Header Ads
Showing 48001 words to 51000 words out of 159513 words

Chapter 17 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1228

Ads at the middle of Article

da suka bari yanzun....
Da k'yar take iya turawa,fuskanta zuwa jikinta duk yayi gumi kan wahalar da tasha na turo kuran,idan ta gaji ta tsaya ta huta haka taita fama har ta fara shigowa cikin garin....


Jama'a sai kallonta suke da mamaki yayin da wasu ke binta,ita kam ko a jikinta,dan ta d'aura aniyar neman halak enta,sana'a babu fashi yanzun ta soma duk abunda mutane za suyi babu ruwanta,za ta toshe kunnenta daga tsaigumin su,haka taita turawa tana wucewa,line ta soma bi d'aya bayan d'aya,wani line en idan ta shiga za ta tarar da shi cike da mutane y'an gulma wad'anda labari ya iske,ba maza ba mata,hatta da k'ananan yara binta suke duk inda tayi,ita ko ko a jikinta....


Ganin wannan sabon al'amari yasa mutane siyan ruwan ga wand'an dama basuyi niyyaba duk dan su shaida labarin da ya iske su,duk gidan da suka siya dai kaga wasu daga cikin y'ay'ansu maza suna saukewa suna shiga da shi,idan sun juye su bata kud'inta da jarkanta,haka zata k'ara gaba su kuma su bita da idanu...
Kafin wani lokaci babu komai cikin kuran nata duka ruwan an siye babu sauran,bakin wata bishiya ta zauna tana lissafa kud'in naira d'ari biyu #200 cif,hamdala tayiwa Allah kafin ta huta abunta,bakin kasuwa ta sake komawa ta nemi mai abinci a gurin,tunani ta tsaya yi to na nawama ya kamata ta siya ne?
Ta d'an jima tana yanke shawara,kan ta bayar duka ko a'a.....
Mik'awa tayi duka ba tare da ta tantance ko yayi yawa ko baiba...
Mai abincin ce ta kalleta da alamar mamaki tana fad'in
''Ke ko y'ar nan me za kiyi da abinci har na d'ari biyu,ai yayi miki yawa,ungo wannan''
Ta mik'o mata d'ari da hamshin,d'an murmushin k'arfin hali tayi ta karb'a tana mata godiya...


''A robber zan zuba miki ko kuwa a leda?na ga kamar bak'uwace ke ko?''


'Dan murmushin ta sake yi tana fad'in
''Eehh!ni bak'uwa ce''

''Allah sarki ai na ga alama tun zuwanki gurin nan''


Bata kuma magana ba ta karb'i abincintan a gefe ta samu guri ta zauna,ko rabi bata iya cinyewa ba ta mik'e tana dawowa matar da robber enta da sauran abincin ciki,kallon mamaki tayi mata kafin ta iya tambayarta
''Me ya faru kika dawo da shi haka?''


''Uhmm!babu komai wollah babata na k'oshi ne''


Kalmominta da ta kira matar da shi wato ''BABATA'' su suka sa matar yin k'wallar farin ciki,kasancewarta bata tab'a haihuwa ba,har Allah ya d'auki ran mijin nata,tun daga nan kuma bata kuma wani auren ba...


Ganin matar na hawaye ya sanyayawa KHUBRA jiki,haka taita kallonta uwa wata doluwa....


''Y'ar nan gidan wa kika zo a garin nan?''
Tambayar ta bawa KHUBRA mamaki,amma sai bata nuna ba
''Ban san kowa ba a garin nan,nima kawoni akayi nan''


Da mamaki matar ke kallon KHUBRAN tana fad'in
''Kawoki akayi kuma?''


Kai ta kad'a mata,mik'ewa tayi tana kad'e jikinta da niyyan barin gurin
''Yanzun ina kika nufa y'ata?''


''Zan wuce ne''


'Dan tunanin matar tayi da sauri kuma ta katse KHUBRA dake haramar barin gurin
''Y'ata idan za ki yarda kuma kin amince ba zan tab'a cutar da ke ba,kuma idan har kin d'aukeni uwa a gareki......
Zaki iya bina gidana mu zauna tare,kin ganni nan tsawon shekaru talatin da biyar da aurena Allah bai tab'a azurtani da d'aba,amma yau na farko kin kirani MAHAIFIYA wannan dalilin yasa naji ina k'aunarki,tabbas zan rik'eki a matsayin y'a,idan har kin amince''....
Ta k'arashe maganar ta tare da goge wani layin hawaye dake kan fuskanta....


'Dan tak'aitaccen murmushin yak'e tayi,kafin zuciyarta ta tuna mata abunda aka mata yanxun da ko awanni biyar ba ayiba....
Da sauri kuma wata zuciyar ta bata amsa da cewa
''Haba KHUBRA duniyar nanfa ba duka aka zama d'ayaba,ya kamata ki tuna yadda rayuwar ki ta faro,wasu na sonki wasu na k'inki,kada kiyi saurin yanke hukunci,kiyi addu'ah dan shi ne gatanki a rayuwa a kuma duniyarki''......


Siririyar ajiyar zuciya tayi,kafin ta furta
''Na amince BABATA amma da sharad'i''


Matar tana murna ta kalleta
''Koma wane irin sharad'ine na yarje miki fad'i kome kike so in sha Allah bazan gazaba''


''Dama ina so ne nace...... Baba don Allah kada ki hanani neman abunda zan rufawa kaina asiri,komai tsafta,k'azanta,k'ask'anci ko samu da sana'ar take d'auke da shi''....


Kallonta kawai matar tayi
''In sha Allah bazan hanaki ba.....
Amma wace irin sana'a ce wannan?''


''Ba wata sana'a bace illa *GARUWA.............''*


A d'an tsorace ta kalli KHUBRAN,ita ko sai murmushi take abunta,da fuskanta da har yanzun tak'i komawa dai²....
Gudun kada tayi magana akan sana'ar ta KHUBRAN tak'i amincewa da buk'atarta,yasa taja baki tayi shiru,tana nai fad'in
''To shi kenan Allah ya wuce mana gaba,yayi miki jagora''


KHUBRA ta amsa da ameen.....


''To yanzun dai da kin bari sai zuwa gobe ko dan mu tafi tare kinga kyaga gidan namu ko?''
Ta fad'a tana d'an murmushi,itama KHUBRAN murmushi tayi ta sake neman guri ta zauna,tana ta kallon mutane da keta zuwa siyan abinci,tana zaune har abincin ya k'are tas,tana kallo matar ta kammala had'a kayan al-majirai suka d'aukan mata kayan nan ta juyo tana kallon KHUBRA
''Taso mu tafi y'ata''


Babu musu ta shiga bin matar a baya suna tafe tana tura kuranta na ruwa har suka isko wani k'aramin gida,nan suka shiga suka nemi guri KHUBRA ta adana kuranta da niyyan gobe da wuri zata fita sana'anta.....


《《》》


Kallonta yayi duk ta wani birkice
''Me yake damunki SISNAH?''


Bata iya bashi amsaba,hannunsa kad'ai ta jaa zuwa guarding suna tafe tana waiwayawa tana kallon hanya,guri suka samu suka zauna sannan a d'an tsorace ta juyo
''YAYANAH wallahi ina jin tsoro kada wani abu ya samu KHUBRA......Duk abunda ya faru BB MAMA ta san komai kuma wollahi da hannuta komai da ya faru,MAMA ce sila......Dan Allah YAYANAH ka nemomin ita pleasee''
Ta k'arasa tana rintse idanunta....


Tashin hankalinsa k'aruwa yayi jin ta ambaci MAMA,amma ya akayi tasan da sa hannun MAMAN a ciki?Yama kansa tambayan.....


''Me yasa kikace da sa hannun MAMA?''
Ya mata tambaya yana mai jin fad'uwar gaba,dan bai san wane amsane zai fito daga bakintaba
''YAYA Allah ina jin tsoro sosai.....YAYA yanzun na fito naji tana waya,amma bansan da wa suke magananba....Wallahi YAYA ita tasa aka sace KHUBRA''


Shiru yayi ya kasa magana kansa sai dad'a sarawa yake kan ciwon da yake masa vains en kansa duk sun gama bayyana a fili....

''Kuma YAYA ko ta ce sai ta k'ona duk wani abu da ya shafi KHUBRA shi yasa na rufe d'akintan......YAYA ansa key en ka adana ni kasan MAMA zata iya buguna amma dan Allah kada ka bari ta sani kaji BB nah''
Ta fad'a tana d'ora masa key en a hannunsa,da sauri ta mik'e ta bar gurin tana had'awa da gudu,har ta shige bed room enta basu had'u da kowaba,da sauri ta maida k'ofan ta rufe.....


A hankali ya mik'e yana tafiya,har bakin k'ofan bedroom en,key en ya sanya ya bud'e yana shiga ya maida k'ofan ya rufe yana mai locking enta ta ciki.....
Kan katifanta ya kwanta yana sauke ajiyan zuciya,yanayin d'akin kad'ai ya bashi nutsuwa ko ba komai k'amshinta da yayi remaiming ciki ya kwantar masa da hankali,yana haka wani bacci mai dad'i wanda ta jima rabon da yayi shi ya d'auke shi.....


《《》》


Cikin d'aki matar ta mata iso tana mata shimfid'a,a hankali ta shiga ta zauna tana ta kallon ko ina na d'akin,zama matar tayi tana fad'in
''Ohhhh!niko ko sunanki ban tambaya ba,ina can d'okin tahowa da ke''
A hankali ta furta ''Suna na KHUBRA''


''Allah sarki ni kinga suna na ZUWAIRA''
'Dan murmushi kawai KHUBRAN tayi sai dai tambayan matar ya sa fuskarta saurin rikid'ewa zuwa tsantsar tashin hankalii..........




*~#KEEP FOLLOWING FAN'S....~*




*Mu tara bayan sallah da yardar Allah,da fatan Allah ya karb'i ibadunmu,na barku lafiya,Allah ya sada mu da alkhairinsa....Ameen thumma ameen.*




*~UR'S & ONLY~*






*_REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*19/ʝųŋɛ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


_Ina taya d'aukacin al'ummar musulmi na duniya murnan sallah da fatan ubangiji ya amshi ibadunmu ya kuma sanyamu cikin y'antattun bayinsa.....ameen._ 👏👏
*HAPPY EID-EL-FI'DR.*
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*2⃣9⃣*








*"O* ohh! Ni ko na miki wata tambaya d'azun sai dai amsan da kika bani ya tsayamin a rai,na kasa fuskantar abunda kike nufi
"...
'Dan d'agowa tayi tana kallon matar saboda rashin fuskantar maganar ta new mother en nata..
Gane hakan da tayi shi yasa tayi d'an murmushin yak'e kafin ta furta
"A d'azun na miki tambaya kan gurin wa kika zo a garin nan,sai dai amsan da kika bani yasa nake son sanin me yasa aka sato ki kuma wane azzalumi ne ya aikata miki haka?"
Fuskanta cike da tashin hankali haka ta sunkuyar da kai k'asa,dan kam ta tabbata mai afkuwa na shirin faruwa,tunda matar ta soma tambayanta lallaine a k'arshe matar ta koretama gaba d'aya,wannan tunanin shi yasa ta dad'a sunkuyar da kanta k'asa gudun kada matar ta gane k'aryan da take shirin yankowa bata iya d'agowa ba,idanuntan nan sun dad'a fitowa kan tsoro da ya cika zuciyanta,duk da dai tasan ba wai laifinta ne yasa aka aikata mata hakanba...
Tana nan zaune tayi shiru amsa tambayan ya gagareta tana ta taradaddin sanar da BABA ZUWAIRA,ta tsinkayo muryanta tana fad'in
"Niko KHUBRA idan babu damuwa zan so sanin daga wane gari kika fito da kuma asalinki?"


Jin wannan tambayan yasa ta sauke ajiyan zuciya a tunaninta ta tsira daga wancan tambayan,shi yasama cikin k'warin gwuiwa ta bata amsan
"Daga KANO nake,BABATA dan Allah nan wane gari ne? ban san ina ne nan ba" KHUBRA ta fad'a yayin da wasu hawaye masu d'umi suka fara sakko mata,gefen hijab na jikinta ta kama tana gogewa,duk wani motsinta idon matar na kanta tana binta da kallon tausayi...


"Allah sarki nanma duk cikin kano kike ae sai dai nan muna daf da jihar jigawa,sunan wannan garin ZAKIRAI,amma cikin kano wani gari kike?"


Raba ido ta hau yi tana son tuno sunan unguwan da suke,tunani take ko zata iya tuno sunan unguwan da suke,amma ta kasa.....


Katseta BABA ZUWAIRA tayi da wata tambayan
"Ke kuwa mene ne ya faru dake da har wasu suka satoki daga gidanku kuma hannun iyayeki zuwa wannan gari,kuma me kika aikata musu da zafi har haka?"


Kukanta tayi k'ok'arin had'iyewa,kafin cikin nutsuwarta ta soma da fad'in
"Dan Allah MAMA kiyi hak'uri kuma ki yarda da ni,ko da na fad'a miki gaskiya baza ki koreni ba"...
'Dan tsagaitawa tayi ta d'ago kanta tana kallon new mother enta BABA ZUWAIRA..
Kai ta soma kad'a mata kafin ta bud'e baki cikn sanyin jiki ta furta "In sha Allah babu abunda zai faru,ke dai ina son ki fad'amin gaskiyarki,dan da ganinki bana tsammanin k'arya daga gareki,ina fatan kuma zaki d'aukeni matsayin mahaifiya ki sanar da ni komai"..
"In sha Allah" KHUBRA ta fad'a a zahiri,yayin da can k'asan zuciyarta take fad'in "kiyimin afuwa amma kam tabbas bazan iya sanar dake *SIRRIN RAYUWATA* ba",in sha Allah dana fad'a dama sai Allah ya baka iko,kuma k'arya wajen kare kai ta halatta,tana kaiwa nan ta datse tunanin had'e da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya...


"Kamar yadda na sanar miki ni sunana KHADIJA amma mahaifina na kirana da KHUBRA,saboda kasancewar sunan mahaifiyarsa gare ni wannan dalilin yasa mutanema ke kirana da KHUBRA kamar yadda mahaifina ke kirana,mahaifiyata Allah yayi mata rasuwa tun ina jaririya"
Daga nan ta shiga bata labarin irin zamanta a gidansu ZUHRA,sai dai ta b'oye alak'arta da gidan da kuma irin zaman da take,hakama alak'arta da MA'U,LADIYO da ma k'auyensu,abunda ta iya sanar mata kad'ai kishiyar mamanta ce take son ta auri k'aninta ita kuma bata so,kan wannan dalilin ta d'ora mata karan tsana,tun daga ranar take zuga mahaifinta,ganin yak'i amincewa ne yasa tasa aka satota daga gidan wanda k'arshe suka yasar da ita a bakin kasuwar garin nan.....


Shiru tayi tana jan numfashi a hankali,kanta har lokacin yana k'asa saboda tunaninta tana d'agowa suka had'a ido matar zata gane k'arya ta mata..


"Allah sarki y'ata,in sha Allah da sannu duk mai hannu a ciki sai ya ga sakamako,amma mai zai hana na d'oraki a hanya ki koma gida,saboda kinga baki san halin da mahaifinki yake ciki ba".....
Cikin sauri KHUBRA ta katseta da muryar tausayi, "dan Allah BABATA kiyi hak'uri kada kuma ki ce nak'i bin shawararki,wallahi ina son sanin halin da mahaifina yake ciki,amma ina tsoron zuwa gida saboda ban san me zan je na tarar ba,ki kyale ni na zauna tare da ke har zuwa wani d'an lokaci,in sha Allah da kaina zan miki maganar tafiyata idan lokaci yayi" ta k'arasa tana goge fuskarta da hijab enta...
Yanayin yadda tayi maganar shi ya sanyayawa matar jiki,tausayin KHUBRAN duk ya lullub'e mata zuciya haka take ta bin KHUBRAN da kallon tausayi..
"Shi kenan babu komai KHUBRATA in Allah ya yarda zaki ci gaba da zama a nan,Allah yasa hakan ya zama alkhairi a garemu baki d'aya"
Tako amsa da ameen,wani sashe na zuciyanta yana farin ciki da amincewar da matar tayi....




《《》》




Daf da za a shiga masallaci ya farka har an idar da kiran sallan maghreb,da sauri ya mik'e ganin garin yayi duhu,agogon dake d'akin ya kalla,da mamaki a kan fuskansa cikin rashin gasgatawa ya nufi window yana mai d'aga cottains en aiko take ya gasgata abunda ya gani danko rana ta jima da fad'uwa,da sauri ya juya ya shige toilet en d'akin....
Cikin sauri ya idar da alwalan lokacin har an tayar da sallah a nan saman carfet ya kabbara sallah da yake yana iya jiyo masallacin kuma gudun kada ya rasa jam'i kafin ya fita...
After ya idar yayi nafila,nan ya zauna yana addu'ah..
Ko da ya idarma kasa fita yayi ya kishingid'a jikin katifan yana tunanin baccin da yayi cikin d'akin,yayi nisa cikin tunani ya jiyo ana jijjiga k'ofan a d'an zafafe ya mik'e saboda yadda ake bugun k'ofan kamar za a karyata,shifa yanzun baya son damuwa kamar yadda yake jin haushin kowa a gidan idan aka d'auke ZUHRA da damuwarsu take kusan iri d'aya...
Key en yasa ya bud'e k'ofan kamar an cillota ta shiga k'ok'ari fad'owa kansa cikin sauri ya kauce ta hanyar ja baya kad'an a kan hanyan,Allah ya taimaketa ta rik'e k'ofan bata kai ga fad'uwa k'asa ba,ganin tana k'ok'arin shigowa yasa ya tare hanyan,ta hanyar tsaiwa tsakiya...

'Dagowa tayi cikin fushi ta furta "KHALEED yaushe na fara wasa da kai da zaka tsayamin a hanya?.........Ammm!mene ma ya kawoka d'akin nan tukuna kana neman wani abune ciki?"


Kamar an dasa gini haka ya mata ko "A" bai furta mata ba,kuma yak'i barin gurin...
Hannunsa ta kamo da niyyar janyeshi daga gurin saboda a tunaninta zata iya,sai dai ko gizau baiba,ganin ta kasa yasa shi sakin wani murmushin yak'e mai sauti da yasata kallonsa....


Had'e fuska tayi alaman babu wasa..
"KHALEED kaa matsa a nan ko kuwa sai ranka ya b'aci dan yanzun zan baka mamaki?"

"Uhhhmmm!MAMA ai an gama bani mamaki duk duniya,abunda kika aikatama kad'ai ya isa ya gama bani mamaki,amma MAMA ki tuna idan kin aikata haka akan y'ar wani shin bakya tunanin naki y'ay'an? idan Allah ya tashi kamaki me zaki fad'a masa lokacin da kika tsinci kanki a gabansa a lokacin da kowacce gab'a ta jikinki sai ta bada shaida akan abunda ta aikata,MAMA ki tuna da lahirarki sannan ki tuna irin tanadin da kika yi mata''.......


"Kaiiiiiiiiii! dakata ni sa'arka ce da zakamin wa'azi?kada ka manta ni na haifeka ba kai ka haifeniba da zaka tsaya kana fad'an maganar da ranka yaso,kuma yanzun maza ka kauce ka bani hanya".....
Cikin tsawa da fusata take magana tana jifansa da wasu mugayen harara....

'Dan murmushi ya sake yi mai ciwo yana kallonta,shi kam yau yaga ikon Allah,gaskiyan ne bata so a fad'a mata kenan?.......
"Shi kenan MAMA duk abunda kikayi dai² ne,amma ki sani nasan duk wani shirinki akan KHUBRA da kika sa aka d'auke,sai dai hanzari ba guduba duk wani yunk'uri da za kiyi idanun jami'an tsaro na kanki,saboda haka babu laifi kiyi duk abunda kike ganin ya kamata"......
Mari ta d'aukeshi da shi da yayi saurin sashi yin shiru yana dafe da gefen fuskansa da ido ya bita,lokacin ita kuma ta juya ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads