Showing 36001 words to 39000 words out of 159513 words
Chapter 13 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt
mahaifiyar tasa
''UMMI mene laifinta,yanzun ita ba mutum bace da baza a sota ba,kuma tana da iyaye......Ni gaskiya da in auri wannan yarinyar Allah gara na k'are rayuwata babu aure''.........
Kafin ya k'arasa ta wanke shi da mari tana nuna shi da hannu
''Wallahi SON baza ka kunya tani ba ASHNA ce baka so,to ka sa aranka kai da ita anyi an gama sha³''.......
Dafe da kumatunsa yake kallonta,tsawon tasowansa bata tab'a masa fad'a ba,amma yau har da mari,shi kam a ransa a k'udurce shi da ASHNA sai dai kallo,me zaiyi da wannan ballagazar?
Jin kalamanta na k'arshe ya tsorata,take hawaye ya shiga biyo kumatunsa,yasa hannu ya goge kallon UMMIN nasa kawai yayi ya fice....
Hawayen da ta gani a fuskarsa shi ya bata tsoro,da girmansa yake mata kuka,tabbas tasan bai tab'a ce mata ga wata mace da yake soba,lallai ko wannan yarinya duk inda ta fito ta daban ce.....
Tunani duk ya addabeta,haka ta zauna duk kuma sai taji babu dad'i,tasan gaskiya ya fad'a,to wai kam ita ya za tayi ne????
Yana fita daga parlorn direct gidan ya bari dan yasan hakan kad'ai shi ne solution,idan ta nemeshi ta rasa a gidan zata sakko....
Shi kad'ai yayi wani murmushin takaici,lokaci guda kuma wata tsanar ASHNA ta diro masa,aiko nan ya lashi takobin wallahi ko me za ayi bazai tab'a aurenta ba,da haka ya d'auki hanya wanda baima san inda zai nufa ba.....
《《》》
Tsawon kwanaki uku kenan bai sake sata a idonsa ba,duk inda ya so da ya ganta kamar wacce tasha sab'ani haka suke ta bugawa,da zaran ta shigo shi kuma yana d'aki,lokacin kuma da ta fita zai fito....
Yana kwance kamar wanda aka tsikara da allura ya mik'e parlor ya fito ya kwanta babu kowa cikin parlorn...
K'amshin da yake jiyowa daga kitchen shi ya sa ya mik'e fuskarsa ta dad'a kyau saboda yanda tayi fayau uwa wanda yayi jinya,a bakin k'ofan ya tsaya ya jima yana kallonta,sam bata san da mutum a bayanta ba,ya jima a haka hannayensa a hard'e kan k'irjinsa.....
MAMA ce ta fito cikin shirin fita da yake gidan ba kowa duk suna skul,kallon hanyan kitchen en tayi saboda ta ga kamar da mutum a tsaye,mamaki fal zuciyarta yanda ta ganshi yayi a gurin....
''SON zan fita''
Tayi maganar cike da k'ulewa,aiko ya juyo a d'an firgice yana kame² ya dawo cikin parlorn,sam ya rasa wace kalma zaiyi amfani da ita gurin kare kansa,kansa ya d'an kawar gefe
''Allah ya kiyaye hanya''
Ya furta a hankali,da harara ta rakashi ta fice,nan ya kwanta yana d'an murmushi,duk wani shige da ficenta akan idonsa take yinsa,zuciyansa fal far in ciki....
*********
''Tabbbb tun kafin wannan al'amarin ya afku gara nayiwa tufkar hanci''
Fad'in HAJIYA MURJA kenan da suke tafiya cikin motor
''Taya ma za ayi da raina maza biyu su nuna suna son wannan kuchakar yarinyar,ni kuma nawa suna zaune,ai sam haka ba zai tab'a faruwa ba,duk cikin su babu rabonki yarinya''
Wata k'awarta ta tuno take ko ta hau binciken number enta a wayanta...............
*_~TEAM KHUBRA~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*8/ʍɑվ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*2⃣4⃣*
*D*a k'yar ta iya lalubo number matar,wata dariya tayi ita kad'ai tana sak'a abubuwa da dama cikin ranta,bata jira ta b'ata lokaci ba ta danna mata kira....
Ta jima tana ring ba a d'aukaba,haka ta ci gaba da mai²ta kiran kusan sau uku tana kira wayan na katsewa,har wata zuciyar ta bata shawaran kar ta sake kiran ta ji ba zata iya hak'uri ba,kiran ta sake yi,cikin sa'a wannan karon aka d'auka,zuciyarta tayi kar saboda murna,sai dai me tana d'auka taji an ce
''Hello! wa ke magana,naga an dameni da kira tun d'azun''
Baki ta sake tana mamakin lamarin dama akwai ranar da HAJIYA LAURA zata manta da ita haka,matar da tun k'uruciya suke tare...
Zuciyarta ta danne tana fad'in
''HAJIYA LAURA amma alk'awari baice haka ba,yanzu a kwai ranar da zaki manta da ni k'awarki da muka tashi tun yarinta?''
''Laaaa!HAJIYA MURJA kin san Allah wannan kalaman naki su suka sa nayi saurin ganewa,da yake sim card en nawa ya sha welcome back ne,saboda ana yawan sacemin waya ko na yar,to ke kuma ba gwanar kiran mutum ba bare na samu numbrki''
''Eyyahh!Allah ya maida alkhairi''
''Ameen''...........
Nan suka gaisa,kafin HAJIYA MURJA ta soko mak'asudin kiran da tayiwa ita HAJIYA LAURAN,bata b'oye mata ko da wasali ba kan abunda ke shirin faruwa.....
Dogon numfashi ta sauke,kafin ta cema da HAJIYAN
''Gaskiya HAJIYA yanzun bana so muyi saurin yanke hukunci,amma abunda ya kamata muyi shi KHALEED tunda gida d'aya kuke da shi da kanki zaki sa masa ido kan al'amuransa,tunda kinga har yanzun bamu gane sonta yake ko kuwa,shi kuma wancan KHALEEL kika ce sunan sa ko?''
''Ehh!haka ne''
''Yawwa to abunda za kiyi shi ne duk hanyar da zai ganta idan ya zo gidanki ki tosheta,sam kada ki ba shi wannan damar,idan yaso sai ki dinga tura su ASHNAR ko ita ZUHRA,idan kuma ya tambayi yarinyar kawai kice ai ta koma gidansu aure za su mata,fak'attt magana ta k'are kinga an yiwa tufkar hanci''
Shiru tayi tana sauraren k'awar tata,take ko tayi na'am da shawarar tata,sun jima suna magana kafin suka yi sallama kan sai kuma sun had'u ko ta sake kiranta.....
《《》》
Da ihuu su HANEEF suka shigo kamar kullum,sai dai suna shigowa parlor suka yi d'iff saboda ganin OGA a kwance,babu wanda yayiwa magana suka b'ace kowa yayi hanyan d'akinsa....
Allah sarki ZUHRA ko da ta shigo cikin parlorn waige² tai tayi coz sai da ta biya d'akin KHUBRAN bata ganta ba,hanyan kitchen tayi nan ta hangota ta juya baya,hakan yasa ta lallab'a bata sani ba sai ji tayi an rufe mata ido,y'ar dariya tayi mai sauti,itama ZUHRAN dariyan tayi kafin kuma ta zare hannunta daga fuskan KHUBRA,juyowa tayi ta kalleta
''Har kun dawo?''
''Lallaima wai har,ina fa har,kina gani tun safe fa muka futa bamu dawo ba sai yanzun''
''Ai kuwa dai kam,Allah ya bada sa'a''
''Ameen kam,barin shiga na fito''
''Toh!a fito lafiya''
Ta juya tana tafiya had'e da murmushi,har ta fice ita kuma ta ci gaba da aikinta.....
Dai² ta zo giftawa ta parlor BB dake kwance ya d'an bud'e ido saboda yaji maganarta a kitchen
''My SIS idan kin fito ki zo ina nemanki''
''To BBNAH''
Da sauri tayi ciki,cikin sauri² tayi wanka ta shirya,a parlorn ta tarar da shi,kusa da shi ta nemi guri ta zauna,parlorn daga ita sai shi
''Aaamm!MY SIS kin san me zan tambayeki?''
''A'a YAYANAH''
''Yawwa dama kan wannan k'awar taki ce,me kika sani dangane da ita?''
Yanayin tambayar ya d'an d'aure mata kai,ganin bata gane ba yasa ya mata bayani,y'ar dariya tayi kafin ta sake maimaita masa abunda ta sani game da KHUBRAN kamar lokacin farko da ta tab'a bashi labarinta......
''Ok ba komai jeki na gode''
Yana gama fad'in hakan ta mik'e ta nufi kitchen,kasancewar ZUHRA yarinyace amma akwai basira ta harbo inda maganar BB ta dosa,dan tafi kowa sanin halayyarsa ta rashin shiga abunda babu ruwansa,idan ko har kaga yayi magana kan abu to da walakin (Goro a cikin miya).......
Kitchen en ta koma ta tarar har ta gama abunda take,da murnanta ko ta hau tsokanarta
''Matar YAYA har kin kammala ne,dan nifa da yunwa na dawo''
Da sauri KHUBRA ta kalleta tana mata alamar neman k'arin bayani
''Wane YAYA kuma?''
''Nawa mana ko zan fad'i wani ne ba shiba?''
''Uhmmm!rufamin asiri matsayina bai je nanba''.....
''Tabbb ai wollah har kin wuce nanma,ke wollah da izinin Allah ke rabon YAYANA ce dan ko naga alama''.......
Maganar ce ta mak'ale saboda shigowar ASHNA cikin kitchen,kallon da ta yiwa ZUHRAN da ita kanta KHUBRAN shi ya tabbatar musu ta ji abunda suke magana akai....
Sai da ta gama d'aukan abunda ta zo nema sannan ta kalli ZUHRA
''Ke kam koi banza,ta ina ma zaki had'a YAYA da wannan matsiyaciyar,wacce iyayenta basu damu da sanin inda take ba,sun turota aikatau saboda neman abun duniya,ki rasa da wacce zaki had'a shi sai wannan,to wallahi yafi k'arfinta,banza sha³ kawai''
''Eeehh!an fad'a en naga itama ai mutum ce,ke har kina da bakin magana,wannan en da kike gani kina rainawa naga dai ta fiki duk wani abu da kike tak'ama da shi,k'ark'ari ki nuna mata gidanku suna da wadata, bayan wannan babu abunda zaki gwada mata''......
Bata k'arasa ba ASHNA ta kwasheta da mari da yasa tayi shiru tana binta da kallon mamaki
''Ni kika mara kan na baki amsa?''
''Duk ranar da kika sake min irin wannan maganar wallahi sai nayi miki wanda yafi wannan''
''Tabbbb to wallahi baki isa ba,Allah yau babu abunda zai hanani ramawa''
Nan tayi kan ASHNA suka hau kokawa,ita kam KHUBRA sai hak'uri take basu,duk da maganar da ASHNA tayi kanta ranta ya sosu ganin suna fad'an kuma ta shiga k'ok'arin rabasu amma ina sunk'i rabuwa....
Hayaniyar da ya jiyo daga kitchen en shi yasa ya taso yana zuwa ya tarar dasu suna kokawa,tsawa ya kwad'a musu duka
''Uban me ya had'aku da zaku sa mutane a gaba kuna rigima?''
''YAYA wai fa kan muna maganarmu shi ne daga zuwanta ta sa mana baki,dan nayi mata magana shi ne ta mareni''
''Ai ke dama baki da hankali kullum girma kike kina dad'a cin k'asa,wawiya kawai zo ki b'acemin a nan ko na b'alaki''
Fitowa tayi tana turo baki k'asa² ta hau k'unk'uni,duk abunda take idanunsa na kanta,sai da ya bari ta zo zata gifta ta kusa da shi ya fizgota aiko nan ya shiga knocking kanta
''Ni nake miki magana kikema k'unk'uni ko?''
Ta kasa magana saboda azaba,ta sa hannayenta tana son k'are kanta ganin yak'i barinta ta hau masa ihuuu,k'afa yasa ya ture ta gefe
''Gobe ma idan na miki magana ki sake min irin wannan kiga yadda zanyi da ke sha³''
Da gudu ta bar gurin tayi d'aki sai kwala ihu take uwa wacce akace uwarta ta mutu.....
Kallon ZUHRA yayi ''Ke kuma ki ci gaba da fitsara kinji,da dai ban sanki da wannan halinba,amma yanzun kin sauya hali''
Kanta a k'asa har ya gama abunda zaiyi ya bar gurin,kuka ZUHRA ta sa,matsowa tayi ta kamata ta zaunar da ita tana bata hak'uri itama kamar za tayi kukan
''Kinga kiyi shiru kije ki bashi hak'uri kar yayi fushi da ke,kina ganin dai yanda ya bar nan''
Shiru tayi ta hau goge fuskanta,bin bayansa tayi a parlor ta tarar da shi ya dafe kansa da hannu,a k'asa ta zauna dai² kusa da k'afafunsa
''Pardon please BB''
Shiru tayi tana neman kalmomin da za tayi amfani da su
''Allah YAYA ka yadda ni ba rashin kunya nayi mata ba''
Shiru yayi mata baice komai ba,ita kuma hakan da yayi yak'i mata magana tasa masa kuka....
A hankali ya bud'e fuskansa,tashi yayi ya zauna
''Ya isa haka,amma abunda bana so ki dena biye mata kuna wannan shirmen kinji ko?''
''In Allah ya yarda bazan sake ba''
''Yawwa to goge fuskanki''
Goge fuskanta tayi,kafin ta mik'e
''Na gode YAYANA''
Murmushi ya mata,ita kuma ta juya ta bar gurin........
《《》》
Tun da ya fice bai koma gidan ba sai dare sannan ya shigo gidan,babu kowa a parlor haka ya lallab'a ya shige bed room ensa,yana shiga ya rufe door en ko light en d'akin bai kunna ba haka ya gama abunda zaiyi ya kwanta....
Da safe ko bai bari sun had'u da UMMI ba yayi saurin ficewa....
Yau kwana uku kenan UMMI bata sa KHALEEL a idonta ba,abun duniya duk ya dameta,tun safe ta fito amma tana duba d'akinsan ta tarar har ya fice,kuma ta tabbatar a gidan yake kwana,yau kam ta k'udurce duk tsayin lokacin da zai shafe zata jira don magance matsala....
Tun da ta nemi guri ta zauna bata ko tashiba,duk abun da yayi ya dameta,ko sallah za tayi a nan cikin parlor take yi duk dan kada ya shigo ba ta saniba.....
《《》》
Shigowarta kenan cikin gidan,aiko muryanta kad'ai ASHNA ta jiyo tayo waje tana kuka uwa yanzun ne abun ya faru....
Tana zuwa ta fad'a jikin MAMA tana gunjin kuka,kallonta MAMAN tayi tana fad'in
''Me aka miki?me ya faru?maza sanar da ni''
Kasa yin magana tayi sai kuka take kamar ana zarar ranta,rarrashinta MAMAN tayi har sai da tayi shiru sannan ta hau fad'in k'arya da gaskiya duk ta sanar mata,aiko ranta iyayi million ya b'aci
''Yi shirunki dama abunda nake hasashe kenan amma ba komai yi shiru karki damu kinji y'ar lele''
Dariyar kissa tayi tana fad'in
''MAMA dan Allah ina YAH KHALEEL,yaushe zaki je gidan su?''
''Uhmmm!ASHNATA kenan mene kike tambayarsa?''
''Babu komai MAMA kawai tambaya nayi''
''Fad'amin dai in da wani abu''
Da gudu ta bar gurin tana dariya,ita ko MAMA dariya kawai tayi tana kallonta.......
《《》》
K'arfe 1:00am ya shigo gidan,tafiya ya ci gaba da yi a cikin parlorn,sai da yazo tsakiya yaga haske ya gauraye cikin parlorn,juyowa yayi yana kallon cikin parlorn.Tsaye yaga UMMIN nasa wani kallo da ta yi masa shi yasa shi sunkuyar da kai k'asa
''Yanzu SON abunda kayi ka kyauta kenan?akan wannan maganar za kayi fushi da ni?shi kenan duk abunda kaga ya dace da kai kayi kaji?''
Ji yayi gaba d'aya jikinsa yayi sanyi,sam ya kasa motsawa daga gurin,har tayi ta gama fad'an da zatayi masa,kansa a k'asa ya fara tafiya da k'yar har ya zo gabanta,durk'usawa yayi har k'asa ya rik'e k'afafunta.Gafaranta ya shiga nema da yake ba ta da rik'o ta yafe masa...
''SON maza je ka kwanta gobe in sha Allah zamu je gidan HAJIYA MURJA duk abunda kake so nima ina sonsa matukar bai kaucewa hanya ba,kuma bai sab'awa addini ba''....
''Yawwa UMMINA na gode sosai,shi yasa nake sonki''
Ya bata peck a kumatu ya fice yana mata sai da safe,farin cikin dake kwance kan fuskarsa shi ya bata nutsuwa tayi murmushi,kafin ta bar parlorn ta nufi bed room enta.....
11:45am ya fito cikin shirinsa,k'ananan kaya ne a jikinsa tun daga parlor yake kiran UMMI dai² ta fito daga d'akin take fad'in
''Kai SON ban sankafa da fitsara ba,irin wannan kira haka kamar wanda zai bar garin,saurin me kake yine?''
''Uhmmm!Allah UMMI bana son rana tayi mana ne''
''Za dai ka fad'i gaskiyama''
Dariya yayi yana yin gaba,ba tare da ya furta komaiba,cikin minti goma sha biyar suka iso gidan...
A parlor suka tarar da yaran,nan ko suka shiga gaida su,ASHNA sai kallon KHALEEL take wanda baima san me take yi ba,da sauri HAJIYA MURJA ta fito tana fad'in
''Maraba da zuwa,ina fad'in zanzo ashema zaki rigani zuwa''
''Uhmm!ai kuwa dan ko d'anki ne ya tasoni ba zuwana bane wannan zuwansa ne''
Y'ar dariya ta yi suka shiga d'akinta,sun gaisa a mutunce,kafin HAJIYA FATEE ta sanar mata da dalilin zuwan nasu.A ranta kam sam bata ji dad'in maganar ba,amma a fili sai ta nuna mata babu komai,nan suka ci gaba da fira kamar babu komai a ranta....
'Ban garen KHALEEL da BB kuwa,a bed room ya tarar da shi yana kwance,shigowansa yasa ya tashi ya nufi hanyan toilet yana shirin shiga wanka,sun gaisa ya juya zai shige KHALEEL ya dakatar da shi ta hanyar fad'in
''Yeahhh!ka fara tayani murna kafin ka wuce mana ko so kake ka barni nan da kad'aici?''
'Dan juyowa yayi ya kalleshi,wucewa yayi zai shige kalaman KHALEEL suka dakatar da shi
''Haba mana YAYANMU ai sai ka''.......
Bai k'arasa ba ya juyo ya kalleshi
''Ai kai kam baka da girma,mene kuma na wani cemin YAYANKU banda iskanci irin naka YAYANKU kai da wa?''
''Ni da abar k'aunata mana''
'Dan dawowa yayi ya zauna kusa da shi
''Ka ce mene,wa ce kuma haka?''
''Wannan k'anwar taka fa nake nufi''
Yayi maganar yana kwanciya da baya saman bed en,yana rufe ido
''Ai kam ban san me kake fad'a ba''
''Da Allah wannan balabiyar nake nufi''
Ido ya fito waje coz ya gane inda maganar tasa ta dosa,mik'ewa yayi baiyi maganaba,ya sake tafiya zai shiga toilet en coz ya d'an fara jin haushin maganar
''Banza ne kai ai idanma baka so to barin sanar da kai tunda ba kai zaka bani ba.....Yauma dalilin da yasa kaga UMMI kan maganar ne''........
Cikin tsawa ya juyo yana fad'in
''What?''
Tambayar