Showing 207001 words to 210000 words out of 227252 words
Chapter 70 - Uku Bala'i Complete Romantic Book By kamala Minna.txt
buɗewa yayi yana kallon ko wani sashi na cikin sa kaya ne makil a cikinsa a shirye hannu ya sa ya shiga dagawa yana kallo so yake yi ya zabi wanda zai saka amma gabadaya kayan ma jin su yake yi wani iri ya jima a tsaye yana zarowa yana mai dawa ya rasa wanda zai dauko lokaci kankani duk ya yamotse sif din kafin ya zaro wani lallausar yaɗi light-blue mai dikon dark anyi masa dinkin zamani wanda ya fita sosai.
Bakin gado ya ajje su sannan ya juya ya koma wajan Mirrow din fuskarsa ya dan gyara sannan ya koma ya zura kayan a jikinsa wanda sukayi matukar hawan sa sosai suka kara fidda masa da kyansa gami da kwarji agogon Rolex ya daura a hannunsa gami da kafa hularsa wacce ta hau kayan sosai takalmin kafarsa sau ciki baki sai daukar idanu yake yi glass ya saka a idanuwansa wanda ya kara sirrinta yanayin da yake ciki.
Key din motarsa ya dauka gami da wayoyin sa bayan ya feshe jikinsa da daɗaɗar turarurruka masu sanyin kamshi a hankali ya shiga taka kafafuwanta yanayin sa kadai zai nuna maka ba ya cikin nishadin zuciya saidai cikar halintarsa da mazatakarsa da ka kalla zaka gane namiji hadadde mai ansa sunan sa na mijin.
Kokari yake yi ya aikata abin da zuciyarsa take hana shi so yake yi ya koyi wannan rayuwar da aka zaɓar masa bashi ya zaɓa ba so yake yi ya koyi rayuwar da ake cewa ba zai yi nadama akan ta ba so yake yi ya matse zuciyarsa ta koyi abin da ake so ta koya so yake yi a wannan ranar komai ya canza so yake yi zuciyarsa da koyi kaunar wacce ake so ya mikawa soyayayarsa ya sani SO ƘADDARAR ZUCIYA ne so ne kadai ke wahalar da ita ya sata cikin duk wani kunci da gangar jiki zai wahala shi ma.
Da wannan tunanin ya isa gaban sabuwar motarsa kirar Benz mai kalar baki sai faman daukar idanu take yi sai da ya kare mata kallo yau ne rana ta biyu da zai hau ta tun da yayo odarta haka kawai yaji yana bukatar ya fita da ita daga can nesa ya hango mai gadin sa hannu ya daga masa da gudu ya iso gareshi yana mai kwasar gaisuwa kafun ya mike ya nufi wajan Get ya hangame shi a daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya shige motar har yayi mata key ya doshi Get din a hankali har ya fice mai gadi nayi masa a dawo lafiya sannan ya mai da Get din ya rufe.
****
Gabanta ne ya yanke ya fadi sallamar da tayi ba ta karasa ta ba taja burki ta tsaya sai faman rarraba idanu take yi shi kuwa ya kafe ta da idanu kamar zai haɗiyeta hakan ya kara rikita mata lissafi ji tayi kamar ta juya ta falle da gudu amma jin muryar Hajiya ya sanyataa motsa kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa a hankali ta shiga takawa tana karasa cikin falon ko ina na jikinta rawa kawai yake yi ga wani dokawa da gabanta ke yi musamman irin kallon da ta ga Tareeq na yi mata kau da kai tayi shiyasa sam bata son zuwa gidan nan ko don saboda shi ba ta son irin abin da yake yi mata.
"Ina yini Mami".
Mariya ta fadi bayan ta isa gareta ta zauna.
"Lafiya lau Mariya ya gida ya su Umman taki da Abban naki?".
Gyaɗa kai tayi kafun ta ansa da cewa.
"Lafiya lau duk suna gaishe ku".
Daga nan bata sake tsinkawa ba sai Mami ce ta sake cewa.
"Shekaran jiya ai mun je kina Islamiyya ba mu tadda ki ba".
Murmushi tayi gami da kokarin mikewa.
"Umma ta gaya min Mami Allah ya saka da alheri ya kara buɗe gami da rufin asiri...".
"Mariya kar ki sake kin ji ko ai mun zama daya komai aka yi muku a gidan nan ai ba faduwa bane kun zama yan uwanmu mu ma haka duk an zama abu daya...mutuniyar taki tana ciki kisan dai san halinta kullum tana kunshe a daki kamar mai zaman takaba".
Dariya ta sake yi sannan cikin hanzari ta nufi sama sashin Baseera zaune ta same ta hannunta rike da littafi da sauri ta karasa kusa da ita ta zauna sam hankalinta ba ya jikinta domin tunani take yi ba wai karatun littafin ba da sauri Mariya ta zungurar mata kafaɗa a firgice ta dube ta ganin Mariya ya sanyata zaro idanu waje tana mai da numfashi ta shiga motsa laɓɓanta tana son yin magana amma ta kasa.
"Kin kyauta Baseera wato shi ne kika dauke mani kafa ko kirana ma da kike yi a wayar Umma kin daina sabida na yi miki laifi mai girma ko har da ya kai kiyi mani hukunci irin haka....Hmm Hakuri na zo na baki akan abin da nayi miki ba daidai...".
Da sauri Baseera ta rufe mata baki wasu kwalla na taruwa a idanunta ta shiga girgiza kai .
"Ba haka bane wallahi ba na jindadi ne...".
Turo kofar da akayi ne ya sanya Baseera saurin yin shiru tana goge fuskarta Mami ce ta shigo duban su tayi ganin yanayin da suke ciki batare da tace komai ba sosai suka gane kallon zargin wani abu take yi musu.
"Baseera kin yi bako".
Abin da ta fadi kenan ta fice daga cikin dakin gaban Baseera ya buga gami da duban Mariya da ita ma idanuwanta suke kanta kallan kallo suke yi wa juna kafun Mariya tayi murmushi tana mai dafa kafaɗarta.
"Kin yi bako aka ce".
Runtse idanu Baseera tayi tana jin yarda gabanta ke yankewa ya na faduwa.
"Ban san waye ba Mariya ba muyi da wani zai zo waje na...".
Daga mata hannu tayi tare da mikewa tana kamo kafarta doguwar riga ce a jikinta don haka ta janyo mata gyalan rigar ta yafa mata fuskarta ba wata baci tayi ba don haka ta ja hannunta suka fice.
A harabar gidan suka hango mota girke da sauri suka dubi juna gaban Mariya ne ya fadi tana tunano inda ta san motar nan sosai ta ke ji a ranta ta taba ganinta amma ta rasa waye mai ita...
Bata gama tunanin tuno mai motar ba ta ga an buɗe kofar ana kokarin fitowa da sauri ta runtse idanu jin yarda kirjinta ya doka rikon da taji Baseera tayi mata ne jikinta na karkarwa tana jin yarda take kokarin yi mata magana amma ta kasa hakan ya tabbatar mata da zarginta da sauri ta zare hannunta daga na Baseera tana kokarin juyawa ta koma ciki amma jin amon muryar sa ya sanyata tsayawa cak! tana mai da numfashi takun takalminsa da yake tunkaro su hakan ya kara rikita mata lissafi ta kara danke idanuwanta kamshin turarensa take ji ya dokar mata hanci zuciyarta take ji tana matsewa da wani irin yanayi tana mikata wani mataki bata san ya za tayi ba bata san da wani idanu zata kalle shi ba sosai take jin rashin adalcin da tayi masa a ranta haka kawai take jin wata kunyarsa ta ratsa ta.
"Gani na zo domin yiwa so biyayya Mariya abin da kika bukata shi na zo yi domin tabbatar da abin da kike tsammanin ba haka bane".
Wata irin bugawa taji zuciyarta tayi da sauri ta juyo gami da buɗe idanuwanta da suka kaɗa sosai ta dubi Baseera da tayi fakare da idanu tana dubansu daya bayan daya zuciyarta na bugawa da tashin hankali ashe da gaske Mariya take ashe abinda take faɗi mata zatayi ashe zata yi din da gaske.
girgiza kai ta shiga yi tana saka idanuwanta cikin na Mariya da ta gama shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
"Ban gane ba Mariya mai hakan ke nufi?".
"Soyayyarta ta sadaukar gareki".
Zare idanu Baseera fuskarta da wani irin yanayi mai girma a zuciyarta sosai take jin zuciyarta na matsewa da tashin hankali maganganun Dr.Aqeel take jin su wani iri a gareta sosai take jin suna hawa mata kai hannunta taji Mariya ta kama ta damke sosai da sauri ta dago ta dube ta idanuwanta ta gani cike da hawaye suna kokarim zuba.
"Kin yi mani alkawari in har ya amince ke ma zaki amince don Allah karki watsa min kasa a idanu Baseera ki dubi Dr.Aqeel a matsayin masoyi mai kaunarki tsakani da Allah kiyi mani wannan sadaukarwar don Allah ban taba neman alfarma gareki ba sai yau don Allah ki anshe ta".
Fizge hannunta Baseera tayi tana mai da numfashi zuciyarta take ji tana bugawa da wani irin yanayi.
"A,a Mariya ba na tunanin hakan za ta faru karki takurawa zuciyoyin da ba sa kaunar junansu karki yi kokarin hada abin da kika san ba zai taba faruwa ba karki hada abin da kika san zuciyoyi ba za su samu farin ciki ba".
Ta fadi muryarta na rawa wasu hawaye na zubo mata a hankali ta shiga ja da baya tana girgiza kai.
A daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya kara takowa kusa da su sosai zuciyarsa yake ji tana matsewa da kuna gami da radadi runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan Mariya wacce gabadaya ta gama shiga wani yanayi idanu suka hada tayi saurin dauke nata zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
"BASEERA!".
muryar Dr.Aqeel ta doki kunnuwanta sautin na ansawa a kwanyar zuciyarta na buɗewa sosai tsayawa tayi cak! tana mai da numfashi kafun ta dube shi kallonta yake yi da wani irin yanayi wanda ba zata ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
"Na anshi soyayarki in har zaki iya bani nima zan baki zuciyata gabadayanta".
Ya fadi yana mai runtse idanuwansa zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin yanayi mai kokarin haifar da bugun zuciyar sosai yake jin idanuwansa na zafi da raɗaɗi ko ina na jikinsa yake jin lokaci guda ya tsaya jinin jikinsa yake ji ya shiga gudu da sauri-sauri kwanyarsa yake ji tana hayaki kamar zata kama da wuta.
Mariya kuwa mutuwar tsaye tayi ba abin da take fadi sai 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un' wata katangar tashin hankali ne taji ta rikito mata hannayensa duk biyun ta saka ta dafe kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa kanta taji ya shiga dokawa kamar zai rabe biyu muryar Dr.Aqeel da taji yana furta kalaman so jin saukar su take kamar garwashi wuta runtse idanu tayi gami da kokarin saita kanta kafun ta taka kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita kasa hannayenta ta kamo ta sarke a cikin nata.
Idanuwansu suka sarke da juna murmushi Mariya tayi mai tafe da hawaye.
"Ki amince ke ma Baseera zuciyoyinku su kasance waje daya su rayu tare su zama abu daya har gaban abada".
Girgiza kai Baseera ta shiga yi idanuwanta na kara ballewa da hawaye a hankali ta zare hannayenta gami da duban inda Dr.Aqeel yake wani kallo tayi masa kafun ta juya cikin hanzari tayi cikin gida.
Mai da numfashi Mariya tayi tare da duban Dr.Aqeel shima ita yake kallo kafun ya girgiza kai yana cizon laɓɓa wani murmushi yayi tare da juyawa ya nufi motarsa...
*Kamala Minna*💞💞💞💞
[10/25, 5:38 PM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA NA SITTIN DA SHIDA
A hankali take tafiya kanta akasa ga wani zundumemen Hijabi da ta saka a jikinta har yana sharar kasa hannayenta cikin hijabin sai wasa da su take yi.
Kallo daya zaka yi mata ka gano yanayin rashin kwanciyar hankali a tattare da ita fuskarta tayi fari sosai ga wata rama da ta zabga kamar wacce tayi ciwon shekara guda.
Ratso layin take yi tana bin gefe mutane sai binta da kallo suke yi kamar sun ga watan ramadana sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗin wannan fitowar da tayi bata taba zaton zata tsani kanta ba sai a cikin wannan kwanakin da fita ma gagararta take yi in kuwa ta fito an dinga zundenta kenan ana nuna ta da baki wasu har tararta suke suna gaya mata magana son ransu sai dai ba yarda zatayi ita ta jawo wa kanta.
Cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani taji an janyo mata hijabi ta baya wata irin dokawa taji gabanta yayi zuciyarta harba da sauri ta dago kanta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici dubansa take yi tun daga kasa har sama bata san shi ba bata san daga ina yake ba.
"Ke ba kya ganin mutane ana yi maki magana kin yi banza da mutane iye wacece ke dan kan...".
Ya lailayo ashar ya dire gami da daga hannunsa daya yana kokari kife ta da mari mai ya gani kuma sai ya sauke yana mai da numfashi.
Sosai tsoro ya bayyana a fuskarta a hankali ta shiga ja da baya tana raɓashi zata wuce don ta lura dan iskan gari ne dan kwaya in ba don haka ba ai bai isa yayi mata wannan cin mutuncin ba ta kyaleshi da sai ta keta masa rashin mutunci amma halin da take yanzu ba zata iya ba duk da zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke yi akan zagin kare dangin da yayi mata.
Sake fizgo mata hijabin yayi ganin tana kokarin raɓashi ta wuce ya tsaya dab da ita har suna shakar numfashin juna ba abin da ke tashi a jikinsa sai warin solisho da sukuɗaye kau da kai tayi da sauri gami da toshe hanci wani yinkuri taji zuciyarta ta nayi tana kokarin yin amai.
Ganin abin da take yi masa yasanya shi duban fuskarta da take yatsine masa tana toshe hanci wata irin ashariya ya danna mata gami da cafko hijabin jikinta ya cikuikuye.
"Ke dan kan uban ki ni kike toshewa hanci to ubanki ne ke wari ba ni ba matsiyaciya karuwan banza da wofi".
Yana fadin haka ya fizge hibajin gabadaya daga jikinta daga ita sai zani da ves ga katon cikinta da ya fito sosai wanda haihuwarsa nan kurkusa runtse idanu tayi gami da toshe kunnuwanta wani kuka ne ya zo mata da sauri ta durkushe tana mai sakin sa shi kuwa sai faman danna mata ashar yake yi.
Lokaci kankani mutanan layin duk suka taru aka rasa wanda zai zo ya kwace ta domin kuwa suna tsoron TANGA ba wanda bai sanshi ba a fadin garin nan tattarin dan jagaliya ne kashe mutum a wajansa ba komai bane yayi zaman gidan kaso yafi a lissafa a fitowa dashi.
"In kana yiwa Allah da Annabi ka bani hijabi na".
Ta fadi cikin muryar kuka jikinta sai rawa yake yi wani takaici take ji a zuciya ji take kamar ta hadiye zuciyar ta mace.
Cilli yayi da hijabin da sauri ta rarrafa za ta dauka ya danne mata yatsun hannu ta kurma uban ihu a daidai lokacin motar Dr.Karami ta sanyo kai ganin abin dake faruwa a layin ya sanya shi taka burki ya fito da sauri yana duban mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallon rigimar Hafsat da Tanga da sauri ya isa wajan sam bai san wacece ba amma ganin irin cin zarafin da ake yi mata ya sanya shi zuwa ya hankaɗe tanga a daidai lokacin ita kuma Hafsat ta dago kai.
'Innalillahi' abin da Dr.Karami ya furta kenan yana ja da baya duban ta yayi kafin cikin hanzari ya isa ya dauko mata hijabin nata ya yafa mata a jikinta cikin sauri duban mamaki yake mata da al'ajabai ganin yarda ta koma kamar ba ita ba.
"Hafsat me ya hadaki da wannan mutumin har yayi miki wannan cin zarafin?".
Girgiza kai kawai take yi zuciyarta na suya hawaye sai ambaliya suke yi mata a fuska numfashi taja mai cike da takaici ta mike kan kafafuwanta ta dubi Tanga sannan ta dubi Dr.Karami a hankali ta raɓashi zata wuce gabanta ya sha yana mai sake tambayarta amma ta kasa bashi ansa kuka kawai take yi abin duniya ya yi mata yawa abin da bata so a gane yau gashi a bainar jama'a kowa ya gani kuma ya san halin da take ciki dama an dade ana zarginta yau dai gashi zargin ya tabbata kowa zai tsine mata da kazamar rayuwar da ta zaɓawa kanta wanda take ciwa mutunci take yi wa kallon banza ta sani yau sai sun zuba ruwa aka sun sha.
Ihun da taji ne ya katse mata dogon tunanin da take yi cikin razana ta juya Dr.Karami ta hanga ya cakumi Tanga sai jibgarsa yake yi gabadaya ya kumbura masa fuska bakinsa har ya fashe yana zubda jini ware idanu tayi mamaki ya sake cikata da sauri ta ja jiki ganin hankalin mutane ya bar kanta ya koma wajan su Dr.Karami.
Tafiya take yi cikin sauri-sauri kamar zata kifa hijabin sai harɗe ta yake yi tattareshi tayi sosai ta rike a hannu ta shiga jefa kafarta a duk in da taji ta dira idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir tana kokarin karya kwanar da zata shigar da ita gida suka yi arba da Abulle kallo ta bita dashi daga sama har kasa kafun ta dauke kanta cike da takaici da bakin cikin wannan rayuwar da 'yarta ta tsinci kanta a ciki Allah na gani tayi bakin ciki tayi takaici tayi kuka sosai a kan wannan lamarin zuciyarta ji take yi kamar za ta soye don raɗaɗin da take ji tun da abin nan ya faru ta kasa kwanciyar hankali kullum cikin fargaba take akan abin da zai je ya dawo.
"Daga ina kike?".
Ta fadi fuskarta a daure tamau kamar bata taba yin dariya ba ba alamun tausayi amma in da zaka fasa zuciyarta tausayin 'yar ta ta ne makil a cikinta.
Girgiza kai Hafsat tayi hawaye na sake balle mata sautin kukan da take boyewa ya bayyana sosai hakan ya kara tayar da hankalin Abulle da sauri ta riko mata hannu tana mai tambayar ta cikin yanayi na firgici amma ta kasa magana sai girgiza mata kai take yi tana kai hannayenta saman bakinta tana toshewa.
Riko ta tayi sosai ta sanyata gaba suka nufi gida tafiya suke yi gabadayan su zuciyoyinsu na suya musamman Hafsat in ta tuna cin zarafin da