Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 159513 words

Chapter 16 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1219

Ads at the middle of Article

da ita da har za ka fad'i haka?Wannan damuwar da nake nunawa duk na banza ne ko ba haka ka fad'a ba?''
Wani murmushi yayi wanda da gani kasan sam bai dace da lokacin da aka yishiba....
''Yeahhh! na fad'a idan da ace ka damu ya kamata ka biyoni muje''


''Baza ka tab'a fuskata ba''
BB ya fad'a yana girgiza kansa....


《《》》


'Bangaren MA'U kam zuwa yanzun duniya sabuwa,al'amura sai dad'a ta'azzara suke,neman maza yanzun ya zame mata jinin jikinta,duk inda take suna manne da farkokintan,babu gida babu waje yanzun har ta kai ga takan kulle gidan tayi ficewarta sai ta yini bata gidan....
Idan ta dawo kuma to za a tarar da ita da wani suka dawo bata tab'a iya kwana ita d'aya...


Duk ko ranar da duniyancintan ya motsa ranar ba zaka tarar da ita gidaba gaba d'aya k'arshe a hotel zata kwana,koma ta shafe tsawon kwanaki kamar dai wacce tayi tafiya ganin gida.....


《《》》


''Unguwan Miltara ko Rijiyan lemo......Wanne ne ma a ciki?''
Tama kanta tambayan,tana ta faman son ta tuna,idanunta sun koma ciki,duk kuwa da yanda KHUBRA ke da yalwar idanu...

''HAJIYA na ga kin kasa tunawa,me zai hana muje gidana''
Ya fad'a yana kallonta,yana kuma kallon abunda ke rungume jikinta,d'an kallonsa tayi da jan fuskanta,ita dai haka kawai taji ta aminta da shi,amma kuma taya za ta amince,ta sani ko bashi da aure,haka kawai ya kaita gidansa alhalin bashi da aure...
Shiru tayi bata ce komaiba,shi kuwa sai kallonta yake da k'unshin bak'in ledanta dake rungume jikinta har lokacin...


Kamar ya san abunda take tunani akai aiko ya shiga fad'in
''Ki yarda muje babu abunda zai faru dake yanzun haka y'ay'ana hud'u da mata ta''


Jin haka yasa ta mik'e ba tare da tunanin komaiba tana fad'in
''Muje to na gode sosai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi''


Y'ar dariya yayi ba tare da ya amsa ba,ya shiga tura kurar ruwansa ita kuma tana biye da bayansa,suna tafiya babu wanda ya kuma tankawa wani a cikinsu.....


《《》》


Car keys ensa ya fizga kan mini table dake gurin,sai huci yake yayi gaba,da d'an gudu KHALEEL ya biyo bayansa,yana zuwa saitinsa ya fizge keys en yayi saurin bud'e driver seat yayi starting motan...
Kallon mamaki BB yayi masa kafin ya zagaya ta d'ayan side en yana mai rufewa.....
A 360 suka bar gidan,basu tsaya ko ina ba sai police station,office en DPO aka shigar dasu da yake yasan ABBAN KHALEEL,shi ya bada report en b'atan KHUBRA wani sergent dake gefe yana nad'ar bayanin..
Kasancewar ba komai ya sani game da b'atan nata ba,yasa ya dubi BB dake zaune ya dafe kansa
''Ka masa bayani kasan ba komai na sani game da case enba''


DPO ne ya kallesu su duka biyun ganin irin yanayin fuskokinsu da abunda yake d'auke akansu ya tabbatar suna cikin damuwa da b'atan yarinyar
''Ina ganin da kunzo da photonta da binciken zaifi zuwa da sauk'i''
Ya fad'a cike da alhini...


KHALEEL ne ya bashi amsa da fad'in
''Gaskiya ABBA bana tunanin akwai photonta nan kusa''


''To babu komai duk da haka in sha Allah gano inda take bazai yi wahala ba,Allah ya bayyanata''.........

Kan BB ya juya yana fad'in
''Daurewa za kayi d'ana ka sanar damu abunda ya faru kaji,bayanin kane kad'ai zai taimaka mana ta hanyar gano inda take a halin yanzun''


Da k'yar ya iya tattara bayanan ya sanar da shi DPO yana zaune yana saurarensu har suka gama,sergent en ya fice...
Godiya suka masa had'e da sallama suka fice jiki a sanyaye.....


《《》》


Gefen LADIYO itama ba'a barta a baya ba,zuwa wannan lokaci kam mu'amalarta da bokan nasu abun duk ya isheta kawai dai dan bata da yadda za tayi ne shi yasa ta zuba ido..


Da ta kaiwa TABAWA kukanta ko dariya tasata a gaba tana yi cikin muryan da yake nuna jin dad'i take fad'in
''Ke kam LADIYO ban san lokacin da zaki waye ba,shi MALAM BUBAN kashe miki k'ishirwa yake?ina ganinma kam kafin ki samu kansa ae sai da aka miki taimako......Yawwa kwana biyu babu labari ya ake cikima kuwa baki zomin da labariba''

Kai LADIYO ta yasar gefe tana fad'in
''Kayya dai kam TABAWA abun ba a cewa komai,dan lamura sai dad'a tab'arb'arewa suke,ni kam ina ganin hak'ura zanyi kawai.....Tunda na samu an rabashi da zancen wannan shegiyar y'ar tasa hakama ya isheni kam''


''Aike kam dama wollahi kina da damuwa,banda abunki kin tab'a ganin an hak'ura da neman mafita,matsalarki kenan gidadanci''
(A raina nace duk uwar d'arin ce ae).......


Hud'uba iri daban-daban haka ta ci gaba da cusawa LADIYON munanan d'abi'u,wanda kafin ta bar gidan sai da ta kwashi kaso mafi yawa cikin abunda TABAWAN ta sanar da ita......


《《》》


Tun da ZUHRA ta shige bedroom enta da plate a hannunta ta kulle k'ofan.Plate en ta tusa a gaba sai juya indomein take ta kasa kai ko da one spoon bakinta,hawaye ne ya ci gaba da saukowa kan face enta,damuwa duk ya mata yawa ga ba mataimaki sai Allah...


Yini tayi a bedroom en ta kasa fitowa da k'yar ta rarrashi kanta ta soma cin abincin nata da yayi sanyi,spoon biyar ta iya ci ta ture plate en gefe,tunani duk ya dameta...


''Me yasa MAMA zata aikata haka?........Sam banyi tunanin da sa hannun MAMA ciki ba....Amma me yasa?''


Haka ta yini cikin d'akin dan kam itama bata jin za ta iya fita bare har ta samu damar hira da wani....


'Bangaren MAMA da y'an fadarta ko damuwarsu bai wuce rashin abincin break da suka saba da cin mai kyau a kowane lokaci ba,sai dai wannan ranar ta zo musu da sauyi,ta yanda sun tashi cikin k'oshin lafiya sai dai babu garar da suka saba da ita kullum rana....


Yinin ranar haka suka wuni cin cornflakes,MAMA kam sam bata da kwanciyar hankali ta b'angaren girki coz ita sam bata jurar yin girki ko da sau d'aya a yini,shi yasa ma ta k'ule a d'aki ta gagara fitowa,su kuma yarantan ba shiga kitchen suke ba bare su iya yi da kansu...
A wani gefen kam tana jin alhini na rasa KHUBRA a matsayin housemaid da tayi sa'a kaf cikin y'an aikin da sukayi a gidan....
(Ni ko nace kad'anma kika gani,ai yanzun aka fara).........


《《》》


Binsa kawai take suna tafiya yana tura kurar ruwansa sai da sukayi nisa da cikin jama'a dan har sun fara shiga cikin gonaki dake bayan garin....
Da k'yar take tafiyan saboda gajiya da tayi,d'an tsayawa tayi tana hutawa har yayi gaba bai san ta tsayaba,waiwayowa yayi ya ganota can baya,kuran ya bari a gurin ya dawo baya...
''Yi hak'uri kinji mun kusa tarar da gidan''


Murmushi tayi tana kallon gurin,ita kam sam bata hango gidaba a gabanta,gudun kada ta masa wuk'anci a matsayinsa na wanda yake shirin taimakonta yasa ta daure ta ci gaba da binsa...
Ci gaba sukayi da tafiya har suka tarar da inda ya ajiye kuran,suna tafiya yana juyawa baya,ganin babu mutane a gurin ko kad'an ya fakaici idon KHUBRAN d'an sakin kuran yayi ya sunkuya yana dafe cikinsa,a d'an tsorace ta matso gaba kad'an gareshi tana fad'in
''Lafiya k'alau kuwa kake,me yake damunka?''


Damuwa sosai ta bayyana akan fuskanta har tana neman mantawa da nata damuwan....


Sai da ta gama sakewa tukun ya fizge ledan hannunta take ko ya shek'a a guje ya nausa cikin jejin dake gaba kad'an da su..................




~Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu,bana jin dad'ine dats y baku ga posting ena ba,,,,,,, _1 luv my peps._~






*_~TEAM KHUBRA~_*






*_REAL SMASHER_*


💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*16/ʍɑվ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
_Ga ubuk'atar kasancewa da group na *Y'AR GARUWA* za ku iya yin joining ta hanyar amfani da wannan link en..._
👇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EvdAvnFbBaX2BBMAwCCH4E
*~________________________~*
_MASOYA INA MAI BAKU HAK'URI,SAKAMAKON DAKATAR DA POSTING DA ZANYI,BISA GA GABATOWAR WATAN *RAMADHAN* IN SHA ALLAH,SAI MUN HA'DU BAYAN SALLAH DA YARDAR ALLAH,IDAN ALLAH YA ARA MANA LOKACIN,INA MUKU FATAN ALKHAIRI,DA FATAN UBANGIJI YA KARB'I IBADUNMU WANDA MUKAYI DA WANDA ZA MUYI,ALLAH YA DATAR DAMU,YA SANYAMU CIKIN BAYINSA Y'ANTATTU..._


🌙⭐ *HAPPY RAMADHAN IN ADVANCE.* 🌙⭐
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*2⃣8⃣*










*T*saye tayi tana kallon yadda yake gudu,k'afafunsa uwa robber band wajen talewa da suke kan tsabar gudun da yake,abunka da mara gaskiya akace ~{ko a ruwa gumi yake}~ .....
Ta rasama me ya kama tayi ita dai sai kallonsa take duk da yayi mata nisa....
''KHUBRA ya kamata kiyi wani abu ko dan ceton rayuwarki''
Wata zuciyar ta kawo mata d'auki da shawara..


''To ni me zan iya yi yanzun?''
Ta tambayi kanta tana mai ci gaba da tsaiwa ba tare da ta iya yanke hukuncin aikata komaiba,a hankali ta sulale ta zauna tsakanin kunya² dake gurin,da hannu biyu ta buga tagumi ta rasa meke damunta...


Tana nan zaune har ya b'acewa ganinta,ajiyan heart ta shiga saki masu matuk'ar k'arfi kan kukan da ta shak'a a yau....


Rana ta dad'a yin zawali,a b'angaren KHUBRA sam zafin ranar bai ko damunta,dan kanta ta mik'e lokacin da ta gaji da zaman gurin baya ga yunwa da ta fara damunta....
Kuran da ya bari gurin shi zuciyarta ta gama bata shawaran ta tura,ta wannan hanyar ne kad'ai zata iya samun abunda za taci,cikin duniyar nan ba kowa ke iya taimakon wani ba.....

Pushing enta ta shiga k'ok'arin yi sai dai ko kad'an kuran bai motsa daga inda yake ba,iya k'arfinta tasa ta shiga dannawa amma ina abun ya gagareta,haka ta zube gurin ta sake sakin wani marayan kuka,wanda baka iya jin sauti sosai cikinsa.....


《《》》


Tunda suka baro police station en babu wanda ya iya kula wani tafiyan kurame suke,babu d'aya da ya tankawa d'ayan....
Dai² gate ensu ya perker,fita yayi sai da ya zo center ensa kafin ya bud'e baki da k'yar
''Sai mun yi waya''
Ya fad'a tare da juyawa ya shige gida...

Tun fitar KHALEEL a motan ya kasa motsi,zama ya ci gaba da yi a motan,sai da ya shafe tsawon wani lokaci,kafin ya matsa zuwa driver seat,dan sam bai jin zai iya fitowa a motan sannan ya koma da k'afarsa.Ko da ya koma enma da k'yar iya starting motan yayi gaba..Yanayin da yake driving en kad'ai ya isa ya bayyana rashin energy a tare da shi,da haka ya lallab'a ya isa gida.....


Shigan KHALEEL gida yana tafiya uwa kazan da k'wai ya fashewa a ciki haka ya shiga parlor...
Kwanciya yayi idanunsa a rufe ya d'ora hannunsa a kan fuskansa,fitowar UMMI daga kitchen ta ganshi nan kwance,yanayin yanda yayi ya tabbatar mata d'an nata ba k'alau yake ba,k'arasowa tayi ta dafa kansa,da sauri kuwa ya bud'e idanunsa yana sakin ajiyan zuciya...
Hakan da yayi ya dad'a tabbatar mata da zarginta
''SON lafiya kuwa kake?
Na sha fad'a maka ka dena sa damuwa a ranka,saboda ba abunda take haifarwa sama da dana sani,baya ga ciwo da zai shigeka ba tare da yayi shawara da kaiba.....
Har kullum ina maka nasiha da ka ci gaba da mik'a lamarinka zuwa ga mahaliccinka,shi ne zai maka maganin damuwarka,damuwa bata tab'a zama magani,sai dai ma ta zama silar k'aruwar matsaloli''


Hannayenta da ta dafa shi dasu ya rik'e sosai,uwa wanda ke tsoron za a rabasu
''Na gode sosai UMMINA da sani a hanya da kike,Allah ya miki sakamako da mafificin alkhairi''


''Ameen MY SON,Allah ya maka albarka,ya karemin kai daga dukkan wata fitina ta zamani''


''Ameen UMMINA''


Su duka sukama juna murmushi,mik'ewa tayi da niyyar barin gurin maganar KHALEEL ta dakatar da ita


''UMMI ki tayamu da addu'ah mu samu a gano inda take''


'Dan waiwayowa tayi tana masa kallon rashin fahimta,tun kafin ta kai ga tambaya ya katse mata kalmomin dake shirin fitowa


''UMMI sun sace ta''
Cike da al-hini yayi maganar yana yada kai gefe...


''Ban fuskanci me kake son fad'a ba SON.........
Wace ce aka sace kuma?''


Damuwa ta dad'a bayyana saman fuskarsa a hankali ya furta
''Wannan yarinyar ta gidansu KHALEED!''


''Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un''
Bakinta keta maimaitawa har sai da ta samu nutsuwa kafin wasu tambayoyin suka shiga tseren fitowa daga bakinta
''Yaushe?kuma a ina hakan ta faru? garin yaya?ita HAJIYA MURJA tana wane sakacin aka d'auke y'ar mutane?ko kuwa bata sani ba?''


Kallon UMMIN nasa ya shiga yi uwa wanda ya fara ganinta yau
''Wallahi UMMI abunda na manta ban tambayi KHALEED ba kenan......
Amma gaskiya UMMI ina zargin da sa hannun HAJIYANSA''


Ta gefe ya d'an kalleta yana mai rik'e bakinsa,tunawa da warning da tayi masa
''Amma kiyi hak'uri UMMI idan na fad'i abunda ba dai² ba''


Kai ta kad'a masa kafin cike da mamaki ta soma magana
''Tabbas ko ni da kaina jin wannan maganar yasamin zargin HAJIYA MURJA....Da gangan akayi......Ko tantama babu wannan aikin shiryashi akayi,akwai sa hannu cikinsa''


Shiru dukansu sukayi suna jinjina lamarin...


''Allah ya kyauta,Allah ka kare baiwarka a duk inda take''
Abunda ya iya fitowa daga bakinta kenan ta sake yin shiru tana jaddada al'amarin a zuciyarta....


《《》》


ZUHRA ce ta fito da kumburarren fuskanta zata kitchen danko k'ishi ke damunta,ta fito da niyyan d'auko ruwa,dai² zata wuce ta k'ofan MAMA ta ji ana magana k'asa²,kunnenta ta d'ora jikin k'ofan take ko kalaman da ta jiyo suka sake firgitata....


''Ehhh!ba damuwa HAJIYA LAURA ai kin gamamin komai da kika samomin mafita''
Dariya ta saki mai k'arfi kafin ta ci gaba
''Wallahi kuwa mun rabu da kaska.....Yo to ta inama za ayi wata Housemaid zata zo tana neman juyamin kai.......maza biyu lokaci guda fa duk sun haukace kanta,shi wancan da yafi kowa haukama harda turomin mahaifiyarsa bayan ga y'an mata nan ina da su bai zab'i kowacce ba sai ita........Uhmm!shi kuma KHALEED......Ai ki barni da su tunda yanzun munyi maganinsu.....Allah kuwa,to ameen...Sai kin jini''


Jin maganganun tayi suna mata yawo akai,kenan zarginta ya zama gaskiya kan MAMA,hawayene suka sake b'alle mata,dafe bakinta tayi tana jiyo maganar MAMA,daga jima ka san da kanta take


''Ya zama dole na raba gidan nan da duk wani abu da zai sake tunamin da ke......
Barima kiga na tashi kaf kayanki dake gidan nan k'onasu zanyi,mun dai rabu da kaska sai aje can a sha jinin wani''


Jin kalamanta na k'arshe yasa ZUHRA saurin mik'ewa hanyan fita daga parlor ta nufa tana tafe tana hard'ewa kamar za ta kifa,har ta fice daga parlorn...


Kansa ya had'e da steering motan ya shiga tunanin da bai san me yake tunawa ba,tsawon mintuna arba'in yana cikin motan ba tare da ya iya fitowa ba,kuma har lokacin ya kasa kashe motan...


Fitowan ZUHRA daga cikin parlor tana waigawa tana kallon hanya tamkar wacce wani abun tsoro ya biyo,shi kuma ya d'ago yana bud'e motan had'e da kashewa ya fice,tafiya yake jikinsa babu k'wari...
Buge juna suka yi da sauri ta d'ago ba tare da iya yin maganaba ta d'aga masa hannunta alamar ban hak'uri,tayi gaba abunta,tana kuma ci gaba da waiwayen hanya....
Kallonta kawai yayi,yanayin da take ciki ya tabbatar masa akwai damuwa,har zai shiga parlor ya fasa a baya ya bi hanyan da ta bi,har k'ofan d'akin..
A ciki ya tsintota tana ta faman binciken kayan dake d'akin,da k'yar ta iya gano keys en d'akin,kayan ta shiga d'iba tana zubawa a closet dake had'e cikin wall en d'akin.....
Yana tsaye bakin d'akin yana kallonta har ta kammala ta fito,da sauri ta maida k'ofan ta rufe had'e da danna mata key.....


Sai da ta juyo zata bar gurin sannan ta ganshi tsaye ya hard'e hannayensa a chest yana kallonta...


《《》》


Sai da ta gama kukan sannan ta mik'e ta karkad'e kayanta da suka b'aci da k'asa,zuciyarta cike da kishin kanta da tausayin rayuwarta ta sake d'ora hannunta a kan marik'in kuran....
Dannawa ta shiga yi,duk k'ok'arinta bai wuce taga ta taimaki kanta ba,addu'ah ta soma duk wacce tazo bakinta yi take kan neman taimako daga mahalicci,cikin ikon Allah tana ta k'ok'arin turawa bakinta kuma bai fasa ambaton Allah ba,tafiya kuran ya soma ta juyo da akalar kuran zuwa garin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads