Showing 39001 words to 42000 words out of 227252 words
Chapter 14 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
take tsaye tana faman yatsine fuska duk da bakin glass din da ya rufe mata idanu hakan bai hana bayyanar yarda take yi da fuskarta ba cikin wani irin yanayi ta tura murfin kofar gami da sanya mata secure kafun ta fara kokarin jan kafafuwanta.
Sanye take da wasu kaya riga da wando fitted sosai wandon ya matse ta wanda iyakarsa gwaurinta mai kalar pink rigar dake jikin yar shara-shara ce mai kalar white da hannayen rigar ves ne wanda hakan ya bayyanar da rabin kirjinta sosai da ilahirin damatsan hannayenta fuskarta dauke take da Make-up sosai hakan ya kara ƙawata fuskarta ta laɓɓanta sun sha pink din jan baki sai daukar idanu suke gashin kanta ya ci gyara sosai sai fama daukar idanu yake yi ta barbaza shi a gadon bayanta a hankali take takawa saman takalamanta masu matukar tsine sosai komai nata motsawa yake a duk lokacin da tayi taku daya.
Sannu a hankali har ta isa cikin wajan wanda kallo daya zakayi masa ka tabbatar da wani babban ma'aikace bene mai dauke da hawa goma sha biyu daga yanayinsa in ka kalla sai ka rantse ba a kasar najeriya yake ba.
Kofar da zata sada ta cikin wajan ta dosa mutane da yawa masu harkokin gaban su sai bin ta suke da kallo na mamaki har ta isa kofar glass da take watayawa da mutane domin zuwa duk wani bene da suke bukata.
Ba tayi kokarin barin baban Falon dake kasa na cikin ma'aikatar ba domin ba ta bukatar haka koma ta bukata dole tayi hakuri a dalilin rashin sanin in da ta dosa ko ta shiga yau ne karo na farko da ta tako kafafuwanta zuwa cikin wannan waje yau ne farko da ta fara ajje idanuwanta akan wannan waje a zahirance yau ne kuma take bukatar duk wasu mafarkanta su tabbata yau ne take so ace sun yi gaba da gaba da shi yau ne take so komai ya zo kamar yarda ta jima tana burin abubuwa daban-daban kafin wannan rana tana so ace wannan rana ta kasance cikin ranakun da nasarrorin ta za su fara shawagi cikin duniyarta yau ne take da yakinin lissafinta zai fara aiki kamar yarda ta tsara komai nata...
"Madam!".
abin da securty din wajan babbar kofar da suke zaune daya daga cikin su ya fadi kenan yana mai mikewa bisa kafafuwansa ya tsaya gabanta.
Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da take yi ta sauke idanuwanta gabadaya akansa tana wani yatsine fuska gami da da sauke glass din fuskanta kadan manyan idanuwanta farare fes suka sauka akansa sai da ta gama kare masa kallo kafin ta gyaɗa kai cikin nuna halin-ko-in-kula gareshi.
Shima bai damu da irin kallon da take masa ba haka ya sanya abin binciken dake hannunsa yana yawatawa dashi a sassan jikinta kafin ya dago kai ya dubeta yana mai bata hanya domin karasawa wani murmushi ta saki wanda ita kadai ta san in da ya saka gaba a hankali ta kama Handle din kofar ta tura cikin wani irin taku na musamman wanda kallo daya zakayi mata kasan akwai abin da ta taka karan takun takalmanta bisa tayal din dake shimfiɗe a harabar wajan duk ya karkato da mafiya yawancin mutanen da suke zazzaune suna gudanar da aiyukansu kowanne mutum daya akwai table a gabanda da kuma fiyal fiyal gefe guda kuma kwafuta ce girki tacin glass dinta take ƴawatawa da idanuwanta a dukkanin sassa da kowa ni mutum dake zaune sosai ta lura ita suka zuba wa idanu murmushi ta saki har gefen kumatun ta na loɓawa sosai taji wani abu na yawatawa a cikin kirjinta wanda take jin sa ba abin da ke cikin sa sai hango abubuwan da take tsammanin za su faru.
"Heyy".
Abin da ta fadi kenan gaban wani table da wata mace ke zaune hankalinta gabadaya ya ta'allaka ga aikin da take yi sanye take da jallabi mai kalar Ash ta nannaɗe fuskarta da kallabin jallabiyar fuskarta fayau ba wata kwaliyya ta azo a gani amma hakan bai hana bayyanar tsantsan kyan da Allah yayi mata baiwarsa ba.
A hankali ta fara dago kanta ta na saukewa a in da ta ji maganar sosai ta ware idanu ganin wacce take gabanta cikin yanayi na mamaki da wani irin haushi da ya kasa boyuwa har sai da ya fito cikin idanuwanta gyaɗa kai tayi kafin ta mai da kanta kan Aikin ta.
"Dr.Abdurrazaq Erena".
Abin da ta fadi kenan tana mai wani kara bayyanar da wani murmushi dake fuskarta wanda kallo daya zakayi masa ka san ba a so ba.
Ba tare da ta dago da kallonta ba murya kasa kasa.
"Hawa na biyar hannunki na dama office mai lamba Uku".
Ba ta tsaya ansa ta ba ta dauko kafafuwanta ta fara tafiya a haka har ta hau Abin da zai kaita wajan cikin yan sakanni ta isa bayan ta sauka ta kalli kwatance da kayi mata wata kofa glass ta hango sannan ta kalli samanta murmushi ta saki ta fara takawa a hankali ta isa sakatariya ta gani zaune tana ta faman aikinta hankali kwance kwankwasa kofa glass din tayi kadan tana mai kallonta cikin wajan a hankali ta dago kai ita ma ta sauke a kanta murmushi akan fuskarta lokacin da ta dago amma tana cin karo da wacce ke gabanta ta tsuke fuska hadi da jan guntun tsaki tana kau da kanta.
Sai da ta shafe sakanni kafin tayi mata alamun ta shigo a hankali ta taka ta shiga ta dan yi kasa da glass dinta ta shiga motsa laɓɓanta.
"Please wajan Dr. Abdurrazaq Erena nake bukatar zuwa".
Kallon ban gane ba sakatariyar tayi mata tana mai kwaɓe baki kafun ta kau da kai hadi da fadin.
"Ya san da zuwan ki ne?".
Shiru tayi ba tare da cewa komai ba na yan dakiku hakan ya kullar da sakatariyar da sauri ta shiga duba cikin kwafutar dake gabanta tana yawatawa da idanuwanta cikinta.
"Duk yau a cikin jerin mutanan da za su zo gare shi ban ga alamun da ke a ciki ba".
Ta fadi tana mai dago kanta ta saukewa gareta.
a dan harzance ta sauke glass din ta sosai idanuwanta kan sakatariya kallonta take yi tana karantar yanayin da alamun so take ta samu wani tangarɗa da zata jona mata amma cikin nuna na fiki.
"ki je ki ce masa Areefa Saifullah ita ce take son ganin sa ya san da zuwana".
Yanayin yarda take maganar a dake da yanayin bacin rai ya sanya sakatariyar ware idanu sosai gami da tallaɓe haɓa tana kallon yarda wannan mai kalar gangar ke mata magana akai.
A hankali ta mike saman kafafuwanta masu sanye da wasu takalma masu matukar tsine kamar za su karye a hankali ta fara taku da dan guntun suket dinta wanda iyakarsa guiwa kadan taɓe baki Areefa tayi tana bin dumemiyar matar da kallo wacce tayi biyunta.
Mintina kalilan sai gata ta dawo tana faman tsuke fuska.
"ki Shigo kofa ta uku ita ce in da yake ciki".
Gyaɗa kai kawai tayi gami da wucewa tana taku ko ina na jikinta rawa yake yi lokaci guda ta canza tafiyar da take yi ita dai sakatariya sakin baki tayi tana kallon ikon Allah har sai da Areefa ta bace mata sannan ta saki ajjiyar zuciya ta koma ta cigaba da aikin da take yi.
"Areefa Saif...".
Abin da ya fadi kenan yana hanzarin mikewa cikinsa har ɓari yake yi ya zagayo izuwa in da take tsaye hannunta rike da Handle din kofar sai faman yawatawa da idanuwanta take yi cikin Office din har ya iso ya tadda ita nan tsaye sai faman sakin wani murmushi yake yi hakan ya bayyanar da wawulan hakorin sa daya na gaba da ya cire amma in ba ka gane ba sai kayi zaton wushirya ce ta buɗe sosai a jerin hakoransa masu dan duhu kadan.
"Ban yi zaton ai yau zaki zo ba, domin Alhaji Abdulwahab ce mani yayi sai nan da gobe".
Ya fadi har lokacin idanuwansa na bin duk wani sashi na jikinta yana kallo kafun ya yi mata nuni da kujerun dake cikin office din alamun taje ta zauna sosai take kallonsa ta cikin glass dinta tana karantar yanayinsa sosai take hango komai kamar ma ya yuwu kallonsa take yi tun daga fuskarsa har kafafuwansa babban mutun ne don a kalla zai baiwa shekaru hamsin baya amma hakan bai nuna a fuskarsa ba saboda yanayin huta da jindadi da suka taimaka ma jikin nasa baki ne amma ba can ba yana da idanuwa masu dan girma sun dan yi ja kadan hancinsa ba dogo bane yana da fadi haka ma bakinsa mai dauke da manyan laɓɓa masu kalar baki baki haka zai tabbatar ma da yana shan wani abu.
Ba tare da ta ce da shi kala ba ta doshi cikin Office din sosai tana wata irin tafiya ta firgita duk wani namiji da yake gabanta har ta isa ta zauna ta ajje jakar dake hannunta gami da daura kafa daya kanta daya a hankali ta sauke glass din dake fuskarta gabadaya shima ta ajje shi kan Table din dake gaban kujerun ajje numfashi tayi alamun gajiya gami da dan dafe kai.
A hankali ya fara takowa in da take kallo daya zakayi masa kasan sosai Areefa ta tafi da guntun imaninsa jikinsa sai ɓari yake yi fuskarsa tana sakin murmushi idanuwansa kamar za su fado kasa.
"Areefa Saif...".
Ya sake fadi cikin salo na yin kasa da murya kamar wanda yake rokon wani abu a gareta.
Kaɗa idanu tayi gami da dan daga girarta tana mai yawatawa da idanuwanta akan sa zuciyarta nayi mata wani tsalle na murna da jin wani dadi amma bata bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba domin a gimtse take ba alamun dariya.
A hankali ta fara motsa laɓɓanta da wani irin yanayi tana mai kaɗa idanuwanta.
"Ya kamata ace ka koma ka zauna domin time dina a tsare yake akwai in da zan je ne".
Ta fadi tana da murmushi a fuskarta da sauri ya ja gefe gami da ware idanuwansa sosai ba tare da yace komai ba ya koma can inda kujeransa take mai juyawa ya zauna gami da saka kan biro a bakinsa yana cizawa kujerar na watayawa dashi idanunsa akanta sai faman sakin murmushi yake yi a hankali ta kau da kai gami da tura masa fiyal din da ta zo dashi.
Hannusa guda ya kai yana janyo fiyal din yana mai sauke idanuwansa akansa buɗewa yayi a hankali yana yawatawa da idanuwansa a cikin tsayin minti daya kafun ya mai da ya rufe ya dan bugeshi kadan ya dago kansa ya dubi Areefa wacce ita ma hankalinta na kansa ta na kallon yarda yake duba fiyal din.
"Komai yayi daidai zaki iya fara aikin zuwa On Monday in kuma akwai Time din da kika zaba zaki iya amfani dashi...".
Hannunta ta dan daga kadan tana dan murmushi.
"No ba ni da wani lokaci sai wanda ka yanke mani domin ina bukatar fara aikin ne akan lokaci ba tare da zabina ba sai zabin da kuka bani".
Ta karashe tana mai mikewa kan kafafuwanta gami da daukar jakarta ta.
"Ina Godiya".
Ta fadi tana mai kara sakar masa murmushi shi dai idanuwansa har zuwa lokacin suna kanta kamar wanda aka jona wa mayen karfe har ta fara taku amma bai motsa ba motsin Handle din da ya ji ne ya fargar dashi da sauri ya ware idanu yana kokarin tashi amma ina kafun ma ya kai ga tashi ta fice daga cikin Office din komawa ya yi ya zauna jikinsa ba kwari hannu bibbiyu ya tallaɓe haba da su yana kallo kofar yana faman sauke numfashi a hankali.
[8/26, 7:29 PM] 80k: UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA GOMA SHA UKU.
Kai komo kawai take yi a tsakar dakin ako wani takunta daya sai ta dubi Huzaif tana mai ajje numfashi sosai da sosai take jin haushinsa da takaici akan abin da ya aikata sosai take kallon abin a matsayin babban kuskure mai girma sosai a idanuwant sosai take ganin wautarsa da ganganci da kuma yada zuciya kare ya dauke.
Numfashi ta ajje bayan ta tsaigata da kai komon da take yi sosai ta ajje ganinta akansa.
"kasan kuwa abin da ka aikata kasan kuskuren da ka aikata ya girmama sosai a idanuwa...Well bana tunanin kai lamarin ka dauke shi a matsayin kuskure mai girma a idanuwanka".
Ta fadi tana mai cizon laɓɓanta bayan ta turasu cikin bakinta sosai zuciyarta ke zafi da raɗaɗi akan komai da ya aikata sosai take jin abu mai nauyi ya tsaya mata a kirji ya samu gurbin zama sosai take jin tamkar ita ce akayi wa wannan cin kashin.
"Bana tsammanin Huzaif din dana sani ne wannan bana tunani Huzaif din asali ne wannan anya kuwa ba wasu abu akan ka ba na tunanin abin da kake sha zai sanya ka aikata wannan kuskuren mafi girma a idanuwana".
Ta sake fadi tana mai girgiza kai sosai take jin komai da ya faru yana dawo mana ina ma tasan hakan zata kasance da tabbas sai Mariya ta raina kanta kamar ta yarinya karama har tasan ta daga hannu ta mari namiji namijin ma Huzaifa.
"Kaico!".
Cikin wani irin sauti ta furta kalmar tana jin ɗacin lamarin ako ina na zuciyarta da ruhinta.
Harɗe hannayenta tayi a kirjinta tana kallon yarda komai na Huzaif ya canza sosai take ganin lalacia tsakanin idanuwansa da zuciyarsa sosai take hango gazawa a gareshi kau da kai tayi domin in har ta cigaba da dubanda da ganinta tabbas zuciyarta zata iya bugawa don tsananin takaici.
"Yaa Allah ta ya ya zan dubi wannan lamarin a wani MIZANIN HANKALI ya dace na ajje wannan lamarin bana tunani ko mai tabuwar kwakwalwa zai iya abin da ka aikata...".
"KHAIRIYYA".
Muryar Huzaif ce ta karaɗe dakin cikin wani irin sauti mai tsoratarwa cikin rashin tsammanin samun maganarsa ta ji ya ambace sosai ta saki zaren kalamanta ta saki baki tana kallonsa sosai take jin gabanta na bugawa gabadaya ganinta ta ajje a fuskarsa komai na shi take kallo da yarda tashin hankali da bacin rai suka nuna a filin komai nashi har zuwa lokain idanuwansa a rufe suke hannayensa saman fuskarsa sai faman juya su yake yi.
"Excuse me. Please".
Abin da ya sake fadi kenan idanuwansa a rufe tana kallon yarda laɓɓansa suke rawa sosai wajan furta ko wani harafi guda na kalaman da ya furta.
"ki bar ni naji da abin da ke kokarin yayyaga mani zuciyata please ki barni naji da abin dake kokarin tafiya da ruhina sosai da sosai nake jin bani bane Khairiyya bana zaton ni Huzaif".
Yanayin yarda laɓɓansa ke rawa da yarda kalaman nasa suke turereniya ga junansu hakan zai tabbatar maka akwai tashin hankali mai girma a zuciyarsa da ruhinsa wanda bai yi zaton wanzuwansa ba a duniyarsa sosai komai na tashin hankali ke bayyana kansa a ko ina nasa.
Rintse idanuwa Khairiyya tayi sosai da sosai take jin wani abu mai nauyi na samun gurbi a zuciyarta sosai da sosai take jin zata iya daukar kowa ni tashin hankali da take hangowa cikin idanun Huzaif ba za ta iya daura ganinta ta cigaba da ganin halin da yake ciki ba ba za ta iya cigaba da jin numfashin sa mai cike da tashin hankali ba.
A hankali ya fara kokarin daga dan yatsar sa dake fama karkawa sosai yake jin wani iri cikin zuciyarsa da inda take zaune a kirjinsa gani yake kamar wauta ya tafƙa sosai a duniyarsa amma ban yi amanar haka a zuciyarsa ba hango Mariya yake yi a matsayim wacce take kokarin kashe kan ta da kanta domin kuwa sosai ta dauka wa kanta fitinar da ba zata iya saukewa kanta ba sosai yakke ganin hauka cikin komai da take aikatawa sosai yake ganin rashin kunya da fitsara tsantsa cikin idanuwanta dole ya dau mataki ko ba komai ya koya mata rayuwar duniyar nan da yarda 'ya mace bata isa ta galaba akan ko wani ɗa namiji ba dole ta san waye HUZAIF ABDURRAZAQ.
A hankali ya mike yana duban Khairiyya da ta zuba masa idanu sosai murmushi yayi gami da dauke kan sa.
"You can go".
Abin da ya fadi kenan ya fara daga kafafuwansa cikin wani irin yanayi mai cike da abubuwa marasa dadi ga zuciyarsa Toilet ya nufa har zuwa lokacin idanuwan Khairiyya na kansa sai faman suke numfashi take yi a sauri-sauri sosai take jin wani iri a zuciyarta sosai take hango abin da zai dauko mata tashin hankali ya ajje mata a rayuwa sosai take hango abin da zai hanata rawar gaban hantsi a duniyar Huzaif sosai take hango komai na wargaje.
Numfashi take ajjewa mai dauke da abubuwa masu yawa da take zaton za su sayo mata tashin hankalin rayuwa a hankali ta daga jakarta zuwa kafatar tana faman gyaɗa kai kawai take yi tana tana jin wani abu mai nauyi na sakar mata a zuciya da duk wani gurbi na cikinta a hankali ta fara takunta domin ficewa daga dakin zuciyarta na wassafo mata abubuwa ma bambanta.
********
Sosai da sosai take jin wani irin tashin hankali na kokarin samun masauki a ko ina na sassan jikinta sosai take jin yarda kwakwalwarta ke kwala ihu akan tunanin da ya zo mata a bazata sosai take jin wani sauti mai kara sosai yana amsa kuwwa a kunnuwanta sosai.
Bugun zuciyarta yake kara sauri sosai da sosai takun da take yi da kafafuwanta suke aika mata da wani lamari na daban wanda yake kara hargitsa tunaninta idanuwanta a rintse suke komai take hangiwa komai da komai da ya faru yake dawo mata baya kamar yanzu ne yake faruwa a gigice take ajje numfashi mai tauri a kokarin janyo mata ruhi zuwa waje.
Bata san lokacin da tayi cilli da fakar dake hannunta ba ta sanya hannayenta zuwa kunnuwanta ta rufe su ji take kamar za su tarwatse dalilin sauti da ke musu sukuwa a ko wacce dakiƙa.
"Yaa Allah!".
Abin da ta furta kenan a kasan laɓɓanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa a gareta jin gina tayi da kofar da zata sadata da cikin dakin gabadaya taji kafafuwanta na kokarin gaza daukar gangar jikinta ji take yi kamar jikin ba nata bane sosai take hango fuskarsa tun ranar farko komai yake dawo mata har izuwa wannan lokacin sautin saukar marin da tayi masa take ajin yana samun wajan ajje sautinsa a