Showing 126001 words to 129000 words out of 227252 words
Chapter 43 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
kisan Allah ba zan fita ba ai in na fita kamar bani da zuciya ne".
Zaro idanu tayi waje kafun ta shiga dubanta sosai ganimn take yi kamar ba Mariya ba komai take ganin ya canza game da ita fushin da ba nata ba take ganin Mariya ta aro ta daurawa kanta akan mutumin da sam bai dace ace tayi wa haka abin yayi matukar daure mata kai don haka sai ta koma gefe tana mai latsa wayarta ta ba banza ajiyar Mariya.
******
Da sauri ta sauka a Napep din ta nufi hanyar shiga gida ko gabanta bata kallo idanuwanta gabadaya a rufe suke ba zato ba tsammani taji tayi karo da mutum da sauri ta dago kanta ta na fiddo su waje cikin yanayi na tsoro da firgita tsuke fuska tayi ganin wanda yake gabanta da sauri ta kau ce tana kokarin wucewa cikin gida caraf! taji ya rike mata hannu ai ji tayi kamar ta kurma ihu wani kallo ta watsa masa kafun ta fizge hannun nata rai bace ta shiga nuna sa da yatsa.
"Huzaif kana da hankali kuwa kasan abin da kake aikatawa hannu na fa kari ke...".
Wani kallo da yayi mata yana kokarin sake riketa da sauri ta ja baya kafun ta daga hannu ta zabga masa mari cikin tsananin takaici da bakin ciki.
"An gaya maka ni irin watsantsun matan da kasani ne an gayamaka RA'AYINMU DAYA da su ne ko an gaya maka halayarmu daya da su ne tun wuri ka dawo hayyacin ka in kuma ba haka ba na rantse da Allah zan yi maka abin da baka taba zato ba".
Murmushi ya saki yana yawatawa da idanuwansa a jikinta kafun ya shiga kokarin kaiwa gareta a hankali ta shiga ja daya baya idanuwanta a warwaje cikin tsananin tsoro da firgita yanayin da ta ga Huzaif a ciki ya tabbata mata ba ya cikin hankalinsa da sauri ta juya tana kokarin kwasa da guda sautin karar marin da taji ya karaɗe kunnuwanta ne ya sanyata tsayawa cak! kafin ta juya a firgice.
"Dr.Karami!".
Ta fadi a firgice jikinta har rawa yake yi wani irin huci yake yi kamar kumurci yana faman cika fuskarsa ta rine tayi jajir idanuwansa sun kaɗa sosai hannusa akan Huzaif da ya dafe kuncin sa domin kuwa sosai yaji shigar marin da Dr.Karami yayi masa kallon kallo suka shiga yi wa juna a tsakanin su sosai suka so tuna in da suka san junansu.
Dr.Karami ya ja numfashi mai zafi kafun ya dubi Mariya da tayi matukar shiga firgice kamar wacce zata saki fitsari ba abin da jikinta yake yi sai rawa sosai ta tsorata da yanayin da taga Dr.Karami a ciki musamman irin kallon da taga yana watsa mata kau da kai tayi tana kokarin barin wajan wata irin razananniyar tsawa ya doka mata lokaci guda ta tsaya da tserewar da take kokarin yi a hankali ya shiga takowa inda yake gabanta na dokawa da tashin hankali mai girman gaske nuna ta yayi da yatsa bakin sa sai motsi yake yi yana son yin magana amma ya kasa ya dunkule hannu ya naushi iska yana mai cizon laɓɓansa kafin ya juya ya kalli Huzaif da har lokacin yake tsaye dafe da kuncin sa karasawa yayi gareshi yana kallonsa ido cikin idon kafin ya ja huci mai zafi.
"In har kasa sake gangancin ka ya sake dibarka har kayi kokarin taba ko da gyalan jikinta ne na rantse maka da Allah sai na daureka har igiya tayi rara don na lura kuruciya na damun kwanyarka zan saita maka ita".
A hansale Huzaif ya dube shi.
"kan wannan kucakar yarinya ka mare ni kan wannan mai kama da birin ka mare...".
Ji kake kau! Dr.Karami ya sake dauke shi da mari wanda yafi na dazu ya cakumi wuyar rigarsa.
"wai kan dan gidan uban wanene fada min uban waye uban ka a garin nan na rantse da Allah in bakayi wasa ba kafatanin zuri'arku sai sun ji a jikinsu".
Yana gama fadin haka ya watsar dashi gefe kafun ya dubi in da Mariya take cikin tsananin firgice da razana bata yi zaton zafin Dr.Karami ya kai har haka ba sosai taji tsoronsa ya sami ma sauki a zuciyarta kasa tayi da kai ganin wani kallo da ya watsa mata mai cike da tuhuma zuciyarta taji tayi wani irin dokawa da hanzari ya isa can gefen hanya in da yayi parking lokacin da ya ga abin da ke faruwa tsakanin Mariya da Huzaif a hanzarce ya isa yayi mata ki ya fizge ta cikin tsananin bacin rai huci kawai yake yi zuciyarsa na wani irin zafi da raɗaɗi ji yake kamar ya hada Huzaif din da Mariya yayi musa dan banzan duka.
Sai da taga bacewarsa sannan ta juya ta dubi Huzaifa tana mai galla masa harara tayi hanyar shiga cikin gida a soro ta ci karo da Hafsat tana kokarin fitowa taci uban kwalliya da dinkin atamfa wanda yayi matukar kama mata jiki ainun in ka ganta sai ka rantse wata rikakkiyar wayayyice nan kuwa kanta empty ne a hankali take taku Mariya na binta da kallon mamaki da tu'aji bi da yarda Hafsat ta bari duniya ta buɗe mata ido haka ko da yake bata ga laifin ta ba Goggo Marka ce ta daure mata kugun yin abin da take so tun da suka hadu da Huzaif shikenan ta daina zaman gida kullum yana hanyar daukar ta suna ficewa ita dai nata ido domin bazata taba mance cin amanar da Huzaif da ita kanta Hafsat din sukayi mata ba kallon su kawai take yi girgiza kai tayi tana mai shigewa cikin gida zuciyarta a jagule komai take jin ya kwance mata duniyar gabadaya tayi mata zafi ji take yi kamar ba ita ba.
"Kan Uban can!".
Hafsat ta fadi lokacin da taga Huzaif na faman huci hannunsa dafe da kuncin sa idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir kamar wanda kayi wa sura ce da barkono.
"Me ya same ka haka?".
Ta fadi tana mai duban sa, tsaki ya ja kafun ya shiga safa da marwa a wajan sai fama huci yake yi.
"wani dan iska ne wai don kawai waccan yarinyar ta gidan ku za ta gaya min ba dadi shine ya zo ya daura min tafi a fuska".
Zaro ido tayi waje kafun ta dubi kofar gidan su.
"Mariya ko?".
"to akwai wata yarinya ce a gidan ku bayan ita".
Ya fadi a hassale kamar zai kifeta da mari ita ma tsaki ta ja tana mai galla masa harara.
"Huzaif na lura so kake yi ka raina min hankali in ba don haka ba ina ruwanka da ita ai ko me akayi maka kai ka ja yasin".
Wani wawan cafka ya kai wa hannunta ya murɗe ta saki kara mai sautin.
"Ni zaki raina wa hankali Hafsat kin san Allah in bakiyi wasa ba sai na sauke akan ki".
"Sauke mana in ka isa ai bani na saka ka kula ta ba Malam balle ka sauke fushin ka akai na".
Dunkule hannu yayi kamar zai kai mata naushi amma sai ya bugi iska gami da jan tsaki ya isa in da yayi parking ya buɗe mota ya shiga ransa a bace zuciyarsa sai faman tururi take da takaici
Hafsat dake tsaye ganin yarda ya shiga motar rai bace ba tare da yayi mata magana ba haushi ya cika ta ja tsaki kafin ta isa gareshi kallonsa kawai tayi ta watsar kafun ta buɗe motar ta shiga ko kula ta bai yi ba ya yiwa motar Key ya fizge ta ya bar layin yana mai fadin.
"Billahillazi sai na baiwa Mariya mamaki ba dai ni ta saka akayi wa cin mutuncin ba zan nuna mata na fita iya shege".
Hafsat da ta kula tsaki taja a ranta tana fadin 'Allah ya kara ai ni nafin son haka dama kiyayya mai karfi ta ratsa tsakaninku'...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA BAKWAI.
A hankali take taka benan har ta isa bakin kofar tana jin yarda gabanta ke dokawa ba ta san ya zai kalleta ba bata san ya zai karbeta ba ita dai ta san tana son sa so mai tsanani wanda tun da take a filin duniyarta bata taba jin son wani ɗa namiji ba kamar Dr.Erena zuciyarta da ruhinta sun jima suna kai kawo akan son shi ta dalilin son sa ta zo aiki cikin Company sa saboda burinta ya cika take zaman aiki a company ba wai saboda kudi ba amma ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya dace tayi a gareshi domin ya amince da ita har ya so ta sosai ta lura sam! baya kula duk yanayin da take nunawa don ya sota amma hakan sam ba ya wani tasiri akansa ba ta san ya za tayi ba abin da ya ke kara tayar mata da hankali yarda lokaci guda wata ta shigo cikin Company din take kokarin bata mata duk wani shirinta ta lura Dr.Erena son ta yake yi so kuwa mai tsanani abin da ta lura dashi ita Areefa ba son sa take yi ba shi yake kiɗin sa yana rawar sa ga inda ake son sa amma ya kwashi jiki ya tafi in da ba a son sa.
Ita dama tun da Areefa ta shigo cikin Company nan gabadaya taji bata kwanta mata ba sosai take ji a ranta akwai abin da zai faru don ta lura ita ma Areefa ba wai aiki ne kawai ya kawo mata ba har da wani KUDIRI nata na daban.
Tsaki taja kadan kafin ta gyara zaman rolling din da tayi wa dan kwallin jallabiyar dake jikinta sosai ta gyara zaman glass din dake fuskarta kallo daya kayi mata ka san ita ma ba baya b wajan kyau da kirar jiki fara ce amma ba can sosai ba.
A hankali ta turo kofar Office din ta shiga zuciyarta na bugaawa da halin tsoro don bata san abin da zai je ya dawo ba bata san yarda Dr.Erena zai karbeta ba ta san ya zai anshi abin da za taje masa dashi ba.
"...Bobby karka sake ka bata min rai kayi kawai abin da nace da kai ba wai ka kai shi can in da ba a dawowa ba a,a kawai so nake yi yaji a jikinsa ya san har yanzu Dr.Erena yana nan a yarda ya sanshi ba wai canzawa yayi ba".
Tana kokarin buɗe baki tayi sallama ta tsinkayi muryar Dr.Erena ya na fadin haka ai mutuwar tsaye tayi idanuwanta a warwaje lokaci guda jikinta ya shiga ɓari kamar wacce akayi wa wankan ruwa mai tsanani sanyi gumi ya shiga tsantsafo mata a jiki lokaci guda duk taji jikinta ya shiga narkewa da duk wani kudiri da buri da ta zo don cimmawa a hankali ta shiga jan numfashi tana mamakin kalaman Dr.Erena bata taba zaton haka yake ba bata taba zaton akwai rashin imani har haka ba a ransa.
A hankali ta shiga kokarin juyawa don ficewa amma zuciyarta tana hanata akan kudirin da ta zo dashi sosai taji komai ya fara canzawa tsoro da fargabar da take yi ya ragu sosai zuciyarta na kara mata jarumta akan kawai taje ai mai nema ba ya rasawa ita fa abin da ta zo yi daban maganar da yake yi bai shafe ta ba kuma ba ta san abin da yasa yace haka ba.
Da wannan tunanin ta shiga saita kanta gabanta na faduwa kadan kadan.
Sallama tayi tana mai cusa kanta cikin Office din tsaye ta hangeshi yana kai kawo fuskarsa da murmushi wanda daka kallashi zaka gane na mugunta juyowa yayi jin sallamar da kayi dubanta yake yi cikin wani irin yanayi kafin ya kau da kan sa.
"Sannu Sir".
Ta fadi da kokarin dauko jarumta ta azawa kanta ansawa yayi a ciki kafin ya dube ta ba yabo ba falla sa.
"Lafiya me ke faruwa ne Mufeeda?".
Sosai taga yayi mata kwarjini a idanunta gabanta taji yana bugawa wata irin burgewa take jin lokaci guda tana karuwa akan Dr.Erena juya idanunta ta shiga yi tana faman yak'e kamar wacce bata da gaskiya.
Dubanta ya shiga yi da wani irin yanayi na tuhuma kafi ya tako inda take tsaye.
"Akwai wani abu ne?".
Ya fadi yana kureta da kallo da ya kusan narkar mata zuciya da gangar jiki. A hankali ta shiga motsa baki zuciyarta na tsallen tsoro akan yarda zai anshi lamarin.
"Sir, dama akan maganar Areefa ce".
Dan yatsine fuska yayi kafun yace.
"Me ya faru da Areefa din wani abu tayi miki ne?".
Girgiza kai tayi kafun ta ja numfashi mai tauri tana jin yarda wani abu da ya tokare mata kirjiya ya sauka.
"Gaskiya Sir. Ban yarda da ita ba jikina sam! Bai kwanta da ita ba tun da ta zo Company din nan sosai nake ji ajiki kamar ba alheri bace a gareka da ma mu kafatanin ma'aikatanka...".
Hautsine wa fuskarsa ta shiga yi da wani irin bacin rai idanuwansa suka shiga kaɗawa da tsananin haushi kafin ya dube ta sosai da sosai yana faman hirji kamar wani kumurci.
"Me kike cewa Mufeeda Areefa din ce ba alheri ba Areefa ce kike jifa da wadannan kalaman naki kina da hankali kuwa anya ba wani abu kika sha ba wanda ya rabaki da duniyar hankali gaskiya bana zaton kina cikin hayyacinki na lura ke ma kin fara yan kurɓe-kurɓen nan na yan matan wannan zamani in ba haka ba ina ruwan ki da ita mai ya shafe ki da ita rayuwarki daban ta ta daban don haka tun wuri tun muna kallo juna a mutunce ki fice mani daga Office tun kafin na keta miki rashin mutunci.".
"Am...amma Sir. Daka tsaya ka fuskance ni gaskiya ce fa nake sanar da kai...".
Wani kallo ya watsa mata kafun ya shiga nuna ta da hannu.
"I Say Get Out! tun kafin nayi miki abin da baki taba zato ba".
ware idanu tayi sosai jin furucinsa ya taba mata zuciya amma sai taki barin haka yayi tasiri a zahirancen cikin jarumta ta sake dubansa murya alankwashe.
"Sosai na fuskat kamar akwai wata alaka a tsakanin kai da ita Sir hakan kuma bai dace ba sam ya kamata ace ka nemi mace mai daraja mutunci a matsayinka na mutum mai daraja da mutunci mutane da yawa yanzu kallon wani daban suke yi kamata ganin alakarka da Areefa...".
"Mufeeda! Which can of nonsense kike kokarin gaya mini me kike nufi dani me kike so ki ce da nine akan Areefa ya kamata tun wuri ki gyara kalaman ki kuma ki sani indai akan Areefa ce kika zo kina yi mani wannan haukar wallahi tallahi gaf! kike da barin Company din nan".
Gwalo idanu tayi waje sosai zuciyarta na wani irin raɗaɗi da zafi komai take ji na jikinta yana canzawa sosai take jin komai nata kamar ba nata ba kalaman Dr.Erena ba karamin taba mata zuciya sukayi ba ji take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu bata san ya zatayi ba bata san me zatayi Dr.Erena ya kalle ta a mutunce ba bata san hanyar da za ta bi ba domin ya kulata ya anshi tayin da take masa ya sota kamar yarda ta kamu da son sa a filin duniyar zuciyarta sosai take son sa so bana wasa ba tana kishinsa ba ta son duk wata mace ta ga tana kusantarsa sosai tashiga tashin hankali lokacin da ta ga Areefa ta fado rayuwarsa.
Wasu kwalla taji suna neman zuba mata da sauri ta dauke su ba tare da Dr.Erena ya gani ba amma sai dai tayi shuka a idon makwarwa domin kuwa duk motsinta akan idonsa take yi da mamaki yake dubanta sosai hawaye da ta shafe ya kara sanya shi a mamaki sosai sakanni ya dauka yana kallonta kafun ya ce da ita cikin muryar tuhuma.
"Hawaye Kuma me yayi zafi shi ba wuta ba Mufeeda me yake damun ki wani abu akayi miki ne Pleaae Leave my Office ba zan dauki wannan haukar taki ba kin ji ko I need to be alone ba na son abin da zai kawo mani ciwon kai don ba dauka zan yi ba".
Murmushi tayi wanda ya fi kuka ciwo sosai take jin bakin ciki da takaici na rashin darajawa da Dr.Erena yake nunawa akanta sosai take ganin rawar kanta da gangacin da zuciya tayi mata na son wani wanda bai son tana yi ba ga ta yanzu a gaban shi amma yana nuna ita da banza duk daya bata san mai ya sa haka ba ta san dai SONE SILA wanda bai yi mata adalci ba bai dace ace yayi mata haka ba bai kamata ace AKAN SO tana kuka ba kukan ma akan wanda ba tayi tsammanin zuciyart za ta so shi ba ko a mafarkin ta ba ta taba zaton zuciyarta zata dauko mata son Dr.Erena ba ta kawo mata tun da ta fara aiki a Company tun ranar da ta daura idanuwanta akan sa taji ta kamu da son sa amma bata san ta yaya zata bayyanar son da take masa ba a gareshi domin sosai da sosai yake mata girma da kwarjini a idanunta.
Ba ta zaton za ta iya barin nan batare da ta amayar masa da abin da take ji game dashi ba bata zaton zata iya daukar gangar jikinta ta fice daga cikin Office din nan batare da ta bayyana son da take masa ba ko da kuwa hakan zai sanya ya kore ta daga Company din nan. Ba za ta iya cigaba da dakon son sa ba tana bukata zuciyarta ta sarara mata da tashin hankali da take samun kanta kullum a ciki runtse idanuwanta tayi kirjinta cike fargaba da tashin hankali mara musaltuwa tana jin yarda kirjinta ke bugawa da sauri-sauri motsa laɓɓanta ta shiga yi kanta take ji yana juyawa amma haka ta kinkimo jarumtar duniya ta daurawa kanta.
"Dr.Erena...".
Ta fadi tana jan wani numfashi mai tauri gaske shi kuwa dubanta yake yi da mamaki cike da fuska jin a RANA DAYA Mufeeda ta kira sunansa abin da bata tabayi ba tsayin lokacin da ta fara aiki sosai ya natsu yana dubanta kafin ya ja kujera ya zauna.
"Na jima a duniyarka ina shawagin son ka amma sam baka lura da haka ba, na jima ina jiyar zuciyata da tayi gangancin daukar sonka ta azawa kanta, na jima ina kwaɓarta amma ta ki ji tayi