Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 159513 words

Chapter 10 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1213

Ads at the middle of Article




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*3/mąყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~________________________~*
_Masoyana a ko ina kuka kasance bazan iya mantawa da k'auna,halacci tare kuma da kyatatawarku gare niba,tabbas kun nunamin karamci wanda ba zai tab'a gogewa a cikin raina ba har sai bayan bana numfashi,Allah ya bar k'auna tare da zumunci.._
N
A
G
O
D
E
_Sosai da sosai,Allah ya barmin ku,duk inda kuke ina tare da ku da izinin Allah... *#1 luv my peps..*_
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._


*~________________________~*



*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*2⃣0⃣*








*K'*afafunta saboda tsabar kid'imewa da tayi har neman kasa d'aukarta suke,kamar an cillota ta fad'o d'akin aiko bata jiraba ta afka kan MALAM dake ta sharara bacci abunsa...
Shafa shi ta shiga yi shi ko maimakon ya farka kamar yadda yayi d'azun saima dad'a gyara kwanciya da yayi,yana sakin numfashi abunsa...


Haushi duk yabi ya cika mata zuciya,haushin rashin farkawarsa yasa ta kirb'a masa wani naushi aiko take ya bud'e ido,murmushi ya mata ya sake kulle idonsa yana mai dad'a gyara kwanciyarsa......


Kamar mahaukaciya ta fice tana sosa jikinta........


《《》》


Tsaf suka gama shek'e ayarsu a daren,har safiya suna mak'ale da juna...
Yanayin kwanciyar da suka yi kai da gani kasan ba shiryawa baccin suka yiba,dan kam da gani kasan suna tsaka da harka baccin yayi awon gaba da su.....


Ko da ta farka lokacin har gari ya gama haske,sannan ta bud'e idanunta da suka mata nauyi...
Jiki ba k'wari ta fita tayi wanka,bata tashe shiba dan kansa ya tashi yayi wanka,lokacin ko a takure ya ganta wanda ita kad'ai tasan halin da take ciki...
Sai da ya gama shirin ficewa tukun ya dawo
''Yahhh!d'an kawo wani abu mana''


Da rinannun idanuwanta ta kalleshi tana neman k'arin bayani...
''Ko zaki cemin oga bai sallamekiba?''


''Ohhh!kuma nufinka ni zan baka wani abu cikin kud'in ne?wato baya ga biyan da na maka har wani sabon tukuicin kake nema?''


Dariya yayi irin tasu ta y'an duniya,kafin ya juya yana nufar hanya yasan kam duk inda ya kai da son duniya MA'U ta fishi,haka ya fice yana fad'in
''Sai kin ganni''
Bata ko d'aga ido ta kalleshi ba bare ta bashi amsa.........


《《》》


Ko da ta farka bata wani b'ata lokaci ba ta koma bakin aikinta,har ta kammala ta fito da niyyan komawa b'angarenta..
A parlor ta tarar da ita tayi shirim cikin sofa,har zata fita ta kwad'a mata wata tsawa,ba shiri KHUBRAN ta dawo dan ita kam a yanzun baza ta so abunda zai rabata da gidan ba,dan ko shi ne rufin asirinta a wannan halin da take ciki...


''Wanki yana nan ya taru,saboda haka kiyi maza ki soma''


Shiru tayi ta kasa magana,zuwa wani lokaci kuma ta mik'e uwa kazar da kwai ya fashewa a ciki.Haka ta jido kayan masu uban yawa sai wari suke uwa masu kayan basu san wani abu mai kama da turare ba,ko da ta kaisu bakin washing machine en gani tayi kayan sam ba zata iya wanke su iya yau ba,dan ko kaya ne har na mutum biyar,bata b'atawa kanta lokaci gurin tunani ba ta hau abunda tasan shi zai fishsheta,tun tana na marmari har ta gaji.A haka su ZAHRA suka dawo suka tarar da ita,ko kallon arzik'i bata samu daga gurin ASHNA da FATAHIYYA ba..
ZAHRA kam dama tuni ta riga kowa shigowa,nan tai ta mata sannu,haka suka shiga ciki...
Ko cikakken mintuna talatin batayi ba ta fito ta dawo gurinta aiko tare suka ci gaba da aikin shanya,har malaminsu na islamiyya ya zo,a nan ne ta barta ta tafi,har suka dawo bata kammala ba,k'arshe dai yinin ranar haka ya shud'e mata tana abu d'aya..
Wajen k'arfe goma na dare ta tattara ta ajiye su akan ta k'arasa idan Allah ya kaimu washe gari........




Rayuwa ta mik'awa KHUBRA cikin wannan gida,wanda iya wannan lokacin babu wani abu dake shiga tsakaninta da y'ay'an gidan,ta kame kanta had'e da rik'e matsayinta na y'ar takala,duk wani aikinta tana gama shi take barin cikinsu ta koma guarding tai zamanta,mafi yawancin lokaci nan ne gurin da ke d'ebe mata kewa,musamman idan ta tuna ABBANTA ko MAMANTA da bata tashi tayi rayuwa da ita ba...


Cikin sauri² ta fito zata shiga cikin gidan,karo suka kusa yi da ZAHRA,da saurinta kuma ta tsaya tana kallonta duk sai murna take uwa wacce akama wata gagarumar kyauta,kallonta ta tsaya yi...
Da sauri ZAHRA ta rik'eta tana jan hannunta suka nufi kitchen,aikinta ta fara suna ta hira,duka yau tana kula da yanayin ZAHRA wani murna take tayi ita kuma tak'i tambayan dalilin,suna ta aikin su,can ZAHRA ta d'ago tana kallon KHUBRA...
''Wai kam sis kin san wani abu?''
Kai kad'ai ta kad'a mata kafin ta bud'e baki tayi magana ZAHRA ta katse ta da fad 'in
''Cikin month ennan YAYANMU zai dawo fa''
''Eeyyahh!Allah dawo da shi lafiya,yasa ya samo abunda yaje nema''
''Ameen dear,aiko zai sha labarinki duk ranan da mukayi waya''
Ita dai KHUBRA bata sake magana ba,ta ci gaba da aikinta,ZAHRA kuwa nan taita bata labarin YAYAN nasu,wanda har zuwa yau bata tab'a tsintar sunansa ba..


Har suka kammala,ZAHRA nata mata surutu,ita ko sai dai tayi murmushi yanayin yanda suke rayuwa da yadda ZAHRA take bata labarin irin rayuwarsu abun sosai yake bata sha'awa,har wani lokaci ma ta kanji inama itama tana da d'an uwa,duk lokacin da ta tuna haka takan yi kuka sosai...


*SOME WEEKS LEAP.*


Da sanyin safiya ta tashi,bata b'ata lokaci ba ta shiga kitchen,tunanin irin girkin da za tayi ta hau yi,dan kam tun jiya HAJIYA MURJA ta sanar da ita suna da babban bak'o,saboda haka tana son tayi girke² kaloli da yawa had'e da drinks na gargajiya,coz ta san bak'on baya son tamalli da kayan gwangwani...


Tana cikin tunanintan ZAHRA ta shigo da saurinta,sis bafa muga ta zama ba,kinga tunda ke kad'aice barin fasa binsu airport,muyi abunda ya kamata,nan ko suka hau aiki ba ji bare gani,suna yi suna hiransu...

Tsawon awanni da dama suna ta aikin kafin suka kammala,ficewa suka yi bayan sun gama shirya table kafin kowa ya kama hanyarsa...


*SOME HOURS LATER...*


Wani bak'in PRADO ne ya Parker a haraban gidan,cikin k'asaita aka bud'e k'ofan ko kafin ya bud'e ya fito sai da ya d'auki lokaci kafin ya ziro k'afarsa ya fito,cikin k'ana nan kaya wanda suka matuk'ar amsarsa uwa bature,gashinsa ya d'an yi tudu ta gaba sai shek'i yake da gani kasan yana shan gyara,idanunsa saye cikin sunglasses bak'i na GUCCI,komai yayi kyau yake masa,cikin takun k'asaita ya soma tafiya,har cikin parlor da ya sha gyara.A baya suka bishi har cikin parlorn sai rawar kai ASHNA da FATAHIYYA suke zubawa,shi kam yana gaba bai ko kula ta kansu ba,a zaune suka tarar da HAJIYAN sai wani dare baki take tana dariya had'e da fad'in
''Oyoyo my son''


Fuskarsa d'auke da murmushi da ya dad'a k'awatar da ita,ya amsa yana zama cikin sofa..
Cike da ladabi uwa ba wanda ya fito daga k'asar turawaba ya gaidata,tana amsawa fuskarta da fara'a wacce ban tab'a zaton tana da ita ba...


'Dakinsa ya nufa cike da gajiya,yana shiga wani sanyayyen k'amshi ya doki hancinsa,take kowace gab'a ta jikinsa ta amsa,jinsa yake uwa an masa duka,da k'yar ya k'arasa kan bed,aiko ya zube saman bed yana dad'a shak'an k'amshin turaren kasala na dad'a saukar masa a jiki,jin abun zai masa yawa yasa ya mik'e da k'yar ya iya nufar toilet,ya jima ciki kafin ya fito,ko minti biyar bai ba ya shirya cikin singlet fari da boxer,ai ko ya haye saman bed take baccin gajiya ya kwashe shi...


Tun bayan da suka gama aikin suka k'ule a guarding sai fira suke suna dariya abunsu uwa ya da k'anwa duk da baza su wuce sa'annin juna ba...
Sam basu ji shigowar motor ensu ASHNA ba,sai shewansu suke KHUBRA na bata labarin k'auyensu,ita ko ZAHRA sai kwasar dariya take...


Three hours ya d'auka yana baccin gajiya kafin ya farka,jin cikinsa fayau yasa cikin sauri² ya sake watsawa jikinsa ruwa,jallabiyya ya zura,sai da yayi sallah sannan ya fito,suna zaune cikin parlorn su HANEEF duk sun cika gurin da hayaniya,ganin fitowansa yasa take suka shiga hankalinsu ba tare da ya furta ko a ba,k'ala bai ceba amma gaba d'ayansu kowa ya k'ame kamar doll...


''MAMA ni kam ina Sis ena?''
Tab'e baki tayi kafin cikin b'acin rai ta iya furta
''Tana can tare da wannan shashashar yarinyar''

''Wace wannan kuma?''
Yayi maganar yana yamutsa fuska...


Saboda tasan halinsa na rashin son magana yasa tace
''Wata ce''
Daga haka ko ta bar maganar ba tare da ta sake furta komai ba ta ja bakinta tayi shiru...


*******
''Laaa!sis kinga lokaci ya tafi nasanma yanzu haka BB ya dawo,taso muje dan Allah''


''A'a y'ar uwa ki je yanzun zan biyoki daga baya ''


''Ba wani nan nasan ba zuwa za kiyi ba''


Murmushi kad'ai tayi,ita kuma tayi saurin barin gurin tana fad'in


''Sai na ganki duk da ba yarda nayi akan za kizo ba''
Tana tafe da d'an gudunta ta shiga parlorn,idanunta na sauka kansa ta fasa wani ihu da gudu kuma ta fad'a jikinsa....


Jin an fad'o jikinsa yasa ya kalleta,sai murmushi take dokawa,shi ko ya had'e fuska yana fad'in
''Matsamin a nan,ai ke kam fushi nake da ke''


''Wayyoo YAYANAH dan Allah kayi sorry kar kayi fushi da ni,kasan duk duniya bana k'aunar naga kayi fushi da ni,ko so kake nayi kuka?''
Ta fad'a tana narke fuska za ta masa kuka


''Haba mana sis ina kika b'oye?ko kije tarona kuma na dawoma ban saki a idona ba why?''


''Ammm!YAYANAH Allah ko aiki mukayi shi yasa kaga banje taroka ba,kaima kasan ba haka kad'ai zan k'i zuwa ba,aiiii dai ka hak'ura ko?''
Tana d'an murmushi had'e da lek'en fuskansa da ya kawar da ita gefe...


Murmushin shima yayi mata,yana kad'a mata kai...


''Yeeehhhh!thnks BB na''

''Laaa!YAYANAH taso kaga abunda muka maka''
Ta kama hannunsa tana jaa zuwa dinning,a hankali ya bita har gurin tarin warmers en ya kallah yana tab'e baki,yasan dai wannan kam sai dai ko idan y'an aiki suka yi amma ba MAMAN ba bare kuma wad'ancan sangartattun biyu...


''Nikam sis kyale ni da wannan shirman masu aikin''


''Laaaa!YAYA fa mu mukayi,zauna kaga Allah yayi sweet sosai,kuma favourite naka mukayi''


Ta jaa masa kujeran tana turashi har sai da ya zauna,shi sam baya jin zai tab'a iya cin abincin masu aiki duk k'azamai dasu su maka wani abinci kuma mutum ya ci,k'amshin da ya ziyarceshi shi ya dakatar da shi daga maganar da yake yabi warmers en da kallo...
Drink en da take tsiyayawa a cup shi yabi da kallo sai k'amshi yake,murmushi yayi mata ganin yadda take ta rawar k'afa a kansa ya juya parlor ya kallesu duk sun zuba musu ido suna jiran ganin abunda zai faru,juyowa yayi ya sake kallonta yanda take masa yasa ya k'udirce a ransa ba zai bata kunya ba,ko da zai ci ya haras da shi zai gwada...


Cup en da ta cika da sob'o ta mik'a masa tana fad'in
''YAH bismillah!''


Karb'a yayi ya d'an d'osana cup en a bakinsa har da runtse ido,duk da yadda yake k'amshi bai gama tabbatarwa a ransa zaiyi dad'i ba sai da ya sha,aiko take ya shanye cup en hannunsa zuciyarsa cike da tunanin waye yayi wannan drink en haka?


Cup en ya mik'a mata,zuciyansa ta lula duniyar tunani.....


《《》》


Tun bayan da ZAHRA ta bar gurin itama ko zaman ya isheta,bata wani jima ba ta bar gurin,inda ta k'ule cikin d'aki tana aikin kuka da ya zame mata abokin rayuwa duk lokacin da ta tuna MAMANTA....


Ta jima a haka kafin da k'yar ta tsaida kukan,ta hanyar d'auro alwala ta tada sallah......






*_~#TEAM KHUBRA~_*






*_REAL SMASHER. 🤞🏻😘_*


💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*4/ʍɑվ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~________________________~*
_íղɑ ʍɑԵմҡ'ɑɾ ցօժíվɑ ՏօՏɑí ʍɑՏօվɑ,Տɑҡ'օղҡմ ɑ ҡմӀӀմʍ վɑղɑ ɾíՏҡɑԵɑ,ղɑ ցօժҽ ɑժժմ'օ'íղҡմ,ɑӀӀɑհ վɑ ҍɑɾ ҡ'ɑմղɑ.._ *ɾҽɑӀӀվ ӀմѵՏ մ ʍվ ԹҽԹՏ..💓💓*
*~________________________~*
_Tabbas ba dan bak'ar addu'ah babu kyaubaa da babu abunda zai hanani kwana yi miki addu'ar da sai kin gwammace baki zo duniyarba, amma kam tabbas mun barki da Allah shi kad'ai zai nuna miki ishara, Allah ya isar mana....._


*~________________________~*



*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*2⃣1⃣*










*T*un kafin ta idar ko bacci ya fara fisganta,da sauri tayi sallama da rarrafe ta haye kan katifan ko addu'anma idanunta a kulle suke kan bacci haka tayi addu'an kwanciya bacci,ko ninke abun sallan bata yiba bare hijab en da ta cillar a k'asa...
Cikakken mintuna uku sun yi mata yawa take bacci mai nauyi ya d'auketa......


《《》》

Zuba masa ta sake yi,shi ko sai dad'a kafa kai yake yana shanyewa a haka har sai da ya sha rabin jug en,sam bai sani ba yana can duniyar tunani,dariyan da ta saka ne ya dawo da shi diniyarsa yana mai binta da kallo,hannunsa ya sake sauke idanunsa har lokacin cup en na mak'ale a hannunsa,d'an murmushi yayi yana shafa kansa...


''YAH me zan sa maka?''
Tambayanta ya katse mishi tunani


''Anything ma sis''


Murmurshi tayi tana jin dad'in yadda yake nuna kulawa kan komai da take yi...
Wani warmer ta bud'e take ko ta zaro faifan sinasir,aiko yana gani ya hau murmushi coz yana sonsa sosai MAMA ce dai da yake ba wani iya girkin gargajiya tayi ba,ko da yake na zamaninma dai da sauk'i,(auu kada ta jiyo ni) ☺.......
Ai ko take ya dakatar da ita ta hanyar fad'in
''Sisnah bar shi haka ai kin gamamin komai tunda kikamin favourite nawa,sauran ki kyauta idan na gama abunda nake''


Sosai ya dage yaci sinasir en da miyan agusi,sukam su ASHNA suna cikin parlor duk abunda ke faruwa tsakanin ZAHRA da YAYAN NASU sun zuba ido ne suga ya zasu k'arke shi da ba cin abincin masu aiki yake ba,sai dai kuma kash abunda suka zata bai faruba,duk kuwa da sun san suna shiri sosai da ZAHRA a kan abuncin masu aiki komai zai iya faruwa hatta kuwa ita kanta ZAHRAN,sosai ya basu mamaki,sai da yaji uwa bazai iya tashiba sannan ya hak'ura tas ya shanye sob'on,fuskansa d'auke da fara'a ya kalli ZAHRA yana fad'in
''Thnks Lil sis''


Murmushin itama ta mayar masa kafin suka koma parlor da yake tsit uwa ba mutane...
Tabbatarwa da sukayi ya gama MAMA da muk'arrabanta suka dira a dinning en,har suna rige² gurin bud'e warmer en sinasir aiko dai² lokacin ya juya ya kallesu a hankali ya furta
''Lil sis maza ki adanamin sinasir ennan,coz da safe shi nake son ci''


''Laaaaa!BB ya maka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads