Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 227252 words

Chapter 15 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

1387

Ads at the middle of Article

bangarori masu yawa daga sassa na jikinta sosai take hango wautar ta cikin aikata wannan kuskuren mai girma da zuciyarta ke ganin tayi sosai take ganin girmar lamarin na kara girmama a zuciyarta da tunaninta.
'Mai ya kai ta, mai ya kai ta aikata wannan danyen aikin, ta ya ya ma haka ta faru gareta tun da take ba ta taba marin wani mai girma kamarsa ba ko da bai kai shi ba bata taba mai yasa tayi haka ina tunaninta ya kai ta lokacin ina zuciyarta ta cilla a lokacin mai yasa bata hana ta ba'.
Gyaɗa kai kawai take yi cikin daukar tashin hankalin da taji yana kawo mata hari, ta tabbata ba zai yafe mata ba, ta tabbata ba zai rabu da ita ba, ta tabbata zai shigo duniyar rayuwarta.
Ta ya ya ta wacce suffa zai zo mata?
Tunani da zuciyarta ke ta hasko mata ke tana kara gigita mata kwakwalwa da lamarin da take kara girmamashi.
Abu taji mai dumi na saukar saman kumatunta ko bata tabbata ba ta san Hawaye ne bayan HAWAYEN ZUCIYA da taji ma tana yi abin har ya kai ga bayyana dole ta firgita da lamarin ita Mariya ta mari wani wanin ma mai girma girman da ya dace ace ta ganshi ta daraja shi amma ina! ZUCIYA BATA DA K'ASHI.
'Akan mi akan wani dalilin zaki damu kan ki. Kina zaton in da ya cimma buri akan kudirinsa a kan ki tashin hankalin da za ki shiga mai ya girmema wannan ba kawai don mari har zaki bari tashin hankali ya yi girma mafi girma gareki karki yi sake har wannan kankanin abun ya hanaki abubuwa cikin rayuwarki'.
Wani sashi na zuciyarta ne taje tana amayo mata sautin zantukan nan.
Sosai tayi shiru tana nazarin kalaman sosai komai taji yana kokarin dawo mata daidai a hankali ta fara gyaɗa kai tana jin yarda zuciyarta ta cigaba da wanzar mata da wasu batutuwa masu girma a gareta.
'Shin in da ya keta miki haddi mi kik zaton zai faru dake a duniyarki'
Numfashi mai girma ta ajje gami da buɗe idanuwanta gabadaya sosai take kallon kanta sosai take kallon yanayin kankatarta tana kara nasarin abin da ta aikata a hankali komai da zuciyarta take fadi mata ya fara tasiri sosai a kanta sosai da sosai zuciyar ta dake komai na tsoronsa ya kai sai dai abu daya da take jin sa a zuciyarta duk a dalilinsa sai dai bata dan me nene ba bata san a me zata fassara shi ba sai dai zata iya barin sa a matsayin 'Mala' har zuwa nan gaba.
A hankali ta fara daga kafafuwan ta da taji sunyi mata nauyi kamar an daura mata wani abu da yai karfin girman jikinta sosai take kokarin amfani karfin zuciya tana jansu tana sanya hannayenta tana dauke guntayen hawaye da suka zobo mata sosai take takaicin zubarsu akan wani can wanda bai san darajarta ba mai san kimarta ba mai san martabar ta ba...
"Mariya".
kamar daga sama taji sautin muryar ya sauka a kunnuwanta da sauri ta ja kafafuwanta da take ja daƙyar ta ajje su waje guda ko ba a fada mata ba ta san waye hakan ya hanata juyawa domin adaidai wannan lokaci tana bukatar zaman kadaici ita kadai ba ta so ta sake daukar wani abu da zai so canja masa lissafin da take faman yi azuciyarta runtse idanu tayi jin takunsa na isowa gareta sosai take nuna rashin so wani abu a yanzu sosai fuskarta ta bayganar da haka.
A hankali ya isa gareta hannayensa sarƙe a juna jikinsa sanye da wani lallausar boyel mai kalar fari anyi masa dinki babu wuyar rigar an mata aiki da jare mai kyallin gold sosai kayan suka dace da jikinsa kansa sanye da hula ita ma dai kalar kyallin Gold ne doguwa ya dan rangwafar da ita kamar yarda yarbawa suke yi fuskar nan tashi fayau ba zaka ce ya hau shekaru talatin a duniya.
Sosai yake karantar yanayin ta da yarda ya hango damuwa dauke a fuskarsa sosai yaji rashin jin dadi a ransa ciza laɓɓansa yayi kafin ya gyaɗa kai.
"akwai abin da ke damunki Mariya".
Ya fadi yana sake kafeta da idanuwansa manya sosai take jin rashin son magana a daidai wannan lokaci amma ba za iya ajje Dr.Aqeel a matsayi marashin girma gareta ba tana jin sa sosai a ranta da irin ALHERI da yayi a rayuwarta.
"Uhmm bakomai kawai dai...".
"Mariya mana".
Ya fadi cikin muryar mai sauti da rarrashi a cikinta.
A hankali ta dago kanta ta dube shi na yan sakanni kafin ta kau da kai tana hango yanayin kulawa sosai cikin idanuwansa gareta tana hango yarda ya nuna alamun damuwa da damuwarta.
"Baabana".
Ta fadi murya na rawa yanayin da tayi maganar zai tabbatar maka kamar iyakar gaskiyarta ta fadi ko da dai ba karya tayi ba lamarin bacewar Baabanta cikin rayuwarta yana cikin sahun abin da take zaton ƙaddara zata kawo mata na rashin natsuwa.
"Yaa Salam!".
Dr.Aqeel ya furta cikin rauni sosai kafin ya daura hannunsa akai yana mai cigaba da cewa.
"Please Mariya ya kamat ace ki na sanyawa zuciyarki natsuwa gami da kwakwalwarki ke fa karamar yarinya ce sam bai dace ace har kin fara cin karo da irin wannan lamarin ba a rayuwarki kwakwalwarki ba komai zata iya dauka ba tsorona kar damu tayi miki yawa sosai wani abun zai iya kama ki na rashin dadin rai Please Mariya Rayuwarki tana bukatar komai mai dauke da sauki".
Yanayin da yake ajje furucinsa da rauni a ciki da kuma rarrashi sosai hakan ya taba zuciyar Mariya ji take yi kamar ta rushe da kuka ita a karan kanta ta san sosai take cikin SIRAƊIN RAYUWA sosai take ganin yarda rayuwarta ke zuwa a a hagu ita kanta ta dani komai na duniyarta ba mai natsuwa bane ta sani sosai da sosai ƙaddara ke dawainiya da ita a duniyarta.
"Mariya komai zai shige in har baki dau komai da zafi ba, rayuwarki tana da muhimmanci ga rasu rayuka masu yawa sosai wasu rayuka za su shiga tashin hankali mai girma in har ba ki rangwantawa kan ki ba".
A dan tsora ce ta dago tana dubansa sosai taji kalamsa sosai take fahimtar in da ya saka gaba rintse idanu tayi kafin ta buɗe su ta fara kokarin daga laɓɓanta.
"Ta ya ya hakan zata kasance, ta ya ya zuciya zata iya daukar wannan lamari mai girma ta ya ya karamar kwakwalwata zata iya daukar wannan lamarin mai girma, bana tunanin zan iya amfanar da wasu rayuka a halin da nake ciki bana tunanin ƙaddara zata iya bani wannan damar bana zatom ƙaddara zata juya daga shafin da ta buɗe mana mai dauke da kaya mai girma na rashin kwanciyar hankali bana zaton hak...".
A hankali ta rintse idanuwanta tana tura laɓɓanta cikin bakin ta sosai take jin abu mai nauyi yana samun gurbi a zuciyarta sodai take jin kirjinta na nauyi da girma a cikinsa.
"Bana tunanin Mahaifin ki zai guje ku a halin rayuwar da kuke ciki. Bana tunani zai samu kwanciyar hankali don ya bar ki bana tunanin saboda gazawa ce ko halin da mahaifiyarki take ciki ya sanya shi bacewa daga rayuwark...".
"Dr.Aqeel mai yasa kake cewa haka, mai yasa kake kokarin sanar dani abin da zuciya ta ba zata iya samun wajan ajjewa ba".
Nisawa tayi tana jin yarda zuciyarta ke wani karfi a duk fitar kalma daya daga bakinta.
"Mai yasa mai tsaya mun tafi tare ba, mai yasa da zai tabi bai tabbatar mani da in da zai je ba, mai yasa ya boye mani wani abu kuma ya san zuciyata ba iya dauka za tayi ba mai yasa ya tafi tsayin kwanaki fiye da arba'in ba tare da ya waiwayo mu ba ina jin zafi a zuciyata ina son Baabana sosai da sosai yarda baka zato ina bukatarsa kusa da ina ina bukatar kullum na dinga kallonsa yana wanzuwa a DUNIYARMU a kullu yau min. Ban so ya tafi wata duniya ba ta daban wacce ba musan a wani hali yake ba kullum tashin hankalin rashin sa kara girna yake yi a ko wani sashi na zuciyata".
Yanayin yarda take ajje kalmominta sosai suke taɓa zuciyarsa zuciyarsa yake jin tana wani iri tana saukar da wani lamari mai nauyi gareshi sosai tausayinta ke kara samun gurbi a ko ina na zuciyarsa sosai yake jin ba zai iya cigaba da kallon yarda komai na muryarta da zuciyarta ke kara rauni ba.
"Yaa Salam! Mariya kiyi hakuri don Allah komai zai zo karshe, kuma Mahaifinki zai dawo gareki na sani duk in da yake kuna ransa domin ku ne rabin rayuwarsa ko ina ya ajje kafarsa dole ya kasance tunaninku yana zuciyarsa".
"Amma...".
"Haba mana Mariya".
Ya tare da sauri domin sam ba ya bukatar ya sake jin wani furuci nata mai rauni ya daki kunnuwansa. A hankali ya fara juyawa domin komawa Office dama ita ya fito dubawa sosai yake jin yarda numfashinta ke sauka a hankali har ya bar wajan.
A hankali ta daga kai ta bashi da kallo sosai idanuwanta suka cika da kwalla suna kokarin zubowa bayan hannunta ta saka ta dauke su ta kwashe mintina a tsaye a wajan kafin ta kokarta jan jiki sosai take jin nauyi a ko ina na sassan jikinta musamman kirji don ji take kamar dutsen Dala aka daura mata kanta a kasa take tafiya sam bata lura da wanda ya ke gabanta ba sai da ya ga ta kokarin tureshi sannan yayi gyarar Murya a dan razane ta dago kai sau kadan ta bugi kirjinsa ta ja baya kadan tana mai jikin kunya sosai da sosai.
Ya lura da haka Murmushi yayi kafin ya fara kokarin magantuwa duk abin da suke yi da Dr.Aqeel akan idanunsa komai ya faru sosai ya ji nauyi mai girma a ransa da zuciyarsa musamman yarda ya ji muryar ta na amon kalamai mausu dauke da rauniya da gazawar zuciya.
"Mariya".
Ya fadi a dan tausashe. Ba ta dago kai ba balle kuma ya saka ran amsawarsa ko da dai ba sosai yake bukatar amsawar ta ta don ya sani dole ya ji rauni a muryarta ko da kuwa ta amsa din shi kuma abin da baya so kenan a ransa.
"Me ya sa?".
Kan ta ne taji ya daure sosai da abin da ya fadi ba ta san ina furucin masa ya dosa bata san mai zata iya cewa a matsayin amsa gareshi ba ta san tambaya yayi amma kuma bata san mai ya dace ta fadi a matsayin amsa ba sosai take jin tsauri a furucin nasa sosai take jin komai na kwance mata domin ita dai ta san ba zata ce ga abin da ya dace tace dashi ba.
Gyaɗa kai take faman yi sai motsa laɓɓanta take yi amma bata da abin cewa.
"Na rasa dalilin da baki daukar shawara, zuciyarki sam-sam bata daukar abin da ake sanar dake, Me ya sa?".
Sosai take jin nauyinsa a zuciyarta sosai take jin kamar bata kyauta masa ba don a yanayin da take jin furucinsa ya tabbatar mata kamar bai ji dadi ba. Amma kuma ba ta san dalili ba, ta san abin da yasa yayi wannan furucin ba, sosai ta fuskanci akwai abin da yake nufi da furucin nasa.
A Hankali ta fara kokarin dago kai domin kallonsa amma tana jin yarda gabanta ki bugwa da sauri sauri a hargitse ta kalle shi idanuwansa na kanta sosai yake kallonta fuskarsa ba ta san a wata matsaya zata ajje taba. Bata hango haushi a ciki ba kuma ba ta hango fara'a ciki ba. A hankali ta fara daga laɓɓanta da taji sun mat nauyi sosai bayan ta kau da idanuwanta daga gareshi.
"Hakuri...".
"Bana bukata ni ba abin da kika yi mani, kuma ba abin da nake son ji daga gareki ba kenan".
Yanayin da yayi maganar tasa sosai taji faduwar gaba don ta hango damuwa a cikinta sosai da sosai rintse idanu tayi ba ta so, ba ta so ko kadan ace ta dalilin ta mutum mai ALHERI ya shiga damuwa rashin kyautawa take hangowa a gareta.
"Ban san mai zance da kai ba, ban san ina ka dosa da maganar ka ba, bani da abin cewa domin maganar taka sosai na rasa inda zan ajje ta kayi hakuri don Allah".
Maganar ta ta tayi rauni sosai hakan ya sanya shi sassautawa a muryarsa don ya fuskanci kamar taji damuwa a maganarsa.
"Ban so na shiga rayuwarki don ta kura miki ba, ban son abin da zai kara rikitar miki da tunani, bukatata kawai shine damuwarki a ranki ki rage ta sam! hakan bai da ce ba a matakin shekarun ki Mariya sosai take jin rashin dadi a rai na da lamarin daukar ki nake kamar kanwata ban son abin da zai dinga saki damuwa bana jin dai har kasar ruhina".
Hannayensa ya yarfar cikin yanayi na rashin jindadi kafin ya sake cewa.
"ki shiga ciki don Allah ki wutar wa ranki Umma ta tashi na bata magani haka Mu'azzam ya faka amma ya koma don haka ba abin da za kiyi yanzu illa ki zauna ki ragewa kan ki tunani in kuma kina da abin yi ki je kiyi don karki zauna kuma ki fada wata duniyar ta tunani na san halin ki Please Alkawari".
Ya karashe cikin muryar rarrashi sosai da sosai taji wani iri a ranta hakan ya haifar mata da kasa mai yawa daga cikin abin da ke damunta a rai.
Kanta a kasa ta wuce shi sumui-sumui kamar maras gaskiya sai da ya ga shigewarta sannan ya saki ajiyar zuciya mai cike da tausaya kafin ya saki murmushi don ya lura ta amince da abin da yace kuma za tayi din rufe idanuwansa yayi na yan sakanni kafin ya buɗe su fuskarsa da fara'a kamar koyaushe ya fara taku domin ficewa.
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I


NA


KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.




BABI NA GOMA SHA BIYAR.
Sosai yake jin rashin natsuwa da kwanciyar hankali suna samun waje a filin zuciyarsa. Sosai yake jin wasu abubuwa masu kama da kibiyar ajali ga zuciyar na sassoke masa kirjinta. Sosai yake jin duk wata natsuwa tana fallewa da gudu daga filin rayuwarsa ta duniyarsa. Komai tafe yake da tashin hankali a yanzu cikin duniyarsa sosai yake tsammanin ba shi da wani farinciki a rayuwarsa cikin rashin zato da tsammani yake kallon komai na rugujewa a duniyarsa na farinciki kamar tubalin toka.
Sosai yake jin zuciyarsa na zafi da raɗaɗi in ya tuna abin da faru dashi kwanakin baya sosai yake ji kamar zuciyarsa zata yayyage daga kirjinsa yana jin yarda kunci ke wanzuwa a duk tuni da yayi akan abin da ya faru dashi sosai yake jin wani makaƙi mai daci daga makogoronsa har saman harshensa.
"Mu'iz ban san abin da yake damu na ba, ban san abin da ya ke kokarin dauke min farinciki da walwalar duniyata ba sosai komai ya ke kwance mani sosai nake jin bacin rai a cikin kokon zuciyata da ruhi...".
Sosai yaji wani nauyi mai girma ya na samun mazauni a kirjinsa gami da saman harshensa gabadaya yaji maganar da yake kokarin karasawa ya kasa hakan laɓɓansa wanda suka dan bushe kadan ya tura cikin bakinsa yana cizawa hadi da rintse idanuwa ji yake yi kamar ba gaske ba gani yake yi kamar a mafarki ne komai ke faruwa dashi bai taba kawo wa kansa ƙaddara mara armashi zata fado masa ba ya yi zaton shi mai sa'a ne a duniyarsa dama rayuwarsa baki daya.
A hankali ya dago kansa dake sunkuye hannunsa rike da igiyar shisha da ya gama bankawa cikinsa a tunanin sa zata dawo masa da duniyarsa kamar da a tunaninsa komai zai wuce kamar ba ayi ba a tunanin sa za tayi masa maganin matsala ko ma yace matsalolinsa da suka tokare masa duniyar farincikinsa amma abun ya ci tura.
Nisawa yayi sosai har sai da kirjinsa ya harba.
"ba zan iya ce maka ga kwanakin da na dauka cikin wannan yanayin ba amma dai zan iya tuna ranar. Ranar da takasance mani SANADI ga duniyar natsuwa ta ranar da ta kasance mani tamkar BAKAR RANA mai cike da kwazazzaban tashin hankali...".
Nisawa yayi sosai yana kokawa da numfashinsa ji yake yi yana yawo dashi a wata duniya yana kokarin barin gangar jikinsa.
Mu'iz da ya tallabe haɓa idanuwansa kan Abokin nasa yana kallon yarda yake sauyawa lokaci guda mamaki abin yake bashi yarda yake ganin tashin hankali da wani abu wanda shi kansa bai san menene ba cikin idanunsa a hankali yake gyaɗa kai yana kara gyara zaman hannayensa a haɓarsa.
"Ban san in da bahagon zancen nan naka ya dosa ba ya kamata ace ka fito ka fada min dalili ba wai abin da kake ji nake so ba a'a yarda akayi komai naka nake ganin yana canzawa lokaci guda Me Ya Sa?".
Ya ida yana mai yawata idanuwansa kan abokin nasa sosai so yake yi yana hango wani abu wanda zai bashi karin haske akan lamarin amma sam bai gani ba sai tsagwaron tashin hankali da yake cikin idanuwansa da suka kaɗa sukayi jajir matuka.
"Mu'iz me ya sa ka kasa fahimta ta ya kamata ace duk wannan furucin da nake yi ka san in da na dosa ba wai ka nuna halin-ko-in-kula ba".
Ya fadi yan gyada kai fuskansa na kara bayyanar da kuncin da yake ciki sosai zucyarsa ta fara kwaso masa wani lamari tana ajjewa a kokon kansa cikin mazaunin tunaninsa.
To da yake wannan hayagagar yace wa Mu'iz me mai zai ce masa me zai ce masa dalilin kuncinsa shi sai yanzu yake ganin wautarsa kamar yarda Khairiyya tace dashi taga rashin wayonsa da dabara akan wannan lamarin ba ta san abin da yasa yake zuzuta kankanin abu irin wannan ba wanda shan ruwa ma ya fishi sauki matuka.
Girgiza kai ya shiga yi yana jin wani sashi yana kambama lamarin sosai wanda hakan yake kara masa kunci a ransa da ruhinsa sosai yake jin wani hali na daban mai dauke da tsanani musamman in zuciyarsa ta bankado masa abin da ya faru gami da sunan da yake ji a ko wani sakan yake amsa masa kuwwa yake kara haifar masa da wasu abubuwa a zuciyarsa da ma gangar jiki baki daya.
"kai nake sauraro".
Mu'iz ya katse masa tunanin da ya afka ciki yake yawata dashi wata duniyar ta daban.
Mikewa yayi daga

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads