Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 159513 words

Chapter 12 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1216

Ads at the middle of Article

anan ko sai jikinki ya gaya miki?''
Yi yayi uwa zai tashi,aiko ba shiri ASHNAR ta kwasa a guje sai bedroom nata,bata sake fitowa ba,ta ci gaba da zama ciki....


FATAHIYYA ce ta fito idonta uwa na aljanu duk ya sha hauka,shi da ya kalletama dariya taso bashi,amma ya doje yak'i yi
''Ke je ki kiramun AUNTYNKI''


''YAYA wacce AUNTYN?''


kanta a k'asa uwa munafuka tayi tambayar,d'agowa yayi ya kalleta
''Wacce kika san ina nufi''


Ya bata amsa a d'an hasale,ba shiri ta fice dan tasan bata cikin gidan kam,d'akin KHUBRA ta nufa direct,sun rashe saman katifa sunata faman dariya ta shigo ,ko kallon arzik'i bata musuba su duka ta furta
''Ki zo inji YAYA''
Daga haka ta juya,ba tare da ta jira amsar ta ba...

"To barin je inji me kuma BB zai ce yanzun,yaukam ina shan kira gurinsa''

Kai KHUBRA ta sunkuyar k'asa dan yanzun kam bata san me zata yiba wanda zai ceceta don ma kada ZUHRA tace ta zo su tafi tare.....
Cikin ikon Allah da sauri ZUHRAN ta fita bata ko neme ta kan su tafi tare ba....
Godiya tayiwa Allah da hakan ta faru,aiko ta d'auko littafinta na da take rubutu cikinsa,nan ta shiga (bahas) kan girkin da za tayi yau.....
ZUHRA ce ta shigo tana tsalle,a hankali ta janye littafin daga kan fuskanta tana kallonta...


''Maza ta so sis,yau akwai aiki a gabanmu,dan BB ya sanarmin zaiyi bak'o yau kam,so yanzun ya kamata musan abun yi''


''Tohh!muje kada mu b'ata lokaci''
Da sauri ta zari hijab enta,ita kuma ZUHRA ta kama hannunta suka fice suna rufe d'akin....


A kitchen suka yada zango,nan kuwa suka kachame a kitchen en sai aiki suke suna hirarsu duk da mafi yawanci surutun na ZUHRA ne....
Misalin k'arfe 1:30 suka jiyo maganansu k'asa²,da yake lokacin sun kusa kammalawa,aiko nan suka dad'a bada himma......


Sun d'an jima da shigowa sannan HAJIYA MURJA da muk'arrabanta suka fito,ASHNA tana ganin bak'on aka chanza tafiya sai kwarkwasa take,aiko FATAHIYYA ma na ganin haka itama ta shiga gyara tafiyarta,ko wajen magana ma sai ta sirance murya tana gaida shi.....


A hankali ya d'ago yana kallonsu,gaye ajin farko a kyau,iya kwaliyya,tsafta,gayu,ya had'e cikin wasu k'ananan kaya sam banyi tunanin yana jin yaren da suka masa ba,take ko ya musu wani kallon k'asan ido yana amsawa da k'yar....
Duk bidirin da ake babu ZUHRA a gurin,suna can suna fama a kitchen....
Sun kammala komai setting teble kad'ai ya rage musu,aiko nan ZUHRA ta hau tsokanar KHUBRA kan sai dai ta fita da kayan,dan ta san da wuya ta fitan,coz ta fuskanci tun da YAYAN nata ya dawo bata tab'a gigin barin sun had'uba,ko mene hakan ke nufi ohhoo???....


Da kyar ZUHRAN ta soma kwasar kayan tana fita da shi dan tasan kam KHUBRAN ba zataba,tun da ta jiyo muryansu ASHNA da MAMA....
Drink en da take had'awa ne kad'ai ya rage basu fita da shiba,jin parlorn shiru yasa KHUBRAN zura hijab enta ta nufi hanyan fita a tunaninta tana ajiyewa sai tayi waje ba tare da sun had'u da kowa ba....


Sam bata yi tsammaniba,kanta a k'asa take tafiya har dinning arean,k'asa² taji magana wanda yasa ta d'ago a d'an tsorace,suna zaune dukansu a gurin wata harara HAJIYAN ta aiko mata da yasa ta dad'a sadda kanta k'asa still tayi a gurin har sai da HAJIYAN tayi magana....
''Me kike jira a nan gurin,kina b'atawa mutane lokaci''


A hankali ta ci gaba da tafiya har dinning en,sai dad'a janyo hijab enta take tana rufe fuskanta....
Ajiyewa tayi zata bar gurin,HAJIYAN ta sake dakatar da ita
''Waye zaiyi servings da kike k'ok'arin barin gurin?''
Dawowa tayi jikinta a sanyaye jikinta sai rawa yake,plate na farko da tayi serving ta mik'a gaban HAJIYAN saboda tafi kusa da HAJIYAN...


Duk su biyun sun tsaya kallonta yanda ta wani k'udundune kanta cikin hijab...


Shi dai BB tab'e baki yayi yana pressing wayansa,shima dai abokin nasa bakin ya tab'e ya koma yana duba wrist watch en sa....


Ta side ensu ta zagayo ta shiga serving nasu,tsaf ta kammala ta janyo cup's ta zuba drink ciki....


Hannu ya mik'a zai d'auka,ita kuma tana k'ok'arin ajiye d'ayan na hannunta,hannunsa ne ya tankwab'e nata aiko take suka zube masa a jiki,cikin sauri ya furta
''Ya salaam!''


Da saurin itama ta soma bashi hak'uri,still hijab enta na a yanda ta sashi,sweetest voice nata shi ya dokesu su biyun suka bita da kallo,ko kafin suyi aune tuni suka tsinkayo muryan HAJIYA MURJA tana fad'a cikin kaushin murya....


''Amma wannan kwoi sha³ kin rufe fuska dama uwa wata munafuka taya zaki san me kike?''


Dukkansu basu ji dad'in abunda tayi ba,hayaniyan da ZUHRA ta jiyo ne yasa ta fito da sauri daga kitchen,lokacin da ta k'araso gurin a lokacin ita kuma KHUBRA ta juya tana kuka ta nufi hanyan fita ko gabanta bata iya gani sosai....


*KHUBRA!!!*
ZUHRA ta shiga kiranta da d'an k'arfi,a tare suka d'ago suna masu bin hanyan da tabi da kallo,basu ga kowa ba lokacin ne kuma ZUHRAN ta bita,hakan ya tabbatar musu da sunan wacce ta fita kenan......
Har suka gama babu wanda ya sake magana,sun d'an jima suna hira kafin ya ta shi tafiya....


BB ne ya kira HAJIYANSU,sallama yayi mata yana fad'in zai tafi sai an kwana biyu kuma.....
''Toh *KHALEEL* ka gaida gida da HAJIYAN ka dan Allah,kace mata zan shigo cikin wani satin''
Amsa mata yayi,suka nufi hanyan fita.....


《《》》


Tun da ta fita bata tsaya ko inaba sai guarding a can taja breke aiko take ZUHRA ta k'araso nan ta rungumeta tana bata hak'uri,har tayi shiru,nan suka ci gaba da firansu....


Dariya KHUBRA take kan labarin da ZUHRA ke bata,aiko me za tayi banda dariya,nan ko ZUHRAN ta shiga tsokanarta "Mai kuka tana dariya........ai mata d'an kwad'on daddawa",guje² suka hau yi cikin guarding en,sam ta kasa kamata haka sukayi ta yi har sai da suka fito waje,kwata² basu kula da fitowan mutum ba sai gudun suke lokacin KHUBRA ta zo giftawa sukayi karo,take gefen hijab enta tayi ta tafi tana shirin fad'uwa.................






*_~TEAM KHUBRA~_*






*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*7/ʍɑվ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
_Gaisuwa tare da fatan alkhairi gareku y'an uwa,masoya *KHADIJA IBRAHIM YUSUF (KHADEEY)* da bestei en ki *NUSAIBA IBRAHIM ISSAH (NUSEEY)* ,Allah ya k'ara muku k'aunar juna,Allah kuma ya k'arawa sis *KHADEEY* lafiya mai d'orewa,tabbas *SMASHER* taga sak'onku,ina godiya wacce bata da iyaka,Y'an group en *SMASHER ND HUBBEEY* suna godiya,Allah ya bar zumunci.._
*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*2⃣3⃣*








*J*ikinta gaba d'aya banda rawa babu abunda yake,yayin da idanuwanta ke a kulle coz ta gama saddak'arwa sai ta sha k'asa.....
Ita kanta ZUHRA sai da ta tsorata bama kamar kallon da BB yake watso mata,sukam sun k'ame uwa poster,shi bai saketa ba,ita kuma bata yi k'ok'arin kwacewaba,jin abu ya tare ta yasa ta soma bud'e ido a hankali.....
KHALEEL dake gefensa time en sun jero ya juya ya kalli BB dake rik'e da ita.......


Gaba d'aya idanunsa na kanta,coz babu abunda ya b'uyan masa na daga fuskanta,kallonta suke like no other,wanda yanda take bud'e idanun tama ya bada wani style na daban....
Arba da tayi da fuskan mutum shi yasa tayi k'ok'arin mik'ewa daga rik'on da yayi mata,sassauta mata rik'on yayi ta mik'e da kanta....
Tafiya suka ci gaba da yi suna masu waiwayowa dukansu suka sake binta da kallo,kowa da abunda yake sak'awa a ransa....


BB ne ya fara janye eyes ensa daga kanta,zuciyarsa fal tunanin
''Ina Sis ta samo wannan shuwa-arab en?''
Dan kam shi dai ya tabbatar sai an tona kafin a samo mai kyau irin nata,dan shi kam a cewarsa wannan batayi ruwa da nan ba sai dai ko UNITED ARAB.....


Shi ko KHALEEL zuciyarsa taff take da tambayoyi,wanda yake jin ba zai iya barin ya tafi da su ba tare da ya amayarba...
BB ya kallah dake gefensa yana fad'in
*KHALEED!*
''yaushe kukayi bak'uwa,dama kuna da y'an uwa wata k'asar ban tab'ajin ko a labariba?''


Rasa abun cewa *KHALEED* en yayi wato *(BBN ZUHRA)* ,yana can kogin tunani,bai sanma *KHALEEL* na masa magana ba,har sai da ya dafa shi...
''Wannan k'anwace a gurinka ba?''


'Dan murmushi yayi yana nodding kansa.....


Rasa abun fad'a KHALEEL en yayi,kawai sai ya hak'ura yayi shiru,amma a zuciyarsa yana godiya ga Allah da KHUBRAN ta kasance k'anwa a gurinsa kuma y'ar gidan,duk da dai bai san ya alak'arsu take ba....
Haka suka yi sallama ya shige motor ensa ya fice daga gidan suna waving wa junansu....



Tun da ta samu ya saketa,ta sunkuyar da kai k'asa ganin irin kallon da suke mata,bata sake d'agowaba har sai da suka bar wajen tukun,shima tsokanarta ZUHRA take shi ne dalilin da yasa ta d'ago,sai da ta gama k'arewa gurin kallo tukun suka sake d'orawa daga inda suka tsaya.......
''Yarinya kinga kallon da mazaje suke miki kuwa,Allah na fad'a miki kina da kyau kink'i yarda,soon zaki tabbatar''
Tana gama fad'a ta shek'a a guje,nan ko KHUBRAN ta bita (niko cewa nayi baki daddaraba kenan).....


Dan kansu suka zube cikin guarding suna dariya,ba kuma su fasa tsokanar junanba.....




Tun da ya samu KHALEEL ya tafi,ya juyo kallon sides na gidan ya shiga yi ko zai sake arba da fuskanta,amma kamar aljana,haka yaita kalle² a gidan ko mai kama da ita bai gani ta b'illoba bare itan......
Hak'ura yayi ya shige bedroom ensa,kwanciya yayi fuskanta ta shiga yi masa gizo,shi kad'ai sai dai yayi murmushi,haka yaita juyi saman bed (Uhmnmm!BB ayi a hankali kar a fad'o k'asafa inji HUBBEEY☺)......




《《》》


Driving yake amma tunani duk ya dame shi,shi kad'ai yake magana a motern
''Gaskiya zan sanarma UMMI gara ta nemomin mafita,tun kafin wani ya rigani gara tayi magana''
Wannan tunanin da yayi shi ya bashi nutsuwa da murnansa ya isa gida......


Ko bari ya isa perking lot baiba a haraban gidan ya percker,da d'an saurinsa ya fito ya nufi cikin gidan....
Sai da ya gama bulayinsa a parlor zuwa kitchen amma baiga UMMIN nasa ba,d'akinta ya nufa direct,aiko nan ya tarar da ita tana ta duba closet enta kayan ciki duk ta fiddo shi...
Sallama yayi mata,jin maganar KHALEEL en ne yasa ta juyo da murmushi a fuskarta take kallonsa
''A'a SON har ka dawo?''


Kansa ya d'an shafa yana murmushin shima
''Ehh wollah na dawo,duk suna gaishe kima''


''Aiko ina amsawa,ka baro su lafiya?''


''Lafiya k'alau''


Har yayi shiru kuma,can dai ya ga hakan ba zai fishshe shi ba,aiko tuni ya bud'e baki
''Ammmm!UMMI dama wata magana nazo muyi,amma na ga kina aiki''


''Wace magana ce SON?''


Nan kuma ya tsaya kame²,hakan da yake yi ne yasa ta bar abunda take,kusa da shi ta dawo ta zauna tana fuskantarsa
''Ka ce magana kuma kayi shiru,akwai abunda yake damunka ne?''


K'eyansa ya sosa kafin ya bud'e baki,uwa wanda maganarma take masa wahala
''UMMI dama fa''......


Sai kuma yayi shiru,kallonsa ta tsaya yi
''Yau naga ikon Allah,SON yau kuma kunyata kake jine ko me?''


''No UMMI kawai dai ban san mesa na kasa fad'a ba kuma''


''To sai ka ficemin anan tunda ba fad'a za kayi ba''


''A'a UMMI zan fad'a wallahi''


''Oyahh!to ina saurarenka''


Sai da ya sake yin jimmm kafin ya soma magana
''Ammm!UMMI dama fa wata yarinya na gani ne,to kuma''....
Ya sake yin shiru yana d'an sosa k'eyansa....
'Dan murmushi tayi,tana kallonsa
''Uhmm!SON kenan wato kan maganar nan ne kake jin kunyata kuma yau?''
Kwanciya yayi kan cinyanta,yana b'oye fuska
''Ohh!ni FATIMA yau na ga abunda ya isheni mamaki''


''Uhmmm!nifa UMMI so nake kiyi magana da ABBA tun kafin lokaci ya k'ure,kada wani ya''.....

K'eyarsa ta doke,aiko ba shiri ya hantsilo k'asa yana dafe kai,da d'an murmushi ya nufi hanya zai fice
''Kai dawo nan,baka ma fad'amin a inda ka ga yarinyarba''


''UMMI a gidansu KHALEED fa na ganta''

''Jimin ja'iri cikin y'an gidan waye baka sani ba,da zaka bani zance a rufe''


''No UMMI bafa cikin wad'annan fitsararrun bane,wannan daban take,Allah ko UMMI saima kin ganta''
''Idan ba suba to wace kuma take zaune gidan?''


''Ni dai yacemin sister ensu ce itama''


''Ok duk koma mene ne zanji bakin HAJIYA MURJA''


''Yawwa UMMINA na gode irin sosai ennan''
Ya fad'a yana dunk'ule hannu,kallon da ta masa ne yasa ya fice babu shiri yana dariya....
Kai ta girgiza itama tana jinjina al'amarin d'an nata.....


《《》》


Wuni guda yana cikin d'akin sallah kad'ai ke fito da shi,bayan haka ko sai dai ko idan tunani ya dame shi ya fito,haka zai ta zagaye a cikin gidan tun daga kitchen har harabar gidan amma sam ya neme ta ya rasa,shi kad'ai ya soma magana da kansa
''Anya kuwa wannan mutum ce? to amma da aljana ce ai baran ganta tare da sis ena ba,to wai nikam me yasa ma na damu da son ganinta?''
Shi kad'ai yaita fama da zancensa,sis en nasa ma ya rasa ina ta shige da ya mata tambayoyi kan yarinyar da ya gansu tare....
Hak'uri ya bama kansa ya koma parlor ya zauna,amma sam ya gagara samun sukuni,haka ya koma bedroom ya kwanta....




《《》》


Kamar kullum yauma haka suka yi zamansu cikin guarding en,lokacin da aka kira sallan asr da gudu kamar yara sa'annin HANEEF haka suka shiga tsere zuwa bakin tap en,kafin suyi alwalanma sai da suka yita watsawa juna ruwa,da kyar suka gama suka bar gurin,a d'akinta suka yi sallah,sannan suka fito,ita KHUBRA tana haramar zuwa had'a dinner,ita kuma ZUHRA zata shirya kafin malaminsu ya k'araso,har kitchen ta raka KHUBRAN ko kafin ta tafi sai da ta taimaka mata da wasu ayyukan kafin ta mata sallama ta fice....


Aikinta taci gaba da yi ita d'aya,da yake ma ta saba da aikin,nan da nan ta kusa kammalawa......




《《》》

Wayanta dake kuka ta kalla,duk kuwa da yadda take kusa da wayan sai da ta lek'a kafin ta d'auka daf da zata tsinke,sunan HAJIYA FATEE data gani shi yasa ta d'auka tana dariya,bayan sun gaisa HAJIYA MURJA ke sanar da UMMIN KHALEEL
''HAJIYA ina fatan sak'ona ya iskoki?''


''Sak'o kuma na me?''


''Na ce a sanar miki zuwa wani satin zan shigo in Allah ya kaimu''


''Tohh Allah kuwa ya kawo ki lafiya,ammm!HAJIYA dama d'anki ne ya zo min da wani labari''


''Labari kan me kenan?''
Cikin son jin zancen HAJIYA MURJA tayi maganar
''Ammm!dama cemin yayi ya ga yarinya a gidanki,to shi ne daga zuwansa yake sanarmin kan a nema masa izinin gurinku shi dai yana so''


''Aarrhh!ai abu yayi kyau,amma baki bambancemin wacce daga ciki yake nufi ba ASHNA ko ZUHRA yake nufi?''


''Gaskiya yacemin duk basu bane,amma dai ya tabbatarmin a gidanki yarinyar take''


Take ko zuciyar HAJIYA MURJA ta soma skipping,ranta duk ya b'aci da wannan maganar,daga jin wannan zancen babu alkhairi cikinsa,dan ko bata raba d'ayan biyu wannan shegiyar y'ar mai kama da aljanu yake so...
Zuciyarta ta danne kafin cikin kissa ta furta
''Aiihhhooo!KHUBRA yake nufi ba...........Ai ko tabbas gidana take,sai dai wani hanzari ba guduba,gaskiya HAJIYA kiyi hak'uri da abunda za kiji yanzun..
Ita dai wannan yarinya da ake magana kanta babu wata alak'a tsakaninmu da ita face matsayinta na 'YAR AIKI,inama laifin ya duba cikin k'annen nasa ko Allah zai sa a dace''


Ita dai HAJIYA FATEE shiru tayi tana mamakin lamarin,a zuciyarta ko fad'i take
''Aiko bari SON en ya dawo,sam baza ta sab'uba(wai akace bindiga a ruwa)''........


Haka sukayi sallama,take bata jiraba ta dokawa KHALEEL waya,katsewa yayi ya kirata coz dama al'adarsa ce hakan...
Bata jira tajima me zai ceba ta hau fad'in
''Maza kazo ina son ganinka''
Tana gama fad'in uzurinta ta katse kiran,sai safa da marwa take a parlor ita kad'ai....


Shigowansa parlorn ya tarar da ita a tsaye,hankalinsa har ya soma tashi ganin yanayinta...
''UMMI lafiya naga hankalinki a tashe?''


''Dakata SON'' ta d'aga masa hannu
''Dama yarinyar da ka dameni akanta *HOUSEMAID* ce?''


''UMMI amma fa''...........


''Bana buk'atar jin komai daga bakinka,magana d'aya zan fad'a maka ka shafe babin wannan maganar a rayuwarka,ko dai cikin k'annenka ka duba wata ko kuma ka nemo wata,amma banda wannan''


INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Yake maimaitawa,kafin ya kalli

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads