Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 159513 words

Chapter 27 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1236

Ads at the middle of Article

shirinsa ya fice MA'U na kwance ta kasa tab'uka komai kuma bata d'aga kai ta kalle shiba,da k'yar ta iya lallab'awa ta yi wanka shima jikinta sai kyarma yake haka dai ta shirya ta fice tare da kulle k'ofan ta nufi hospital...


《《》》


Lokacin da ya gama waya da UMMI yayi dai² da isowarsu k'ofar gidan,yana kallonsu suka bud'e gidan suka shiga,hakan ne yasa shi fitowa shima ya kulle motan sannan yabi bayansu.
A tsakar gidan ya tarar da su suna zaune kan tamarma sunyi jigum-jigum.
Guri ya samu ya zauna,sannan suka gaisa da BABA ZUWAIRA wacce KHUBRA ta kanainaye kamar wani yace zai tafi da ita duk ta hanata sukuni.


"Samari duk da dai ganinku nayi sama ta ka,hakan ba zaisa nayi saurin yanke hukunci ba,nasan dai duk inda akaje aka dawo kuna da alak'a da KHUBRA kuma alak'a mai k'arfi,duba da ganin yadda kuke kama da juna"


Kallon-kallo akayi tsakaninsu su uku kowa na burin gano abunda BABA ZUWAIRA ke fad'a a tare da d'an uwansa hatta da kuwa ita kanta KHUBRA dake kwance sai da ta d'ago tabi su KHALEEL da kallo.


"Tabbas ku en y'an uwane na hak'ik'a ko ban tambayaba nasan ku yayunta ne"
Tana magana da fara'a akan fuskarta tana kuma binsu da kallo,tun kafin BB yayi magana KHALEEL yayi tsalle ya dire da fad'in
"K'warai kuwa mu yayunta ne,tun bayan b'acewarta da muka yi neman bamu sametaba wanda ya had'a da jami'an tsaro a ciki,kaf cikin gari sai da aka dubata amma ba a ganta ba,ashema tana kusa-kusa damu kawai dai Allah ya nufa hakan dai sai ya faru"
Yayi shiru yana kallon BB daya kafe shi da kallo,ita kuwa KHUBRA kanta ta sauke k'asa tana sauraron maganganunsu.


"To ALHANDULILLAH tunda dai yau Allah ya nunamin wani naki KHUBRA kuma in sha Allah a yau ba sai gobe ba zaki bi danginki ku koma gida,saboda dama zamanki tare da ni ba shi ne mafi a'ala ba,ki zauna tare da danginki shi ne babban kwanciyar hankali kuma kema da su duk zakufi samun nutsuwa saboda kuna tare da juna.
Ni da kike tare da ni Allah ne ya had'amu kuma ina fatan Allah ya sake sadamu cikin amincinsa da alkhairinsa,yanzu zan baku labarin yadda akayi na samu KHUBRA da kuka ganmu tare"
Take ta shiga labarta musu yadda akayi suka had'u da zamansu tare tun daga ranar da ta fara ganinta kawo yanzun da suke zaune suna sauraronta ba tare da ta b'oye musu koda wasali ko harafi ba.
Jikinsu duk yayi sanyi kan irin wahalar da ta sha da irin rayuwar da tayi duk da kuwa sun ganta kan sana'ar tata,kallon tausayi had'e da al'ajabin yadda ta juri wahalar sana'ar suke binta da shi kafin daga bisani suka sako maganar tafiya da KHUBRA'N.


Haka BABA ZUWAIRA ta shiga d'aki ta had'a kayan duk data san na KHUBRA'N ne ta fito,tana d'an matse idonta da k'walla ta tarun mata.
Mik'ewa sukayi cikin shirin barin gidan,nanfa KHUBRA da BABA ZUWAIRA da suka ga dai tabbas tafiyar nan zasu yi,suka k'ank'ame juna suna kukan rabuwa da juna a lokacin da d'ayansu bai tab'a tsammanin faruwar hakanba.


KHALEEL ne ya ja BB gefe yana fad'in
"MAN baka jiba"


'Dan matsawa BB yayi jikin KHALEEL tare da kallonsa yana d'aga masa kai

"Gaskiya a shawarana ina ganin rabasu yanzun akwai damuwa duba da yadda suka shak'u da juna,ina ganin me zai hana mu tafi da su duka kaga ta wani b'angarenma BABA'N zata mana amfanifa ko kuwa me kake gani?"


Shiru BB yayi yana hasashen maganar KHALEEL en sannan kuma ya d'an daki kafad'ansa
"Yeahhh!ka kawo shawara mai kyau kawai muyi hakan"


Komawa gurin da su KHUBRA suke tsaye sukayi har lokacin suna manne da juna,KHALEEL yana y'ar dariya yace
"Ina ganin BABA da kun daina kukan nan haka nan,saboda mun yanke shawaran tafiya dakune duka"


Da sauri KHUBRA ta d'ago kanta ta kalleshi,shi kuma ya kad'a mata kai dan ya fuskanci so take ta tabbatar da abunda ya fad'a.
Aiko da sauri ta shiga gogewa BABA ZUWAIRA hawayenta itama ta goge nata tana dariya,cikin sauri ta shiga d'akin ta d'ebowa BABA ZUWAIRA kaya sannan suka d'unguma suka fice daga gidan,sai da ta shiga mak'otanta tayi musu sallama,tukun ta dawo inda ta barsu a k'ofar gidan jikin mota,daga nan suka shige tare da d'aukan hanya sai cikin gari wato cikin k'waryar KANON DABO.......................










*~#TEAM KHUBRA.~*










*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*4/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣0⃣*












*"B* EAUTY me ya sameki kike kuka?wani abu yana damunki ne?"
BIGGY ne yake wannan maganar cikin rud'ewa yana tambayar ASHNA dake sunkuye ta had'a kai da guiwa sai risgar kuka take kamar wacce aka aiko mata da sak'on MAMA ta rasu.
Kukan da take yine ta kuma k'i bashi amsa yasa ya ajiye package en hannunsa,kusa da k'afafunta ya nemi guri ya zauna had'e da lank'washe k'afafunsa,fuskarsa cikin wani irin yanayi yake kallonta
"Please BEAUTY kiyi shiru hakanan ki daina wannan kukan kinji,yanzun fad'amin duk abunda kike so ayi kinji?"
Da sauri ta d'ago fuskarta da tayi kacha-kacha da hawaye tana kallonsa,kai ya d'aga mata alamar da gaske yake.
"Da gaske nake miki BEAUTY amma sai kin daina kukan nanfa kinji?"
Da sauri ta shiga goge fuskarta ta sake kallonsa had'e da d'anyin murmushi,aifa BIGGY wannan murmushin da ASHNA tayi masa ba k'aramin tafiya yayi da shiba take kuwa ya kafeta da idanu har bai sanma tana magana ba sai da tayi clapping a dai² fuskansa,sannan yayi saurin dawowa hayyacinsa yana fad'in
"Ammmm!BEAUTY me kika cene?"


Da d'an mamaki ta kalleshi wato dukma maganar da tayi bai san tana yiba kenan ko mene yake nufi?
Daurewa tayi ta fara magana cike da shagwab'a kamar tana gaban MAMA.
"Ni gurin MAMANA nake son zuwa.....Dan Allah ka maidani gida...Ina son na san halinda MAMATA take ciki...Please kaji"
Yanayin yanda take magana duk ta wani narke ita a dole y'ar lelen MAMA.


Ga BIGGY kuwa wani yanayi yake tsintan kansa aciki duk lokacin da tayi magana to shi kuma nan zaiyi da nasa kan dan duk inda ta lank'wasa kanta yana biye da nasa kan,yana faman zuba murmushi.

Tsuke fuska ASHNA tayi tana kallonsa da mugun haushi d'auke cikin idanunta kan yadda taga duk ya wani kafeta da ido.
"MALAM lafiya kake min irin wannan kallon?
Nifa kaga banson irin wannan kallon k'urillan haka kawai duk ka gano munin mutum,to gaskiya ya isheka haka"
Cike da tsiwa take maganar tana zabga masa wata uwar harara,dariya yayi mata wanda yasa farare tas en hak'oransa suka bayyana,dariyan da yayi shi ya bawa beauty point dake gefen kumatunsa lotsawa,take kuwa ASHNA ta saki baki tana kallon ikon Allah
"Ammafa GUY en ba laifi,duk da kasancewarsa bak'i,da wad'annan jajayen idanun nasa amma ai yana da hanci ga beauty point,wow inama ba cikin mugayen nan yake ba,kuma kyau ace yayi boko,omg ya zai kasance?"
Kanta ta d'an d'age tana son tuna ya wannan GUY en zai kasance,sai dai tayi murmushi had'e da fad'in
"Kaiiiii ammafa wollahi da ba k'aramin HANDSOME za ayiba"
Gintse fuska ta dad'a yi ganin yadda yake sake kallonta
"MALAM nafa ce maka ka denamin irin wannan kallon ko? har da wani yimin murmushi,ka rik'e abunka bance maka ina soba ai
Yanzu kawai ka fad'amin zaka mai dani gidanmu?"


"A'a BEAUTY bazan iya mai daki ba yanzu"


"Da Allah ni ka dena wani cemin BEAUTY tunda ba maidani za kayiba,kawai ka tashi ka bani guri"


Ko rufe bakinta bata yiba taga ya mik'e yana shirin barin d'akin,baki ta dad'a b'arewa tasa masa kuka.
Daf da bakin k'ofan ya tsaya had'e da rufe idanunsa lokacin da take kukan,da sauri kuma ya fice daga d'akin tare da rufe d'akin...


Fitowansa daga d'akin ya tsaya nan cikin corridor en,number HAJIYA LAURA ya shiga kira,bayan ta d'auka ya shiga labarta mata abunda suka yi ASHNA yanzun.

Ko gama rufe bakinsa baiba HAJIYA LAURA cikin tsawa ta dakatar da shi
"Nooo!BIGGY kadama ka kuskura ka tafka wannan d'anyen aikin,taya zaka biyewa wannan y'ar mitsitsiyar yarinyar
Baka gudun abunda zai je ya dawo ne hala idan ka maidata gida?
Ko kuwa baka tunanin gane fuskarka da tayi zai jawo mu fad'a hannun hukuma to gaskiya tun wurima ka kama kanka da wannan maganar
Sam hakan ba mai yiwuwa bane ina fatan ka gane"


Jiki a sanyaye yayi mata sallama ya kashe,nanfa BIGGY ya jingina jikin ginin gurin ya rufe idanunsa yana tuna irin yadda yarinyar ke nuna damuwarta da son ta koma gida ko don sanin halin da mahaifiyarta ke ciki.
Tambayoyi ya shiga yima kansa
"Shin mema yasa muke irin wannan aikin ga wasu mutanen da babu tausayi a zuk'atansu?ko don na rasa iyayena ne tun ina yaro shi yasa na biyewa irin wad'an nan mutanen suna sani aiki irin wannan,shin bana gudun ranar da Allah zai tashi kamani? Dame zanje masa wanda zan kare kaina a gurinsa?
Gaskiya ya kamata na nutsu.....Ina buk'atar shawara daga gurin wani......Ina buk'atar canja halayena.....To amma wa zan tunkara da wannan maganar?


Shi kad'ai yana ta magana da zuciyarsa,rashin samun maka yasa shi saita kansa sannan ya bar gurin jikinsa duk yayi sanyi saboda tunanin da yayi.


《《》》


Shigowar dattijon gidan kenan da sallama sai dai babu kowa tsakar gidan,hakan ne yasa shi tunkaran d'akinsa ya sanya d'an k'aramin key en ya murza tare da bud'e k'ofar yana mai kunna kai cikin d'aki.
Kan y'ar lank'wamammiyar katifan ya kwanta duk abun duniya ya dame shi,zuciyarsa duk babu dad'i haka yake jinta,haka dai ya juya ya kwanta cike da damuwa da ya rasa ta mene ne.


Lek'e ta shiga yi ta saman dangar karan dake kewaye da gidan duk burinta bai wuce ta hango cikin gidanba,k'ofar d'akin MALAM en ta hango a bud'e da alama ya dawo kenan.
A hankali cikin sand'a ta shigo gidan,wuf tayi ta shige d'akinta da ganin yadda take tafiya kasan babu gaskiya wai akace "awo a d'aka".
Wuf tayi ta afka cikin d'aki tana dafe k'irjinta had'e da fad'in
"Waii Allah ya taimakeni MALAM bai kamani ina wannan sand'arba da yau kam ina da tabbacin komai zai iya faruwa"


Wata irin dariya ta tsinkayo a bayanta data sata saurin juyowa tana bin inda taji dariyan da kallo
Zaune saman gadonta na k'arfe ta hangoshi ya hard'e k'afafu kamar a fada
Tsoro ne ya cika mata zuciya,duk da tasan waye hakan bai rage mata tsoron da take cikiba.
Da k'yar take had'iyan yahu dan ta san ko me ya kawoshi a wannan lokacin,haka LADIYO ta shiga jan jiki har ta k'arasa gurinsa dan ta san bata isa ta bijireba,ko dan tsoron da take ciki,hakan ba maganin komai zai mataba.


A dai² lokacin da LADIYO suke tsaka da shek'e ayarsu da HATSABIBIN BOKA'N nasu ne shi kuma ABBA'N KHUBRA yake bacci mai cike da mafarkai da ya saba yinsu ko wane dare.


Cikin duhun dare cikin wani irin k'ungurmin daji da babu komai cikinsa face koke-koken tsun-tsaye da wasu halittun marasa dad'in ji.
Kamar daga sama ya tsinkayo muryar yarinyar tana kuka
"ABBA ka taimakeni....Wayyoo Allah ABBA zasu kashe ni....ABBA kada ka bari su cutar dani dan Allah"
Abunda ya iya jiyowa kenan shima cikin wani irin sauti da yake nuna ta gama galabaita ne take masa magana.
Yunk'uri yayi domin ya taimaka mata sai dai me ya kasa ko da taku d'aya saboda yadda yake d'aure jikin wani k'aton dutse,hannu da k'afafunsa duk suna sanye cikin ank'wa,wacce baya tunanin zai iya tsira daga gareta.


Hankalinsa a tashe saboda ganin yarinyar da yayi wasu irin mutane da baya iya hango fuskokinsu bare yasan su waye,sun rik'eta suna tunkarar wani k'aton rami da wuta ke ci a ciki da nufin jefata,ita kuma sai turjewa take tana waigowa tana kiransa kan neman taimako daga gare shi.


'Dagata sukayi da niyyan jefata,kafin su ida nufinsu suka fara jiyo gudu had'e da haniniyar dawaki,samari ne su biyu sun ratso ta cikin jejin haye bisa dawakai fuskokinsu rufe da k'yalle,iya k'arfinsu suka bud'e baki suna furta
"Laa-ilaha'illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz-zalimiiyn"
Fad'ar wannan kalmar babu b'ata lokaci yarinyar da ake k'ok'arin jefawa wuta,ta shiga maimaitawa cikin k'arfin hali da bud'e murya iyakar iyawarta.

Wutar dake ci cikin ramin tayi wani irin tasowa kamar an hurota,harshen wutan da yayiwo wajensu take ya laso su wutan ta kama jikinsu suka kama da wuta,sakinta suka yi a k'asa,sai dai abun mamaki wutan ko kad'an ita bai sametaba.
Cikin sauri d'aya daga cikin mahayan ya sauko tare da d'aukanta ya aza saman dokinsa ya haye shima.
Da gudu suka bar jejin inda take a nan shi kuma ya dena ganinsu sun b'ace b'at kamar iska.


B'acewan nasu ya dad'a jefa zuciyarsa cikin tsananin tsoro da fargaba,kamar daga sama yaji yo muryan yarinyar lokacin da take maimaita abunda taji wad'annan mahayan sun ambata.
Yunk'urin fad'a ya shiga yi shima,inda yana maimaitawa yaji ank'wan dake d'aure jikinsa ta zube k'asa,juyawa yayi ya kalli jejin gaba da baya sannan ya shiga shek'a gudu iya k'arfinsa ta hanyar da yaga sunbi,yana cikin gudun ya fara hangosu can nesa da shi,sosai yake gudun kamar wanda ya hau takalmin taya sai da ya kusa cimma mahayan duk da kasancewar suna kan abin hawa shi kuma yana k'asa,har ya fara murna kawai sai ji yayi ya daki wani irin dutse a gabansa da ya sashi fad'uwa a gurin,kansa ne ya daku da dutsen take idanunsa suka soma k'ank'ancewa saboda azaba...


A firgice ya farka jikinsa duk ya had'a zufa duk kuwa da yanda garin yake cike da iska saboda hadirin daya had'u a d'azun sai dai iska kawai ya bayar mai sanyin dad'i,amma shi gare shi duk ya jik'e da gumi.
Tunanin mafarkin da yayi ya tsaya yi,yana mamaki had'e da al'ajabin mene ne had'inshi da mafarkin?
K'wak'walwarsa ta dawo masa da maganganun yarinyar da yayi mafarki da ita,take ya tsinci kansa da fad'in
"Laa-ilaha'illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz-zalimiiyn"
Maimaitawa yayi tayi cikin zuciyarsa,wanda k'arshe har kalmomin suka bayyana a fili.


Jiki a sanyaye ya mik'e daga gurin yayi hanyan fita daga d'akin zuciyarsa wasai babu zafi da kuma rad'ad'in da yake ji a baya.
Har ya d'auki buta zai shiga bayan gida ya dawo tare da ajiyewa a gefen randa,k'ofar d'akin LADIYO ya tunkara,kasancewar yasan su kad'ai ne a gidan ba tare da ya k'wank'wasaba ya kunna kai ciki da y'ar torchlight ensa da yake haska hanya da ita.
Mugun gamon da yayi yasa shi dafa bango saboda wani jiri da yake neman d'ibansa,cikin sauri kuma ya juya ya fice daga d'akin zuciyarsa na k'una.......


Tashin hankali kenan wanda ba a sa masa rana...


《《》》


Misalin k'arfe 1:40pm motan ta kunno kai cikin haraban gidan,har lokacin KHUBRA na lafe jikin BABA ZUWAIRA,baiwar Allah tana zaune sai kalle-kallen cikin gari take,har suka k'araso cikin gidin wanda had'uwa da tsarin gidan yasa take bin ko'ina da mamakin yadda akayi KHUBRA ta iya rayuwa a wannan k'ungurmin k'auyen nasu kuma har ta iya jurar wannan wahalar.
KHALEEL dake driven yayi parking sannan ya fita,inda BB shima ya mara masa baya yana fitowa ya ja k'ofan baya inda su KHUBRA suke,cikin taushin murya ya furta
"Bismillah"
Had'e kuma da nuna musu hanya suka fito KHUBRA rik'e da hannun BABA ZUWAIRA suka bi bayansa,KHALEEL a gaba BB biye da shi sai kuma su KHUBRA dake bi masa.


Ummi tsaye cikin kitchen tana gyara zaman warmer's en akan tire da take son fita dashi,gefe kuma basket ne shima da wasu had'ad'd'un Flak's,tana shirin fitowa sallaman su ta kawo kunnenta.
Da sauri ta fita tana fad'in
"Lale marhaban da Y'AY'ANA,gaskiyafa kunsha hanya"


Turus ta tsaya tana kallonsu ganin ba su kad'ai suke tafeba..
"A'aa da bak'i kuke tafe ashe,amma ya akayi baka sanar da niba da kayimin waya?"
Ta kalli KHALEEL cike da tuhuma,kunnensa ya d'an rik'e alaman ban hak'uri,murmushi tayi tare da fad'in
"Ai kaikam ka iya bada hak'uri idan kayiwa mutum laifi"


Kallon BB tayi da ya riga ya zauna tana k'arasawa dinning lokacin da ta ajiye tiren hannunta, sannan ta dawo cikin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads