Header Ads
Showing 51001 words to 54000 words out of 159513 words

Chapter 18 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1221

Ads at the middle of Article

bar gurin cikin sauri.....


Wani murmushin ya sake yi,kafin ya juya ya kulle k'ofan yana mai barin gurin shima,zuciyansa duk ta cushe da tunani....


《《》》




"Amma kuwa wollahi za muyita dan wollahi sai anji kanmu da MA'U a yau kam,dan ta raina ni ta kama hanya ta bar garin nan da yarinya lokaci mai tsayi amma ko kobo bata tab'a kawomin ba,tabbas kam sai nayi maganinta".....
Ita kad'ai zaune sai surutai take kamar wacce ta zautu,duk ta dad'a ramewa ga wani tsufa da ta dad'a yi kamaninta sun d'an jirkita....


Sallama akayi k'asa² daga bakin k'ofar shigowa gidan,hannunsa d'auke da robber 25 litres guda biyu dattijon ya shigo haka ya wuce ya juye ruwan cikin randunan dake jikin dangar kara ta gidan...


"Wai tun d'azu daka fita sai yanzu ka dawo gaskiya anyi malalaci a nan"
Ko juya ya kalleta baiba bare ya tanka mata,yana gama juye ruwan ya shige d'akinsa baiko bi ta kantaba.....


"Bari dai kiga na mik'e ni inama zan samu aron tarho na kira wannan y'ar banzar na jita shiru,ga shi ni kuma ban san inda take ba a garin na kano"
Tayi maganar lokacin da take k'ok'arin yafa mayafin hannunta da ya cukuikuye saboda daud'a da rashin guga,nan ta bazama tayi waje......


《《》》


Shigansa bed room ya kwanta yana tunanin abunda ya kamata ya aikata,sam baya son a sake jefata wani halin duk da dai yanzunma bai san a wane yanayi take ba....
"Ya zama dole na nemo ki duk inda kika shiga a fad'in duniya.........Tabbas MAMA kin aikata kuskure mafi muni a rayuwa amma da sannu zaki girbi abunda kika shuka.....
Wani tunani ne ya bijiro masa take ya mik'e yana laluban phone ensa,kaf d'akin ya duba bai gansuba,d'an tsayawa yayi yana tunani da sauri kuma ya fice daga room en,cikin sauri² ya kama hanyan fita..
A mota ya gano su,inda ya tarar da tarin miss-calls duk daga KHALEEL,kira yabi line en nasa da shi....


"Dallah MALAM ina ka shiga kasa sai nemanka nake tun d'azun?"


"Sorry BRO na manta phone a mota.....Ammm a kwai maganar da nake so muyi,idan kana gida yanzun zan k'araso"


"Ok ba damuwa sai ka k'araso"


Sukayi sallama,motan ya bud'e cikin y'an mintuna ya bar gidan.....
Bai wani b'ata lokaciba ya isa gidan,inda ya tarar da KHALEEL en a parlor,nan suka gaisa da UMMI tana zaune suna kallon AL-JAZEERA....
Ta saba duk lokacin da yazo zata tambayeshi mutanen gida amma yau kam suna gaisawa tayi shiru ta juya taci gaba da kallonta....


KHALEEL ya kalla yana fad'in "MAN muje ko?"


Mik'ewa sukayi suka fice,yayin da UMMI ta rakasu da kallon tausayi....


A haraban gidan suka nemi guri suka zauna,nan kowa yayi shiru...
KHALEEL ya kalleshi da mamaki "ya dai ka ce da magana kuma kayi shiru"


"Wallahi ina jinjina maganar da zan fad'a ne kawai"


"To Allah ya kyauta"


"Ammmm!abu na farko dai da nake son sanar da kai yanzun,ina son mu koma gurin D.P.O da kai gobe,saboda ina son a bamu y'an sanda da zasu dinga kulamin da al'amuran MAMA"


"MAMA kuma kan wane dalili?"
KHALEEL yayi tambayan cikin hanzari...


"EHHH!MAMA....."


"K'wak'walwarka ta tab'u ne da zaka sa ayi mata haka ko kuwa ta aikata wani laifi ne?"


"Uhhmmm!ni dai abunda nake so ayi kenan idan zaka to".....


"Kaga MALAM babu inda zani,ta inama zan biye maka mu aikata wannan shirmen"


Cikin fushi KHALEED ya mik'e yana fad'in
"Kada Allah yasa kayi en,dan ka nunamin haka bazan damuba saboda baka san dad'i ko ciwon k'anwa ba idan wani abu ya sameta saboda kai kad'ai ne,amma ka sani akan KHUBRA zan iya aikata komai......
MAMAN da kake maganar ba zaka bada goyon baya akanta ba,itace silar faruwar komai".....


"Meeeeee?kana nufin ita tasa aka sace KHUBRA ko me,ta yaya ka tabbatar da hakan?"


"Ban saniba,idan ka d'auka wasa nake to ka daina,tabbaci nake baka kan MAMA tasan komai kuma ITA CE SILA"......


《《》》


Washe gari da wuri KHUBRA ta shirya ta fita don yau kam sai ta dangana da rafi zata d'ebo ruwa,shi yasa tun kafin rana ta gama haske garin ta fice,inda tayi sallama da BABA ZUWAIRA sunama juna fatan sa'a....


Lokacin da BABA ZUWAIRA taga fitar KHUBRA binta tayi da kallon tausayi idanunta duk sun ciko da hawaye,fatan samun nasara tayi mata,tana jinjina al'amarin yarinyar,yarinya kyakyawa amma ana neman nakasta mata rayuwa,tabbas dan dai kada tayi magana ne kan wannan sana'ar ta KHUBRAN ta janyo abunda zaisa ta gudu daga hannunta amma kam tabbas da sai ta hanata dan sana'ar ba ta y'a mace bace,ko shi kansa d'a namijinma wannan sana'ar tayi wahala gareshi,sai dai dan kawai neman halak.....
Cike da alhini ta kammala shirinta ta fice zuwa bakin kasuwa.....


《《》》


Tun bayan da MAMA tabar gurin da BB yake zuciyarta ta kasa samun nutsuwa jin ya ambaci police..
"Aiko ko ba don Allah ba na saurara hakanan tun kafin a kamani a gark'ama a jail"


Tana gama maganar ta afka d'akin tana mai rufewa da key......




Niko nace
*"KOWA YA TUBA DAN WUYA BA LADA"*......








*_~#TEAM KHUBRA~_*








*_REAL SMASHER._*
💠?💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*21/ʝųŋɛ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*

_Wannan shafi tukuicine gareku masoyana kuma masoyan wannan novel nawa na *Y'AR GARUWA* a duk inda kuke a fad'in duniya ina al'fahari daku,idan babu ku tabbas babu ni ina sonku so irin wanda bazai fad'uba da baki,Allah ya barmin ku a duk inda kuke....Na gaisheku oll 👌 kuyi komai ba komai *SMASHER* taku ce..._
_Fatan munyi sallah lafiya, ubangiji ya maimaita mana..Ameen.._
*~________________________~*


_Sisinah wollah *GENTLE,SMASHER,HUBBEEY,LIPTON* tare da *AUFANA* muna matuk'ar alfahari dake wollai muna godiya da sadaukarwarki gare mu,jinjinar ban girma ga *CWEET DIDEEYLOV* Allah ya d'aukaka mana ke ki jima kiyi k'arko lokacinki ne yanzun ki ci gaba da haskawa cikin duniyar yanar gizo-gizo,muna nan biye dake duk inda kike...Godiya mai tarin yawa Allah ya k'ara miki lafiya da nisan kwana mai amfani.._


*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*3⃣0⃣*






*Z* ama yayi kamar wanda aka dangwarar abun da yaji daga bakin KHALEED en duk ya d'aure masa kai,kallonsa ya sake yi yana son sake tabbatarwa dan kada suzo suyi abu da ka shi yasa a wannan lokacin da ya sake kallonsa ya furta
"Da dai ka nemi guri ka zauna,dan ni har ga Allah ina buk'atar kamin k'arin bayani kada muzo muyi abunda zaisa muyi DANA SANI"


Wani banzan kallo BB ya bishi da shi had'e da sakin tsaki,ba tare da ya zauna ba kamar yadda KHALEEL en ya buk'ata ya fara magana
"Kafi kowa sanin halina kamar yadda kasan ba zan yi maka k'arya ba"

"Hakane amma kasan shi al'amari irin wannan ba a masa gaggawa,da ka dakata munyi bincike tukuna"


"Heeyy!MALAM har wani BINCIKE kake neman muyi bayan wanda nayi,ko an fad'a maka nima ina cikin mutanen da suke yanke hukunci cikin gaggawa?
Idan mafarki kake to maza ka farka dan wannan kwana² da kakemin bazai hanani abunda nayi niyyaba"...


"To Allah ya kyauta,kai matsalarka kana da shegen taurin kai,baza ka tsaya kayima mutane bayaniba sai dai ka bada magana a dunk'ule"


"Kai kuma gaka mai kullallen kai da baka iya fuskanta ko?"


"Mtssssss!Allah ya shirye ka,amma zauna muyi shawaran hanyan da ya kamata mubi kafin muje wajen D.P.O"


Jin da yayi ya ambaci D.P.O shi ya bashi damar zama
"To yanzun mene abun yi ne kam?" BB ya tambayi KHALEEL


"Ummmm!ina ganin mu bari zuwa gobe sai muje mu sanar masa duk halin da ake ciki,ina tunanin haka ya kamata muyi"


"Toh!hakanma yayi Allah ya kaimu.....Muje nama UMMI sallama zan wuce gida dare na dad'a yi"
"Ok ba matsala muje"


Mik'ewa sukayi suna masu nufan cikin gidan....
A parlor suka tarar da ita har time en tana kallo,sallama ya mata,ta bishi da fatan isa gida lafiya..
Har bakin motor KHALEEL ya rakashi sukayi sallama tare da musabiha,yayima motor en key........


《《》》


'Daya bayan d'aya take bin robber's en nata tana zuba musu ruwa yayinda cikin k'arfin hali da k'arfin zuciya take d'auka tana jerasu cikin kuran nata,haka taita fama har ta gama jerasu..
Hannu ta mik'a saman pore head enta tana goge sweat da ya tsatsafo mata,sai da ta d'an huta tukun kafin ta kama hanyan shiga cikin gari,kamar jiya haka tayi ta zagaye cikin garin,kafin wucewar awa d'aya babu komai cikin kuran nata,kasancewar garin sun d'anyi nisa da gurin da ake d'ebo ruwan,shi yasa wasu daga cikin mutanen garin basa son zuwa d'iban ruwan,yayinda wasu kuma suka fi son *"Y'AN GARUWA"* su kawo su saya....


Ta bakin kasuwa ta biyo zata koma,a dai² lokacin BABA ZUWAIRA na kan ciniki itama,ta hango KHUBRA lokacin kuma rana har ta bud'e sosai,da murmushi a fuskanta ta k'araso...


"Y'ata ta kaina da ganin wannan murmushin da kike akwai alamun nasara"
BABA ZUWAIRA ta fad'a itama tana murmushin


"Wollahi kuwa BABATA anyi nasara"


"Aaa!masha Allah,maza zo kici abinci kafin ki tafi"


"Laaa!BABA nafa ci abinci d'azu kuma ni bana jin yunwa yanzun"


"To shi kenan maza zo ki huta kafin ki tafi ko"


"A'a gara dai na koma bakin sana'a anjima sai na huta"


"To shi kenan Allah ya bada sa'a"


KHUBRA ta amsa da "ameen" sannan ta kama hanyan komawa rafi,kamar wancan lokacin haka ta kammala ta sake biyo hanyan jejin zuwa cikin gari......


《《》》


"Haba HAJIYA LAURA nafa fad'a miki yanda al'amarin nan ya kasance,wallahi yaran nan yana neman ya jagulamin lissafi,gaba d'aya ya gama sanin duk wani abu dana aikata kan wannan matsiyaciyar yarinyar...
'Dazufa da yanamin magana kamar shi ya haifeni,har da yimin wani wa'azi"


"Kai HAJIYA MURJA kina d'aukan komai da zafi,banda abunki dan yayi miki wannan maganar shi ne zai sa ki tashi hankali akan wannan maganar"


"To me kike so ayi kina ganin yadda yake maganar police kinga kuwa shirinmu yana neman rushewa"......


"Ni kam dan Allah HAJIYA MURJA ki kwantar da hankalinki,zan san yadda zanyi na ganin babu abunda ya faru"


"Uhmmm!HAJIYA LAURA kenan lallai baki san halin KHALEED ba,ko ni da nake matsayin mahaifiyarsa ina shayin shiga al'amuransa,saboda halinsa kaf irin na maifinsa ne,idan sukayi magana basa tab'a canzawa,suna da matuk'ar taurin kai,shi yasa nake jin tsoron su furta wata magana dan ina da tabbacin ba janyewa zai yiba"....


"To ai shi kenan amma dai duk yanda ake cikima zan sanar miki"


Ko sallama HAJIYA MURJA bata iya yiwa HAJIYA LAURA ba ta datse kiran,saboda hankalinta tashe yake da abunda yake shirin faruwa tsakaninta da KHALEED da yake neman tada mata K'AYAR BAYA...
Kaiwa da kawowa ta shiga yi cikin d'akin,sam ta kasa tunani hankalinta sam ya kasa kwanciya.....


《《》》


"Ke dallah kefa nake jira kin wani kwanta kamar kayan wanki,bayan kin san ke nake jira,bana son wannan rainin wayon,kawai hajiya ki tashi ina son jina a sama cikin hazo ina yawo"

Da kyar MA'U ta d'ago tana kallonsa "Haba mana kayi hak'uri zuwa anjima,ina jin bacci yanzun kome kake buk'ata idan na tashi kayi,amma yanzun ka kyaleni"


"Ke ai kinji matsalarki da an tab'aki ki ambaci gajiya ko bacci"


"To me kake so nayi maka idan ban hutaba so kake na mutu a tsaye ko da yaushe kana aiki a kaina sai kace wata engine"


"Kai baki fahimceni bane,amma ai ba haka nake nufi ba,kin gane so nake ko da one round ne na k'ara kin gane ai"
Cike da duniyanci yayi maganar yana mata winking...


"Uhmmm!baka da dama idan kaso abu kamar d'a yaso fitowa daga cikin mahaifiyarsa,idan ban amince bama bazaka barni nayi bacci cikin kwanciyar hankali ba ya zanyi da kai"


Dariya suka saka duka kafin su lula duniyar masha'a kamar yadda suka saba....


《《》》


"Yawwa y'ata ta kaina gara da kika dawo kinga yamma tayi sosai dama kuma ke nake jiran ganin dawowarki maza yanzu mu wuce gida"


"To BABA barin sa kayan a can"


"Su kuma robobin ki kaisu ina?"


"Laaaa!bari kiga yadda zanyi zasu shiga gaba d'aya"


Da saurinta ta k'arasa bakin kuran robber's en ta hau d'ora wata kan wata a kwance,sannan ta shiga d'ora coolers a gurin data samar tana gamawa suka kama hanyar komawa gida,suna tafe kowa da tunanin da yake a zuciyarsa.....


Duk inda suka gifta kaga mutane na k'usk'us akan neman sanin alak'ar dake tsakaninsu sai dai duk gulmar tasu babu wanda yasan gaskiyar al'amarin......




"Kai KHUBRA aikin nan yayi miki yawa ki bari muyi tare"


"A'a wallahi BABA ki bari zanyi,yanzu zaki ga har na gama fa"


"Kawai dai dan babu yadda zanyi shi yasa zan bar miki aikin nan,Allah yayi miki albarka"


"Ameen ya Allah....Laaa!na manta BABA ban baki cinikin da nayi d'azuba"


'Dan murmushi BABA ZUWAIRA tayi bata ce komaiba,ta zauna cikin rumfa tana gyara kayan miyan da zatayi na abincin gobe..


Har ta gama wanke cooler's en ta kawo su cikin rumfa ta kife su duk dan ruwan ya fita daga ciki..
Kud'in ta fito da ta kawo shi gaban BABA ZUWAIRA ta ajiye,a hankali BABA ta d'ebi kud'in tana lissafawa,da murmushi a fuskanta ta kalli KHUBRA
"Masha Allah,gaskiya kinyi ciniki sosai Allah ya k'ara bud'awa"
Suka amsa da ameen...


"Yawwa KHUBRA abunda nake so dake gobe idan Allah ya kaimu zan siyo miki banki na k'asa da zan na sa miki kud'in a ciki kema"


Bata iya,magana ba sai murmushi da tayi,ita kam tana son matar ganin yadda ta d'auketa kamar ita ta haifeta,tana son matar saboda bata da hayaniya kamar sauran mutane........




《《》》




Tun da sanyin safiya ya gama shirinsa cikin k'ananan kaya,fuskansa yayi wani fresh sai dai rashin fara'a kamar kowane lokaci ya fito,har ya kai bakin k'ofa akayi magana da yasa shi juyawa


"YAYANAH barka da safiya"
Fuskanta da fara'a take maganar a hankali ya d'anyi murmushi ta gefe a hankali cikin nutsuwa ya amsa mata...


"YAYANAH fita za kayi da safen nan?"
Da kai ya amsa mata yana juyawa yaci gaba da tafiya
"Ammmm!BB da ka bari kaci wani abun kafin ka fita,na kammala dama yanzun nake shirin zuwa na kiraka muyi break"


Tsayawa yayi a inda yake,kome ya tuna kuma ya dawo,d'an murmushi sukayi suka nufi dinning tare...
"Woww!delicious CWEETY yaushe kika iya girki ne kam,nasan baku iya komai ba,ko dai wani yayi ba keba?"


"Laaaa!BB Allah ni kam na iya babu wanda ya taimakamin da kaina nayi...
Tun kafin kaci har ka fara santii"

"A'a fa CWEETY ni kam babu wani santii da nake,kawai dai na fad'a ne"


"Uhmm!to ai shi kenan idan ka ci sai kunnenka ya fice kan dad'i"


"Aaaa!ai kuwa na fasa kada ina ci kunnena ya fice kiyiwa mai ni asara,maza kici abunki ke d'aya"


Dariya sosai sukayi kamar ba sune suke cikin damuwa ba,sun maida damuwansu nasu su kad'ai yayinda akan fuskokinsu babu wani abu da ya wuce annuri duk dan kada kowa ya gane halin da suke ciki...


Da kyar ta dawo dashi saboda mik'ewa yayi zai tafi,dariya suka sa dukansu,haka suke break da annashuwa..

"Amm!BB kace wani abu d'azun d'an dad'a maimaitawa naji"


Kallonta yayi yana murmushi "Me na fad'a da kika manta"


"Ba kace baza kaciba ko dan kada ko ayiwa wa asara?"


Dariya sosai yayi saboda ya tuna me take nufin ya fad'a
"Nak'i wayon na fad'a miki kiji ki dinga fad'awa saura......."


"Laaaaaa!wallahi BB a'a nawa nakema da zan fara kula samari"


"Yawwa CWEETY gara ki tsaya kiyi karatunki dama na fad'i hakane dan na tsokaneki"


"To YAYANAH d'an fad'amin kaji"
Ta marairaice fuska kamar za tayi kuka...


Mik'ewa yayi ya soma tafiya,tana kallonsa har ya kai bakin k'ofan fita daga parlor sannan ya juyo yana murmushi
"Mai ni nace"
Yana fad'a ya fice da sauri har da dariya,nan ko ZUHRA ta zauna tana ta kwasar dariya,sai da tayi iya yinta sannan ta tsaigaita
"BB nah kenan wai mai shi"


Tana ta faman dariya ta ji maganar ASHNA "Ke kuma lafiyarki kike faman dariya kamar wata tab'ab'b'iya"


"Ke dallah dakata,kuma daga yau duk ranar da kika sake cemin tab'ab'b'iya wallahi saina nuna miki tab'in hankali,banza kawai"


"Dan uwarki dawa kike?"
ASHNA ta tambaya tana nufo inda ZUHRA take


"Dake nake sai me?"


Kamata ASHNA tayi da kokawa nan ko ZUHRA ta shammaceta ta timata da k'asa ta shiga jibgarta baji bare gani,sai da taji dukan ya isheta gashi ta kasa ture ZUHRA daga kantane yasa ta fasa ihu wanda ya janyo hankalin MAMA da sauri ta fito tana fad'in
"Me ya faru ne ASHNA kike mana ihu cikin gida da wannan safiyar?".......
Maganar ce ta mak'ale ganin ZUHRA a kan ASHNA tana jibga


"Ke baki da hankali

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads