Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 159513 words

Chapter 19 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1226

Ads at the middle of Article

kike mata irin wannan dukan?bazaki d'aga taba sai na zo kanki?"
Har ta k'araso gurin ZUHRA bata san me take cewa ba,fizgota tayi ta kifa mata mari wanda yasata sakin k'ara wadda tafi ta ASHNA....


Cikin sauri ya fad'o parlorn kamar an harbo shi yana raba eyes,ganin ZUHRA na kuka ya nufi inda take
"Me ya sameki CWEETY?waye ya tab'aki?"


"Ba MAMA bace ta mare ni akan waccan dak'ik'iyar"
Wani mugun kallo ya jefesu da shi,kafin ya kama hannunta
"Yi shiru kinji maza je d'auko vail enki mu tafi"
Da gudunta ta bar parlorn,cikin sakanni ta dawo ya rik'e hannunta suka fice,MAMA da yar lelenta suka rakasu da harara....




A mota BB yake tambayan ZUHRA me ya had'asu da ASHNA,nan ta kwashe komai ta sanar masa dariya yayi yana fad'in
"Kinyimin dai² amma abunda ke so dake duk abunda za tayi miki ki daina biye mata kinji ko"


"To BB in sha Allah hakan bazai sake faruwaba"


"Yawwa CWEETY"


Motan shiru suka d'auki hanya.......


《《》》


"Aikin banza aikin wofi tarho d'inma tsabar tsiya irin ta y'an garin nan an rasa wanda zai taimaka ya kiramin MA'U naji halin da ake ciki..
Gashi ta barni da bashi fal kaina,gashi har yau ta gagara zuwa garin nan,kuma babu wani aike da tayimin,ba danma boka na saman dutse yana taimakona ba da yanzun mutanen dake bina bashi duk an mantar da su ba da sun zo sunmin rashin mutunci"
Ita kad'ai sai surutai take kamar wacce k'wak'walwarta ta kwance


"Amma babu komai,ai duk inda take dole wata rana zata kawo kanta zata ci gidansu a hannuna,ita da cin moriya wato ni kuma da wahala"


Sai k'wafa take saki ita kad'ai talauci duk ya isheta,MALAM en kuma da take ta faman bankawa asiri babu wata mafuta da ta samu daga gurinsa,abunda take so babu dan kuwa bai samu ba dan kuwa so take ta dinga juyashi amma yak'i juyuwa,nasara d'aya da tayi kansa an rabashi da y'arsa abar k'aunarsa,ya manta da ita wanda yanzun ko maganarta bayayi....


Wannan kenan.......


《《》》


A gidan su KHALEEL kuwa tun da KHALEED yace masa ga shinan ya fito,daga yanzun zai taho yake ta faman jiran ganin zuwansa amma shiru,hakan ne yasa shi kiran line ensa...


"MAN ina ka tsaya ne kam,kasa sai jiranka nake tun d'azun kace kana hanya fa"


"Idan ka gama min fad'an sai ka ajiye waya muna bakin gate fito mu wuce"
Daga haka ya ajiye wayan ba tare da ya kashe ba,saima hand's free da yasa ta...


"Amma kai kam koi bak'in mugu maimakon ka kashe shi ne zaka sani a hand's free?"


Dariya yayi mai sauti,KHALEEL na jin haka yayi saurin kashewa dan ya san KHALEED ba kashewa zaiba...
Yana fitowa ya tarar dasu cikin motor en...


"Aaaaaa!kace tare kuke da Momcynah"


Sukayi murmushi dukkansu kafin suka shiga gaisawa..


"Ammm!nace ba"


KHALEED ya kalleshi yayin da ita kuma ZUHRA ta sunkuyar da kanta k'asa tana murza hannunta...


"Mu shiga ku gaisa da UMMI sai mu bar ZUHRA a nan muje mu dawo"


"Noo! kada ka damu tare zamu je da ita,idan mun dawo sai mu shiga,ai ina jin nan zamu yini yau"


"Wow! kace UMMI tana da manyan bak'i"


"Ka jika da wata magana mune bak'in?"


"Noo! sub'ucewa bakina yayi ya fad'i haka" sukayi dariya gaba d'aya su uku...


Seat en baya ZUHRA ta koma daga nan motansu ta cilla kan titi sai police station..........










*_~TEAM KHUBRA.~_*








*_REAL SMASHER._*
💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*22/ʝųŋɛ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


🍰🍩🍯
🎂🎂🎂🎂🎂
🌹🌹🌹🌹
*~HAPPY HAPPY BIRTHDAY.. ~*


_May it be the best day of your life thus far, & may your happiness grow with each passing day through the many many birthdays that surely are ahead of you._


*~HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY SISTER'S~*
_NI'IMATULLAH M.U (AUNTY G) & RAHMATULLAH M.U (AUNTY U) wishing u many more blessing year's........Happy fruitful year's dearies._


🎂🎂🎂
🎁🎁
_Here is my gift.._ 😋📦
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*3⃣1⃣*










*A* office en D.P.O aka sauke su,da yake ya d'an shiga ciki yana zagayen duba masu laifi..
Suna nan zaune kusan 30 minutes sannan ya shigo,ganinsu da yayi yasa shi sakin fuskarsa,yana mai mik'a musu hannu,sunkuyar da kawuna sukayi k'asa alaman girmamawa kafin suka bashi hannu..


Bayan sun gama gaishe² ya kallesu su duka coz bai san abunda ke tafe da suba a wannan safiyar
"Ammm!me ke tafe daku?duk da dai nasan zuwan naku ba zai wuce kan yarinyar da kuka bada report na b'atanta ba"


"Yallab'ai ba b'ata tayiba saceta akayi"
ZUHRA tayi katsalandan d'in yin magana
'Dan murmushi yayi,kafin yayi magana BB ya rigashi duk da yayi maganar ne k'asa² ta yadda ita kad'ai taji me yace
"Tambayanki akayi da zaki yi magana?"


Bata kalleshiba ta d'an sunkuyar da kanta k'asa


"Ehhh!tabbas kina da gaskiya ba b'ata tayiba saceta akayi,shin kina da masaniyar yadda al'amarin ya faru ne,kuma mene ne alak'arki da ita wacce aka sace en?"


Sai da ta kalli BB tukun,ganin ya d'aga mata kai alaman tayi magana yasa tace
"Ehh!yallab'ai tabbas ni witness ce akan wannan case en,kuma ni Y'ar uwace ga wacce aka sace ta jini"
Kaf abunda ta sani na yadda al'amarin ya faru ta sanar da shi,sai dai abunda ta rage cikin labarin bata sanar da shi mahaifiyarsu ce tasa aka aiwatar da abunba,tana gama jawabi tayi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba..


Dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara magana
"Shin ko akwai wani abu da zaki iya ganewa game da mutanen da suka aikata wannan d'anyen aiki? misali:kamannin wani ciki,suturan da suka sa da kuma mota ko number motan?
Shin zaki iya gane wannan ko makamancin haka?tunda kinyi bayanin kuna tare lokacin da al'amarin ya faru"


Kanta ta d'an d'age alamar tunani
Fitowarsu daga gida zuwa aiken MAMA da yadda akayi al'amarin ya faru take tunawa,da sauri kuma ta d'ago
"Yallab'ai bazan iya gane kamanninsu da number mota ba,amma motansu k'irar CRV ne bak'i sannan kuma kayan jikinsu duk bak'ak'e ne,sun rufe fuskokinsu da bak'in handkey idanunsu saye cikin black glasses,wannan shi ne kad'ai abunda zan iya tunawa game da su"...


Shiru cikin office en yayi na d'an wani lokaci,baka jin komai sai kukan AC dake aiki...


"Ammmm!gaskiya wannan case en yana da matuk'ar d'aure kai,da kamar ace mun samu photon ita yarinyar da aka sace sannan kuma an gane fuskar ko da mutum d'aya ne cikin masu laifin da sauk'i,ina tunanin aikin da sai yafi zuwa mana da sauk'i,amma duk da haka abun bai b'aciba...
Yanzun akwai wani taimako da kuke buk'ata?"
Yayi tambayar yana kallonsu duka...


A hankali KHALEED ya d'an tab'a KHALEEL
"Uhmmm!kai baza ka iya magana bane?"
KHALEEL ya tambaya yana murmushin mugunta...


Harara BB ya sakar masa sannan yayi gyaran murya,hankalin D.P.O na kansa jin yayi gyaran murya yasan akwai magana a gurinsa
"Ehhheemm!yi maganarka muna sauraronka"


"Yallab'ai dama kan maganar photo ne idan muka samo zaku iya nemota kenan?"


"In sha Allah muna fatan samota duk inda take,saboda zamu baza photonta ne cikin garin nan,idan ma bata cikin garin nan zamu bada cigiya a kafafen sadarwa da yardar Allah zamu sameta"


"To Allah ya taimaka yallab'ai,amma akwai wata alfarma da nake nema idan babu damuwa"


"Fad'i maganar da kake son yi ina saurarenka"


"Dama Yallab'ai ina son ka taimaka mana da y'an sanda da za suyi mana bincike ne su kuma lura da al'amuran wasu mutane,saboda akwai zargi akan su ina tunanin da hannunsu cikin wannan d'anyen aikin"


"To! babu damuwa in sha Allah duka ai ba zai gagara ba,za ka bada address na inda suke idan yaso komai ake ciki zasu dinga sanar da kai"


Basu suka bar police station enba sai da suka tabbatar sun samu mafita akan yadda zasu b'illowa al'amarin....
Suka yi masa sallama...
Ta hanyan kasuwa yabi dasu,da mamaki KHALEEL yake binsa da kallo,sai dai bai kai ga tambayarsa ba yaga ya fice...


Cikin kasuwan ya shiga da tambaya ya samu store en,tun da akayi maganan photo zuciyarsa ke ayyana masa abubuwa da dama,shi ya sama yanzun ba tare da yayi shawara da kowa ba ya shiga siyan kayan zane abun mamaki kamar wani Artist haka ya siya kayan,yaran store en suka bishi da kaya fal hannunsu...


Cikin ZUHRA ko KHALEEL babu wanda yasan me yake shiryawa kamar yadda babu wanda yaga kayan da ya siyo aka zuba masa su a booth...


Ya sallamesu suka kama hanyan komawa store,shi kuma ya shiga motor en yayi mata key zuwa gidan su KHALEEL...




《《》》


Tun safe kowa cikin su biyu BABA ZUWAIRA da kuma KHUBRA suka kama hanyar sana'arsu...


'Bangaren KHUBRA babu wani damuwa da yake a ranta wanda har zai dinga damunta a wannan lokaci,burinta bai wuce ganin ta kafa kanta a rayuwa ba,shi yasa ta jajirce dan ganin rayuwarta ta inganta..


Can k'asan ramin ta gangara,gurin babu mutane sosai sai y'an tsirari da suke d'iban ruwa suma,har ta gama tana shirin barin gurin wata matashiya ta matso kusa da ita fuskanrta a sake,da sallama a bakinta dai² lokacin KHUBRA tana niyyar haurawa sama
"Sannu baiwar Allah"


"Yawwa sannu"
KHUBRA tana kallonta da mamaki ganin babu wanda ta sani a garin..


"Suna na HAFSAT ina zaune cikin garin ZAKIRAI,babana shi ne SARKIN KASUWA"


"Allah sarki na gode"
KHUBRA ta fad'a tana d'an murmushi..


"Kefa baki fad'amin naki sunan ba"


"Suna na KHUBRA"


"Amma ke bak'uwa ce a garin nan ko?naga ban san fuskarki ba"


"Ehhh!haka ne,ban jima da zuwa garin nanba"


"Allah sarki na gode sosai,sai mun sake had'uwa"


Kowacce ta kama hanyanta,da yake ita KHUBRA ta riga ta gama abunda ya kawota gurin,ita kuma HAFSAT zuwanta kenan shi yasa tafiyan nasu ya bambanta......


《《》》


"Oyoyo TAKWARA yau kam ina da manyan bak'i,yaushe rabona da ganin k'afarki a gidan nan,gaishe nima da kuke zuwa kun daina yanzu, ince ko HAJIYA MURJA ta hanaku zuwa??"


"Wallahi UMMI abunda na fad'a kenan lokacin da KHALEED ya sanarmin wai nan zasu yini"


Harara BB ya sakar masa ba tare da yayi magana ba...


"Ai kuwa dai gaskiya KHALEED ya fad'a,kai dan gidanku idan kaje a matsayin wa kake zuwa??"


"Aaaaa!UMMI nifa na fishi zuwa kinga kuwa dole na zama d'an gida,shi kuma idan ya zo nan bak'o ne"


"A'a ni d'ana ba bak'o bane a gurina,kai ne dai ka maida minshi bak'o"


"Yawwa UMMI gara da kika fad'a masa dama na fad'a masa ni ba bak'o bane a gurinki"


"K'warai kuwa ka wuce matsayin bak'o a gurina,bama kaiba ko da wani ka kawo gidan nan wanda ban saniba ai bazan kira shi da bak'o ba,saboda matsayinsa ya wuce haka"


"Lallai yau zuwanka yasa UMMI ta mai dani gefe kun had'emin head kai da UMMI,sauk'i d'aya Allah yaso nima ga k'anwata da yau ina jin sai nayi kuka"
Yanda yake maganar ya bawa kowa dariya cikin parlor....


Yini guda sun k'auracewa gidan MAMA,sai dare suka yi niyyan komawa gida,turaruka masu kyau da tsada UMMI ta bama ZUHRA,suka rako su har bakin mota,sai da suka ga fitarsu daga gidan sannan suka juya....


《《》》


Tun bayan fitarsu ZUHRA daga gida MAMA ta rasa abunyi,kallon y'ar lelenta tayi fuskarta duk ta soma tasawa saboda dukan da ZUHRA tayi mata...
"Kin ga irin abunda nake fad'a miki ai,duk lokacin da kika takali yarinyar nan da fad'a sai nayi miki magana,daga yau ai ba sai na sake ce miki komaiba,gobema kya k'ara"


"To ni MAMA me nace mata bayan itace bata da gaskiya dan kawai nayi magana shi ne ta zage nifa"


"Ni dai ai bance miki komaiba,amma dai kam wata rana zaki ci ubanki a hannun YAYANKU,kinsan ba a tab'a ZUHRA a gabansa"


Tura baki gaba ASHNA ta shiga yi dama gashi ya kumbure,abun dai sai wanda ya gani....


Yinin ranan MAMA tana zuba idon ganin ta inda su ZUHRA zasu shigo gidan amma shiru kake ji wai "MALAM YA CI SHIRWA".....

*8:40*
MAMA ce cikin parlor sai kaiwa da kawowa take,abun duniya duk yayi mata yawa,ita kad'ai sai surutai take,ga wayan a hannunta amma ta kasa kiran KHALEED bare ta tambaye shi ina suka tafi,ganin ta rasa mafita yasa ta nemi guri tana shirin zama,horn data jiyo shi ya bata daman sake mik'ewa ta nufi hanyan fita daga parlorn....
A haraban gidan suka had'u lokacin yana k'ok'arin fitowa daga mota...


"Kai daga ina kuke tun safe da kuka fita sai yanzu"


Babu wanda yayi magana cikin su biyu,suka kama hanyan parlor,binsu ta shiga yi har cikin parlorn yanayin fuskar BB ya hanata sake yin magana dan ko yanda ya had'e fuskansa za kayi tunanin bai tab'a sanin wani abu da ya danganci dariya ba,wannan yanayin da ta gani shi yasa ta kasa sake yin magana....


Ita ko ZUHRA suna shigowa ta kalli BB da ya zauna tana fad'in
"YAYANAH sai da safe"


Kansa ya kad'a mata ba tare da yayi magana ba...


MAMA sai kallonsa take amma ta kasa magana kan dole ta jaa bakinta tayi shiru,dan tana da tabbacin ko tayi maganar ba kulata zaiyi ba,tunda y'an miskilancin suka motsa....


Zaman gurin ne ya isheta haka ta tashi ba tare da ta samu abunda take nema ba,tana barin gurin shima BB ya mik'e da niyyar barin gurin har ya d'auka hanyan bed room ensa,ko me ya tuna kuma ya dawo,fita yayi har parking lot,booth ya bud'e duk kayan dake ciki ya fito da,d'iban kayan yayi a hankali ya shiga dasu bed room en...
Fito dasu ya shiga yi d'aya bayan d'aya ya baje komai,k'aton allon ya kafe a tsakiyan bedroom en nasa yanda ko da mutum ya tashi daga bacci da shi zai fara arba...


Toilet ya shiga ya sakarma kansa ruwa,ya jima k'asan shower kafin ya fito,ba tare da ya b'atawa kansa lokaci ba ya zira farin singlet da boxers,sai sprays da perfume's da ya bajewa jikinsa kamar ba gobe...

Bacci ya k'auracewa idanunsa ,dai² lokacin wall clock en d'akin ya nuna 10:30pm....


Idanunsa ya rufe yana tuna wasu moments nata,a hankali ya bud'e idanunsa masu haske ya sauke su kan allon da ya shimfid'a white card board paper...
Sake rufe idanunsa yayi bayan ya d'auki alk'alamin,cikin nutsuwa ya dad'a bud'e su,a hankali ya shiga zane saman paper en,abun gwanin sha'awa haka yake sarrafa hannunsa da yake d'auke da alk'alamin...


Bayan shud'ewar wani lokaci ya dakata yana k'arewa zanen dake kan board en kallo,dai² lokacin idanunsa sun gama k'ank'ancewa kallon zanen dake jikin paper yayi,ya saki wani k'ayataccen murmushi,shi kad'ai yake surutansa,bed ya nufa bayan ya gama sumbatan picture en ya kwanta,dai² lokacin 12:00am...
Bacci mai nauyi ya d'auke shi cike da mafarkin KHUBRA......




Da safe misalin k'arfe 11:00am ya fito cikin shiri hannunsa rik'e da paper ya fito sai k'amshi yake bazawa,har ya fita babu da wanda ya had'u haka ya fice daga gidan...


Direct police station ya wuce,sergent da suke kan counter suna ganinsa suka shiga gaidashi saboda sun ganeshi office en D.P.O suka raka shi,dan sun san basa rakiyar banza...


After sun gaisa da D.P.O ya shaida masa abun da ya kawo shi,take kuwa ya buk'a ci ganin pic en yarinyar da ya fad'a masa ya zo da shi,babu b'ata lokaci ya mik'a masa...


Duk abunda ya kamata shi D.P.O suka tattauna akan yadda za a yad'a photon cikin garin Kanon dabo...
BB ya masa godiya ya fito dan tafiya gida,wanda k'arshe ba shi ya bar station enba sai da D.P.O ya had'a shi da y'an sandan da zasu yi masa aiki suka gaisa,sannan ya wuce.....


《《》》


Kwanaki sun ci gaba da gangarawa b'angaren KHUBRA rayuwarta cikin nutsuwa babu wani abu dake damunta rayuwarta take babu takurawa...

Kulawan da BABA ZUWAIRA ke bata ko lokacin da take gida hannun iyayenta bata samu irinta ba,shi yasa ta saki jikinta sosai babu damuwan komai cikin ranta....




Duk lokacin da BABA ZUWAIRA ta kalli KHUBRA tana tausaya mata irin rayuwar da take ciki,duk da ta kafu akan sana'arta ta *GARUWA* wanda yanzun ta kai duk line da zata gifta cikin garin na ZAKIRAI an santa,duk inda ta gifta za kaji ana fad'in *KHUBRA Y'AR GARUWA*,wannan d'aukaka da ta samu kan sana'arta yana mata dad'i da yadda mutane ke yabon halayenta cikin garin....


Wannan kenan......








*~KEEP FOLLOWING........~*








*~TEAM KHUBRA.~*








*_REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads