji na Mariya sosai zaka fuskanci zallar so mai ansa suna so a filin fuskarsa har da gurbin zuciyarsa.
Nishi yake ajjewa yana kallon Dr.Karami da wani irin yanayi kafin yayi taku daya zuwa uku ya daga dan yatsarsa daya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads