Showing 21001 words to 24000 words out of 159513 words
Chapter 8 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt
ita har bayyanarsa..
Kamar wancan lokacin ya zayyano musu abunda ya faru tun daga tafiyarsu kawo yau da suka dawo..
Kana ya d'ora da fad'in
''Dalilin dawowarku shi ne,Mijin naki ya fito miki da wani hali,idan yasa k'afa ya fita baya dawowa sai tsakar dare''
Nan taita d'aga kai kamar k'adange tana fad'in
''Haka abun yake''
Wata dariya ya saki mai kama da kukan jaki
''Zai dena da sannu,sai dai ki guji abunda zai had'a ku fad'a,yana da matuk'ar taurin kai,muma da k'yar muka shawo kansa,saboda haka a kiyaye''
Har za tayi sub'ul da baka na tambayan kud'in aiki sai kuma ta dafe bakinta tana tuno irin yadda sukayi wancan karon...
''Ku tashi ku bani guri,y'ay'an shaid'anu sun fara nema na...
Babu shiri suka baro gurin cikin sassarfa,ba tare da kowacce tayi gangancin waiwayawa ba...
A k'ofar gidan TABAWA sukayi sallama kowacce ta nufi gidanta...
《《《》》》
Shaf ta manta bata rufe fuskantaba,saboda tsananin murnan yadda ta samu nasaran taradda matar bata d'auki wata y'ar aikinba..
Burinta a yanzun bai wuce ganin KHUBRA a cikin mawuyacin hali ba,shi yasa ranta fes ta nufo titin da niyyar hawa mota..
Tsaye take tana kallon abubuwan hawa suna gilmawa a titin...
Gani tayi an tsaya a gabanta,da wani mataccen babur,wani matsiyacin kallo ta bishi da shi,cike da jaraba ta d'ago idanu zata zazzage masa,karaf suna had'a ido sha'awa ya motsa mata fiye da ko wane rana da tayi shi a gida...
Shiru tayi ta kasa magana,jikinta har rawa yake,lokacin da ta ganshi
''Hajiya ina zuwa ne?''
Yana magana yana lasar leb'b'ansa kamar maye
''Rijiyar lemo zani''
''Toh Bismillah!hau muje na kaiki''
Ko jira batayi ya k'arasa ba tayi tsalle ta d'afe bayansa,shi kuwa ya figa machine en,tafiya kawai suke,MA'U gaba d'aya ta kasa samun sukuni,sai matsawa take jikinsa,tana ta faman mutsu² take masa a baya,shi kuwa yana jinta yayi shiru dama abunda yake nema kenan tunda d'an bariki ne,kuma abunda ya fito nema kenan,inda zai rage dare ba tare da kwabonsa yayi ciwo ba..
Sha'awanta sai dad'a k'aruwa yake fiye da farkon ganinsa,haka sai da ta kai gaba d'aya sun koma kan tank en machine en,shi dai yana jinta yayi shiru,har suka shiga cikin line en da gidan MA'U yake...
A bakin k'ofa da zata sauka kasancewar maghreb yayi,da k'yar ta sauka shima sai da ta dafa shi sannan ta sauka,idanunta duk sun k'ank'ance saboda masifa...
''To Hajiya sallame ni na tafi,kinga machine en nawa ba wani Fitilar ce ke gare shi ba mai kyau''
K'afafuwanta take matsewa tana tsaye,duk ta shiga damuwa jin zai tafi
Da damuwa take fad'in ''bari na kawo maka kud'in ina zuwa''...
Shigewa tayi cikin gidan tana cije leb'e ta san idan har ya kufce mata wannan ta shiga tarama ba uku ba.....
Kwanciya tayi a d'aki tana k'walawa KHUBRA kira,da gudu ta shigo har tana tuntub'e
Ai kuwa MA'U ta dad'a rashewa a tana fad'in
''Yi sauri ki cewa mai mashin a waje,ya shigo bani da lafiya,ke kuma ba zaki iya d'aga ni ba''
Da damuwa KHUBRA ta tsaya tana mata sannu
Tsawa MA'U ta kwad'a mata da yasa ta fice a guje..
Fitarta daga d'akin yasa MA'U tayi saurin cire kayan jikinta,ta lullub'a da bargo...
Hankalinta a tashe tana fita ta ganshi tsaye ya kafe machine en gefe
Tana haki take fad'in ''dan Allah bawan Allah ka temakamin bata da lapia karta mutu''
Kallon rashin fahimta yayi mata,can kuma yabi bayanta ganin ta riga ta shige..
Har tsakar d'akin MA'U dake k'udundune cikin bargo,tayi shiru kamar gawa
''Fita KHUBRA zamuyi magana''
Umarnin da MA'U ta bata kenan,tuni tasa kai ta fice daga d'akin,ta koma nata tana jimamin halin da take ciki...
Fitarta ke da wuya MA'U ta mik'e,babu komai a jikinta,tana girgiza
Wata dariya yayi irin ta y'an bariki
''Shegiya duniya,yo ae ba sai kinyi haka zaki sameni ba,da kin fad'ama da baki b'atawa kanki lokaci ba''
Ita dai MA'U babu baki,sai ido,take kuwa sabon saurayin nata ya shiga rud'ata da salo iri² kasancewarsa k'wararren d'an tasha..
Sun lula wata duniyar daban,bayan gurnaninsu babu abunda kake jin sautinsa na fita,sai da suka shafe tsawon awanni 5 suna abu d'aya,ba tare da MA'U ta gaji ba,shi kuwa dama haka yake so...
K'arshe ma a gidan ya kwana,inda ya janyo machine ensa ya shigo dashi har cikin gidan...
Tun da safe kafin KHUBRA ta tashi ya bar gidan,da alk'awarin zai dawo anjima tunda ta fad'a masa yau yarinyar zata tafi,amma yazo da wuri...
Tun kafin rana ta take MA'U ta kira KHUBRA akan ta had'a kayanta,baiwar Allah tayi tunanin ko gida za a kaita,tana ta murna...
Sai da taga ba tasha suka nufa ba,tad'an kalli MA'U a kaikaice tace
''BABA MA'U ina zamuje ne?''
''Gidan uwarki da ubanki zamu,shegiya mai bak'in halin tsiya''
Ido KHUBRA ta fiddo waje,me yayi zafi?
Ta tambayi kanta,ba tare da samun amsa ba......
*_~#TEAM KHUBRA~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*23/ąpril,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*ADDU'AH BAYAN GAMA KIRAN SALLAH.*
_A LOKACIN DA LADANIN YAYI KALMAR SHAHADA SAI MAI SAURARO YACE:-_
_WA-ANA ASH-HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAH,WA-ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA-RASULUH,RADHIYTU BILLAHI RABBAN WABI MUHAMMADIN RASULAN WA-BIL ISLAMA DIYNAN.._
*BAYAN YA GAMA SAI YAYI SALATI GA ANNABI (S.A.W),SANNAN YA 'DORA DA FA'DIN...*
_ALLAHUMMA RABBA HAZIHID-DA'AWATITTAAMMAH,WAS-SALATUL K'A'IMA ATIY MUHAMMADANUL WASILATA WAL-FADHIYLAH,WAB'ASHU MAK'AMAN MAHMUDANIL-LAZIY WA'ADTTAH,INNAKA LA TUKHLIFUL MIY'AD.._
*DAGA NAN KUMA SAI MUTUM YAYIWA KANSA ADDU'AH,DOMIN YIN ADDU'AH TSAKANIN KIRAN SALLAH DA IK'AMA KARB'AB'B'IYA CE..*
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*1⃣7⃣*
*T*un da tayi shiru bata sake ko da tariba,har suka shiga unguwan tana ta bin ko ina da kallo kamar wacce take fadar shugaban k'asa,haka suka k'araso k'ofar gidan...
Tana tsaye MA'U ta sallami mai NAPEP,tayi gaba ita kuma tana binta a baya har cikin gidan,da sallama suka shiga ita dai KHUBRA kanta na k'asa ta kasa kallon komai,duk kuwa da yanda gidan yake cike da abubuwan kallo..
A parlor suka tarar da ita ta hikimce kamar basarakiya,tana murmushi ta amsa musu,suka shigo suna zama,a k'asa kan rug KHUBRA ta zauna tana gaishe da hajiyan,ita ko MA'U ta hakimce akan sofa,suna gaisawa cikin sakin fuska..
Yanda MA'U ke k'asa da kai,sai ka rantse matar ta girme mata,ta mata bayani tsaf game da KHUBRA,lokacin da MA'U ta ambaci sunan KHUBRA matar ta bita da kallo hakan yayi dai² lokacin da KHUBRAN ta d'ago kanta....
Sai da taji wani mugun fad'uwar gaba,kan tsananin kyau d'an usul da ta gani a tare da KHUBRAN,a hakanma wai dan tana matsayin y'ar k'auye,ina kuma ga ace ta waye?''
Tunani iri daban² haka haka matar da ake kira HAJIYA MURJA take a ranta,a fili kuwa sai murmushin yak'e take uwa an mata dole...
Cikin sakin fuska wanda da gani bai kai zuci ba,haka suka rabu da MA'U,ta mata alheri na Soap ne da su detergents a cewarta tayi wanki...
Cike da murna MA'U ta amshe ta k'arawa k'afafunta wuta,ko sallama bata jira sunyi da KHUBRA ba....
Ga KHUBRA kuwa wannan ba bak'on al'amari bane da zai d'aga mata hankali,hakan da ta riga ta sani shi yasa ko damuwa batayi ba...
Dawowar matar daga rakiyan da tayiwa MA'U tana dad'a mata godiya,tayiwa KHUBRA dake zaune wani wawan kallo,ko me hakan ke nufi? ohoooo....
Tana nan zaune ba tare da HAJIYAN tayi mata magana ba,ta sake hakimcewa a saman sofa tana watching T.V....
Da ihuuuuu suka shigo gidan,maimakon sallama da aka san d'an musulmi da ita,y'an mata ne su uku,sai yara biyu maza...
Duka babbar bazata haura 18 yrs ba,inda mai bi mata nake tunanin zata kai 17 da gani tsakanin ta farko da ta biyu ba a sami wata tazara ba,sai ta ukun mai shekatu 14,sai namijin dake bi mata mai shekaru 12,in da na k'arshe d'an shekara 9 ke tsalle² uwa yaron biri...
''Oyoyo autanah'' HAJIYAN ta fad'a tana bud'e hannu..
Da gudunsa ya nufeta yana tab'ara,ita kuwa ta biye masa
''Kai hajiya dan Allah mu banda mu?''
Fad'in d'aya daga cikin y'an matan
''A'aaaaa ni na isa,haba uwar masu gida,taho nan maza uwata''
Duk abunda suke tana zaune ko tari bataiba,sai da sukai son ransu,sannan hajiyan ta turasu suje suyi wanka,dukansu suka mik'e suna bin hanyoyin d'akunansu....
Wani kallo ta mata cike da tsoro ta juya tana kallon hajiyan a zatontama gamo tayi,baki na rawa take tambayan hajiyan
''Hajiya wace wannan kuma?''
Sai lokacin Hajiyan ta kalli inda take nuna mata
''Oohhh!ASHNA sabuwan housemaid ne da mukayi,yau aka kawota,maza nuna mata inda zata na kwana''
Tana yi tana tana yatsina fuska,duk da fara ce ba zaka sata a sahun masu kyauba,sai dai kawai kud'i da suka hana a gano hakan...
''Tabbb!wallahi hajiya ba dani ba,sai dai ko waccen shashashar,da bata damu da darajarta ba''
''To maza turomin ita,sai ta nuna mata''
Haka ta wuce tana hararar KHUBRA da bata sanma me take yiba
Fitowar d'aya yarinyar alamun ranta a b'ace yake,ta zauna kusa da hajiyan tana fad'in
''Hajiya gani ASHNA tace kina kira na''
''Yawwa yi maza ki nunawa waccan d'akin da y'an aiki ke zama''
Inda hajiyan ta nuna ta kalla,aiko cike da farin ciki ta k'araso kusa da KHUBRA tana mik'a mata hannu
''Suna na ZUHRA kefa y'ar uwa?''
Cikin halin ko in kula take maganarta,murmushi KHUBRA tayi mata tana mik'a mata nata hannun
''KHUBRA suna na''
Ko kafin hannunsu ya had'u da juna,hajiyan ta doke hannun KHUBRA,cike da masifa ta kewa ZUHRA fad'a
''Kinga ZUHRA ki kiyayeni wallahi bana son rawar kai,har zuwa yaushe zaki gane matsayinki?''
''Nifa hajiya ba wani matsayi gareniba,naga dai duk d'aya muke a gurin Allah,wata k'ilama tafini a gurinsa,idan har ta fini kyautata masa''
''To uwar tsari,bazan gaji da nuna miki hanya ba,saboda haka kibi ni a sannu,dan wollahi wata rana sai na b'allaki idan bakiyi a hankali ba''
Ta k'arasa tana zabga mata harara
''Ke kuma ta nuna KHUBRA dake sunkuye,ina son kisan cewa
_BAKIN RIJIYA BA GURIN WASAN MAKAHO BANE_
So ki tsaya iya matsayiki,karki manta mun kawoki ne dan kiyi mana bauta,ina fatan zaki kula da aikinki''..
''Wuce ki rakata d'akin y'an aiki''
Ta fad'a a tsawace
Jiki babu k'wari ZUHRA ta wuce ita kuma KHUBRA na bin bayanta,har b'angaren y'an aikin gidan..
Suna shiga ZUHRA ta dawo kusa da KHUBRA tana fad'in
''Dan Allah kiyi hak'uri da duk abunda hajiyanmu za tayi miki,wallahi haka halinta yake,kaf y'an aikin gidan nan basa jimawa idan ankawo,dalilin halintane suke barin aikin''
Ta d'an saurara tana kallon KHUBRAN
''Kada ki damu in sha Allah zan zama mai hak'uri da duk abunda zan gani,na gode sosai da nuna kulawarki gare ni''
Sukama juna murmushi,daga nan ta taya KHUBRAN suka gyara d'akin tsaff,kamar ba shiba,sannan ta mata sallama ta koma cikin gida...
《《《》》》
Tun data fita daga gidan,take cin karo da maza iri² duk kuwa da yanda take ta rufe fuska,hakan bai hana maza sun biyo ta ba,kamar jiya haka ta samu wani Alhajin k'auye dan kuwa harda y'ar motarsa mai kama da zallan k'arfe,haka da dad'in baki da komai suka k'ulle,sai gidan MA'UN..
Kamar jiya haka yauma suka shek'e ayarsu,sai dariya suke b'ab'akawa,bayan sun gama,dai² lokacin da tasan wannan mutumin na jiya da ko sunansa bata sani ba zai zo,ta sallami alhajin da bawai ya gama kashe mata k'ishirwarta bane..
Har da y'an kud'ad'ensa ya kawo ya bata ita kuwa ganinsu ta dingayi kamar ya bata duniya...
Yana tafiya kuwa mutumin na zuwa,da murnanta ta tare shi,tun daga tsakar gida suka fara watsi da kayan jikinsu,suna shiga d'akin kuwa ya shiga service en ta,tako ina ihunsu kake ji,abun ban haushi,tsawon awanni suka b'ata batare da sun gundiri juna ba,ranar da k'yar yayiwa MA'U dabara ya tafi,kan sai gobe,cike da k'aryar aiki gareshi...
《《《》》》
Tun kan gari ya gama wayewa,ta tashi ta shiga gyara gidan,duk da har lokacin bata san specific aikin ta ba,tsaff ta share ko ina duk kuwa da girma da yake da shi,sai harabar kad'ai da taga wani namiji yana sharewa..
Sakkowanta daga sama,kamar zata rushe matakalar benen,har ta k'idasa sakkowa,a kan sofa ta zauna tana jiran yaran su kammala sakkowa..
ZUHRA ce ta fara sakkowa,har k'asa ta gaida hajiyan,tana amsawa da k'yar kamar ba y'ar cikinta ba...
''Ina FATAHIYYA da ASHNA?''
''Suna d'aki ne hajiya''
''Ok!maza kiramin wannan yarinyar''
Ficewa tayi tana amsa mata
A hanya ta ganta zaune kusa da shuke²n lambu tana ta kallon tsuntsaye dake gurin suna wasa,ita ko abun ya mata dad'i sosai yanayin gurin gwanin sha'awa..
Ta baya ZUHRA ta lallab'o ta rufe mata ido,murmushi tayi tana zare hannunta daga kan fuskanta,ta juyo tana kallonta,gaisawa sukayi ta hanyar musabiha da juna,ta nemi kusa da ita ta zauna suna hira jefi²,tun KHUBRA na murmushi kad'ai har ta soma bata answer,sosai suka saki jiki da juna...
''Laaaa!wallahi na manta''
Kallon ZUHRAN tayi tana fad'in
''Me kika manta?''
''Hajiyace fa tace na kirawoki''
Ai tuni KHUBRA ta d'auki hanya,sai biyota ZUHRA tayi a baya
A parlor ta tarar da Hajiyan da ASHNA na gefenta na dama,FATAHIYYA kuwa tayi pillow da cinyanta,suna zuba sangarta..
Kan rug ta zauna tana gaida Hajiyan,da k'yar ta amsa,kamar ana mata dole ta shiga yiwa KHUBRA bayanin duk wani aiki da zatana yi a gidan,kafin ta bata umarnin fara aikin daga ranan..
Babu musu kuwa KHUBRAN ta nemi a nuna mata kitchen,ZUHRA ce ta raka ta,tana d'an nuna mata wasu abubuwan da bata gane yanda za tayi amfani da shiba,cikin dabara KHUBRAN taita tambayarta abubuwan da suke so da wanda basa so,aiko taita mata bayani...
Tana aiki ZUHRA na mata hiran yanda gidan nasu yake,kamar ta tambayeta,har ta kammala girkin duk da ba wani sanin abincin zamani tayiba tayi k'ok'ari,haka ta jeresu a dinning kamar yadda ZUHRA ta nuna mata,ita kuma tana tayata...
Tare suka fita daga parlorn ASHNA na jin haushin KHUBRA da ta rasa dalilin hakan,ita ko ko ta kantama bata biba,coz bata san tana yiba...
A guarding suka zauna k'afafunsu a cikin ruwan gurin,sai wasa suke suna dariya uwa sun saba dama can...
''Laaaaa!na manta ban baki labarin YAYANMU ba''
ZUHRA ta fad'a tana washe baki
''YAYANKU kuma,dama kuna da wani wa namiji?''
'Ehhh! muna da amma baya k'asarma,karatu ya rabamu da shi,karki so kiga yanda yake sona sosai''
Tayi maganar cike da jin dad'in yanayin da take ciki
''Allah sarki,Allah ya dawo da shi lafiya,suka amsa da ameen oll''
************
Kwanaki sun riski KHUBRA a cikin gidansu ZUHRA wanda bayan ZUHRA babu da wanda take sakewa,bayaga haka kuwa bata wani samun sakin fuska daga sauran y'an gidan bama kamar k'ananan da kana yi musu magana zasu maka rashin kunya komai girmanka kuwa,hakan yasa ko me za suyi KHUBRA bata musu magana.........
Wannan kenan....
_#Haaaaaaa!Kunawa *MA'U* fatar ciwo ko,to maza ta jiku ni ba iya cetonku zanba,karta d'oramun k'afa na kasa tashi,dama bawani k'wari gare niba._
_Naga sak'onninku na addu'ah ina godiya sosai,Allah ya bar zumunci._ 👏👏
*_~#TEAM KHURA.~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*