Header Ads
Showing 102001 words to 105000 words out of 159513 words

Chapter 35 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1232

Ads at the middle of Article

bautawa...Allah na gode maka da ka nufeni da tuba tun lokaci bai k'ureminba..."










*~#TEAM KHUBRA.*~








*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*22/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣9⃣*








*"A* lak'ar data had'amu da SAFWAN itace auratayya inda na auri k'anwarsa mai suna FALMATA"
A nan ABBA'N KHUBRA ya dakata saboda wani tunanin daya bijiro masa wanda sam baiji dad'in hakanba,sai yanzu yake nadama da dana sanin abunda ya aikata,ciki kuwa harda saurin yanke hukunci,wanda Annabi (S.A.W) ya hanemu da mu yanke hukunci cikin fushi.
LADIYO ya kalla da rinannun idanunsa da babu komai cikinsu face zallar b'acin rai wanda kana kallonsa zaka tabbatar had'e kuma da gano abunda ke k'unshe k'asan zuciyarsa.
Muryarsa a shak'e ya kalli mutanen gurin ya kuma kallon LADIYO data sha jinin jikinta,sai da yayi gyaran murya sannan ya fara da fad'in
"Da farko dai zan fara da yiwa wannan matsiyaciyar matar Allah ya isa,sannan kuma in shaida muku ina son ku zama shaida ni ABUBAKAR SA'ADU (MALAM BUBA) na saki LADIYO saki uku babu ni babu ita,daga yau ina son ta tattara kayanta tabarmun gidana na sallameta......"


Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un...
Abunda mutanen gurin keta maimaitawa kenan kamar sa ari baki,ABBA'N KHALEEL ne ya fara magana
"Haba MALAM ya zaka yanke irin wannan hukunci haka,bayan ka sani cewa ubangiji da kansa yana k'yamar saki irin wannan,sam bai dace kayi hukunci irin wannan ba koda kuwa wane irin laifi ta aikata maka,idan ka kyaleta da mahaliccinmu zai hukuntata komai girman laifinta kuwa..."
Bai kai k'arsheba MALAMA BUBA ya dakatar da shi ta hanyar fad'in
"Haba ALHAJI yanzu ita wannan matar da kake magana akanta kasan girman laifukanta kuwa?ko kuwa ni kasan meta aikatamin?kasan tsahon loacin data d'auka tana cutata?to ku saurareni yanzun zaku ji irin cutarwa da azabtarwar da wannan munafukar tayimin ni da iyalina...."

*19 YEAR'S BACK......*

"Shekaru sha tara 19 baya,na kasance malamin makarantar islamiyyane kamar yadda kuka ji suna na ABUBAKAR SA'ADU wanda akafi sani da MALAM BUBA,kaf garin nan idan ka tambaya tun daga kan manya da yara babu wanda bai sanniba saboda baiwa da Allah yayimin ta ilimin islama,ta wannan baiwar ne har na samu nake koyar da mutane da dama cikin garin nan namu,a lolacin ina da mata d'aya wacce itace LADIYO,muna zaune da ita lafiya tun bayan aurenmu wanda yake tun na saurayi da budurwa,tsahon rayuwar da mukayi da ita a wannan lokacin Allah baisa tana da rabon haihuwa ba,har muka kai kimanin shekaru goma Allah baisa ko da b'atan wata ta tab'a yiba,a kwana a tashi maganganu sunata yawo a gari kan matata bata tab'a haihuwaba,kai in tak'aice mukuma wasu har samuna suke sunamin magana kan idan na amince zasu bani auren k'annensu wasu suce y'ay'a ga mutanen da suka manyata kenan a wannan gari,gidanmu kuwa wajen mahaifana suma ba a kyale suba da wannan maganar,sai dai na basu hak'uri tare da godiya saboda karramawa da girmamani da sukayi wanda har ya jawo sunamin kyauta mai girma amma ni kuma ban karb'a ba,kwanci tashi asarar mai rai a shekara ta sha d'aya da aurenmu sai nayi wata tafiya zuwa garin DUTSE inda za a gudanar da wata *SEMINER* ta addini,cikin hukuncin Allah bayan zuwana garin duk yinin duniya idan muka gama abunda za muyi a gurin seminer sai mu fita don zaga gari.A wata ranar *LITININ* wacce bana jin zan iya mantawa da ita a iya tsahon rayuwata,kamar kullum mun fito muna zaga gari muka had'u da wata y'ar matashiyar budurwa kyakykyawa da ita,wacce ko ni idan aka bani abun zane ba lallaine na iya zana wacce ta kaitaba bare kuma wacce ta fita saboda kyau da Allah yayi mata sam bata da makusa ta kowane b'angare,nan dai maganganu iri-iri sukaita fitowa daga bakunan abokan tafiyata kan yaba kyau irin nata,jin abun da sukeyi yasa ni dai nayi shiru ban furta komaiba muka ci gaba da tafiya,wani ikon Allah yarinyar tana tafiya a gaba garemu mu kuma muna bayanta kusan duk hanyar data bi to ko muma ita muke bi daga dukkan alamu kuma aikenta akayi,mun biyo wata hanya ne kuma muka ga yarinyar na k'ok'arin shiga gida inda a nan wani mutum daya fara manyanta daga dukkan alamu kuma mahaifintane ya dakatar da ita,babban abun burgewa a tare da ita lokacin data tarar da shi a zaune tun daga nesa da shi kad'an ta cire takalmanta,sannan ta durk'usa ta gaida shi,bayan nan ta shige gida..
Tun daga wannan lokacin naji zuciyata ta kwad'aita da yanayin tarbiyya irin ta wannan baiwar Allah wacce ko sunanta ban saniba bare na tabbatar da nan ne gidansu ko a'a.
Tun daga wannan ranar bamu sake biyo hanyar ba sai da muka kwana uku,sannan a yammaci na hud'u na shirya cikin shiga ta kamala kamar ko wane lokaci na d'auko hanya,ban zame ko inaba sai hanyar da muka gamu da wannan baiwar Allah,ina tafiya ina kuma duba gine-gine da yanayin unguwan har Allah yasa na kawo dai-dai wannan k'ofar gida data shiga,nan ko na samu guri na tsaya ina kuma k'arewa unguwar kallo,layin shiru babu mutane sosai zuwa wani lokaci sai wani yaro daga mak'otansu ya fito nan dai zuciyata ta rayamin na tambayi yaron ko Allah zaisa ya santa,banyi wani dogon tunaniba ko na kira yaron na tambayeshi ko yasan wata a gidan nan?,nan na siffanta masa ita da yanayuita,bud'ar bakin yaro ya furta eh yasanta sunanta *FALMATA* na masa dai y'an tambayoyi wanda bazasu gagara yaro ya amsaba ya bani amsa dai² da saninsa,sannan na zaro murtala na dank'a masa had'e da yi masa godiya,a guje yaron yabar gurin yana murna.Na jima tsaye a gurin kafin na bar unguwar.Tun daga wannan ranar ya zamemin d'abi'a kusan kullum saina je unguwar amma haka zan dawo ba tare da nayi magana da itaba.
Bayan sati uku da faruwar wannan lamari ne kuma muka kammala abunda ya kaimu garin,nan muka shiga shirye-shiryen komawa gida,to kuma a cikin wannan lokacin ne na yanke shawaran tunkarar gidansu da magana ko nasamu nasara ko akasin haka,nan na shirya na ko kama hanyar gidansu,cikin sa'a ina zuwa unguwar tun daga nesa na hango wannan dattijo na ranar farko zaune a k'ofar gida,da sallama na tarar da shi bayan mun gaisa ban tsaya k'wauron bakiba nayi masa bayanin abunda ke tafe dani,nan dai yayi dariya shima mutumin sannan yayimin albishir d'in cewa shi ne mahaifinta,kuma yaji dad'in abunda nayi,sannan ya d'ora da fad'in zai samu yarinyar zasuyi magana idan har ta nuna ta amince to idan kuwa ta nuna akasin haka tofa sai dai nayi hak'uri dan shi kam ba zai mata doleba duk abunda take so shima shi yake so kuma shi zai bata,bayan nan yamin tambayoyi akan inda nake da sana'ata,ban b'oye komaiba na daga abunda ya shafeni na shaida masa,daga k'arshe kuma nayi masa sallama gami da godiya na kama hanyar komawa inda na fito.
Kamar yadda yayimin alk'awarin bayan kwanaki na dawo dan jin yadda sukayi,kuwa na sake shiryawa daga garinmu dan a lokacin mun riga da mun koma gidajenmu,bayan naje mun gaisa da shi ya sanarmin da yadda sukayi,daga nan kuma ya shiga gidan da kansa ya kirawota,mun gaisa da ita bayan nan kuma tayi shiru saboda kunya da take da ko kallona bata iyayi a wannan lokaci,ban b'ata lokaciba na gabatar da kaina a gurinta a matsayin d'an takara na neman aurenta.
In tak'aita muku labari haka soyayya gami da shak'uwa suka k'ullu a tsakaninmu da FALMATA,wanda ba'a d'auki lokaciba mahaifina kafin ya rasu sukaje nemamin auranta,kun dai san yadda ake sa rana a k'auye ba'a d'aukan lokaci kamar na birni su sukan sa lokaci tak'aitacce ne,sun yanke ranar aure watanni biyu masu zuwa,inda kowane b'angare aka shiga shiri,da farko LADIYO bata nuna damuwarta kan auren da zanyi ba ganin yadda mahaifiyata take sonta,bayan auren kuma sai wasu halayya na banza suka fara sako kai cikin al'amuranta wanda da gani kasan zuga ce take aiki a kanta.
Muna zaune da FALMATA lafiya k'alau tun bayan aurenmu da ita da yake ita ba mai magana bace komai nata cikin sanyi take yinsa,wannan yasa ko da ake zugo LADIYO idan ta takaleta da fad'ama bata biye mata sai dai tayi shigewarta d'aki ta barta nan,haka itama zata k'araci masifar fad'anta ta bar gurin,ganin babu nasara sai ta canja salo inda a hankali ta soma jan FALMATA a jiki a gaban kowa tana nuna mata soyayya amma a zuciyarta babu wannan,ganin haka sai mutane suke sha'awar yadda suke zaune da juna,har wasuma suke fad'in ai MALAM BUBA yayi dacen mata na gari babu fad'a tsakaninsu.
Kwanci tashi har muka shafe tsahon shekara aurena da FALMATA amma shiru babu wani labari ganin haka sai hankalin LADIYO ya dad'a kwanciya,ta sake sakankancewa babu su babu haihuwa tunda ga wata nanma na aura amma shiru itama babu labari,haka dai akaita tsegumi da gutsiri tsoma akan nine bana haihuwa,wani hukinci da iko sai ubangiji a cikin shekara ta biyu da aurenmu da FALMATA sai Allah ya azurtata da samun juna biyu wanda babu wani ko wata da ya ankara da hakan da yake babu wani laulayi da tayi,har cikinta ya kai kimanin wata shida,ita dai ajikinta taji chanji wanda mafi yawancin lokaci takan sanarmin amma sai nace mata kada ta damu babu komai,a lokacin data sake sanarmin tanajin abu na mata motsi a ciki sai nake fad'awa iya cewa ga abunda ta fad'a min,bud'ar bakin iya sai tacemin micijin ciki ke damunta,nan ta had'oni da jik'e-jik'en magunguna na gargajiya na kawo mata..."
Nan MALAM BUBA ya dakata yana kallonsu da murmushi a fuskarsa sannan ya d'ora da fad'in
"Kun san wani abun al'abi a cikin wannan labarin?"
Babu wanda yayi magana cikinsu sai dai wasu cikinsu sun kad'a masa kai
"To ku saurara kuji.....Abun da zai baku mamaki shi ne,har cikinta yakai wata tara babu wanda ya gane sai dai ita da kanta ta fuskanci akwai wani bak'on al'amari a tare da ita wanda ganin hakan kuma da tayi baisa ta sanar da kowaba, a lokacin ni kuma nakanje fatauci daga wannan gari zuwa wannan kuma nakan kwashi watanni uku-biyar ban waiwayo gida ba,to kunji dalili kenan daya sa babu wanda ya gane tana d'auke da juna biyu har tsahon lokacin...


Masu iya magana kance "RANAR WANKA BA A B'OYON CIBI" k'warai kuwa haka yake wata ranar alhamis ciwo ya tasammata a cikin d'aki tun cikin dare addu'a kawai take saboda a lokacin bana gari,kuma gidan ya rage daga ita sai LADIYO wacce take nata d'akin daban itama,haka ciwon yake zuwa yana lafawa har dai Allah ya taimaka akayi asuba,a yanda take a haka ta lallab'a tayi sallar asuba,bayan nan kuma gari ya dad'a haske ciwo ya dad'a tadowa fiye da karon farko,tana wannan hali ne Allah ya kawo LADIYO shima zuwa tayi ta dubata ganin bata fitoba,samunta da tayi cikin ciwo wannan yasata hanzarin tafiya gidanmu ta kira mahaifiyata,ko kafin su k'araso gida har Allah ya sauketa lafiya,lokacin da suka shigo basuyi arba da komaiba sai da kukan jaririya nan suka k'arasa da sauri dan ganewa idanuwansu abunda suka ji gaskiyane ko kuwa,da zuwa suka tarar da ita a gefe tana maida numfashi jaririya a gefe tana tsala kuka babu b'ata lokaci iya ta gyarasu duka,tofa a lokacin ne kuma iya taimin aike kan lallai-lallai inzo gida tana son ganina a cikin kwanakin,lokacin da sak'onta ya riskeni banyi wata-wataba na shirya kayana sannan na kamo hanyar dawowa gida.
Bayan dawowata na tarar da wannan abun farin ciki daya sameni,aikuwa nayi murna sosai da ganin wannan kyauta da ubangiji yamin,bayan kwanaki 7 yarinya taci sunan mahaifiyata *KHADIJATUL KHUBRA*,tun daga ranar da FALMATA ta haihu sai LADIYO ta dad'a taso da halayenta na farko ya zamana ko d'akin FALMATA ta daina zuwa,tun kuma ranar data haihu mahaifiyata ta dawo gidan d'akin FALMATA ta tare ta shiga bata kulawa da gyara ta musamman wannan dalilin yasa LADIYO kishi mai tsanani amma sai ta dinga dannewa bata nunawa a fili,sai daifa abunda ke zuciyarta kenan a duk lokacin data bud'e ido taga FALMATA da sabuwar jaririyar ji take kamar ta cinna musu wuta su k'one gaba d'aya kowama ya huta.

Zuga kuwa da hud'uba kullum cikinsu take musamman idan ta fita tofa babu inda take zuwa sai gidan TABAWA,haka itama kullum cikin sintiri take a gidan nan,haka har suka k'ulla abunda suka k'ulla.

Wata rana da asuba lokacin bayan iya ta koma gida KHUBRA nada watanni biyu a duniya,bayan mun idar da sallah a masallaci na kamo hanyan dawowa gida,abunda ya faru a wannan ranar idan na tuno ina jin b'acin rai da nadamar abunda na aikata a wannan lokacin,a ranar ba d'akin FALMATA nakeba bayan shigowata saina tuna ai ranar ban tashetaba da zan fita kasancewar ina sauri zani masallaci,tuna hakan da nayi yasa na nufi d'akinta da sauri kasancewar gari har yayi haske sosai,da zuwana d'akin abunda ya d'agamin hankali shine na tarar da ita kwance tasa KHUBRA a gaba,daga bayanta kuma wani k'ato ne jikinsa ko riga babu ya rungumeta suna bacci a haka,ganin wannan abu ya d'agamin hankali sosai ban tsaya jiraba na shiga jibgar k'aton ihunsa shi ya farkar da ita dama jaririyarmu,dukan daya isheshi yasa shi ficewa a guje,idanuna sun rufe da tsantsan b'acin rai nan babu jira na fice daga d'akin.Faruwar hakan babu jimawa na sake dawowa a lokacin har tayi sallah jikinta duk a sanyaye,tana rungume da y'arta tana bata abincinta,na shigo babu b'ata lokaci nace ta shirya zamuje gidansu,ita dai har lokacin batayi maganaba kuma jikiinta yayi mugun sanyi fiye da farko dana tarar da ita a d'akin mayafinta kawai ta d'auka ta goya KHUBRA a baya muka kama hanya ni da ita haka har muka isa gidansu,da zuwa nace ta shiga ciki idan BABA na nan tamin sallama da shi,ta shige ta barni nan a k'ofar gida.
Bayan fitowar BABA muka gaisa a mutunce sannan na shiga koro masa bayanin abunda ya faru,shi dai yayi shiru yana saurarona har na k'are labari,sannan ya kalleni da mamaki shimfid'e a saman fuskarsa ya shiga fad'in
"Nayi mamaki daka zomin da wannan rikitaccen labarin naka mai kama da k'anzon kurege,kuma tabbas kaima ka bani mamaki da wani yazomin da wannan maganar wallahi da sai nayi k'ararsa amma da yake kaine mun barka da Allah,amma zan tambayeka wani abu game da y'ata,shin lokacin da kazo neman aurenta ka tarar da ita tana tara samari ne ko kuwa? sannan bayan ka aureta ka sameta a cikakkiyar budurwa ko a'a? tana da kamun kai ko a'a a bayan aurenku?"
Duka amsoshin d'aya ne A'a,tabbas ba haka halayenta suke ba,amma a lokacin da yake abunka sa sharrin zuciya sai nake ganin kamar fa ta aikata,nan na k'ek'asa k'asa na kuma dube shi nace
"Nifa BABA duka nasan ba haka bane amma na sani ko ta sauya hali ne bayan nan"
Sosai maganata ta b'ata masa rai amma sai ya danne ya ce
"To yanzu daka dawo da ita kuma me yake faruwa?
Nan ko na furta "Na dawo muku da ita ne,sannan kuma tunda Allah yasa haka halinta yake na saketa saki d'aya idan ta samu miji tayi aure..."
Ba sakin ne ya b'ata masa raiba illa cin mutuncin da nayi musu na saida na kawota har gida sannan kuma nace na saketa a gaban idonsa,nan ya ce
"To BUBA munji abunda ya faru mun kuma gode amma ka jirani na fito maka da y'arka,kamar yadda ka dawomin da tawa y'ar nima ina son tabbatar maka da bazan rik'e maka taka y'arba,saboda haka saika nema mata wata uwar"
Yana gama fad'in haka ya shiga gida ya fito hannunsa d'auke da jaririyar,nan ya mik'omin ita nako sa hannu na karb'a na mik'e zan tafi,maimakon na tafi sai na bud'e bakina na kuma kalli tsabar idonsa nace
"Kamar yadda ka bani y'ata in sha Allah zan rik'eta da yardar Allah kuma babu abunda zai samemu,kamar yadda zan tafi da ita yanzu to ko ku tabbatar na tafi da ita kenan bazaku sake ganintaba haka nima na tafi kenan ni da ku har abada...."
Ina gama fad'a masa ban jira ya sake maganaba nayi gaba abuna..


"Tun daga wannan rana rainonta ya dawo hannun IYA mahaifiyata saboda LADIYO ko kallo bata isheta ba,KHUBRA nada wata uku a duniya mahaifina ya rasu daga nan ne kuma IYA ta dawo gidanmu da zama a d'akin da FALMATA ta zauna,tana kuma ci gaba da kula da ita.
Kimanin watanni biyu da rasuwar mahaifina,IYA ta fara

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads