Showing 39001 words to 42000 words out of 159513 words
Chapter 14 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt
ce ta sa KHALEEL d'agowa ya kalleshi yanayin da yagan shi ciki shi ya bashi tsoro,kasa magana yayi kawai ya juya a fusace ya shige toilet en had'e da turo k'ofan da k'arfi,abunda yayi ne ya bawa KHALEEL mamaki ya bi k'ofan da kallo zuciyansa fal tunani...........
*#Huh! Don't imaging coz yanzun aka soma,chakwakiya na gaba....*
*_~TEAM KHUBRA~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*10/ʍɑվ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*2⃣5⃣*
*K'*asan shower yayi still ruwa sai sauka yake a jikinsa yana zubewa,sam ya kasa samun nutsuwa,gaba d'aya haushin KHALEEL en yake kan wannan maganar da ya zo masa da ita,shi kam duk da yasan abunda zai faru kenan a zuwansu gidan da yayi fatanma bai ga wannan ranar ba,tunani duk ya dame shi,kusan mintuna ashirin ya d'auka a haka hannayensa dafe jikin wall en toilet en....
Da k'yar yayi wankan,bakinsa yaji kamar yana masa d'aci saboda b'acin rai,zuciyarsa ko uwa za ta fito,haka ya b'ata lokaci cikin toilet en kafin ya fito d'aure da towel,jikinsa kad'ai ya goge ya saka kayansa,car key ensa ya zara kan mirror face ensa a murtuk'e yayi hanyan ficewa daga bed room en ba tare da ya san inda zai nufaba......
Duk abunda yake yi idanun KHALEEL na kansa,sam ya kasa ganema kansa dalilin da yasa ya zuba masa na mujiya kenan,sai da yaga yana shirin fita tukun ya furta
''Ina kuma zaka je kabarni nan?''
A d'an fusace ya juyo ya kalleshi
''Ka aikeni ne da zaka tambayeni?''
''No!Allah ya baka hak'uri,amma banyi da niyyan b'ata maka rai ba''
Juyawa yayi zai fice har ya murd'a handled na door en KHALEEL ya taso ya biyo bayansa
''Man wai me yake faruwa,na ganka ba kamar yadda na sameka ba''
Yana tafiya yake fad'in
''Mene ka gani?''
''Please tsaya muyi magana kafin ka wuce''
''Bani da time yanzun letter ma had'u''
Yana gama maganar ya sa kai ya fice,da mamaki a fuskan KHALEEL ya raka shi da ido,shi dai yasan lafiya k'alau ya tarar da shi amma bai san me ya jawo chanjin da aka samu ba..
Phone ensa ya duba sai dai ya tuna ya barota cikin mota,haka ya zauna cikin parlor yana hasashen laifin da yayiwa KHALEED en da yasa ya canza masa lokaci guda...
Yana zaune ZUHRA suka shigo sai dariya suke da yake basu san ya zoba sai yanzun da suka shigo,a ladabce suka gaisheshi kafin sukayi kitchen..
Kallonsu yayi lokacin suna wucewa,a zuciyarsa ko yana sak'a abubuwa da dama game da KHUBRAN,sai yanzun zuciyarsa tayi sanyi ko dan arba da yayi da ita,duk da bata bari ya k'are mata kallo ba,har suka b'acewa ganinsa,sannan ya juyo....
ASHNA dake zaune duk abunda yake hankalinta na kansa,duk ji tai tana jin haushin ZUHRA da KHUBRAN ko dan kallon da taga KHALEEL en nayi musu,musamman ma KHUBRA da taga yafi tsananta kallonta....
Duk ta gama kumbura uwa zata fashe kan haushin da take ji,kawai dai dan bata da yadda za tayi ne,shi yasa take zaune har yanzun cikin parlorn.....
Zaman gurin duk ya isheshi bama kamar zamansu da wad'annan halittun,da ko kad'an bai son ganinsu kusa da shi,fuskarsa ya dad'a tamkewa yana ta spinning car keys....
Fitowar UMMI ne yasa ya d'anji sauk'i dan kam dama zaman ya isheshi haka,mik'ewa yayi yana jiran k'arasowarta,da zuwanta gurin ko suka yiwa MAMA sallama suka fice....
Wani banzan kallo MAMA ta rakasu da shi,tana fad'in da ni kuke zancen,wallahi bazan tab'a barin wannan al'amarin ya faruba....
《《》》
Suna tafe a motan duk sunyi shiru,shi da abunda yake tunani,ita kuma UMMI shirun da tayi nemo hanyan da zata sanar da SON en nata matsalar da ake ciki take sonyi...
''Ammm!SON kasan me nake so da kai?''
Nodding kansa yayi
''Yawwa abunda nake so da kai,duk abunda za kaji yanzun,ka d'aukeshi a matsayin k'addara kaji ko?nasan ka da hak'uri amma ina so ka k'ara''
Gaba d'aya hankalinsa yana kanta ya rasa dalilin da yasa take masa wannan maganar
''Ka nutsu tukun muje gida zan maka bayanin komai kaji koh''
Kai ya sake kad'awa,yana driving amma hankalinsa sam baya tare da shi,driving en kawai yake haka har suka k'arasa gida....
《《》》
Fitowarsa daga cikin gidan ransa duk a jagule,hakan yasa ya rasa ina zai nufa,rashin sanin madafa shi ya haddasa masa fasa fitan,direct ya nufi guarding duk ji yake garin ya d'aure masa wani zafi yake ji a jikinsa wanda bai san dalilinsa ba,sam ya kasa tunanin komai baya ga tuk'uk'i da yake jin zuciyarsa ke masa babu abunda yake ji,haushin kowa yake ji a yanzun......
Kasa zama yayi take ko ya kwanta saman grasses en da ke wajen,duk da rana da ta bud'e sosai a garin sai dai kuma guarding en bishiyu sun masa rumfa ta hakane kad'ai yasa babu rana cikin gurin....
Addu'ah yake kada Allah ya nuna masa irin wannan ranar mai cike da tarin k'unci,tsawon lokaci yana kwance a gurin bai sanma lokacin da su KHALEEL suka bar gidan ba,idanunsa ya kulle da suka sauya launi zuwa jaa saboda jin kansa da yayi tamkar zai tsage......
《《》》
A parlor suka yada zango,kansa a k'asa duk damuwarsa bai wuce sanin abunda UMMI ke shirin fad'a masa ba,maganarta ce ta dawo da shi cikin duniyarsa...
''SON abunda yasa nace maka ka nutsu maganace da ta fito daga bakin HAJIYA MURJA wanda bana tsammanin akwai k'arya cikinta,kuma ban son b'oye maka,nafi son kasan gaskiyar zancen''
'Dan kallonta yayi jin ta ambaci sunan HANIYAN KHALEED
''A halin da ake ciki kuma a yadda ita HAJIYAN ta sanarmin shi ne,yarinyar da kamin magana akanta ta riga ta koma garinsu,dan ta cemin iyayenta suka nemi ta koma za suyi mata aure cikin wannan satin''........
A tsorace ya kalli UMMIN nasa yana fad'in
''Wallahi UMMI k'arya ne''
Tsawa ta buga masa wadda tasa ya shiga hankalinsa ba shiri yayi shiru
''A gaban idona kake k'aryata ta,ko babu aminci tsakaninmu ya kamata ka fad'i wannan mummunar kalmar a kanta,idan na sake jin ka furta irin wannan maganar sai ranka yayi mummunan b'aci''
Cikin fusata take maganar wanda yasa shi sunkuyar da kai yana fad'in
''Ki gafarce ni UMMINA amma wallahi sam wannan maganar ba haka take ba,dan kuwa da idona na ganta yanzun,kawai dai a kwai wata manufa tata da yasa ta fad'a miki haka''....
Zuciyarsa fal b'acin rai dan shi kam wallahi shi kad'ai yasan me yake ji,taya ma za ace wani za ayi mata aure kuma cikin wannan satin amma kuma tana zaune cikin gidan bata koma nasu ba,tabbas shi kam ya san shiri ne da wata a k'asa...
Kalamai masu taushi UMMI ta shiga fad'a masa tana masa nasiha,har ya samu yaji zuciyarsa tayi masa sauk'i,kafin ya mata sallama ya fice daga gidan......
《《》》
Guri ta samu ta zauna bayan sun b'acewa ganinta,lokacin ne kuma muryan ASHNA ta dawo da ita daga kogin tunanin da ta tsunduma duk kan neman mafita ta wannan al'amarin dake shirin jagule mata.....
Tana shirin magana BB ya shigo da ganin yanayinsa ba sai ka tambaya ba za kasan yana tattare da matsananciyar damuwa....
Kallonsa MAMA tayi a tsorace take binsa da kallo danko ba k'aramin firgita tayiba da ganin yanayin nasa,kiransa tayi babu musu ya nemi guri ya zauna yana dafe kansa dake barazanar fashewa....
''SON me yake damunka,kaga kuwa yanda halittarka ta sauya lokaci k'ank'ani,maza sanarmin me yake faruwa''
''Babu komai''
Ya fata cikin cool voice nasa
''A kwai abunda kake b'oyewa SON''
''Babu fa,kawai ina jin headache ne''
''Eyyahh!Allah ya sawak'a maza ASHNA duba kawo masa magani idan ya sha sai ya kwanta ciwon zai sauka''
A zuciyarsa yake fad'in
''Tabbb!ai duk duniya yanzu kam ciwona baida maganin da ya wuce jin gaskiyar maganar da KHALEEL ya fad'amin''
''Wace magana kenan SON?''
MAMA ta tambaye shi,sai lokacin ya d'ago baki ya sake, kenan a fili yayi maganar ko me?
''Babu komaifa MAMA''
''Toh shi kenan ai kai kam dama haka kake da masifar zurfin ciki ba a tab'a gane kanku kai da ZUHRA sai kuyi tayi wata rana sai ciwo ya hallakaku''
Shi kam kallonta kawai yake ya kasa magana,harara ta cilla masa shi abun na MAMA wani lokacin har dariya yake bashi,sai dai wannan lokacin babu halin yi saboda baya cikin mood en da zai yin......
''Ko ka fad'a ko kada ka fad'a magana KHALEEL ya fad'a maka kan waccan yarinyar nasan dai bazai wuce haka ba,to wannan maganarma ba mai yiwuwa bace,dan ko na fad'a musuma aurenta za ayi a garinsu cikin satin nan''
Maganarta ta k'arshe ce ta dakatar da shi daga nutsuwar da ya fara samu,da sauri ya kalleta da jajayen idanunsa
''Dagaske MAMA?''
Yanayin da ya mata tambayar yasa ta tsaya tana wani nazari a kan fuskarsa,shi kuma ganin ta k'ureshi da ido yasa ya tashi ya bar wajen ba tare da ya sake kallon kowa cikin parlorn ba....
ASHNA ce ta kalli MAMA
''Kin gani ko MAMA dama wallahi na fad'a miki akwai abunda yake nufi da yarinyar can,tun ranar da ya dakeni akan maganar da naji ZUHRA sunayi da ita,Allah MAMA kada ki barima wannan abun kunyar ya faru.....
Numfasawa tayi tana kallon ASHNAR tana kad'a mata kai ba tare da ta furta komaiba ta bar parlorn.....
《《》》
Tun da ya fita ya barta take tunanin maganganunsa....
Wane dalili ne zai sa HAJIYA MURJA tayi mata k'arya kan wannan maganar,tunani iri daban-daban sai bijiro mata suke wanda ta rasa amsar su....
Idan ko abunda KHALEEL ya fad'a mata haka yake tabbas akwai manufar da yasa HAJIYA MURJAN tayi mata haka,sai dai koma mene ne ita ta sani,babu damuwar komai a ranta ta kauda tunanin wannan lamarin tana barin parlorn.....
《《》》
Shigowansa bed room en ya kwanta yana pacing ceiling...
Ta wani b'arin na zuciyarsa yana jin nutsuwa na saukar masa,sai dai kuma ta wani gefen yana jin tsoro wanda ya rasa dalilinsa,yana wannan tunanin bacci ya d'aukesa.....
《《》》
Can ta k'ule a bed room enta,number HAJIYA LAURA ta shiga kira,bugu biyu aka d'auka,a daddafe ta tsaya suka gaisa,aiko nan ta shiga koro mata jawabai na abunda ke shirin faruwa,yanayin da ta ga KHALEED a yanzun,da maganar da UMMIN KHALEEL ta zo mata da shi,bata rage mata komaiba ta sanar da ita......
Dogon ajiyar zuciya ta sauke,tana fad'in
''Ni kam na rasa me yaran nan suka gani jikin k'aramar yarinya da suka rud'e haka,kome take da shi ai muma y'ay'anmu nada''
''Uhmmm!HAJIYA LAURA kenan kawai dai ayi sha'ani(wai akace na birni ya zagi na k'auye),wallahi dan baki ga yarinyar bane,ni kaina yarinyar na bani tsoro duk lokacin dana kalleta,bama kamar yanzun a hakama wollahi bata fita ko ina nasan da na wajenma haka za suyita biyota mukuma namu suna jibge a gida (uwa ragunan layya)''
''Bari ke dai maganinsu za muyi cikin lokaci kad'anma kuwa,amma ki bar komai a hannuna,duk abunda ake ciki zan sanar miki zuwa dare''....
Da haka sukayi sallama,wani murmushin mugunta tayi tana bin wayan da kallo.....
Suna gama wayan ta shiga contact enta wani number tayi dialing,tana yin ring aka d'auka
''Allah ya taimaki HAJJAJU''
''Ammmm!BIGGY ba lokacin wannan wasan yanzun so nake kayi maza ka zo ina son ganinka''
''An gama ranki shi dad'e......
K'it ta datse kiran.......
In less-than fifteen minute's ya k'araso gidan cikin wani k'aton jeep black colour,baka iya hango komai na cikinta,motan na gama tsayuwa aka bud'e back seat na motan,wani zabgegen mutum ne ya fito kakkaura,da ganinshi kaga manyan basawa....
Cikin gidan ya nufa fuskarsa babu annuri a samanta,yana shiga y'ar aikinta dake parlor ya kalla yana fad'in
''HAJIYA fa''
''Tana ciki barin kirata''
Ta mik'e da sauri ta nufi hanyan d'akinta
''HAJIYA kinyi bak'o''
''Ina zuwa''
Ta fad'a ita kuma yarinyar tayi waje,bayan yarinyar ta biyo tana tafiya irinta hamshak'an mata,a tsaye ta tarar da shi ya juya baya
''Yawwa BIGGY aiki ne zan sa ka,amma nasan ba mai wahala bane a irin aikinku,a kwai yarinyar da nake son ku d'auke nisanta nake so kuyi da ita daga garin nan,koma inane ku kaita ba ruwana,wannan shi ne aikin''
Wata mahaukaciyar dariya yayi saboda raina aikin da yayi
''Yo HAJIYA wannan aiko yarana za suyi ba sai niba''
''Nasan da haka BIGGY ai shi yasa bana wasa da lamarinka,zan turo maka address na inda gidan yake''
''An gama,sai na jiki''
Da haka ya sa kai ya fice....
Yana tafiya ko ta tura masa komai,take kuma ta kira HAJIYA MURJA
''Toh na gama nawa sauran aiki yana hannunki,duk yanda za ayi anjima bayan Maghreb ki aiketa,zan miki bayani bayan kinyi hakan''
Tana gama fad'in haka ta kashe wayan,tana wani makirin murmushi........
*7:30pm*
KHUBRA ta shigo parlorn HAJIYA MURJA ita kad'ai ta tarar a parlorn,wani leder bak'i ta mik'o mata k'unshe da wani abu da ni kaina ban san mene a ciki ba,amsa tayi kafin HAJIYA ta soma magana
''Maza karb'i wannan kije waje zaki ga wani a bak'in mota ki kai masa injini''
Cike da ladabi ta amsa,har ta mik'e ZUHRA ta fito daga corridor en bed room nasu,kallon KHUBRAN tayi itama tana kallonta tana d'an murmushi kamar wanda basu saba ganin junaba suka k'urawa juna ido,fitowan BB ta waiga ta kalle shi,rana ta farko kenan da ta k'ure shi da kallo a iya zamanta a gidan,tsananin fad'uwa taji gabanta yanayi,a hankali ta waiwaya za ta fita,haka kawai taji idanunta sun kawo ruwa,da sauri ta sa hannu ta goge...
''SIS tsaya na rakaki''
Bata jira amsanta ba ta biyo bayanta,da sauri ta rik'e hannunta har suka fita daga gidan,KHUBRAN ce ta k'arasa kusa da window en motern tayi knocking,ZUHRA kuma tana jikin get,k'ofan aka zuge....
Gaisheshi tayi duk bashi da kad'ai ne a motanba,amma ita kam shi ta gani ta mik'o masa abunda ke hannunta aiko take ya mik'a hannu kamar zai amsa kawai ya fizgota cikin motan take ya datse k'ofan suka figi motan a 360...............................
*_~TEAM KHUBRA~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*11/ʍɑվ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA'IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA'ADAHU........_*
_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI'I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA'U MINHUM WAL-AMWAT...._
*~________________________~*
_Ga masu buk'atar son kasancewa da group na *Y'AR GARUWA* za ku iya yin joining ta hanyar amfani da wannan link en,saboda gujewa had'uwa da maza,mata zallah dan Allah👏..._
👇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EvdAvnFbBaX2BBMAwCCH4E
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*2⃣6⃣*
*B*akinta da hancinta ya danne da wani handkeey take ko ta sulale uwa matacciya....
Ganin abunda ya faru yasa ZUHRA dake tsaye matsowa da gudu kuma ta hau natsowa kusa da motan...
Cikin wani razanannen murya ZUHRA ta shiga k'wala kiran sunan KHUBRA wadda tuni motarsu har ta b'ace daga line en.....
Faruwar hakan ke da wuya ta dawo da gudu ta shiga gidan babu kowa cikin parlor sai BB dake shirin barin gurin shima,a