Header Ads
Showing 138001 words to 141000 words out of 227252 words

Chapter 47 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1400

Ads at the middle of Article

taba gani mace mai taurin rai kamar ta ba tun da yake bai taba ganin an kwaso yan mata an kawo masa ya samu mai taurin rai haka ba har zata iya dubansa ta gaya masa magana son ranta ba tare da fargaba ko tsoro a fuskarta ba gyaɗa kai yayi kafin ya bar wajan yana faman dukan iska.
Ita kuwa kuka ta saki mai taba zuciya da soya ruhi sosai ta durkushe hannayenta saman kanta ji take yi kamar ta hadi zuciya ta mutu ta bar wannan duniyar komai na cikin ta ba dadi sai yau ta kara tabbatar da cewa DUNIYA BA ALJANNA BACE ta tabbata bakomai cikin duniyar na sai ta shin hankali da rashin imani kaicon wannan rayuwa kaicon wannan zamani.
*****
Numfashi take ajjewa kyar idanuwanta sun kaɗa sunyi jajir hannunta dafe da cikinta da take jin sa yana ta faman juyawa sosai ta shiga tashin hankali sosai tayi kuka kuka wanda har zuwa yau take yin sa kuma bata san ranar daina shi ba ta shiga kunci da ukuba da bala'i ta sani bata da wata dama da za ta sake zuwa mata ta dadin rayuwa ta sani ita kam rayuwarta ta gama karewa tunda ta fado hannun wadannan azzaluman mutanan maras imani da tausayi maras ganin darajar 'YA MACE ba su dauke ta a bakin komai ba 'Ya'ya Mata sun mai da su kamar Toilet din su na duk lokacin da suƙa bukata za su je su biya bukatar su ko hali ƙaƙa ne ba sa ganin darajar koma waye bata san wasu irin mutane ba ne su bata san wata alkibla suke bi ba har ga Allah zata iya cewa ba musulmai bane domin bata ganin su da suffar ni'imar musulci ba duk da dai suna ikirarin su din haka amma ita kam bata taba yarda ba.
Nisawa ta sake yi Hawaye na kwaranyo daga idanuwanta kamar daga sama taji ana dauke mata su firgigit tayi ta dawo hayyacinta dubansa tayi kafun ta kau da kanta zuciyarta nayi mata zafi da raɗaɗi ji take yi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu da wannan bala'in da take ciki bata son ganinsa ko muryarsa bata son ji domin ganinsa kamar ganin bala'in rayuwa ne.
Murmushi yayi yana sake kai hannunsa bisa kuncinta.
"Ki yarda dani ki zauna dani mu rayu tare dake a filin duniyar nan ki yarda mu zama abu daya har gaban abada ni dake da abin da ke cikin ki".
Wani irin zillo taji cikinta yayi kafun idanuwanta suyo waje sosai fargaba da tsoron da take ji a zuciyarta akan abun da take zargi shi ne ya tabbata tabbas haka ne maganar sa gaskiya ita kanta ta sani akwai abin da ke damunta sosai taji a jikinta komai ya canza sosai take jin motsi a cikin cikinta runtse idanuwa tayi duniyar taji tana juya mata kanta yana komawa kasa kafafuwanta na dawowa sama zuciyarta take ji tana yayyagewa muryarsa da bakaken kalamansa take ji suna ansa kuwwa akan ta da cikin kunnuwanta tartsatsi da rugugi take jin kwanyarta nayi.
"Ban san ta zan sanar dake ba amma ki sani ina cikin yanayi na bukatarki a gareni ina so ki kasance dani har karshen numfashina sosai nake ji a zuciyata sosai da sosai nake jin zuciyata ta baki wani fili mai girma kina rayuwa ki sani ban taba kaunar wata mace ba ban ta taba son wata mace ba iyakata da mace na biya bukatuna da ita domin ni ban dauki mace a abun darajawa ko girmamawa ba amma akan ki ina ji a zuciyata ke ta daban ce".
Numfashi ya ja mai tauri kafun ya kureta da idanuwansa masu firgitar da ita a ko wani lokaci.
Bata san ya zata dauki wannan lamarin ba bata san a wani mizani zata ajje shi ba sosai take cikin wani mataki na rashin nasara a rayuwa sosai ta hango kaifaffan ALKALAMIN ƘADDARA ya daura tsininsa akan rayuwarta yana rubuta rubutun da take gani a matsayin ajalinta a duniyar nan rubutun da take ganin shine sanadin afkawar wannan rayuwar mai cike da tashin hankali da bakin ciki da ukuba sai yau ta kara tabbatar wa bata da sa'a ko daya a duniyar nan bata da sa'a matsayinta na 'ya mace bata da duk wasu ababe da mace zata yi alfahari da shi a duniyarta komai ya ruguje komai ya lalace wai ita ce yau dauke da juna biyu, juna biyun da ba ta hanyar aure ta same shi ba junan biyun da ya kasance ta same shi ta hanyar bala'i da masifa da jafa'i juna biyun da zata iya kiransa da shine ajalin rayuwarta.
'Yaa Zuljalali wal-Ikram'.
Ta ambata a zuciyarta da take ji tana yayyagewa tana fadowa kirjinta da tashin hankali mai girma ga wani abu mai girman gaske da take jinsa tsakanin makoshinta da kirjinta ya tsaya cak!.
Bata san me zata ce ba ita dai ta san rayuwarta ta kare rokon Allah take ya dauki ranta a filin duniyar nan rayuwar take ji gabadaya ta ishe ta bata son ta bata son komai na cikinta komai baki ne take gani bata burin sake maimaita WATA RAYUWA a duniyar nan burinta kawai numfashinta ya dauke a daidai wannan lokacin lokacin da take ji yafi komai zama bala'i a gareta.
Hawaye suka cika gaba da zuba a idanuwanta shi kuwa sai hannu yake kai wa yana dauke mata su.
"Ki ce wani abu ina son abin da yake cikin ki ina kaunarsa har dake kan ki ki yarda mu rayuwa a inuwa daya a tare har zuwa numfashin mu na karshe".
Daga idanu tayi ta dubi sashin da yan uwanta suke gabadaya sun gama mutuwa yawancin su da sunyi musu fyaɗe suke kashe su wasu kuma in suka ki yarda da bukatarsu suke kashe su su jefa gawarwakin a ruwa tana kallo bata da damar hanawa a gabanta sun kamo mutane masu yawa suna yin yarda suke so da su tana kallon yarda ake nunawa yan uwanta mata zallar rashin imani da tausayi amma bata san yarda zata yi ba agabanta an kashe har bata san a dadi ba an sha daukar bindiga ana bata ko wuka da sunan ta kashe wani amma bata tunanin zuciyarta zata iya zama mara imani da tausayi har haka yan uwanta musulmai ake kashewa har ake bata damar ta kashe batare da laifin komai ba.
Ruwan hawaye suka zuba mataa ta daga kai can nesa ta hango Baaba BG na kallonta tun da ta zo shi kadai ne mutumin da take kallo a mutum wanda ba irin su ba tana zaton shima kamar sato shi akayi kamar yarda suma aka sato su bata taba jin yayi magana ba bata taba jin ya buɗe baki ya furta kalma daya ba tausayinsa take ji mutum har mutum amma izayar da yake sha in da wahala na kisa da tuni ya mutu sosai ta fuskanci hakan bai son aikin da suke saka shi a lokuta da dama tana kallon yarda Malik yake basu umarnin aiwatar da wani aikin na mugunta amma shi sam ba yayi Malik lokuta da dama ya sha daura masa bindiga da sunan zai harbeshi amma sai ya fasa amma fa izaya ya na shanta ko yanzu da yake cikin razana tsaye sai faman gumi yake yi idanuwansa a sama yana kallon ranar da ta kyalla sosai idanuwansa sai faman zubda hawaye suke yi.
Malik ya sanya shi akan idonta yake bashi wannan azabar don kawai yaki yin mubaya'a akan abin da ya saka shi...
Karar albushirin da yaketo cikin dajin ne ya firgita su da sauri Malik ya mike yana kai kawo a tsakiyar wajan ita kuwa gabadaya ta firgice tashima ya gagare ta.
Yaran Malik ne taga suna ketowa kan baburansu a guje kamar za su tashi sama gabadaya wajan ya kaure da karar albushiri sosai da sosai Malik ya nufi cikin Tamfol din sa cikin hanzari lokaci guda kuma ya fito jikinsa da wata riga baka wulik mai kauri ga wasu igiyoyi da suke barbaje a jikinta da hanzari ya keta hanyar da ya ga yaransa na shigowa gudu yake yi kamar zai tashi sama can nesa ya hango bataliyar sojoji sun tun karo wajen bindigogin sa kirar Ak47 ya ya cilla sama tare da caɓe su a hannayesa ya shiga gudu yana sakin wuta ko ta ina cikin dajin sai da yayi tafiya sosai yana zubda sojojin da suka tunkaro alkaryar tasa albushiri ko ta ina amma shi ko a jikinsa domin albushiri da ta fado kansa yake watsewa kasa batare da ya bula jikinsa ba sai dai rigarsa ta dau hayaki a daidai inda albushirin ya sauka sosai ya cigaba da tafiya yana kallon yarda ake ta kashe masa yara hakan ya kara harzuka shi matuka lokaci guda zuciyarsa ta shiga tururi fuskarsa na kara hautsinewa idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir a daidai lokacin da ya tun kari inda yake hango bataliyar sojojin adaidai kuma lokacin albushirin bindigun nasa suka kare watsar da su yayi tare da yin wata uwar sufa ya yi kasa ya tura hannayenssa cikin ciyayin da ke wajan lokaci guda ya dago wata bingida mai saffurin mai jigida ya cilla sama kafin ya sake mai da hannunsa cikin ciyayin ya fizgo albushiri mai matukar tsayin gaske ya mike kan kafafuwansa da wani irin karfi gaske domin inda yayi tsalle ya dire sai da ciyayin wajan suka yi sama bindigarsa da ta shilla sama a daidai lokacin tayo kasa da hannu daya ya caɓe ta tare da zura mata albushirin nan ya shiga sakin wuta ko ta ina yana faman juyi kamar wanda yake amfani da wani maganakisun majajjawa.
Abin da Malik bai sani ba shine sojojin sosai suka shirya domin kuwa ƙawayansu kayi wa dajin can bangaren alkaryar tashi tuni sojojin sun isa cikin ta suka shiga sakin wuta ga duk wani yaransa sosai yan matan suka firgita suka shiga ihu saboda sautin tashin albushiri da suke ta faman ji ko ta ina ba su tsinke da lamarin ba sai da suka mazaje na bajewa a kasa matattu Mubeena dake cikin Tamfol din Malik tana kai kawo hannuwanta saman kai sai faman du'a'i take yi da fatan Allah yasa masu CETON RAI ne a garesu.
Wani albushiri ya ratso ta ciki wajan ya gogi kafatarta wani zafi ne mai cike da raɗaɗi ya ziyarce ta kwalla kara tayi da kafin gaske tare da zubewa a kasa ji take yi kamar hannu aka fizge daga jikinta zafin jinsa tayi a ko ina na sashin jikinta kararsa kuwa amsa kuwwa yayi cikin dodon kunnuwanta a hankali ta shiga jan numfashi da take jin sa kamar zai fice daga jikinta saboda tsabar azaba da raɗaɗi runtse idanuwa tayi a daidai lokacin aka banko tamfol din aka shigo sojoji ne guda biyu ko wane dauke da hula irin ta su ta sojoji hannayen su dauke da jibga jibgar bindigogi a resting din ta sukayi lokaci guda cikin cikin raɗaɗi ta buɗe idanuwanta ta kalle su lokaci guda ta mai da ta rufe tana jin suna surutunsu akan ta amma ko motsin arzuki bata iyayi ba daya daga cikin su ne ya lura da kafataɗarta da sauri yayi wa dan'uwansa alamu hakan ya tabbata masu alburushin ya same ta da sauri suka cinciɓe ta sukayo waje da ita gabadaya wajan ya zama fili sai gawarwaki dake baje can gefe kuma yan matan ne aka tare su waje guda sai faman rusar kuka suke yi gabadaya sun gama ficewa daga hayyacin su can suka nufa da Muneeba yan uwan naganinta da sauri su suka taso suka ansheta ganin halin da take ciki ya sanya su kara sautin kukan su kukan nasu ya farfado da ita daga sumar da tayi na wucin gadi a hankali ta shiga buɗe idanuwanta wanda hasken rana ya saito fuskarta komar da su tayi ta rufe kafin ta ciji laɓɓanta ta sake buɗe su sosai cikin karfin hali sosai ta shiga juya idanuwan nata tana kallon yarda sojoji sukayi wa wajan ƙawanya gabadaya numfashi taja mai tauri kafun ta dubi wanda suka riketa ganin yan uwanta ya sanya ta rushewa da wani irin kuka mai tsuma rai sosai da sosai jikinta har karkarwa yake nan suka sake buɗe babin kuka a tsakanin su sojojin sai bin su da kallo suke yi kafin su cigaba da shiga duk wani sashi na wajan.
A bangaren Baaba BG kuwa lokacin da sojojin suka fara sakin alburushin ba zato ba tsammani yaji saukarsa a hannunsa na hagu da hanzari cikin wahalallen yanayi ya saki wani nishi kamar ransa zai fita ya saukar da kansa daga kallon ranar da yake yi wanda suka gama wahaluwa jijiyoyin kansa sun fito sun burɗun-burɗun da su kwayar idanuwansa sai faman zubda ruwa suke yi.
Zubewa yayi a kasa yana kai hannun damarsa yana rike da hagun cikin wani irin yanayi mai matukar wahala sosai yaji kansa da duk jikinsa sun ansa da alburushin da ya fasa masa hannu runtse idanunsa yayi sosai kafun ya bude su dishi-dishi yake gani duban hannunsa yayi da yake ta faman zubda jini dafe wajan yayi sosai amma hakan bai hana jinin cigaba da zuba ba da hanzari ya shiga kokarin mikewa jiri na dibarsa sautin albushiri ne kawai yake ji ta ko ina zuciyarsa yaji ta kawo masa wani karfi mai girma gaske da hanzari ya tashi yana tangaɗi ko gani sosai bai yayi ya yanki daji yana jan jikin sa zafin raɗaɗi sai kara hauhawa yake yi tafiya ya yanka sosai sai yayi ta har kafafuwansa na kokarin kasa daukarsa amma zuciyarsa bata yi rauni ba karfi yake ji yana kara zuwa masa tun yana cijewa har ya fara gudu yana yankar daji numfashin sa na sama da kasa tafiya mai nisa yayi cikin wannan matsanancin halin har sai da sautin alburushirin dake tashi ya ragu yana jiyo sa daga can nesa bai ankara ba ya gashin gaban wani tafkeken kogi dake gudu cak! ya tsaya da tafiyar da yake yi yana mai da numfashi kafin ya zube kasa yana mai lumshe idanuwansa ko ina na jikinsa yake ji yana masa wani irin ansawa da ciwo mai tsanani buɗe idanuwansa yayi ya kalli hannun nasa da yake digar da jini ganin jinin ya fara bushewa hakan ya tabbatar masa ba karamar tafiya yayi ba ga hannunsa ya kumbura sosai ko ya ya taba shi zafi da radaɗi yake jin suna ansawa a jikinsa.
A hankali ya tashi yana tangadi ya tunkari kogin sosai idanuwansa suna lumshewa bai san lokacin da ya isa bakin kogin ba har ya tsoma kafafuwansa kawai ji yayi ruwan ya fizgeshi da wani irin karfi ya antayashi ciki gudu kogin ya shiga yi dashi ba k'ank'autawa shi kansa bai sam ba a wani hali yake ba sosai ya mika dashi hanyar da kogin yake bi yana faman sama da kasa dashi.
A bangaren su Malik kuwa abu ya kacame fada sosai ake yi ba abin da ke tashi sai sautin albushiri gawarwaki kawai zaka ke gani ko ta ina ta sojoji da ta alkaryar Malik wanda suka rage kalilan ne wuta kawai Malik yake tafiya yana yi idanuwansa a rufe ba zato ba tsammani yaji saukar wani katoton abu ya daki goshinsa ya cilla dashi can gefe ya bugu ta wata katuwar bishiya mai matukar girma kafin ya sake cilla wa wani wajan can daban ya fada cikin ciyayi har sai da ya shiga cikinta sosai da sosai runtse idanuwansa yayi kafun ya bude su sun kaɗa sun yi jajir yinkurin mikewa yayi amma ina bayansa yaji yayi wani irin amsawa kamar an karya bushesshen ice da sauri ya koma ya kwanta yana mai sakin numfashi ga wasu hawaye da suka shiga zubo masa a fuska ba kankautawa.
hannayensa duk biyun ya cusa cikin ciyayin wajan ya damka kana jin sautin yardda suke rumurmushewa da yake sun bushe wani bakin ciki yaji ya tokare masa kirji ga wani abu mai girma ya tsaya masa a makoshi da k'yar yake jan numfashi komai.
A karo na biyu ya sake buɗe idanuwansa jin motsi ta ko ina sojoji akansa sun yi masa ƙawanya sosai da sosai ko wannan su hannunsa dauke da bindiga sun saita shi wani takaici ne ya sake kume shi ya kurma wani irin razanan nan ihu da ya ansa sauti sosai cikin dajin...




*_KAMALA MINNA_*😘😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA TARA.








Juyi kawai take yi zuciyarta na zafi da wani irin raɗaɗi mai girman gaske sosai take jin komai ya sauya mata sosai take jin duniyar da abin da ke cikinta sun zame mata kunci da ukuba komai take kallo a mara dadi zuciyarta da ruhinta suna wani mataki na tashin hankali ba abin da take tunawa sai kalaman Dr.Karami sosai suka taba mata zuciya da ilahirin jikinta bata taba zato ko tsammani ba ko a mafarkinta bata taba zaton Dr.Karami ya dube ta ya na gaya mata magana son ransa har haka ba ko da yake bata ga laifinsa ba har da ita da ta tsaya tana kai kawo akan sa ashe duk kulawa da yake nuna mata a zahiri ba haka bane zuciyarsa sam bata tare da ita.
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata da saurin ta kai hannunta ta shafe su don bata so Umma ta lura da halin da take ciki yau kusan sati uku kenan amma ta kasa manta kalaman Dr.Karami sai faman kuwwa suke yi mata akai da kunnuwa ta rasa mai yake yi mata dadi a filin duniyar nan bata san abin da ke kokarin faruwa da ita ba ta ji zafin kalamansa amma kuma zuciyarta taki bashi laifi taki yarda da laifin da take dorasa masa bata ma san mai haka yake nufi ba tun da abin nan ya faru ta kasa sukuni tunanin Dr.Karami ya sha mata kai ko barci take yi shine dai take tadda cikin barcin nata.
Mikewa tayi daga shingiɗen da take ta shiga safa da marwa a cikin dakin domin samowa kanta mafita sosai take jin ciwo mai girma a zuciyarta sosai take jin gangar jikinta na kawo mata bakutan wani yanayi mai girman gaske wanda ta rasa yarda zata kwatantashi sosai Dr.Karami yashiga yin tasiri

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads