Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 159513 words

Chapter 7 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1210

Ads at the middle of Article

daud'a kamar ba jikin bil-adam ba...


Zama yayi yana fuskantar ta...


Ta bud'e baki za tayi magana ya d'aga mata hannu,alamar baya buk'atar tace wani abu.....


''Aikinki ba wani mai wahala bane,sai dai ta wace hanya kike so ta dinga kawo miki kud'in?''....


''Koma mene ne MALAM tayi bai dame ni ba in dai zata dinga kawomin kud'i''....


''An gama, sharad'in aikinki idan kika kuskure a cikin aikin da zan baki komai zai juya kanki''..


Tun bai k'arasaba tace
''Na amince''
Ta fad'a tana jiran ganin,me zai biyo baya...




Nan take ta ciro wasu layu da kuma k'ullin garin magani,ya mik'a mata...
''Wannan ya nuna layun,zaki binnesu a tsakiyar hanyan da jama'a suke bi...
Shi kuma wannan k'ullin ya nuna mata garin maganin,za ki barbad'a a bakin k'ofar d'akin da kija san za ta tsallaka....
Ki tabbatar ta tsallaka shi,saboda shi ne cikon aikin ki,zai sa mata farin jini wajen mutane,sai dai babu wanda zai zo da niyyar aurenta,zaki samu mahaukatan kud'ad'e ta dalilinta''......
Jin an ambaci mahaukatan kud'i ta shiga b'are baki,dan murna....


Kud'i ta fitar a jakar tata ta mik'a masa,ta masa godiya ta kama hanya,tare da alk'awarin dawowa...


********


Firgitan da tayi yasa ta farka,ga sautin k'ara da ya ratsa kunnuwanta wanda bata san daga ina yake ba,sai bayan ta farka ta fuskanci inda k'aran ya fito,ashe da tayi kenan ba iya cikin bacci kad'ai tayi ba har a zahiri tayi...


Addu'ah tayi ta mik'e tad'auro alwala,ta jima tana neman sauk'in al'amura daga ubangiji,tare da kariyarsa a gareta...
Sannan ta mik'e,ta d'auki garin kwakinta tayi waje.....


Ko rabi bata iya ciba taji ta k'oshi,hakan yasa ta maida ragowar ta b'oye.....
Tayiwa Allah godiya,ta sake kwanciya,tana tunani kan wannan rikitaccen mafarkinta.....


Da yamma tana kwance a tsakar gidan,maranta taji tana tsunkulinta kad'an² take ta gane abunda yake shirin faruwa da ita,tashi tayi ta kintsa jikinta,ta dawo ta ci gaba da sauron kukan tsuntsaye dake kan bishiyar mak'otansu,haka har akayi sallan Maghre...
Sai lokacin wani tsoro ya ziyarceta,take kuwa ta sake k'ulewa a d'akin MA'U....


**********


Cikin dare sosai ta iso,k'ofar ta shiga bugawa da iya k'arfinta...


Jin bugun yayi yawa yasa KHUBRA ta fito ta bud'e coz ta gane mai bugun,sai a lokacin ta samu nutsuwa....


Duk wani shiri na MA'U ta gama k'udurce a daren ranar zata aiwatar da komai,hakan ne ma yasa ko gidan bata nufoba sai da ta aiwatar da nufinta...


Lokacin gari ya dad'a yin shiru ta fito ta k'arasa abunda za tayi,ta koma zuciyarta wasai,sai kuma jiran ganin abunda zai biyo baya..........


#UHMMM!KU BIYONI DAN JIN YANDA ZA A K'ARKE..
LUV U.....












*_~#TEAM KHUBRA.~_*






*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠





*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*21/ąpril,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~________________________~*

*ADDU'AR SHIGA MASALLACI.*


_A'UZHUBILLAHIL AZIYM,WABI-WAJHIHIL KHARIM,WASUL'DANIHIL-K'ADIYM,MINASH-SHAI'DANIR RAJIYM,BISMILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALAA RASULILLAH ALLAHUMMAFTALIY ABWABA RAHMATIK..._


*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*


*~________________________~*


*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._


*~________________________~*


_Ina mai bawa d'aukacin masoya wannan novel na *Y'AR GARUWA* hak'urin jina da kukayi shiru kwanaki da yawa,kumin afuwa na jina shiru tsawon wad'annan kwanakin,coz abubuwa sun min yawa shi yasa ban samu nayi posting ba,hope uzurina zai zama karb'ab'b'e..._


*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*1⃣5⃣*







*C*ikin dare ta farka,sanadin mummunan mafarkin da tayi...
Addu'ah ta jima tanayi,duk da babu halin tayi sallah,haka taita kai kukanta ga Allah akan neman sauk'i da sauyin rayuwa, wanda k'arshe sai da takai kusan asuba bata koma baccinba...
Da k'yar ta samu wani nannauyan bacci yayi gaba da ita....



*********


Da misalin k'arfe 10:15am MA'U ta fito tana ta faman murna ta san ko ba komai yanzun kam ai tayi nasara..
'Dakin da KHUBRA ke kwana ta nufa daga inda take a bak'in k'ofan ta lek'a sai dai duk iya hangenta bata gantaba,murna ta koma tana yi har da rawa na samun nasara...
Har za ta koma d'akinta ta dawo tunowa da maganar da MALAMIN ya mata,akan idan har wacce akayi dominta ta tsallaka babu komai dan ta bi ta wajen...


'Dakin ta nufa tana son tabbatarwa,ai kuwa ta kunna kai cikin d'akin,tana ta murna abunta,sai dai abunda ta gani shi ya tsorata ta ta ko zaro idanu waje,ko me ta tuna kuma ta saki ranta...
Cikin salo na bariki ta shiga tashin KHUBRA kamar da can haka take yi idan zata tashe ta....


Ko ita da kanta KHUBRAN sai da abun yaso ya bata tsoro,mamaki shimfid'e a kan fuskarta take kallon MA'U...

''Yar lele tashi maza kiyi wanka,ga abinci can na tanadar miki,maza taso kiyi wanka,zanje kasuwa zan siyo miki kaya,maza yi sauri kinji ko''


Ita maganganun MA'UN ma sun sa ta shiga wani irin shock,aiko haka taita binta da kallo kamar wata doluwa...


Janta MA'U ta shiga yi,kamar k'aramar yarinya,har bakin band'aki ta kaita,tana murmushi ta turara...


Ga KHUBRA kuwa bata gama mamakintaba sai da tasa hannu cikin ruwan wanka,nan taji shi da d'umi,wannan wane irin bak'on al'amari ne wannan kuma?
Haka taita tunane²,tayi wankan ta fito,jikinta duk yayi sanyi..
Dai² lokacin MA'U ta fito daga d'aki tana fad'in

''Kiyi maza ki shirya kinji ko,zani kasuwa na dawo,kada kiyi girkifa,idan na dawo zanyi komai kinji y'ar lele''
Fuskanta a sake take ta faman zuba kamar lalatacciyar mota,har ta fice daga gidan tana magana wanda ita kam KHUBRA batama san me take fad'aba coz tayi nisa cikin duniyar tunani....


'Dakin MA'UN ta shiga ta tarar da abinci a rufe a cikin plate da wani jug na robber mai d'an kyau...
Bata tsaya b'ata lokaciba ta d'auko ta ajiye a k'asa ta shiga bud'ewa...
K'amshi ne ya daki hancinta,tabi abun da ido,indomie ne da wainan k'wai a sama,sai turiri take,take ta shiga had'iyan miyau,haka ta bud'e jug en nan kuwa ta tarar da shi cike da tea mai kauri....
Ci tayi sai da ta tabbatar ta k'oshi tayiwa Allah godiya bisa ni'imar da yayi mata,na azurta ta da irin wannan abincin da tun da tazo garin bata tab'a cin kamarsa a dad'i ba...


Sai da ta gama d'urawa cikinta d'a'aam sannan ta soma tunanin maganar MA'U...
Tambayoyi dayawa taitayiwa kanta,sai dai babu amsa,ta barwa ranta koma mene ne ta tabbata shirin cutarta take,take kuwa ta hau kuka tana addu'ar neman tsari daga dukkan abun sharri....


Haka ta kusan wuni tana tunane²,shigowar MA'U da ta dawo daga kasuwa shi ya katse mata tunani,ta bita da kallon mamaki ganin yadda ta rik'o kaya a hannunta nik'i²....
Tashi tayi za ta karb'a ita kuwa MA'U ta hanata,haka ta k'yaleta,guri ta samu ta zauna nan ta shiga fito da kaya tana d'agawa tana nunawa KHUBRA sai zuba take...
Kayan marabarsu da babu d'aya,ita kuwa sai binsu take da ido daga KAYAN har MA'UN da ta siyo...



*********


Tunda ya fita daga gidan ko waiwayarsa baiba haka ranar yaita uzurinsa a waje...


Ita ko LADIYO tana ganin fitarsa ta zari mayafi sai gidan TABAWA nanfa suka shiga firar abunda ya faru tsakaninta da MALAM BUBA,bata b'oye mata komai ba ko da kuwa wasali haka ta sanar da ita hatta kwanciyar da sukayi sai da ta labarta mata...
_(Gareku matan aure da y'an mata masu niyyar yin aure,ba ko wane sirri ake fad'awa k'awa ba,bare kuma har ki saki baki ki fad'a mata sirrin yadda kuka kwanta ke da mijinki,ko da kuwa ciki d'aya kuka fito,ahir d'inki da fad'in wannan sirri dan gujewa fad'awa a halaka,,,,,Allah yasa mu dace)... ameen....._


Haka ta kusan wuni a gidan LADIYO kafin daga baya ta tashi ta bar gidan...
Ita kuwa TABAWA dad'i ne ya cika ta jin yadda LADIYO ta kwance mata sirrinta,tana rakata da harara tana tab'e baki,dan burinta bai wuce ganin LADIYON a k'asa ba.....

**********
Ita dai kamar mai koyan kallon wani abu,irin wad'anda akayiwa aikin idanu haka ta zama ranar,duk inda MA'U tayi idanunta na kanta kamar zasu fad'o saboda kallo....




Da yamma kuwa tun bayan sallan la'asar MA'U ta sake sa KHUBRA yin wanka,cikin kayan da ta siyo haka ta sa wani riga da siket,da wani d'an siririn gyale,duk kunya ta hana KHUBRA sakewa haka suka fita,ita dai kallon kanta take kamar wata y'ar iska...
Itama cikin shirinta suka fito,da tambaya suka nemi MALAMIN da yake gyaran targad'e...
Ai kuwa sunyi masa bayani,MALAM na kama k'afar MA'U ya soma matsawa,ta shiga kururuwa,bige² take da hannayenta da k'afa...
Amma MALAM bai saki ba,sai da yatabbatar ya gyara sannan ya saketa...


Tun da aka soma gyaran MA'U na fara ihun nan,KHUBRA take ta b'oyayyiyar dariya,har kifawa tayi saboda dariya...


Da k'yar take tafiya a da,sai gashi yanzun ta dawo normal,sai harare² da take uwa wani ya mata laifin....


Sai bayan da suka koma gida,cikin dabara MA'U take tambayan KHUBRA
''Yau kuwa kin fito daga d'aki?''


Kasa gane inda tambayan ya dosa tayi,ta tsaya tana kallonta kawai
''Baki gane ba ko?''


Kai ta d'aga tana jiran k'arin bayani


''Da safe fa nake nufi,kin fito ko kuwa sai da na shiga?''


'Dan murmushi tayi ta kad'a mata kai,kafin tace
''A'a ban tashi da wuriba ai yau,sai lokacin da kika shiga sannan na tashi''...


Ko kafin ta k'arasa MA'U ta mako mata wata uwar ashar da tasa tayi shiru tana k'ara kallonta cike da rashin yarda...


Zagi ba irin wanda MA'U bata yiba a ranar,kamar za tayi hauka haka tayi²,da taga abun bai mataba kuwa k'arshe rufe KHUBRA tayi da duka,ita kuwa tana zaune inda take ko motsi bata yiba,har tayi ta gaji,dan kanta ta rabu da ita,ta koma gefe tana huci...


Rasa dalilin yin hakan KHUBRA tayi mamakin da takeyi kuwa sai yanzun ta gano dalilin MA'UN na kulawar da ta ringa bata da safe...


Abun duniya duk yabi ya dami MA'U,babu shiri ta tashi ta d'auki hanyar komawa k'auyen SUMAILA....


Da isarta kuwa babu b'ata lokaci MALAMIN ya k'araso,MA'U kamar za tayi kuka haka ta labarta masa abunda ya faru...
Shiru yayi har ta gama,sannan ya sake mata bayanin da yayi mata tun farko,aikuwa saiga MA'U tana kuka,hak'uri take bashi kan idan da hali a karya abun...
Shi kuwa yace mata
''Ai aikin gama ya riga da ya gama,sai dai kuma kiyi hak'uri''....


Wata k'arin muguntarma,bayan da MALAMIN ya bawa MA'U wancan aikin cewa tayi
''MALAM ina son a k'ara mata k'arfin sha'awa ta yadda duk wanda yazo mata da buk'atarsa baza ta iya jurewa ba''


Wannan maganar da MA'U ta tuna shi yasa ta b'arkewa da kuka,kamar ranta zai fita..
Shi kuwa MALAMIN take ya bata guri yana fad'in
''Har yanzun kina da damar yi mata wani aikin''


Nan ta shiga tunani,to idan za ayi wani aikin ai yana buk'atar kud'i,ita kuwa yanzu idan ba sata za tayiba ina zata samu kud'in aikin....
A ranta kam ta k'udirce ko za tayi yawo tsirara sai taga bayan KHUBRA...
Nan ta lula duniyar neman mafita..........






*A YAU NE ABBANA YA CIKA KWANAKI 40 DA RASUWA,INA BUK'ATAR DAN ALLAH DUK WANDA YA KARANTA POSTING ENA NA YAU YA SANYA SHI CIKIN ADDU'AH DAN ALLAH..ALLAH YA MASA RAHAMA TARE DA 'DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI DA SUKA RIGAMU CIKAWA,ALLAH YA KYAUTATA K'ARSHENMU...AMEEN...*






*_~#TEAM KHUBRA~_*






*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠?💠





*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*22/ąpril,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~________________________~*


*ADDU'O'IN KIRAN SALLAH.*


_IDAN MUSULMI YAJI ANA KIRAN SALLAH,ZAI DINGA MAIMAITA ABUNDA YAJI ANA FA'DA,SAI DAI BANDA *HAYYA ALAS-SALAH* DA *HAYYA ALAL FALAAH*,ZAI CE *LAA-HAULA WALA K'UWWATA ILLA BILLAH*._


*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*




*~________________________~*


*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._


*~________________________~*
_Ina mai godiya gareku Masoya da irin addu'o'inku ga mahaifinmu,Allah ya bar k'auna da zumunci... *SHUKHRAN OLL* 👏._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*1⃣6⃣*









*J*iki babu k'wari ta d'ebi k'afafunta ta kama hanyar komawa gida,a ranta kuwa Allah ya isa take ta jawa KHUBRA,da zaran ta tuna sai ta sunkuya tana share k'wallan da ya tarun mata a ido..

Haka ta dawo gida,ita kuwa KHUBRA duk lokacin da zata tuna abun sai ya bata dariya,yanda MA'U taita fisge² da ana mata gyaran k'afa d'azun,ita ko dukan da ta mata bai sata jin haushin MA'UN ba,saima tayi dariya idan taga gilmawar MA'UN...
Da tasamu sarari kuwa MA'UN ta fita ta zauna taita tuntsira dariya kamar wata sabon kamu...


Shigowar MA'U gidan tana jan k'afafu,duk damuwa ya bayyana a fuskanta..
Kallon KHUBRA tayi da ta sunkuyar da kai k'asa kamar gaske,ae ko ta maka mata wata uwar harara,tana shigewa d'aki...


Tun daga wannan rana MA'U bata sake fita ba,kullum tana d'aki kamar daddawa,sai da ta kai kimanin sati a gida ko zaure bata lek'a ba,abun duniya duk ya dameta ta rasa mafita...


Yau tun data tashi take jin wata irin matsananciyar sha'awa na damunta,ta rasa yadda za tayi,ganin zaman bazai kai mata ba ta mik'e ta shirya cikin wasu riga da zani na wata jaan atamfa,babu laifi atamfan ya d'an mata kyau kad'an...
Tun da ta fito KHUBRA ke k'unshe dariya dan har mantawa take da ita a cikin gidan coz ta san ba zaman gidan take ba...


Ba tare da tayi mata sallama ba ta sa kai ta fice,mayafin jikinta tajaa ta rufe fuskanta da shi tana tafe kamar munafuka...
Mai NAPEP ta samu,tsaf ta masa kwatance,dai² k'ofar gidan ya sauketa,ta shiga da sallamanta...


Matar na zaune ta amsata,tana mata maraba,haka ta saki baki da fad'in
''Ina fatan dai kin ganeni koh?''


''Haba ta ya zan mantaki kuwa''


Nan suka gaisa a mutunce,kafin MA'U tace
''Kinga tunda nace zan dawo Allah bai nufaba,sai yanzun,da yake na d'anyi jinya ne shi yasa kika jini shiru''


''Allah sarki,Allah ya k'ara sauk'i''
Matar ta fad'a tana sauraron MA'U...


''To dama hajiya zuwa nayi na sanar miki,gobe idan Allah ya kaimu zan kawo yarinyar,sai ta fara aikin''


''Allah ya nuna mana da rai da lapia''


MA'U ta amsa da ameen,had'e da yi mata sallama,ta tafi akan sai goben...




《《《》》》


Tun daga wannan ranar MALAM BUBA ya zamana zai kwanta da LADIYO a kullum babu fashi,ita kuma zata kwashe ta sanarwa da TABAWA..


Wasu munanan halaye da ta dad'a bayyanawa MALAM en shi yasa idan ya fice baya ko waiwayen gidan sai dare...


Ko da suka koma wajen bokan,babu tsoron komai a tare da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads