Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 159513 words

Chapter 31 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1234

Ads at the middle of Article

b'oyuwa saboda kowa yasan yadda suke da HAJIYA LAURA duk wani tak'ama da take yi da bazar HAJIYA MURJA take taka rawa,lallai ko yau kam HAJIYA LAURA kin d'ebo ruwan dafa kanki......


《《》》


Tun bayan da MALAM BUBA ya gama kora mata jawabi take tsaye a nan inda ya barta k'afafunta duk sun mata nauyi wanda ta gagara d'agasu,a gurin ta zube hannunta a ka ta shiga rera kuka babu ji bare gani...


Haka MALAM BUBA ya shige d'akinsa nan ko ya shiga jero nafilfili yana dad'a rok'on Allah yafiya bisa kuskuren da ya tafka a baya,sai da dare yayi nisa sosai sannan yayi addu'a ya kuma kwanta yana mai dad'a yin tasbihi ga ubangijin sammai da k'assai.



Kwanaki sun dad'a jaa inda a kullum tashin hankalin LADIYO yake dad'a k'aruwa daga lokacin da aka ce mata dare ya kawo kai,zuwa yau kuma babu wani labari dangane da MA'U bare ita kanta KHUBRA da ABBA'NTA yasa LADIYO ta dawo masa da d'iyarsa kamar yadda ya bata umarni.

《《》》


Tun daga ranar da BIGGY yazo gidan har zuwa yau bai sake dawowa ba,wanda zuwa yau an kwashi kwanaki da dama ba tare da ya sake waiwayar gidan ba.


A b'angaren ASHNA kuwa ko wane dare da tunani da kuma mafarkin BIGGY take kwana kuma take tashi,ko wane motsawar second ji take kamar za tayi hauka saboda yanda zuciyarta ta damu da shi fiye da tunaninta,tun bata yarda da cewa sonsa take ba har ya kaiga yanzun ta amincewa zuciyarta da son da take masa..


Tafiya tayi nisa a b'angaren zaman KHUBRA a gidansu KHALEEL a yayin da itama ZUHRA tayi tsalle ta dire kan itafa sam bata amince da a sake rabasu ba,nan ta tsaya kai da fata akan sai dai UMMI ta tafi dasu duka,nan ko UMMI tace taji ta gani kuma tana sonsu duka dan haka ta kwashesu duka suka koma gidanta.
Kulawa ta musamman suke samu daga gurin UMMI inda ta mai dasu y'ay'a tamkar ita ta haifesu da cikinta,d'aki guda tasa aka ware musu had'e da tsara shi da kayan k'awa wanda idanu bazasu iya tantace ainihin yadda suke ba,bare baki ko hannu su samu damar shaidawa masu sauraro.
Rayuwarsu a gidan UMMI kusan za a iya cewa a yanzun sunfi sakewa duba da yadda UMMI ta maidasu kamar wasu k'awayenta,shi yasa suma basa tab'a b'oye mata wani abu daya shige masu duhu,idan ko unguwa zata je zaka tarar dasu tare da ita duk inda ta cire k'afarta to ko nan zasu maida tasu.
Zuwa yanzun KHUBRA har ta dad'a washewa ba kamar yadda ta dawo daga garin ZAKIRAI ba,ta k'ara cikowa fatar nan tad'an yi fresh daga muguwar yamutsewar da tayi.....




Nema kam kusufa-kusufa akewa HAJIYA LAURA tun daga ranar da HAJIYA MURJA ta samu labarin itace shaid'aniyar data sa aka d'auke mata gudan jininta,wannan dalilin yasa HAJIYA'N cin *ALWASHI* (UMMI AISHA) gurin ganin bayanta...


Wannan kenan..........










*~#TEAM KHUBRA.~*










*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠





*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*13/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣4⃣*








*T* un bayan da su KHUBRA suka bar gidan dukkanin wata walwala ta k'are a tare da BB zaman gidanma sam baya masa dad'i bayaga hakama babu wani abinci mai dad'i da suke samu a gidan dama-dama da ace d'aya cikinsu na nan to tabbas da sun samu abinci mai gina jiki musamman ma ace MR'S KHUBRA.
A duk lokacin da yaji bazai iyaba sai dai ya shirya tare da ficewa ranan ko gidan UMMI zai nufa a nan zai cika tumbinsa ba shi zai dawo ba sai dare shima sai dai kwanciyan bacci ne zai dawo da shi.
Tunda ya san sauran yaran babu abunda suka iya,ko da kuwa ace dafa lipton ne,sam basu san yaya tafasan sa yake ba,wannan lokacin ne kuma da dalilin yasa MAMA ta yanke shawaran ganin ta gyara musu rayuwansu gudun kada a zageta nan gaba (kun jifa fan's).
Sosai MAMA ta dage gurin yak'i da son jikinta ta kuma zage damtse gurin ganin hak'anta ya cimma ruwa tare da taimakawar BABA ZUWAIRA da har lokacin take zaune a gidan,dan MAMA sunyi ruwa sunyi tsaki akan baza ta komaba za taci gaba da zama da su har k'arshen rayuwa,duk lokacin da suka taso daga makaranta babu sauran zama a gurinsu gaba d'aya take tusasu a gaba su shiga kitchen bata tab'a rabuwa da su su huta sai dai ko idan akace lokacin sallah yayi ko cin abunci wannan kad'ai ke sawa ta d'aga musu leg.


《《》》


Sanye cikin brown en shirt da black trouser sai wani k'aton Timberland shoe brown colour dake k'afansa,idanunsa sakaye cikin black sun glasses ya ci mazuu,tafiya yake cike da k'asaita kamar kowane lokaci,yana tafiya yana kad'a car keys en dake hannunsa har ya k'araso bakin motan,a hankali ya bud'e sannan ya shige kamar wanda akawa wani abu ya fizgi motan a guje tun kafin ya isa bakin get en yaketa faman doka horn,a guje BABA ya bud'e masa tun kafin ya k'araso,a 220 ya bar wajen wanda ya bar BABA da mamakin irin wannan tuk'i da KHALEED ke yi a yau.
Fitansa daga gidan bai zame ko inaba sai gidansu KHALEEL wanda yanzun ya koma YAYA'N KHUBRA da ZUHRA.


Motansa na kunna kai cikin farfajiyan gidan idanunsa suka sauka akansu sunata guje-guje,sanye da k'ananan kaya kowacce ta had'e cikin colour en da ranta ke so,k'wallo suke bi a guje suna ihu.
Parking yayi a gefe yana kallonsu wanda su sam hankalinsu bai kawo kansa ba,ihun da KHUBRA tayi ne yasa shi dad'a maida hankalinsa kansu,gani yayi ta tsaya tana ta faman dira k'afafu da alama a koi abunda ya faru tsakaninsu,a hankali yayi k'asa da glass en dake side nasa,cikin murya kamar ta mai shirin yin kuka take magana
"Allah ban yardaba tun d'azun sai rinto kikemin dan kinga ban iyaba ko...."


Dariya sosai ZUHRA ta tsaya tana mata,kallonta KHUBRA tayi ta b'ata fuska had'e da fara matsar idanu tana shirin yin kuka,da gudu ZUHRA ta saki boll en ta nufo inda take,ganin haka yasa KHUBRA felle k'afafunta da gudu ta d'auke kwallon sai jin ihunta ZUHRA tayi tana ta faman doka tsalle kan itama ta ci..
Tsayawa ZUHRA tayi kafin ta juyo tana fad'in
"Allah nima ban yardaba ai ojoro kikamin,kuma Allah sai an sake ai ba cin tsakani da Allah bane kikayi"


Tsalle KHUBRA taci gaba da yi abunta tanawa ZUHRA gwalo,duk tsallen da take bata san yana kallontaba,waya ya ciro da niyyan kiran KHALEEL,idanunsa kuma har lokacin na kanta a hankali ya danna kiran had'e da d'orata a kunnensa,ring na farko ya d'auka
"Ya akayi ne MAN?"


"Gani na iso ka fito ina mota...."


"Lallai amma kai anyi d'an air gidan surukanka kazo ne da saina fito na maka jagora sannan zaka shiga?"


Ya tsina fuska yayi kafin ya bashi amsa
"Wa ya sani ne abu a duhu......MALAM idan zaka fito to idan kuma baza ka fitoba na k'ara gaba"


"To jarababbe gani nan fitowa kada kayimin masifa ni....."
K'it yaji tun kafin ya k'arasa maganan,a hankali ya kalli screen en sannan ya kad'a kansa,shi kad'ai yayi murmushi yana fad'in
"Naga ranan da zaka fara yiwa mutane magana da sanyin murya"
Da sauri kuma ya fice dan yafi kowa sanin halin mutumin nasa baya son jira.
A mota ya same shi ya k'ure volume yana ta faman jin 9ja music da suke playing one bye one daga gurin mawak'a daban-daban.
Bud'e motan yayi ya shiga,bayan ya zauna ne ya mik'a masa hannu suka yi musabiha,KHALEEL ne ya katse masa kallonta da yake ta cikin glasses en,juyawa yayi ya kalleshi sannan kuma a hankali ya zare glass en daga idaonsa
"MAN lafiya kuwa kake naga idanunka sun sauya colour,anya kuwa ba wani abu ke damunka ba ko jarabar ce ta motsa?"
KHALEEL ya tambaya yana kuma dad'a k'ure BB da ido duk dan ya gano damuwar tasa,murmushi yayi masa ta gefe d'aya
"Noopp!wani abu ka gani?"


"A'a babu komai kawai na ga ka canja ne kamar kana tare da damuwa"
Yana magana yana kuma kallonsa duk dan ya gasgata abunda yake damunsan,sai da ya kalli side ensa inda suke ta tsalle-tsallensu sannan ya kalli KHALEEL ya kuma yin wani murmushin
"No babu komai......kawai dai ina son......."
Sai kuma ya sake yin shiru
"Kana son me kuma?"
"Uhmmm!nothing.....Kawaifa maganar da mukayi da kai ne kan neman UNCLE a waya da mukayi akan zamu tuntub'e shi ko ya san inda ABBA yake"


"Ohhh!kaga kumafa ni wallahi har na mantama da maganar amma in sha Allah kam ya kamata ace tun kafin lokaci ya k'ure mu tuntub'eshi muji me zai ce mana ko....?"

"Yeahh!dama dai hakan yafi kamata muyi,amma.....yaushe kake ganin zamu same shi a wayan idan mun kira?......ina nufin wane time ne yake free babu hayaniyan aiki a tare da shi?"


"Emmm!ina ganin yanzunma yana gida........yanzunma ya kamata mu jarraba kiran nasa muji"


"Okk ka kira mana shi muji ko"


Wayan ya jima yana ring ba'a d'aukaba,kamar yadda suka jima suna kira har na wani tsayin lokaci,rashin sa'an samun sane yasa suka hak'ura akan zasu gwada wani lokacin.
Shiru dukansu sukayi kamar kurame can kuma KHALEEL ya kalli BB fuskansa da matsanancin farin ciki
"MAN ka san wani abu kuwa?"
Ba tare da ya jira ya amsa masaba yace "Ko da yakema muje gurin UMMI kawai akwai maganar da nake so muyi da ita kuma sai kana gurin zan iya mata magana"
Wani kallo BB yayi masa na rashin fahimta kafin ya bud'e motan ya fita,a baya shima ya bishi suna tafiya dai² zasu shiga parlor KHUBRA ta fello da gudu hannun KHALEEL ta rik'e tana fad'in
"YAH KHALEEL dan Allah kayi mana alk'alanci"


Tsayawa dukaninsu sukayi da sauri BB ya d'auke kansa daga kallonsu,sai dai yana sauraron abunda suke yi
"Haba k'anwata alk'alanci kuma nida ba school of law nayi ba,ina ni ina yin shari'a?"


Shagwab'e fuska tayi kamar za tayi kuka cikin muryan tab'ara take fad'in
"Shi kenan tunda kaima bazaka goyi bayanaba kun nunamin banbanci,barin je gurin UMMI nasan ita zata goyi da bayana"
Hannunta da take k'ok'arin zarewa daga nasa yayi saurin rik'owa yana fad'in


"Haba mana k'anwata ta yaya zamu nuna miki bambanci mu mun isa?ko so kike idan UMMI taji yau ta hanamu dinner?"


"To ba dai kaima kak'i sauraronaba,ni sake ni nama fasa fad'a maka"


"A'aaaaa!ai kam baza ayi haka ba,yi hak'uri ki fad'amin kinji yawwa y'ar k'anwata maza fad'a min..."


Ganin yana bata hak'uri yasa ta b'ata fuska sannan ta shiga fad'in
"To ba ZUHRA bace wai dan naci kwallon da mukeyi tace ita wai bata yarda ba wai kuma wai rinto nayi mata fa tace,bayan ta fini iyawa"


"Aaaaaaa!Haba YAYA ZUHRA ya zaki ce haka bayan kuma ita tayi winning akanki"


K'afa ZUHRA ta shiga dirawa itama a k'asa nan da nan sai ga hawaye ya fara layi a fuskarta
"Allah tunda kace min YAYA saina fad'awa UMMI dama ai na fad'a maka bana so shi ne kake wani cemin YAYA duk dan kasa na tsufa da wuri"
Ihu KHUBRA tayi tana tsalle
"Yeeeeee!YAYA ZUHRA....Nima daga yau haka zan na ce miki"


"Allah baki isaba kuma idan kika kuma sai munyi fad'a dake"
Da sauri ta kwace hannunta daga ruk'on da KHALEEL yayi mata,a guje ta zura sanan ta juyo
"An fad'a en YAYA ZUHRA...."

Da gudu ta sake d'iba nan ko ZUHRA ta mara mata baya suka shiga zagaye filin gurin sune har cikin Guarding saboda dad'in tsokanar juna da suke yi.


A hankali KHALEEL ya juya yana girgiza kai,BB ya kalla ya wani basar kamar baya gurin,fuskar nan ya dad'a d'aureta kamar ba shiba ko lokacin da suka fito a mota dariya ya gama yi yana tsokanar KHLEEL amma yanzun ya wani had'e girar sama da ta k'asa.
Ci gaba da tafiya sukayi har lokacin kuma bai wani saki ransaba,cikin parlor'n babu kowa sai TV dake ta faman b'ab'atu ita d'aya,zama sukayi babu wanda ya kula wani a ciki,UMMI ta fito daga corridor en da zai sada ka da stairs en data sakko
"A'a SON ashe kuna nan..."


"Eh UMMI muna nan amma bamu jima muma da shigowaba"


"To yayi kyau kam Allah ya taimaka..."


"Ameen.......Ammmmm! UMMI gurinki muka zofa"
KHALEEL yayi maganar yana kallon BB da har lokacin bai yi maganaba tun bayan gaisuwa da sukayi da UMMI.
"Toh! ina saurarenku ai...Maganar mene kukayi shiru?"


Inda-inda KHALEEL ya fara ya kasa magana,kallonsa UMMI ta tsaya yi ganin ya kasa cewa komai ne tayi magana
"Lafiya k'alau kuwa kake ta faman inda-inda ka kasa magana?"


Kansa ya shiga sosawa wani kallo BB yayi masa mai wuyar fassara kafin ya sake d'auke kansa ya shiga danna phone dake hannusa kamar mai neman wani abu,sai dai maganar da KHALEEL yayi a dai² lokacin ta kusa tarwatsa masa lissafi a burkice ya kalleshi dan son tabbatar da abunda yake fitowa daga bakin KHALEEL en


"UMMI damafa kan maganarmu da KHUBRA ne nake son yi miki tuni,tunda ALLAH yasa an ganta UMMI mai zai hana ki sake tuntub'ar MAMA da maganar,kinga idan ABBA ya dawo sai ayi maganar auren ko?"


Dariya tayi na jin dad'in maganar da yayi mata cike da farin ciki ta furta
"SON kenan banda abunka wannan maganar itace zata sa ka tsaya kana min magana kamar wani mara gaskiya,ka kwantar da hankalinka indai wannan ne,ina so ka sa a ranka kamar nayi mata maganar kuma kamar anyi an gama kaji koh?"


"Yawwa UMMINAH shi yasa nake ji dake wollahi,ni iya hakama yau kam kin gama min komai,na gode sosai UMMINAH"


Hankalin BB idan ya kai million a wannan lokacin to ya kai k'ololuwa gurin tashi,shi kad'ai lokaci guda har ya nemi farin cikinsa ya rasa,zuciyarsa tayi duhun da baya iya gane me suke cewa a lokacin dan gaba d'aya kunnuwansa suka tafi yajin aiki na wucin gadi,bai san lokacin da ya mik'eba ya shiga neman hanyan fita daga parlor'n,duk maganar da suke masa babu wanda ya iya kulawa haka ya fice motansa ya shiga ya fisgeta fiye da lokacin da yazo gidan,tuk'i kawai yake wanda baimasan inda yake nufaba ikon Allah ne kad'ai ya kaishi gida,MAMA dake parlor taga shigowarsa tana masa magana bai san me take cewa ba bare ya bata amsa,ido itama ta zuba masa har ya wuceta yabi corridor en da zai sada shi da bedroom,da k'arfi yayi banging door en.
A saman bed en ya zube zuciyarsa ta gama yin duhun da baya gane komai,da k'arfi yake sauke ajiyan zuciya wanda daga ji kasan bana lafiya bane,idanunsa ya runtse hango lokacin da KHUBRA ta rik'e hannun KHALEEL yayi da yadda take narke masa fuska tana shagwab'a wani b'acin rai ne ya dad'a kawo masa ziyara da ya dad'a hasala shi take ko ya bud'e idanunsa da k'arfi,gaba d'aya d'akin sai juya masa yake yi.......


《《》》


"Ina kika shiga munafuka maza fito dan yau kam ko ani ko ake,imma dai ki nemomin y'ata ko kuma yau na tona miki asirin abunda kikayimin sannan kuma na kaiki gurin mai gari a gaban dubban jama'a nasa a yanke miki hukuncin da bakiyi tsammaniba"..


LADIYO da ta b'uya a d'akinta jin shigowar MALAM en ne dama yasa ta zurawa a guje tayi cikin d'aki sannan ta k'ara da rufe k'ofar d'akin nata duk a ganainta ta gujewa had'uwa da MALAM en kan wannan maganar ta al'janar y'ar tasa..
A hankali ta bud'e k'ofar ta fito jikinta a salub'e kamar kazar da kwai ya fashewa sai sink'e kai take yi.


"Munafuka algunguma kuma kina jin tsoro ne dama?
Da kina tsoro ai da baki aikata duk wani tuggu da kika shiryaba amma kije ke da Allah,sannan ki sani nan da sati guda na baki duk inda KHUBRA take ki gaggauta nemomin ita idan ba hakaba kuma......"
Yayi k'wafa kad'ai tare da shigewa d'akinsa ya banko k'ofar


Jiki babu k'wari ta mik'e ta koma d'aki,tagumi ta buga da hannayenta duka biyu tana jimamin halin da MA'U ta jefata da kuma irin halin da ita kanta ta jefa kanta,kuka sosai LADIYO take yi tana kuma tsinewa MA'U duk kan damuwar da ta haifar musu,yanzun gashi ta barta a ciki.....


Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads