Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 159513 words

Chapter 34 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1240

Ads at the middle of Article

abunda yarana zasu tsaneni.."

Jinjina kai UNCLE yayi sannan sukayi musabiha tare da sallama da juna suka d'auki hanyan komawa gida suna d'agama juna hannu cike da farin ciki mara misaltuwa...


Tun daga ranar da ABBA ya dawo su KHUBRA ke aikin dafawa da saukewa har tsayin kwanaki bakwai,a ranar ne kuma suke sa ran zuwan UMMI don komawa gida,sosai ABBA ke jinjina musu namijin k'ok'arin da suke,sboda duk girkin da za ayi a gidan idan ya tambaya amsar bata wuce ta kullum wato *KHUBRA da *ZURA* ,idan ko akace ABBA na zaune a parlor haka zasu kewayeshi kowa na bashi labari har rasa na wa zai saurara yake saboda hayaniyansu bata bari yaji labaran nasu,su kuma bazasu bari wani ya bada nashi sannan wanima yayiba,a'a sai dai suce duka zai saurara....

《《》》


A b'angarensu KHALEEL kuwa tun da ABBA'NSA ya dawo bashi da wani abokin hira ko shawara daya wuce ABBA'NSA.
Zuwa yanzun ABBA'N yasan da maganar KHALEEL,yanzun hakama maganar tafiya neman aurenta ake wanda ABBA ya sanar da ABBA'NSU BB zuwansu,da suka gama yanke shawaran zuwa nemo aurenta gurin mahaifinta...


Koda ABBA yasa MAMA ta tambayi KHUBRA yadda zasu samu ganin mahaifinta kuka tasa mata,sai da MAMA tayi aikin lallashi da taimakon ZUHRA da kuma banbaki sannan tayi shiru.
"Ni bansan me zanceba akan haka...."
Abunda ya fito daga bakin KHUBRA kenan fuskarta a had'e


Kallonta kawai ZUHRA tayi
"To banda abunki SISTER sumafa iyaye suna da hakki akanki ko dan sanin inda kike rayuwa da sanin matsayin rayuwarki....yanzun duk son da kikewa ABBA zaki so barinsa?ko kuwa zaki so barinsa cikin mawuyacin hali?
Yanzu baza kiso ganin saba da sanin yana raye ko kuwa akasin haka ba?"


A tsorace ta kalli ZUHRA dake magana,ita kuma ganin yanayinta yasa tace
"Ehhhh!ko kina so ace haka ya faru da ABBA'N?....."


Kaita girgiza da sauri hawaye yana sakkowa kan fuskarta jin ta ambaci mutuwa


"Nooo!bafa kuka za kiyiba....idan har kina son ganinsa to kiyi k'ok'arin bada address na gidanku kinji sister'na"


Cikin sheshshek'ar kuka ta fara magana
"Bazan iya bada kwatance ba....."


Zaro ido ZUHRA tayi MAMA kuma tana gefe tana jinsu tak'i magana
"To sai me kenan?"


"Zan iya gane gidan da kaina amma bazan iya bada kwatance ba"


Sai lokacin suka gane abunda take nufi,aiko cike da jin dad'i ZUHRA ta furata
"MAMA idan zasu tafi nima zan bisu...Kinji?"
Dan tasan abunda ABBA zai ce kenan wato a tafi da KHUBRA..


Nan ko ASHNA ma tace
"Nima haka MAMA....."


FATAHIYYA ta kallesu
"Nima kinji MAMA zani..."


Dariya MAMA tayi
"To shi kenan...kuje ku fad'awa ABBA idan ya amince sai ku bisu......"
Kafin ta rufe baki har FATAHIYYA ta fice dan tambayan ABBA....


*********


Tun da sanyin safiya aka hau shirin tafiya garin na KASHIN DILA dake cikin K'ARAMA HUKUMAR KIRIKASAMMA dake cikin HA'DEJIA a jihar JIGAWA...
Shirin tafiya ya kankama a wajen ABBA,UNCLE dama jagororin tafiyan wato BB da KHALEEL,sai sauran yaran wato ZUHRA,KHUBRA,ASHNA da FATAHIYYA da suke seat en baya,jikin KHUBRA yayi sanyi sosai tunda taga sun d'auki hanya,sai take ganin kamar yaune aka rabota da mahaifinta,kanta ta kwantar jikin ZUHRA zuciyarta babu dad'i,a haka da take kwance take matse idanunta tana hawaye...


BB da KHALEEL na gaba amma babu wata hira da suke sai dai idan KHALEEL yayi magana BB ya Amasa masa da "Eh ko A'a"....


《《》》


"Kina ina maza fito yau ba sai gobeba wollahi sai mai gari ya shiga tsakaninmu,dole ki nemomin inda y'ata take..."


Rab'e-rab'e take tana bin hanya,tana fitowa ko ABBA ya maka mata wata uwar harara da shi kad'ai ya san ma'anarta,sai kuma ita da akayi dominta


Jiki na rawa baki na b'ari take fad'in
"Dan Allah dan sonka da ma'aiki kayi min rai MALAM....... dan Allah ka k'aramin lokaci....Wallahi zan nemota duk inda take...."


"Ke rufemin baki mak'aryaciya munafuka kawai....Har tsawon wane lokaci kuma zan ci gaba da zaman jira....Wallahi yau sai na tona miki asiri ko kuma ki fitomin da inda take...."


"Wallahi MALAM naji zan nemota amma kayimin rai dan Allah"
K'afafunta zube a k'asa take wannan bayanin wanda babu abunda ke fitowa tsakaninta da MALAM BUBA sai uwar harara da yake sakar mata babu k'ak'k'autawa...


"Kin san Allah yau kam ba zan kyalekiba,sai mun dangana da gurin mai gari kuma tabbas sai kin karb'i hukunci a yau ba gobeba....."
Cakumota yayi ya mik'ar tsaye yana shirin yin hanyan k'ofar gidan da ita yana ingizata gaba
"Tsohuwar munafuka algunguma muje....."
Ko rufe bakinsa baiba tsayuwan mota ya dakatar da shi,da sauri ya nufi hanyan zaure yana son dubawa,har lokacin kuma LADIYO na chafe a hannunsa........








*~#TEAM KHUBRA.~*










*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠





*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*21/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣8⃣*










*K'* atuwar motar da tayi parking a k'ofar gidan nasa yake bi da kallo game da tsantsan mamaki a zuciyarsa yake fad'in
"Wannan kam sunyi makuwa da alama gidan mai gari suke nema....."
Bai gama tunaninba mutanen ciki suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya,har lokacin ABBA'N KHUBRA mamaki ne shimfid'e a saman fuskarsa saboda rashin sani wanda ake cewa ''yafi dare duhu''.

KHUBRA da take kusan ta k'arshen fitowa daga motan,idanunta suka sauka kan mahaifinta da ako wane lokaci shi ne farin cikinta,nan ko ta kwasa a guje bata tsaya wata-wataba ta ruk'unk'umeshi,kukantane ya bayyana inda shi kuma ABBA ganin wannan al'amari yasa shi fad'in
"Y'ar nan yi maza ki sake ni kada ki jawomin abunda za a jefeni....kina yiwa Allah ki sakeni tun kafin labari ya isa kunnen mai gari...."
Idanunta da suka gama jik'ewa da ruwan hawaye ta d'ago tana kallonsa har lokacin kuma wasu na ci gaba da sakkowa
"Alhamdulillahil-laziiy bii ni'imatihi tatimmus-salihaat!!!...."
Abunda bakin ABBA'N nata yaketa furtawa kenan har lokacin kuma ya gagara sakinta saima dad'a k'ank'ameta da yayi kamar wanda akace za a rabasu har abada.
"UWATA ke ce ko kuwa gizo kikemin kamar yadda kika saba zuwamin...?"
ABBA'N nata ya tambaya cike da rashin gasgatawa,saboda a ganinsa a ko wane irin lokaci zata iya b'acewa daga gurin.


"ABBA nice ba gizo bane..."


Godiya kawai yakewa Allah daya bayyana masa y'ar tasa kwaya d'aya tal.


ABBA'N BB ne ya matso kusa dasu hannunsa na nuna MALAM BUBA da shi sam ma bai kula ta kansuba y'arsa ce kad'ai abunda idanuwansa ke hango masa,da k'yar ABBA ya harhad'a kalmomin yana fad'in
"M.A....L..A..M......BU....BU...BUBA....."


A d'an firgice ABBA'N KHUBRA ya d'ago kansa yana kallon inda aka ambaci sunansa,kallonsa yake like no other yana son tuno inda ya sanshi,amma sam k'wak'walwarsa ta gagara tunawa da abunda yake son ganewar tattare da wannan d'an gayun mutumin.


"Nasan da wuya ka iya shaidani amma da zaka kalleni sosai tabbas zaka iya tuna fuskata..."
ABBA ya fad'a yana murmushi,aiko kamar wanda aka bawa wani gagarumin aiki ya k'ure shi da idanu duk da ya kasa tunawar hakan baisa ya hak'ura ya daina kallon ABBA'N BB ba..
"A gaskiya ALHAJI ban shaidakaba,sai dai ko kamin k'arin bayani la-Allah sai na iya tunawa"


Sai da ya saki wani k'ayataccen murmushi wanda ke bayyana kyau da kuma zallan hutu da wannan bawan Allah ke ciki sannan ya furta
"Ehhh! to ina ganin mu zauna tukun dan maganar tamu bata buk'atar muyita a haka..."

LADIYO na gefe rakub'e a zaure tana lek'e dan tun bayan da ta samu MALAM en ya saketa tayi zaraf ta shige had'eda lab'ewa tana lek'en wad'annan turawan bak'in.
Duru-duru MALAM en ya shiga yi na neman abun da zai shimfid'a musu su zauna,kafin yayi yunk'urin yin wani abu LADIYO tayi zaraf ta fito tana fad'in
"MALAM ai da ka kaisu cikin gidan ko dan nan yayi kan hanya..."
Wata uwar harara ya sake aika mata wacce take nuni da 'idan kika sakemin shishshigi zanyi maganinki,a fusace ya wuceta dan shi kam gare shi ya tsani ko da ganinta bare har wata magana ta shiga tsakaninsu.
K'atuwar tabarma ya shimfid'a musu sannan ya shiga fad'in
"Bismillah...!!!"
Gaba d'aya ko suka nemi guri suka zauna,LADIYO da MALAM ya barta tsaye da sakakken jiki ta nemi guri daga can gefe ta rakab'e,a inda kuma tayiwa kunnuwanta matsuguni a tsakiyar mutanen da takewa kallon daga wata k'asar suka zo,musamman y'an matan da har yanzu babu wacce ta shaida hatta kuwa da KHUBRA dake kusa da ABBA'NTA ta jingina dashi,idan ta kalleshi sai tayi murmushi a zuciyarta take fad'in
"Yau nima na samu y'anci gani kusa da mahaifina...."
Abu d'aya zai iya sawa kayi saurin gano b'acewar annurin dake kan fuskarta a wannan lokacin,ba komai bane kuwa face tunanin MAHAIFIYARTA da bata tab'a ganiba.
Muryoyinsu ne suka katse mata tunani inda suke ta faman gaishe-gaishe da tambayan juna iyali,bayan nan kuma gurin yayi d'an shiru na wucin gadi kafin ABBA'N KHALEEL yayi addu'ah.
Nan kuma aka koma kan ainihin maganar da ta shigo dasu,ABBA ya sake kallon MALAM BUBA da yake jiran k'arin bayani daga bakinsa,kamar yadda suma sauran jama'ar gurin suke sauraron jin me zai biyo baya.


"Nasan gaba d'ayanku kunyi mamaki musamman dana nuna nasan MALAM BUBA ko?......"


Nan suka hau amsawa da "Hakane....!"


"To Alhamdulillah! yanzun zaku ji yadda akayi na sanshi duk da dai shi bai shaidaniba..."
Kallonsu ya sake yi d'aya da d'aya,KHUBRA kuwa murna take yi jin ABBA'NSU ZUHRA yasan ABBA'NTA,fuskarta sai annuri ke fita

"Ni dai dai farko suna na SAFWAN kuma ni haifaffen garin DUTSE ne ta nan jihar JIGAWA"


Kallonsa sosai MALAM ya sakeyi jin sunan daya ambata,kamaninsa ya shiga hangowa ko tantama ba yayi shi ne dai wanda ya sani shekara da shekaru da suka gabata..

"Tabbas wallahi shi ne!....Shi ne....SAFWAN...."
Sai kuma ABBA'N KHUBRA ya fashe da kuka da alama akwai wani abu da yake damunsa wanda ya tuna a dai² lokacin.


Da k'yar suka lallasheshi yayi shiru,inda gaba d'aya sauran jama'ar gurin suke kallonsu,saboda yadda suka sasu a duhu
"Tabbas sai yanzu na shaidaka...."
Sabuwar gaisuwa suka sake da tambayar bayan rabuwa.


ABBA'N KHALEEL ya kalli ALHAJI SAFWAN yana fad'in
"To ALHAJI mu kam kun samu a duhu,bamu fahimci abunda kuke nufiba.....dama kun san juna ne kam ko yaya abun yake....?"


Kai ABBA ya girgiza masa kafin yayi magana MALAM BUBA har ya rigashi
"K'warai kuwa mun jima da sanin juna...kamar dai yadda kuka gani yanzun zan yi muku bayanin alak'ar dake tsakanina da SAFWAN....
Ni dai da farko suna na ABUBAKAR SA'ADU wanda mafi yawancin jama'a suka sani da MALAM BUBA kamar yadda na taso da wannan suna....alak'ar dake tsakaninmu kuwa ita ce.......


《《》》


Ciwo ne ya soma cin k'arfinta tun bayan zuwanta asibiti da likita ya sanar mata komai lafiya bata sake yunk'urin komawaba,jikinta duk babu kuzari a yanayin yadda take jinsa babban dalili kenan da yasa yau d'in ta shiga shiri babu ji bare gani na ganin ta koma asibitin tunda ciwon yaci k'arfinta..
Tafiya kawai take amma da tayi tayi sai ta huta,saboda rashin kuzari duba da yadda kwanakin take fama da amai da gudawa.
Layin karb'an kati tabi bayan jira da tayi na wani lokaci sannan aka sallameta,hannunta rik'e da katin ta nufi office en likitanta na wancan lokacin.

Shiganta office en ta nemi guri ta zauna kan kujera,katin ya amsa idanunsa sanye da glasses ya kalleta yana mata tambayoyin abunda ke damunta..
A hankali take motsa bakinta saboda ina ganin kamar bakin natama ya tafi yajin aiki had'e da sauran gangan jikinta..
Idanunsa na kanta har ta k'are bayaninta sannan yayi y'an rubuce-rubuce,bayan y'an mintuna kuma ya sake d'agowa yana mata bayanin za taje tayi test a yau ta kawo masa,amsa tayi ta fice daga office en kamar wancan lokacin,bata zame ko inaba sai laboratory na asibitin.Bayan an d'ibi jininta ta zauna jiran fitowan sakamako a nan.
Mintuna sun sake shud'ewa inda wata nurse ta hau kiran sunanta aiko nan MA'U ta mik'e da k'yar tana nufarta
Wani kallo nurse en ta mata sannan ta mik'o mata sakamakon gwajin tana yatsina fuska,haka ta karb'a sannan ta kamo hanyan dawowa gurin likita danjin me kuma sakamakon nata zai nuna a karo na biyu.


Shigowarta office en ta tarar da shi yana waya kan dole ta tsaya jiransa har ya gama,sannan ya amshi takardar dake hannunta,zaro farar takardar yayi da take ninke a cikin envelope ya warware,abunda idanunsa suka fara tozali da shi shine yanda gwajin jininta ya koma *POSITIVE* maimakon *NEGATIVE* wannan shi ne abunda ya tabbatar masa da matar na d'auke da cutar da yake hasashe,ajiyan zuciya yayi sannan ya maida takardar ma'adaninta,cikin sanyin murya ya shiga yi mata nasiha kan yarda da *K'ADDARA* da kuma karb'arta ta kowane fuska tazo maka mai kyau ne ko akasin haka,ita dai MA'U ido ne nata babu baki,sam ta kasa gane inda wannan tatsuniya ta likita ke tafiya duk ta kafeshi da idanu
"Likita nifa har yanzun ban gane ma'anar wannan wa'azin nakaba ,kawai idan zaka sanarmin abunda ke faruwa to,idan kuma bazaka fad'a ba to ka sallameni dan na gaji da zaman gurin nan"


Kallonta kawai yayi jin yadda take magana cikin kaushin murya a ransa ya furta
"Lallai wato bata san meke faruwa ba amma takemin irin wannan maganar....aiko zaki san ni kikewa magana haka"
Yayi niyyan sanar da ita cikin ruwan sanyi amma maganarta tasa shi had'e giran sama dana k'asa ya shiga fad'in
"HAJIYA sakamakon gwajin da aka miki ya tabbatar mana da kina d'auke da cuta me karya garkuwa'n jiki wato *HIV* kenan kamar yadda muke kiranta a turance,wanda a hausa kuma muke kiranta da *K'ANJAMAUU*......."




《《》》


Hannunsa d'auke da envelope yana tafiya yana kare fuskarsa saboda zafin rana dake damunsa,ci gaba da kallon hanya yake saboda hangen abun hawa da zai d'auke shi a lokacin,da k'yar ya samu NAPEP ya fad'a masa inda zashi,tafiyar mintuna k'alilan ta kawosu bakin k'aton get en,kud'i ya fiddo ya sallami mai NAPEP en sannan ya tura get en ya shiga.
Tun daga harabar gidan nake kallon gurin kamar na sanshi haka wani lokaci daya gabata,cikin sauri ya shige k'ofar da zata sadashi da babban parlor na k'asa,shigowarsa ya tarar dasu sun baje kayan shaye-shaye wasu da kwalabe wasu kuma sai had'awa sama hazo suke.
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un!!"
Abunda ya fara fitowa daga bakinsa kenan,cikin fushi ya isa gurin baiyi wata-wataba ya shiga fashe kwalaben a k'asa cikin fad'a yake fad'in
"Ban fad'a muku kada wanda ya sake yimin shaye-shaye a gida ba?.....ko kuwa so kuke ayimin cunen y'an drugs?
To wallahi yau kam kunyi na k'arshe dan dukanku sai kun barmin gida...gara kusan inda dare yayi muku,nima na samu Hutu da nutsuwar zuciya.."


"SO.....SO...SORRY OGAAA...."
Wani yaronsa daya sha yayi mankas ya fad'a idanunsa na rufewa da bud'ewa
"In...sh...sh...sha....Allahu ba zaka sake kamamu da wannan laifinba.."
Tsaki yayi ya wuce hanyan stairs a ransa yake fad'in
"Ya zama dole akaina ko dai ku chanja hali ko kuma dukanku dole na rabu daku"
Kafin ya k'arasa haurawa saman wayansa dake aljihu ta soma k'ara da sauri ko ya zarota ganin bak'uwar number har zai fasa d'auka wata zuciyar tace
"Ina kai ina k'in d'aukan bak'uwar number,ai kawai ka d'auka wata kila ko cikin guraren da ka kai takardunkane aka dace ka samu aikin da kake nema...."
Bai ka'arasa tunaninba yayi saurin d'auka had'eda karata a kunne,cikin harshen nasara daga gefen da aka kira shi ake fad'in
"Ko kaine SADEEQ MUHAMMAD?"
Cikin hanzari har yana had'awa da girgiza kai BIGGY ya amsa da eh shi ne..


"Muna nemanka ranar monday a ma'aikatar revenue ta nan kano a branch enmu dake bomphai..."


Ai BIGGY kam ji yayi kamar zai gangaro daga saman stairs en saboda dacen da yayi bak'aramin dad'i yajiba,dan dama ranar da UMMI tace ya kai mata takardunsa ya amsane kawai amma a ransa ya k'udurce shifa ba zai koma gidanba har sai bayan ya samu aiki wanda yayi k'ok'arin hakan a k'ashin kansa,wannan shi kad'ai zai sa su ganshi da k'ima..
Godiya yayiwa Allah,sannan ya kuma tabbatarwa da kansa lallai duk wanda yake laifi ya tuba ubangiji yana karb'an tubansa,kansa ya d'aga sama hawayen farin ciki suna sakko masa a hankali ya furta
"Lallai ne ubangiji shi kad'ai yafi cancanta da a

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads