Showing 12001 words to 15000 words out of 159513 words
Chapter 5 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt
yayi bak'i kamar an shafa kwalta...
da k'yar ta gama wankewa,ko da ta gama haka ta kwashi k'afafunta ta je k'ofar d'akin
''Na gama'' abunda ta iya fad'a kenan...
''To jirani'' MA'U dake d'aki ta fad'a....
Fitowa tayi da uban kaya a hannunta,haka ta watso mata su,ta sake komawa ta d'ebo wasu...
''Ga shinan maza ki tabbatar kin wanke su sun fita tas,dan idanma basu fitaba,zaki sake ne''...
Juyawa tayi tana k'arewa kayan kallo,gasu da uban yawa,ga kuma daud'a,wanda ko kayan d'an goye ba zai nuna musu daud'aba....
Har ta kai bakin k'ofa KHUBRA ta furta ''Sabulun wankin''....
Shigewarta tayi,sai da ta gama b'ata lokaci,sannan ta cillo mata...
Haka tayita gurzarsu,babu iyaka,har dai ta samu ta kammala,lokacin ana kiran sallan ISHAA.....
Ranar gaba d'aya KHUBRA haka ta yini aiki daga wannan sai wancan...
Haka ta tashi jikinta sai kyarma yake,ga ciwo da yake mata,ga tsananin yunwa,ga uban ciwo da kanta yake tamkar zai rabe...
Tashi tayi da k'yar ta tattara kayan da tayi amfani dasu,ta shiga d'akin shirgin nan ta gyara shi,duk da tana cikin wannan halin haka ta share shi...
Ruwa ta d'iba ta shiga ta wanke jikinta,sannan ta d'auro alwala,ta fara jera sallolin da ake binta bashi,dan kuwa MA'U hanata tayi ta motsa ko nan da can...
Tana yi tana ZUBAR HAWAYE,tana rok'on Allah gafara da kuma neman d'auki daga gare shi.....
Ta jima acikin sujudah tana rok'on Allah,kafin ta d'ago tayi tahiya,ta sallame....
Da k'yar ta iya motsawa daga gurin,ta lallab'a ta fito daga d'akin...
'Dakin MA'U ta shiga sai tare kanta take da hannu wanda ke mata barazanar fashewa...
''Dan Allah BABA ki taimakamin da abunda zan ci,wallahi ina tsananin jin yunwa,kuma kaina ciwo yakemun''
Ta fad'a kamar zata fad'i....
''Ke dallah dakata,karki fad'o kaina,dan kina jin yunwa shi ne me?
Malalaciyar kawai,d'an wannan aikin da kikayi kinzo kina min raki''.....
Haka MA'U ta koroto ba tare da ta tausaya mataba...
Kuka ta fashe da ta nemi guri abakin d'akin ta shiga rerawa...
Ashar en da MA'U ta k'unduma ne ya sata tsagaitawa...
Kamar daga sama ta ga MA'U da jakar kayanta a hannu,cillo mata tayi tana fad'in
''Idan zaki iya tafiya bismillah,abincine banga dama ba,kina iya ki nema da k'arfinki sai ki ci......
*_~#TEAM KHUBRA.~_*
*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*30/mąrcɧ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*
*ADDU'AR SHIGA BAN'DAKI.*
_BIMILLAHI!!! ALLAHUMMA INNIY A'UZHUBIKA MINAL-KHUBSI WAL-KABA'ISI.._
*ADDU'AR FITOWA DAGA BAN'DAKI.*
_GHUFRANAKA...._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_The hole page goes to masoyana kuma masoya novels en *RAYUWAR WANI* da *Y'AR GARUWA* ,iya wuya ina k'aunarku nima kamar yadda kuke k'aunata Allah ya barmin ku aduk in da kuke..._
*_~#REALLY HEART U GUYS..~_* 💔💔💔
*~_________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~__________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*1⃣1⃣*
*T*ana gama fad'an haka ta juya ta shige d'aki,ba tare da damuwan komai a rantaba...
Sai da ta gama cin kukanta sannan ta tashi,ta tattare kayanta da suka zube,ta mai da su ciki..
'Dakin da ta gama gyarawa ta shiga ta sa kayanta daga gefe...
Nan ta takure guri guda tana mai had'a kai da k'afa,tana tunanin wannan rayuwar da ta tsinci kanta a ciki...
Cizon sauro shi yafi takurata,a d'akin haka suke kawo mata farmaki,ga zafi....
Zaman dirshan ta yi bacci ya gagareta,banda koran sauraye babu abunda take,wanda shima da k'yar take iya d'aga hannunta,daga k'arshe ma kasawa tayi,haka ta bar su tanaji tana gani,suke kawo mata farmaki...
Tana daga zaune ta jingina kanta a wall en d'akin,abun tausayi ga jikinta sai faman ciwo yake,ta rasa inda zata sa kanta,saboda azaba kanta kamar zai fad'o haka take jinsa,yanda take ji yasa ta fara cire tsammani da rayuwar duniyar...
Bakinta banda motsi babu abunda yake,da kallo kasan ba abunda take da ya wuce addu'a...
Idanunta a rufe haka hawaye ke layi ta gefen face enta,kukan ya gagareta.....
Da k'yar ta tashi lokacin da taji kiran sallah da asuba tana bin bango haka tayi alwala,ta sake komawa d'akin...
A daddafe tayi sallah daga zaune,ko addu'ah bata samu daman yi ba,wani wahalallen bacci yayi gaba da ita...
**********
Ba shi ya farka ba sai da gari ya gama yin haske,rana harta faso a garin...
Cikin wani irin yanayi na mutuwar jiki haka ya mik'e ya fita,yayo alwala ya dawo,a d'aki yayi sallah ya idar,haka ya zauna yana tunani amma ya rasa mai zai tuna...
A ganinsa akwai wani abu mai muhimmanci da yake son tunawa da shi,amma ya kasa tuna wannan abun...
Badan ya soba haka ya k'yale kansa,yana mai mik'ewa yayi hanyar fita daga gidan....
***********
Har gari ya gama haske rana ta gama haske garin,MA'U bata farka ba,haka itama KHUBRA,Bacci take a wahale...
Sai wajen k'arfe 12:30pm KHUBRA ta farka...
Idanunta take bud'ewa a hankali,duk sun kumbure saboda bata wani samu isashshen bacciba...
Sai da ta gama bud'esu tar,sannan ta mik'e ta zauna,sai da ta zauna ta huta...
Jikinta ba kamar da dare ba,yanzun har tana iya mik'ewa sosai,kantan kuma ta d'anji sauk'insa...
Kayanta ta tattare tana had'asu guri d'aya...
Tunawa tayi da abunda MA'U ta mata jiya kan dole ta mik'e ko dan kar a maimaita irin jiyan,ta d'auka tsintsiya tayi tsakar gida...
Tsaf ta share gidan ta,d'ebi ruwa tayi wanka,haka ta zauna a tsakar gidan,rana sai sake matsowa inda take.....
MA'U ce ta fito daga d'aki tana mik'a,ta nufi band'aki kamar wacce ake tunkud'awa,haka ta fad'a band'akin kamar an cillata,ko addu'ah babu...
Kamar sakkowar ruwan sama haka ta saki fitsarin da shigarta...
Tab'e baki KHUBRA tayi tana daga wajen,fuskarta duk maik'o...
A ranta take fad'in
''Wama ya sani ko ta fara a kwance ne?''...
***********
Tun fitowar ABBAN KHUBRA daga gida bai koma ba,haka ya yaci gaba da rayuwarsa a waje....
LADIYO an shanya baki sai bacci ake,ba ita ta tashiba sai azhur,ba don ta so tashin ba,sai dan cikinta dake ihun yunwa,fun da ta San babu wanda zai bata tana kwance...
Ba tare da tunanin gaida mahaliccinta ba ta shiga neman abunda za taci, rashin komai a gidan, yasata bazama neman MALAM BUBA haka take cilla fasassun k'afafuwanta...
Kitchen ta sake lek'awa neman duniya tayi aciki babu komai cikinsa sai busashshen k'anzon tuwo ta tsinto...
Haka bbau komai ciki bare mahad'i tayi ta garzarsa kamar akuya har ta cinye,sannan ta fito daga ita sai d'aurin zani iya k'irjinta....
Sai bayan ta samu nutsuwa ta zo mata tukun,wani tsoro ya sakko mata,tunanin abunda ya faru jiya ya dawo mata,nan ta tafi duniyar tunani...
''Shin yanzun idan duka wannan abun ya tashi a tutar babu fa suyi yaya ?''
Tunaninta ya tsaya kan da me zata biya kud'in aikin idan har aikin yayi,nan take wani mummunan tsoro ya sake cika zuciyar LADIYO....
**********
Sai da ta gama yauk'inta a cikin d'aki sannan ta fito tana jan k'afa,coz har yanzun ita kad'ai ta san me take ji saboda azabar da yake mata,k'afar duk ta dad'a hawa tamkar kwab'in bread......
A kan KHUBRA ta ja ta tsaya, #50 ta cillo mata cikin tak'ama tace
''Idan zaki iya ki je ki nemo garin kwaki,a shago''....
Ko gama fad'a KHUBRA bata jira tayi ba tayi waje,da hope en ta take tafiya,tana neman shagon da zata siyo garin....
Tayi tafiya mai nisa sosai sannan da tambaya ta samu ta siyo..
Kamar kowane lokaci haka take tafiya,kanta a k'asa,tafiya take har ta kusa da gida...
Kamar daga sama taga an tsaya gabanta..
Da sauri ta d'ago tana kallonsa kamar zai fad'o kanta saboda yanda yake layi....
Hannunsa da wani cukuikuyayyen tsumma,sai dannashi yake a baki...
Idanunsa sun gama rinewa uwa an watsa musu colour....
Wani dariya yayi yana mik'a hannu da shirin damk'ota,yana fad'in
''Y'an mata zo mana''...
Da sauri KHUBRA ta durk'she a gurin jikinta banda rawa babu abunda yake....
Sunkuyawanta shi ya bashi damar dank'an iska,ya sake mik'o hannu zai sake kamota....
Ai KHUBRA kam kan kace mene wannan ta k'arawa k'afafunta wuta,gudu take tamkar taga naman jeji....
Biyota ya shiga yi,yana maganar da ita kam bata san me yake fad'aba....
Gudu take tamkar k'afanta zata cire kan gudu,tana zuwa k'ofan shiga gidan ta daketa da k'arfi tayi ciki,ko tsayawa ta rufe bataiba...
Tai ciki a guje sai d'akin MA'U wanda tana kwance tana jiran dawowan KHUBRA ta ji an fad'o d'akin,kamar an tsikareta ta mik'e tana dafe chest enta....
Cikin tsoro kamar ita tayi gudun ta hau haki tana fad'in
''Me ya faru?''....
KHUBRA ta kasa magana sai k'ofa da take nunawa MA'U....
Ganin tana neman raina mata hankali shiya sata doka mata wata uwar tsawa,data sa jikinta sake ci gaba da rawa kamar an jona mata shocking....
Zuwa wani lokaci jikinta ya jik'e da gumi kamar an watsa mata ruwa....
Magana MA'U ta jiyo daga zaure,hakan ya sata lek'owa ta ga ko waye.....
Mutum ta gani sai layi yake,tana lek'awa ta dawo tana fad'in
''Caarrr uba dama wai abunda kikema gudu kenan,shegiya y'ar bak'in ciki,kin zo kin wuce ko kuwa sai na b'ab'b'laki.............
*_~#Ido na zare ina fad'in ''ina za ta,ba dai gurin wancan d'an magarunba.....~_*
____________________________
_MASOYA *RAYUWAR WANI* INA BAKU HAK'URI NA RASHIN TYPING DA BANYI BA A YAU,COZ KWANA BIYU INA JINA SAI AHANKALI,BANA JIN DA'DI SOSAI,INA FATAN ZAKUYIMIN UZURI.._
_____________________________
*_~#TEAM KHUBRA.~_*
*_REAL SMASHER_* 🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*1/ąpril,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
*ɛɖıɬɛɖ ცყ*
_HAFSAT M.U {rɛąl ɧą℘cყ}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*
*ADDU'AH IDAN ZA A FARA ALWALA*
_BISMILLAH!!!_
*ADDU'AH IDAN AN GAMA ALWALA*
_ASH-HADU AN-LAA ILAH ILLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAHU,WA-ASHHADU ANNA MUHAMMADIN ABDUHU WARASULUH..._
_ALLAHUMMA JA'ALNIY MINAT-TAWWABIYNA,WAJA'ALNIY MINAL MUTA'DAHHIRIYNA..._
_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA ASHHADU ANLAA ILAHA ILLA ANTA ASTAGHFIRUKA WA-ATUBU ILAIK..._
*_~#HISNUL-MUSLIM~_*
*~__________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~__________________________~*
_Y'an uwa muna barar addu'ah daga gareku sis ena babu lapia,jikinta ya sake tashi da fatan Allah ya tashi kafad'unta.._
_Wish u a very quick and speed recovery MY HUBBEEY_
*~_________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*1⃣2⃣*
"Dan Allah BABA kiyi hak'uri wallahi d'an shaye² ne,sai neman fad'omin yake a ka d'azunma"...
"Ai wallahi yau ko nemanki zaiyi sai kin fita idan kuma ba haka ba na rantse sai jikinki ya fad'a miki"....
Tsaiwa taci gaba dayi jikinta sai rawa yake...
Ganin tana neman raina mata hankali yasa MA'U ta fice ta nufi d'akin shirginta...
Fitowa KHUBRAN tayi daga d'akin dan tun da taga ta fita tasan ba zasu kwashe ta dad'iba..
Karo sukaci da MA'U ta d'auko tab'arya,a guje tayi waje tana rafka ihuu...
Taimakon da Allah yayiwa KHUBRA lokacin da MA'U ta lek'a bayan ta dawo shi kuma ya juya ya fice yana faman tangad'i,ya nemi hanya yaci gaba gara rayuwarsa...
Tana fita ta tarar babu kowa,wannan shi ya bata sauk'i da ta fita bata ganshi ba tayiwa Allah godiya...
Ta d'an jima a tsaye a waje kafin ta juyo ta dawo da k'arfin gwuiwarta...
Wani malalacin kallo MA'U tayi mata wanda yasa ta sha jinin jikinta...
Kanta a k'asa ta gagara d'agowa...
''Munafuka da ana kije kina k'i yanzun daga wane gidan uwar kike?''
Ko tari batayi ba bare ta amsata,hakan yasa ta mik'o mata hannu tana fad'in
''Bani abunda kika samo''...
Idonta a waje take kallon MA'U
''Wallahi BABA banma ganshiba da na fita ''....
''Gidan wace uwar kika zauna da kika tarar bayanan?''....
''Sai ki wuce ki d'auka wancan abun ki ci''...
Sum² ta wuce ta d'auka tana shigewa d'akin shirgin nata....
Jik'awa tayi haka ta k'asumawa cikinta ko isashshen sugar babu a ciki...
Tun zuwanta garin wannan shi ne karo na farko da wani abu ya shiga cikin hanjinta,baya ga k'uli² da tayi ta k'amusa....
Tsaf ta share wanda ta jik'a, ita kuwa gogar spaghetti ta d'auko ta silala jellop akan idon KHUBRA sai k'amshi take ta sa gaba ta ci iya cinta...
Tana gamawa ko mintuna 10 bata k'araba a gidan tak'arawa k'afafunta wuta....
Sai KHUBRA dake faman gadin gidan ita d'aya....
Tana nan zaune tana fama da sana'ar tata,nan wani daddad'an bacci yayi gaba da ita...
**************
''Please Ki tsaya ki saurare ni my princess,nasan dai dawowan da nayi kike mamaki,ya akayi na dawo,fushi da ke bazai kaimuba..
Wannan kukan kuma bana son ganinki kina min asarar wad'annan precious tears en''...
'Dan murmushi sukama juna...
Kafin yaja hannunta yana fad'in
''Muje muyi fira toh''
Ya shiga janta zuwa wani k'ayataccen garden....
Gaba d'aya gurin ya k'awatu da wasu irin green en grasses,baya ga dogayen bishiyu masu tsananin kyau,gefe guda kuma k'orama ce take gudu ta ratsa ta cikin lambun....
Can daga gefe wasu fararen tattabaru ne suke shawagi daga sama zuwa k'asa suna wasansu,sai kukan tsuntaaye da ya dad'a k'awata shirun gurin...
Akan grasses en suka zauna,basu kai ga saman fararen kujerun dake zagaye da gurin ba....
Kansa ya d'ora akan cinyanta,suna firansu mai ban sha'awa...
Sai wasa take da bak'in suman kansa..
Idanunsa a lumshe kamar mai bacci,zuwa can ya mirgina yana kallon fuskanta...
Ganin kallon ba na k'are bane ta sunkuya dai² fuskansa ta hura masa iska,wanda ya sashi wani ajiyan zuciya...
A hankali ya shiga bud'e eyes ensa da suke brown colour tsakiyansu da wani haske tamkar na mage...
Janyota yayi yana mik'ewa zaune..
Fuskanta ya tallafe da hannu,ya dad'a matso da ita yanda suna jin fitar numfashin juna...
Bai jira komaiba ya had'e bakinsu guri d'aya sun jima haka,kafin wasan nasu ya canja salo....
Sunyi nisa acikin wata duniyar,wanda gaba d'aya KHUBRA a tsorace take da al'amuransa...
Turashi ta shiga yi amma ta kasa breaking abunda ke tsakaninsu...
Saboda rik'on da yayi mata ba na wasa bane..
Kuka ta fasa masa,wanda ya sashi cikata babu shiri,yana kallon cikin idonta..
''Haba wifey me kike nufi kuma,nifa naki ne,kuma ke tawa ce..
Yin haka dai² yake da nuna rashin