Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 159513 words

Chapter 6 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1214

Ads at the middle of Article

kulawarki a gareni''..


Ita kam kukanta take babu ji...


Tun yana rarrashinta har abun ya soma bashi haushi...


Mik'ewa yayi a fusace yana shirin barin gurin...
Da sauri ta rik'o hannunsa tana girgiza masa kai...


Fisgewa yayi yana ci gaba da jaa baya..
Cikin wani irin murya ya soma fad'in
''Idan har na tafi daga gareki a yau ba zan sake ko da waiwayowaba...
Wancan lokacin na juyo zuwa gareki,amma wannan karon kada kiyi tsammanin sake ganina''..


''Dan Allah kayi hak'uri ka saurareni''....


Ci gaba yayi da tafiya ba tare da ya saurareta ba bare ya ji me zata fad'a....


************


Cikin wani irin firgici ta farka daga nannauyan baccin da yayi gaba da ita...
Dafe saitin zuciyanta tayi saboda wani irin matsanancin bugu da yake mata...


Tsoro duk ya gama bayyana a tare da ita....
Ta kasa fuskantar komai da ya danganci mafarkin nata,hatta kuwa da fuskansa da ta gani,ta kasa tunawa...

Tashi tayi da niyyan yin alwala,sai dai abunda ta gani ya sata fara kuka kamar wadda ake fitarma da rai....




***********




Duk son duniya irinta LADIYO yau itace taci k'anzo abunda bata tab'a tsammaniba ko da a mafarki...


Gidan ta shiga bincikewa ko zata samu d'an wani abun da zata ci da rana..
Tunda ta fuskanci MALAM BUBA baya gidan yau kam,kuma zaiyi wuya ta ganshi....


Kaf ta gama bincika ko ina amma ko k'wayar shinkafa bata samoba...


Haka ta dawo ta zauna a rumfa,kamar wata mutuniyar Allah....




***********
'Bangaren MA'U kuwa yini tayi neman abun duniya,sai sake cigiyan gidajen aiki take dan ita har ga Allah wancan ya mata arha da yawa...


Shi yasa ta yanke shawaran sake neman wani ko za a dace,amma ina haka ta yini tana yawo a gari....


***********
Duk da bawai yau ta fara ganin hakan a tare da ita ba,haka ta zauna tana kukan...
Coz ta san halin MA'U za ta iya cewa yawon iskanci taje....


Kukan da tagani ba shi ne mafita a gareta ba yasa ta bawa zuciyanta hak'uri,ta mik'e....


Cikin kayanta ta laluba nan ta binciko y'an pieces enta da take amfani da shi tunda bata saba da pad ba....


Tsaf ta gyara jikinta ta dawo ta kwanta kamar ba ita ba.....


***********

Sai bayan Maghreb sannan MA'U ta dawo a matuk'ar gajiye kamar wacce akawa duka haka ta shigo tana raba k'afa..


Da yake yawo ne kuma ita tasa kanta,duk da k'afar da take fama dashi,hakan bai hana mata zuwa yawoba.....


************


Shi kuwa ABBAN KHUBRA tunda ya fice daga gidan yaji bazai iya dawowa gidan ba...
Haka yayi ta zamansa a waje,da yaje kasuwa ma k'odagonsa,bayan ya tashi k'in komawa yayi...


sai dare ya koma gidan,shima sai da ya kintaci lokacin tayi bacci sannan ya nufo gidan.....








*_~#TEAM KHUBRA.~_*






*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠



*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*


🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹













*©®2018*
*13/ąpril,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_


🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~__________________________~*
*ADDU'AH YAYIN FITA DAGA GIDA.*


_BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH WALA-HAULA WALA-QUWWATA ILLAHBILLAH._


_ALLAHUMMA INNIY A'UZHUBIKA AN-ADILLAH,AU'UDALLAH,AU'AZILLAH,AU'UZALLAH,AU'AZLIMA,AU'UZLIMA,AU'AJHALA,AU'YUJHALA ALAYYA.._


*ADDU'AH YAYIN SHIGA GIDA.*
_BISMILLAHI WALAJNA,WA-BISMILLAHI KHARAJNA, WA-ALALLAHI RABBANA TAWAKKALNA._



*_~#HISNUL_MUSLIM.~_*

*~__________________________~*


*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._


*~__________________________~*






*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*1⃣3⃣*







*T*ana shiga d'akin tayi shirim akan gadon tamkar kayan wanki,irin su MA'U irin matan nan ne da Sam basu da fasali a tsarinsu, bayaga d'an banzan son jiki da take da shi....
Kamar wacce aka mintsina haka tayi saurin mik'ewa tsaye tana raba ido...
Wani durowa ta nufa,daga jikinsa kuma cikin wani d'an sak'o,ta mik'a hannu,poly bag en dake wajen ta janyo ta hau bud'e cikinta,tana fito da kayan dake k'unshe a ciki...
Suphagetti ne da d'an dama dan idan basu fi 10 ba to zasu iya kaiwa hakan...
K'waya d'aya ta d'auka ta nufi hanyan fita daga d'akin,a zuciyanta kuma tana sak'e²,har ta k'idasa ficewa...


*********


Tana zaune ta idar da sallah ta rasa me ke mata dad'i a duniyarta,tunaninma yau kam tama kasa yinsa,duk jinta take kamar wata daban...
Hankalinta gaba d'aya baya tare da ita a wannnan lokaci,tayi zurfi wajen tunaninta,tana son tuno wane garima dangin mahaifiyarta suke?

Shigowar MA'U d'akin shi ya sata dawowa duniyarta babu shiri,cikin wani irin kallo ta jefeta da shi tana mai mik'o mata suphagettin dake hannunta,ba ko bayani ta sa kai ta fice..
Ita kam KHUBRA da ido ta bita dan zuwa yanzun ko dai bata gama sanin halin MA'U ba duka to tabbas ta san mafi yawan kaso daga halayentan..
Cikin sanyinta ta mik'e had'e da zare hijab en dake jikinta,ta fice tana sak'a da warwara...


Har ta kammala bata sake jin ko da motsin MA'U ba,duk da hakan ba bak'on al'amari bane a gurinta,amma sai duk taji kewa na damunta,na rashin wani d'an adam...
Juyewa tayi ta d'auka ta nufi cikin d'akin nata,tana ajiyewa ta juya ta fice...


Hakimar tana kallonta amma ko sannu bare ta sa ran jin wata kalma mai dad'i,haka ta banzatar da ita,mik'ewa tayi ta janyo plask en..
Sai da ta gama k'oshi sannan ta shiga rafka mata kira...
Cikin sauri ta shigo tana sunkuyar da kanta k'asa...


Kwanon ta nuna mata,bata tsaya b'ata lokaciba ta sungumeshi tayi waje,sanin ko ta ce bata ci,kanta zata zalunta...


Sai da ta tabbatar ta tsaftace duk wani abu da tasan tayi amfani da shi kafin ta nufi d'akin shirgi da a yanzun ya zama nata...
Kwanciya tayi cike da son ganin mutumin ta na mafarki,tana wannan tunani har bata san lokacin da bacci yayi gaba da itaba...


**********


Ko da MALAM BUBA ya shiga gidan direct d'akinsa ya nufa yana shiga kamar jiya da k'yar ya iya k'arasawa zuwa shimfid'arsa wanda baima tsaya tunanin ko lafiyaba ya kifa kamar wanda aka hankad'a,take wani nannauyan bacci yayi gaba da shi...




*********


MA'U ce zaune cikin d'akinta,ta rafka tagumi,tunaninta ta yaya zata samu hanyar da kud'i zasu dinga shigo mata,dan kam wannan rayuwa lamarin yana damunta...
Banda sak'a da warwara babu abunda take,zuciyoyinta biyu kowanne tana kawo mata shawaran da a ganinsu shi ne masalaha....


Ta tabbata idan akace zata ta'allak'a ne akan d'an abunda KHUBRA zata samu to tabbas tana cikin wahala,coz ta san halin yayarta da masifar son kud'i _(kunjifa wai kura ce za tace da kare maye)..._


Kafin wani lokaci mai tsayi zuciyarta ta gama rinjayarta,kwanciya tayi tana mai farin cikin samun mafita....


*IN THE MORNING* *******


KHUBRA dake tsaka da shara,ta d'aga kai ta kalli gurin da ta jiyo motsi,tayi matuk'ar mamaki da ta ganta a lokacin da batayi tsammaniba...
''Shin dama tana iya tashi da wuri haka,amma kullum sai ibada ta wuceta?''...


Haka tayi ta tunanin abunda sam bashida wata fa'ida a gareta...
Tana nan tana tunane² har bata san lokacin da MA'U ta gama shiryawaba,sai ganinta tayi ta fito hannunta rik'e da y'ar jakarta wacce akewa lak'abi da *_(JIK'ATA GUMIN HAMMATA)_*...


Hannunta rik'e da leda ta fito tana jaan k'afarta da har yau bata samu an gyaraba...
Naira #50 ta mik'a mata ''ki siyo garin kwaki''...
Daga haka ta wuce ta fice,har tayi nisa ta dawo,KHUBRA dake sunkuye har tsoro abun ya bata dan bata ga lokacin da ta dawo ba,sai magana taji a bayanta....


_''Idan kinga ban dawo da wuri ba kina iya rufe gidan''_
Haka ta shud'a tayi gaba....


********
Ko da ya farka da safe lokacin gari har ya gama haske,rana tana shirin mamaye sararin samaniya...
Istighfari ya shiga yi,coz har aka idar da sallah bai san anayi ba,abunda a iya tsawon rayuwarsa yau ne rana ta farko da yayi rashin sallah a jam'i...
Da matuk'ar k'unar zuciya ya mik'e ya fita don d'auro alwala...


A tsakar gida ya iske LADIYO ta fito banda susar jikinta babu abunda take,kamar wadda tayi wanka da _karara..._
Ta gabanta ya zo zai wuce,cikin rud'ewa dan tasan zai mata fad'an rashin sallah a kan lokaci ne,ta hau fad'in
''MALAM barka da tashi''
Ba tare da tayi tsammanin zai amsa ba...


Yana washe baki ya juyo yana kallonta ''Arrrhhh! hajajju LADIYO an tashi lafiya?''...


Da mugun mamaki ta d'ago tana binsa da ido,sai dai tana yin wani tunani kuma ta waske tana murmushin mugunta _(hak'ansu ya cinma ruwa)_.......








_#PLEASE FAN'S KUMIN UZURI DAN ALLAH NA RASHIN POSTING,UZURI NE YA MIN YAWA,DA YASA KO ONLINE BA NAYI,YAU KUMA NASO YIN TYPING EN BUH CIWON KAI YA HANA NI,IN SHA ALLAH ZA KUJINI ZUWA GOBE,DA YARDAR ALLAH..._








*_~#TEAM KHUBRA.~_*








*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
💠💠💠💠💠



*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹












*©®2018*
*16/ąpril,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._


*~________________________~*


*ADDU'AR TAFIYA MASALLACI.*


_ALLAHUMMAJ'AL FIY K'ALBIY NURAN,WAFIY LISANIY NURAN,WAFIY SAM'IY NURAN,WAFIY BASARIY NURAN,WAMIN FAUQIY NURAN,WAMIN TAHTIY NURAN,WA-ANYAMINIY NURAN,WA-ANSHIMALIY NURAN,WAMIN AMAMIY NURAN,WAMIN KHALFIY NURAN,WAJA'AL FIY NAFSIY NURAN,WA-A'AZIMLIY NURAN,WA-AZZIMLIY NURAN,WAJA'ALLIY NURAN,WAJA'ALNIY NURAN,ALLAHUMMA A'A'DINIY NURAN,WAJA'AL FIY ASABIY NURAN,WAFIY LAHAMIY NURAN,WAFIY DAMIY NURAN,WAFIY SHA'ARIY NURAN,WAFIY BASHARIY NURAN,ALLAHUMMAJ'ALLIY NURAN FIY K'ABARIY,WA-NURAN FIY IZAMIY,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAHABLIY NURAN._


*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*


*~________________________~*


*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*


_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._


*~__________________________~*






*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*1⃣4⃣*







*B*akinta ta wage mai kama da k'ofar gari,hak'oranta kamar an shafa musu d'orawa...

''Lafiya k'alau MALAM''
Tana yi tana kwarkwasa kamar wata tsohuwar y'ar duniya...


Shi dai binta yake da kallo kamar wani wawa,haka ya sungumi buta yayi band'aki..
Ganin haka yasa itama LADIYON ta nemi guri ta k'ame kamar soja tana jiran ganin me zai kuma biyo baya...


Da mamaki take kallonsa yana alwala,mutumin da sallah bata wuce shi a jam'i amma shi ne zai yi sallah da wannan ranar...


Jikinta taja ta shiga band'aki,har lokacin bai bar gurin ba,itama tayi alwala...
Tana idarwa zata shiga d'aki taga ya biyo bayanta,da mamaki ta sake kallonsa,har ya shige d'akintan,ita kuma ta dafa masa baya...


A kan abun sallah ta tarar da shi yana washe mata baki yace

''Yi sauri kisa hijab muyi jam'i''


Ita dai ido ne nata,haka ya jasu sallan har suka idar...

After sun idar,ya shiga bata hak'urin abubuwan da yake mata,kamar wata uwarsa harda saka guiwoyinsa a k'asa....


Su LADIYO an samu abunda ake so,amma can k'asan zuciyanta tunani take akan yau shene shigowarsa ta k'arshe cikin d'akin nata,sai dai ta kasa tunawa...


Jin da tayi ana shafa jikinta,shi ya dawo da ita duniyarta..
Kallonsa tayi cikin mamakin hakan,ta kasa cewa komi...


''Haba uwar gidan MALAM BUBA kice wani abu mana kinyi shiru''
Ita dai binsa take da kallo,shi kuma sai dad'a shige mata yake...
Su LADIYO da jin haka,bata san lokacin da itama ta biyewa MALAM en suka ci gaba da shafar juna,har zuwa MALAM ya samu damar da yake nema a agurinta na cilla k'wallonsa a kwando....
Ihuuu LADIYO take tana fad'in
''Aradu MALAM kasan takan wanga harka,wayyoo dad'i,MALAM ci gaba''...


Hannu yasa ya rufe mata baki,saboda surutun nata ya soma bashi haushi..
Ita kuwa sai dad'a mak'alo shi take,kamar wata k'wad'uwa.... 😂




********


Duk wani aiki da za tayi sai da ta kammala shi sannan ta saka hijab enta..
Fitowa tayi daga gidan tana tafe cikin nutsuwa kamar yanda ta saba,haka har ta isa shagon,ta mik'a kud'in ya bata abunda zai bata,ta sake kamo hanya ta dawo...
Ko da ta dawo gidan babu ruwa sosai,hakan yasa ta fita da bocket tayi ta faman jido ruwa a mak'otansu har sai da ta cika komai dake gurin...
K'ofar gidan ta je ta kulle ta dawo,d'akin MA'U ta shiga ta kwanta a saman gadon MA'U tayi d'ai²,take kuwa baccin wahala ya d'auketa....




*********


Sai bayan komai ya lafa sannan LADIYO ta cika MALAM BUBA ta koma gefe ta kwanta...


Shi kuwa MALAM sai bayan da ya gama biyan buk'atarsa sannan ya tuna inda yake da kuma k'yamar kusantar LADIYON a yanda take,riga kad'ai ya saka ya nufi band'aki yayi wankan tsarki..
'Dakin ya sake dawowa,bai san dalilin da yasa yake jinsa wani iri ba,kamar mara lafiya...



Kud'i ya zaro ya mik'a mata kan ta samu abinda za ta dafa a gidan,karb'a tayi,shi kuma ya juya ya fice daga gidan....




********


Baccinta take ba tare da tunanin komai ba...
Tayi nisa a baccin,ta hangoshi kamar kowane lokaci cikin fararen tufafi,binsa take amma ta kasa cin masa,hakan ya sa ta durk'ushe tana kuka mai tsanani..


Kiransa take HAYATEEY,amma ko waigowa baiba bare ya kalleta....


Hakan da yayi mata shi yasa ta fasa k'ara ta zube a gurin sumammiya....




**********


Can cikin garin SUMAILA cikin wani k'auye ta sauka ta ci gaba da ratsa hanya har ta billo wani farfajiyar guri...
Gidane guda d'aya wanda ba shi da mak'ota ko k'waya...
Tunkarar gidan tayi ta shiga k'wank'wasawa ganinsa a kulle....


Bud'e mata wata y'ar yarinya tayi,tana mai bata hanya...
Murmushi tayiwa yarinyar ta bita suka shiga ciki...
A wani d'aki aka sauketa ta nemi guri ta zauna tana jiran fitowar MALAMIN...


Sai da ta shafe tsawon awanni 4 sannan mutumin ya shigo,daga shi sai dogon riga,duk ta k'udundune ga

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads