Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 159513 words

Chapter 32 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1243

Ads at the middle of Article

_Niko da nake gefe nace kad'anma kika gani,ki jira zuwa nan gaba...._


《《》》


Tun bayan fitarsa da suketa magana bai saurare suba duk k'ok'arin UMMI bai wuce sanin dalilin canjin da ta gani a tattare da shiba,amma ganin yadda yake tafiya da irin yadda ya fisge daga rik'on da KHALEEL yayi masa a k'ok'arinsa na dakatar da shi daga nufinsa,ta tabbatar ba k'alauba amma sai bata kawo komai a rantaba duba da yanayin da yake ciki kenan lokacin da suka shigo,sai tayi tunanin ko wani abu ke damunsa daban..
FItowansa daga parlor KHALEEL en ya biyoshi duk dan ya dakatar da shi amma inaaa lokacin harya manne motansa,a k'ok'arinsa na yin reverse har round about en dake farfajiyan gidan ya daka da bayan motan amma sam bai kula da hakanba saima ficewa da yayi a 360...


Da gudu KHALEEL en shima ya hau motansa ya biyo bayansa ba shi ya kyaleshiba sai bayan da yaga shigarsa gida sannan KHALEEL en ya juya yana kuma jimamin abunda ke damun aminin nasa da ya zame masa kamar wani mai shafar jinnu...

《《》》


Duniyar ta masa k'unci yahuma da k'yar yake iya had'iyansa wanda yake jinsa kamar judar k'asa yake taunawa..
Wayoyinsa dake gefe ne d'aya ciki ta hau kuka,kamar bazai dubaba haka ya banzatar da ita,zuwa wani lokaci daya ji an ci gaba da kiran ya bud'e idanunsa da suka matuk'ar firgitar dani ganin jini kwance cikinsu kamar dama can idanun nasa babu komai cikinsu sai jini..
Ko dubawa baiba ya danna bottom en da baima san me ya dannaba gefen kunnensa ya ajiyeta sannan ya sake maida idonsa ya kulle.
Maganar da ya jiyo ne ta cikin wayan yasa shi saurin laluben wayan ba tare da ya kuma bud'e idanunba ya karata a kunnensa.


"Hello SON kuna lafiya dai ko?"


Sai da yayi k'ok'ari ya saita nutsuwarsa sannan ya iya amsawa
"Ehh UNCLE muna lafiya ya k'asar Singapore da aiki?"


"Alhamdulillah!kam zamu ce"


Shiru sukayi na d'an lokaci kafin UNCLE yace
"SON are u there.....?"

"Ehhh UNCLE..."


"Ok akwai wani abune najika kamar kana cikin damuwa hope dai komai lafiya?"


Shiru BB yayi yana dad'a hasaso abunda ya faru d'azun bada jimawaba sannan ya dake
"Ehhh to Lafiya dai ba lafiyaba UNCLE"


Da sauri UNCLE en yake fad'in
"Maza sanar dani abunda yake faruwa son kaji ko kada ka b'oyemin,komai kake ciki ka sanar min nima mahaifine a gurinka kaji ko?"


Damuwansa a lokacin ya dad'a kaiwa mak'ura,idanunsa babu abunda suke hasko masa face hotonsu suna rik'e da hannun juna sai dariya suke,da k'yar ya iya furta
"ABBA......................."












*~#TEAM KHUBRA.~*










*_#REAL SMASHER._*
💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*15/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
_As'alullahal aziiym rabbal arshil aziiym an-yasfiyaki ×7...._
_Cweet sis *SAFIYYA BALA (MOM HANAN)* ina miki fatan samun lafiya mai d'orewa kuma ingantacciya,abunda muka rasa kuma Allah yasa mai ceto ne ranar gone k'iyama,Allah ya bamu hak'uri da juriyan rashinsa..._
*~________________________~*
_ALHAMDULILLAH!family nd friends addu'anku a ko wane lokaci garemu tana zama karb'ab'b'iya muna godiya sosai da addu'o'inku,SISTER kuma Allah ya bayyana mana ita,sai dai bata cikin hayyacinta,muna fatan zaku sake taimaka mana da addu'ah akan Allah ya daidaita mata tunaninta...REALLY HEART U MY PEP's 💔..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣5⃣*






*"SON* me ya faru maza sanar dani,wane ABBA'N kake nufi???"
Sai da ya saita kansa zuciyansa kuma na ambaton
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un
Allahumma inniy a'uzhubika minal hammi wal-huzn,wal-ajazi wal-kasali,wal-bukhli wal-jubni,wa-dal'iddaini wa-galabatir-rijaal"
Take ya d'an fara samun nutsuwa duk da idanunsa na kulle har lokacin,kamar yadda har lokacin bai daina ajiyan zuciyan da yake yi da sauri-sauriba.
"UNCLE please dan Allah ka taimakemu idan kasan inda ABBA yake ka sanar damu please........"


Daga b'angaren UNCLE en yayi shiru yana sauraron BB,yanayin da ya jishi ya tabbatar da matsala,amma da yake yana sone BB en ya sanar masa ko akwai wata damuwa da zai iya maganceta sai ya sauya salon maganar tasa.
"SON nace ka sanarmin da damuwarka idan akwai abunda zan iya to"


"Noo!UNCLE babu komai kawai dai muna da buk'atarsa ne kusa damu....behind these ma babu yanda za ayi mu rayu ba tare da shiba,rashinsa tare damu zai haifar mana da matsala a rayuwarmu ko ta b'angaren neman aure,sannan mutane da dama a yanzun sun rigada sun san cewa ABBA ba wai mutuwa yayiba....UNCLE duk duniya a yanzun na tabbata kuma duk inda ABBA'NMU yake ya sanar maka,kuma tabbas kaima UNCLE kasan inda yake....."
Yanayin yanda yake magana kad'ai UNCLE ya karanta,shiru duka sukayima juna har na tsawon wani lokaci,jin shirun yayi yawa yasa BB jiki a sanyaye ya furta
"Shi kenan UNCLE zamu hak'ura daga nan har zuwa lokacin da ABBA zai ji son ya dawo gida garemu,za kuma muci gaba da addu'ah Allah ya juyo mana da hankalinsa kanmu"
Hawaye ne suka ziraro masa ta gefen idanunsa,kasa jurewa ci gaba da magana yayi saboda yadda zuciyarsa ta dad'a yin rauni da sauri ya kashe wayan,saitin zuciyansa yasa hannunsa biyu ya danne bakinsa na ci gaba da motsawa da alama yana addu'ah ne a lokacin...


Ko da UNCLE yaji BB ya kashe wayan tsayawa yayi yana kallon screen en,shi da kansa yana tausayawa yaran nan rayuwar da sukeyi ba tare da mahaifinsuba,alhalin kuma yana raye ba wai mutuwa yayi ba.
Shi kad'ai a cikin k'ayataccen parlor'n daga inda yake zaune yana hango farfajiyan gidan da yadda tsuntsaye keta sauka da tashi kasancewar glasses ne tsakaninsa da wajen,tunani ya shiga yi na ya zama dole a wannan lokacin ya nunawa aminin nasa b'acin rai muddin yak'i amince masa kan maganar tafiyansu tare..
Niyyan fita yayi amma yanayin daya shiga a lokacin na tausayin halinda yaran ke ciki tsahon shekaru yasa shi fasawa tare da fad'in
"Babu inda zani gwarama na jira dawowar ALHAJI SAFWAN en muyi duk wacce za muyi,imma dai ya amince mu koma tare ko kuma na nuna masa kalar nawa fushin a yanzun....."
Shi kad'ai idan ya tuna tsayin shekarun da sukayi a k'asar tare tunma lokacin yana zuwa ya koma har aka basu wannan project en na tsayin shekaru uku wanda ya rik'esu a k'asar da yayi masa shamaki da nasa iyalan wanda yake fatan komawa nan bada dad'ewa.


Yana tsaka da tunani aka bud'e k'ofa sannan aka maidata aka rufe,har lokacin bai juyaba bare ya damu da ganin wanda ya shigo sanin mutum d'aya ne ke da ikon shigowa haka kai tsaye shi ne dalilin da yasa yak'i juyawan..
Idan ba dan shekaruba gami da jin dad'i da wannan mutumin yake ciki to lallai da nace BB ne ya shigo,saboda tsananin kamanninsa dana hango a fuskar wannan mutimin da ya shigo,bambaci na biyu kuma dana gano wannan yafi BB jiki,wannan su ne dalilan da sukasa nak'i amincewa da wannan mutumin BB ne.


"Hey!MR MAN....."
A yanda yake ya bawa k'ofan baya ya d'aga masa hannu,har lokacin kuma bashi da niyyan juyawa.
Hakan da yayi ya tabbatar masa da akwai matsala,saboda basa haka a tsakaninsu,duk lokacin da d'aya ya fita ya dawo to lallaine zaka tarar da d'ayan yana marhaban da d'an uwansa,brief case ensa ya d'ora saman center table,sannan ya zagayo ya zauna a d'ayan kujeran na kusa da ABBA'N KHALEEL.


"Heyy!MR MAN wani abu yana damun kane ka zauna nan,ko kana tunanin wani abune?"


Shiru har lokacin bai tanka masaba,shi kuma ABBA yak'i gajiya da tambayansa abunda ke faruwa,daya gaji ne kuma dan kansa ya furta
"Allah ya kyauta to,tunda yau kam bani da darajar da za a kulani"
Mik'ewa yake shirin yi ganin haka ne yasa ABBA'N KHALEEL ya bud'e baki da k'yar kamar kuma wanda baya son yin magana
"SAFWAN koma ka zauna ina son muyi magana da kai ta fahimta"


Sai da ya kalleshi tukuna ya tabbatar da abunda ya fad'a hakan yake nufi da shi,sannan ya koma ya zauna yana jiran jin me zai fad'a masa mai muhimmanci haka da ya jawo tun daga dawowarsa yake magana amma yak'i kulashi,maganar da yake yi ne ya katse masa tunani
"SAFWAN a yauma zan sake yi maka tuni kan abunda shaid'an yasa kake aikatawa game da iyalinka.....Lokaci ya rigada ya wuce da ya kamata ace ka watsar da duk wani abu daya faru a baya ya kamata ka manta da shi haka,itafa rayuwa itace da kai ba wai kaine da itaba kada ka manta da hakan....Sannan idan kana tunanin kai ka yafe hak'k'inka dake kansu a matsayinsu na iyalinka su suna da girman hak'k'i a kanka wanda ya zama wajibi akanka ka sauke shi tunda har yanzun kana raye kuma kana cikin k'oshin lafiya
Ka godewa Allah da ya barka da rai da lafiyarka sannan kuma kayi godiya ga Allah daya baka iyalin da a kullum suke cikin nema da cigiyar inda zasu sameka saboda basu da burin da ya wuce su sake saka a idanunsu
Wanda yayi maka laifi daban amma kuma wanda kake hukuntawa daban,matarka ita tayi maka laifi kai kuma kana hukunta y'ay'an da ka haifa,shin bama laifi ne mu?ko kuwa mu za muyi laifi ubangiji ya yafe mana mune baza mu iya yafewa wanda yayi mana ba?
Idan har maganar da nake maka a kan iyalinka a lokuta da yawane baka so to tabbas a wannan lokaci a kuma yanzu na yanke hukuncin rabuwa da kai idan har bazaka koma garesuba,kai ba wani aurenba kuma kai baka sawwak'ewa waccan ba,sannan kuma ka fake da sunan kana hukuntata,idan har kasan kana son matarkane to ya zama wajibi ka koma garesu sannan ku gyara rayuwar aurenku,idan ba hakaba kuma wata rana zaka neme ni ka rasa ba kuma zaka sake gani naba saboda zanyi nisa da kai,hukunci yana hannunka ka tsaya kayi tunanin maganata idan bai maka ba kana da damar canjawa amma kada ka manta zab'ar akasin abunda na fad'a nima zan d'auki nawa matakin"
Yana kaiwa nan a maganarsa ya mik'e yabar gurin,ba tare da ya bashi damar yin maganaba....


Hannayensa ya d'aga tare da sauke su a kan fuskarsa danshin daya ji ya shafo yasa shi kasa gasgatawa da sauri ya dad'a gogowa dan ya tabbatar da abunda yake zargi,shi da kansa a lokacin ya tabbatar yayi ba dai-daiba,ya kuma yabbatar da tabbas bai zama adaliba idan har wani zai masa laifi ya hukunta wani daban,a yau ya dad'a tabbatar da kuskuren da ya dad'e yana tafkawa,yasan aminin nasa yayi gaskiya tunda suke wannan shi ne karo na farko da maganar aminin nasa ta shige shi fiye da ko wane lokaci.
Fuskarsa ya goge kafin ya mik'e ya shige toilet,alwala ya d'auro after kuma ya shiga jera salloli ya jima yana addu'ah bayan ya idar kuma ya d'auka al-k'ur'an yana karantawa saboda yadda zuciyarsa take babu dad'i,sai da yaji zuciyarsa ta koma dai² kafin ya ajiye ya nemi guri ya kwanta akan pray mat en saboda yau kam ji yake bashi da k'arfin mik'ewa ya kwancita a kan bed.
Shi kad'ai ya barwa zuciyarsa tunanin hukuncin da ya yanke,ya k'udurce a zuciyarsa ba zai tab'a sanar da kowa abunda ke shimfid'e k'asan zuciyar tasa ba........










*~#TEAM KHUBRA.~*








*_#REAL SMASHER._*
[6:46PM, 7/19/2018] ®ҽɑӀ $ʍɑՏհҽɾ.💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*19/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣6⃣*










*K* wanaki sun ci gaba da wucewa inda ko wane b'angare babu dad'i,kowa ka gani da abunda yake damunsa a zuciyansa amma a haka'n ba kowa ne zai fuskanta ba,musamman idan aka ce mutum ba mai kula bane to ko babu lallai yayi saurin gano haka a tare da su.
Zuwa wannan lokaci MAMA sun sake d'inkewa da UMMI kamar babu wani abu daya rabasu,a wannan lokacin duk wanda ya ga yanda mu'amalarsu take zaiyi tunanin su en y'an uwane na jini saboda aminci da shak'uwa ta musamman data sake k'ulluwa a tsakaninsu.


B'angaren zamansu KHUBRA ko a gidan UMMI basa fuskantar wata matsala saboda yadda UMMI ta maidasu,shi yasa suke rayuwarsu a sake,duk ko ranar da aka ce yau sun zo gidan MAMA wuni suke fira da tsokanar juna ta yadda idan suka tashi komawa sauran mutanen gidan har basa son su tafi su barsu,duk da har wannan lokacin KHUBRA tak'i sakin jikinta da su sosai,idan ka ganta tana fira tana dariya game da tsokana to tabbata da ZUHRA ne,su kansu mutanen gidan har mamakin shak'uwarsu suke.


Kamar ko wane lokaci yauma cikin shirin suka fito sai sauri suke,sakkowansu daga saman kenan suka sake jiyo horn da ake ta faman zuba musu,da gudu-gudu suka nufi k'ofan fita a parlor'n da d'an k'arfi KHUBRA ta furta
"UMMI mun tafi sai mun dawo...."


Tana daga saman stairs en lokacin ta fito daga d'aki kenan tana murmushi tace
"To Allah ya dawomin daku lafiya,ku gaishe su kunji,maza kuyi sauri kada YAYA'N naku yayi tafiyarsa...."


Ai ko k'arshen maganar bata kaiba sun riga da sun fice,kai ta girgiza sannan ta juya ta koma bed room,dan yanzun kam babu wani abu da zata yi duk sun riga da sun kammala duk wani aiki da ya kamata ace anyi a lokacin.


Yana ganin fitowarsu yaci gaba da danna horn,kallon juna suka yi a hankali cikin rad'a ZUHRA tace
"Shifa YAH KHALEEL yana da wani abu ko mene nayin horn en bayan gamu mun fito kuma"


"Barshi mana yana sane wollah,idan ba so yake mu tashi samaba kam ai saurin da mukema ya isa haka"
KHUBRA tayi maganar tana tab'e baki.
Duk abunda suke yana kallonsu har suka k'araso,a hankali suka shige inda ZUHRA ke back seat,ita kuma KHUBRA ta shiga gaba,a hankali ya kallesu sannan ya d'auke kansa tare da yiwa motan key suka fice a gidan.
Tafiyan kurame sukayi har suka iso cikin gidan,ZUHRA ta fara ficewa ta nufi cikin gida da sauri,KHUBRA dake shirin fita da har ta bud'e k'ofan KHALEEL ya rik'o hannunta,sosai ya rik'e yana murzawa har sai da tayi y'ar k'ara
"Dan Allah YAH KHALEEL kayi hak'uri wollahi da zafi"


"Ai dama so nake kiji zafin,d'azun gulman me kuke da kuka fito?"


Shiru tayi tak'i yin magana sai k'ifta idanu take,a hankali ya matso daidai kunnenta cikin rad'a ya furta
"Maza ki ci gaba kinji da biyewa mutane ana yin gulmana dake kinsan idan na kamaki ba da wasa zan mikiba ai...."


Batayi maganaba har ta samu ya sassauta rik'on da yayi mata,kusan mintuna biyar suna zaune cikin motan shi bai kyaleta ta ficeba shima kuma bai ficeba,har lokacin kuma hannunsa na rik'e da nata yana ci gaba da murzawa,kome ya tuna kuma da sauri ya saketa jiki a sanyaye itama ta fita ko sallama bata iya yi masaba,sauri take ta zubawa k'afafunta har hard'ewa suke kan tsaban saurin da take kamar wata mara gaskiya...


Zaune a guarding hannunsa rik'e da magazine,sanye da fara kar en singlet mai hannu sai farin 3quater,kamar wanda aka ce ya d'ago jin shigowan mota,bin motan yayi da ido,daga inda yake zaune yana hango duk wani abu da yake faruwa tsakaninsu,kallonsu yake zuciyarsa kamar zata fad'o

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads