Header Ads
Showing 84001 words to 87000 words out of 159513 words

Chapter 29 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jul 2024

1248

Ads at the middle of Article

sun koma sai haske kad'ai yake gani cikinsu babu wani abu da yake iya shaidawa cikin d'akin bare har ya iya nuna muhallinsa,zaman tahiya yayi sannan ya sallame,zuciyarza tayi k'uncin da baya iya bambance tsakanin fari da bak'i.
Zama yayi had'e da tank'washe kafarsa cikin yanayi dake nuni da yana tattare da matsananciyar damuwa da bata da iyaka a wannan lokacin.


Yarinyarsa ce ta fad'o masa tunaninta duk ya addabeshi,take ya goge fuskarsa ya fito daga d'akin,d'an k'aramin d'akin da yayi bak'i wanda ke nuni da d'akin girki ne ya nufa da niyyan tasota tayi sallah a tunaninsa tana ciki kawai dai sha'afa yayi bai tasheta ba hakan yasa yake ta sauri dan yadda shima yake ganin yau d'in ya makara.


Babu komai cikin d'akin face tarkacen kwanukan girki,tsayawa yayi turus yana bin gurin da kallo,wani irin tunani ya soma yi wanda a k'arshensa babu komai sai tsananin firgici da yasa ABBAN KHUBRA sake nufar d'akin LADIYO kamar zai tashi sama dan sauri...


《《》》


Tun shigansu d'akin da MAMA ke kwance kamar gawa bakinta da hancinya sakaye cikin abun daidaita numfashi,kowa jikinsa ya dad'a sanyaya kamar an jefi kaza da gishiri.
Kusa da gadon MAMA KHUBRA ta matsa saboda tun shigowarsu hankalinta na kanta abun tausayi haka ta zauna gefenta hannunta ta rik'o had'e da damk'ewa cikin nata,nan da nan hawaye suka soma sakkowa daga idanunta,sheshek'an kukanta kad'ai suka tsinkayo BB,UMMI,KHALEEL dama su kansu sauran da suke cikin d'akin,sai dai abunda tayi ya basu matuk'ar mamaki dan suna da tabbacin irin k'iyayan da MAMA kewa KHUBRA.


Cikin muryar kuka take tambayan ZUHRA
"Me ya samu MAMA'N haka?"


Cikin ALHINI ta bata amsan duk abunda ya faru sannan kuma da dalilin kwanciyan MAMA'N jinya.


Bakinta ta shiga motsawa tana mata addu'a wacce ANNABI (S.A.W) ya koyar damu a duk lokacin da wani yake halin jinya wato
_(AS-ALULLAHAL AZIIYM RABBAL ARSHIL AZIIYM AN-YASHFIYAKII ×7)_
Sannan ta sake k'arawa da
_(LAA BA'ASA 'DAHURUN IN-SHA-ALLAH)_

Idanun BB na kanta duk abunda take sai dai ba kowa ne zai gane hakanba saboda ta tsakanin lashes ensa yake kallonta hannayensa zube cikin aljihunsa.

Juyowa KHUBRA tayi da niyyan yiwa ZUHRA magana hannun MAMA dake cikin nata ya motsa,cikin saurin ta juya don tabbatarwa,k'afarta ta sake motsawa sannan sauran wasu sassa na jikinta da suka motsa,a hankali kuma idanunta suka soma bud'ewa.
Duk abunda ake babu wanda ya kula da halin da ake ciki,kabbara KHUBRA tayi wanda yasa su saurin matsowa kusa da gadon suna tambayan lafiya,idanun MAMA da suke bud'ewa da ta kafe fuskar MAMAN da kallo ne yasa su kallon abunda takewa irin wannan kallon cikin wani yanayi na jin dad'i gaba d'ayan d'akin suka d'auki kabbara suma,masu hawaye nayi masu murna nayi saboda halin da suke ciki a wannan lokacin na tashin MAMA ba tare da sunyi tsammanin afkuwar hakanba.....


《《》》


Parking sukayi dai² bakin get en gidan suna shirin fitowa BABA MAI GADI ya fito daga gidan da y'ar radio ensa a hannu,kallonsu yayi yana shirin tambayan wanda suka zo nema idanunsa suka sauka kan ASHNA dake kan gaba.


"K'aaluu innalillahi wa-inna ilaihi raji'un,me zan gani haka?HAJIYA da gaske kece ko kuwa fatalwa nayi gamo da ita?"
Yana tambaya yana kuma had'awa da jaa baya,maimakon tayi magana da fad'a kamar yadda ta saba musu sai yaji sab'anin hakan wanda ya dad'a jefa shi cikin taradaddin anya kuwa itance da gaske?

"Nice BABA ba fatalwa bace"
Ta fad'a tana d'an murmusawa..


Al-ajabi yake na sauyin da ya gani a tare da ita da yasa shi kasa magana,har suka wuce suna niyyan shiga gidan ya dakatar da su ta hanyar fad'in
"Babu kowa cikin gidan HAJIYA"


Da sauri suka juyo suna kallonsa,cikin rud'ewa kuma ta fara magana
"Ina suka tafi suka barni?dan Allah BABA suna ina ?"


"Kiyi hak'uri HAJIYA amma gidan nan ya kai tsawon kwanaki babu kowa cikinsa,HAJIYA ce babu lafiya tana kwance a asibiti cikin mawuyacin halin da ko sanin wanda ke kanta bata iya yi"....


Tun kafin ya k'arasa ta fashe da kuka tana fad'in
"Ni dama nasan hakan sai ya faru,wayyoo Allah MAMANA dan Allah kada ki mutu ki barni,wayyoo MAMA dan Allah ki tsaya"
Surutai iri-iri take wanda bata iya tantance kalmomin da bakinta ke furtawa..


A hankali BIGGY ya matso kusa da BABA yana tambayansa
"BABA wane asibiti ne aka kwantar da ita?"


"Ehhh tana asibitin MALAM AMINU KANO"
BABA ya bashi bayani hatta da d'akin da take a kwance sai da ya musu kwatance,cikin sauri ya figi hannun ASHNA da batama cikin nutsuwarta suka d'auki hanyan asibitin AKTH....


《《》》


Dai² lokacin da suke tsaka da murnan tashin MAMA cikin sauri KHALEEL da BB suka fice dan nemo likita.
Suna cikin d'akin duk sun baibayeta kowa nason ya mata magana,idanunta taketa juyawa tana kallonsu d'aya bayan d'aya.


K'ofar aka bud'e da k'arfi cikin sauri duk suka maida hankali gurin dan ganin waye haka ya dokota da k'arfi.
Abunda suka gani ne yasa su kowa ya bud'e baki da tsantsan mamaki shimfid'e a fuskokinsu...................










*~#TEAM KHUBRA.~*








*_#REAL SMASHER._*
💠







*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*




🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹










*©®2018*
*11/ʝųlყ,2018*






*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹




_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*




*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_




*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._










*4⃣2⃣*










*'D* akin ya afka ba tare da yayi sallama ba yana muzurai had'e da dubawa ko zai ganota cikin d'akin,amma babu kowa ciki sai LADIYO data mik'e saman gado tana faman shirgar bacci uwa wacce ta sha wani abun.
Wata irin tsanarta ce ta dirarwa MALAM BUBA take ya juya ba tare da yayi magana ba,ficewa yayi daga gidan yana ta taraddadin ina yarinyar tasa ta shiga haka.
Abubuwa da dama yake tunani akansu da suka faru dashi a y'an watannin da suka wuce wad'anda basu da dad'in ji bare a fad'esu.
Dai² bakin wata makarantar primary dake k'auyen ya nemi guri ya zauna nan ya shiga tunanin inda ta shiga da halin da take ciki.
Rana ta k'arshe da suka rabu ta fad'o masa da abunda ya janyo rabuwar tasu,kuka ya fashe da shi yana tausaya mata yasan wahala kam da tsanani tana cikinsu a dai² lokacin.
Babu mai rarrashinsa sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita shi kad'ai yake magana da kansa
"Allah kaga halin da bayinka suka tsinci kawunansu ya Allah kaine gatanmu bamu da kowa idan ba kaiba,gareka muke neman taimako ya Allah ka k'ara tsaremu a duk inda muka tsinci kawunanmu,Allah ina rok'onka daka tsaremin yarinyata a duk inda take a kuma kowane hali take ciki"
Ya jima yana addu'a har sai da yaji zuciyarsa tayi sanyi daga mugun zafin da take masa sannan yayi shiru na wasu y'an mintuna bakinsa kuma har lokacin yana motsawa babu abunda da ke fitowa daga bakinsa face
"Astagfirullah wa'atubu ilaih,astagfirullahal azeeym"
A dai² lokacin ba komai MALAM BUBA yake tunawa ba sai wani al'amari daya tab'a faruwa shekaru sha tara da suka wuce wanda sune dalilin da yasa yaketa neman gafara,a zuciyarsa yake fad'in
"Lallai ya zamemin wajibi na nemeki ko dan neman gafara,a yau Allah ya nunamin abunda ko a mafarki banyi tsammaniba tare da LADIYO,lallai wannan ya tabbatarmin da *BA LAIFINKI BANE"*
Wuni guda yana zaune a gurin sallah kad'ai ke tada shi shima da yayi alwala a bakin tap en dake farfajiyar makarantar zai dawo saman varenda a nan zaiyi sallah sannan yaci gaba da zama yana dad'a neman gafarar mahalicci visa kuskuren da yayi shekaru da dama....


《《》》


K'ofar da aka doko ne da k'arfi yaja hankulansu suka kai dubansu ga k'ofan dan ganin waye haka,kallon ASHNA sukayi wacce idanunta suka gama rinewa saboda tsabar kukan da tayi kafin su iso.
Mik'ewa sukayi bakin kowanne na rawa gurin furta sunanta,MAMA dake kwance tsawon kwanaki ko kanta bata san inda yakeba,ganin ASHNA a gabanta dai² lokacin ta mik'e zaune had'e da zare abunda ke bakinta cikin murya k'asa-k'asa ta furta
"ASHNA kece zo nan y'ata naji d'umin jikinki kinji y'ata zo maza"


Gaba d'ayansu suka kuma juyawa jin maganar MAMA,zaune suka ganta saman gadon da suka barta a kwance,mamaki fal cikin zuk'atansu had'e da farin ciki mara misaltuwa.
Da gudu ASHNA ta k'arasa kusa da MAMA,fad'awa tayi jikinta ta saki wani kuka mai ban tausayi kowa sai matse ido yake,hannu MAMA tayiwa KHUBRA alama da tazo kusa da ita,babu musu kuwa ta isa kusa da ita,kamata tayi ta rungume idanun MAMA na fidda hawaye,abun ba k'aramin mamaki ya bawa UMMI,ZUHRA,FATAHIYYA da suke cikin d'akinba farin ciki mara misaltuwa a tare da su,a hankali ZUHRA ta isa kusa dasu tasa hannunta a bayansu itama ta kwantar da kanta bayan ASHNA da KHUBRA tana fidda hawayen jin dad'i.
Muryan MAMA ya katse musu kukan da suke
"Ku yafe min yarana dan Allah badan ni ba,nasan na cutar da ku na kuma b'ata muku rayuwa ban bi nasiha da kuma burin mahaifinkuba kamar yadda ya barmin wasiyyar kula da kuba,kuyimin aikin gafara in sha Allah haka bazai k'ara faruwaba...
KHUBRA ki gafartamin cutar dake da nayi,sanadin haka abubuwa suka sake cukurkud'ewa idan har baki yafemin ba ni kaina bazan tab'a yafewa kainaba"..
Kuka ne yaci k'arfin maganar MAMA,inda kafin taci gaba da magana DR ya shigo had'e da sallama bayansa kuma BB ne da KHALEEL,tun kafin DR en yayi magana wasu dattijai suka shigo,nanfa aka fara kallon-kallo tsakaninsu da MAMA dake zaune gefenta kuma ASHNA da KHUBRA ne sai ZUHRA dake kusa da k'afafuwanta.
Shi kansa DR en ganinta a zaune sai da abun ya matuk'ar bashi mamaki,baiyi tsammanin ganin hakan a tare da itaba amma sai ya bar hakan a ransa
Wayansa ya shiga pressing sannan ya d'orata a kunnensa
"Hello DR LEEMA idan babu abunda kike yi ina son ganinki yanzun"
Abunda ya fad'a kenan sai number room en da ya shaida mata,cikin y'an mintuna akayi knocking door en,izinin shigowa aka bata ta shigo d'akin dake cike da mutane,nan DR en ya basu umarnin su basu guri yana son ya duba jikin nata.
Ficewa sukayi gaba d'aya ya rage daga shi sai DR da kuma MAMA dake zaune har lokacin,da taimakon DR LEEMA suka duba jikin nata inda suka tarar da komai normal,bayan sun gama suka fice,a k'ofan d'akin ya tarar da su nan ya buk'aci ganinsu.

"BABA ina ganin ku yafi kamata da ku je don ganawa da likita dan dama ya buk'aci hakan tun kwanakin da suka gabata"


"A'a KHALEEL ku en dai kuje tunda kun san dalilin faruwar rashin lafiyar tata,kuma kune y'an boko saboda haka ina ganin zaku fimu fuskantar abunda zai fad'a"


'Dan murmushi yayi had'e da fad'in
"To shi kenan BABA amma tunda Allah yasa abun yazo da haka me zai hana muje gaba d'aya,daga nan maji koma mene ya faru da dalilin afkuwar hakan"


'Dan murmushin shima OLD KHALEED yayi sannan ya kama hannun BB yana fad'in
"Takwara muje ko?"
Wucewa sukayi zuwa office en inda da shigarsu suka nemi guri suka zauna suna masu sauraron abunda zai fito daga bakin DR.
Shiru ne ya biyo baya na tsawon wasu mintuna,kafin DR ya sanar musu da yadda jikin nata yake a halin da ake ciki
"To yanzu DR nan da zuwa wane lokaci zaku sallameta?"
KHALEEL ya tambaya
"Ehh to duk da jikin nata sa sauk'i sosai a yanzun zamu rik'eta a nan har nan da tsawon kwanaki biyu zuwa uku".

《《》》


Likkafa taci uban na da a gurin MA'U dan ko tun bayan da likita ya tabbatar mata da babu matsala ta sake kafa sabon kasuwanci da yafi na da a yanzu MA'U da mutane suka sani a baya wannan har ta dame waccen a rashin mutunci da duniyanci,idan abun nata ya motsa mata kwana biyu sai ta haukace yini take tana kan network babu sassauci,su da kansu mazajen nata suna mamakin wannan sauyi nata a y'an kwanakin da hakan ya faru....


Mu dai sai muce Allah ya kyauta na gaba...


《《》》


Kwanaki sun dad'a tafiya inda zuwa yanzun MAMA ta dawo gida kamar ba itace tayi jinyan da bata iya sanin duk wanda ke kantaba.
Yau ta kama kowa da kowa yana gida hatta da su BABA KHALEED da suka zo daga JIHAR JIGAWA,gaba d'aya suna zaune bayan gaishe-gaishe da akayi da tsokanar juna,MAMA ta kalli duka jama'ar gurin sannan ta fara magana wanda sai da taja hankulan jama'ar dake gurin gaba d'aya
"Da farko kafin na fara cewa komai ina buk'atar neman yafiyarku saboda wasu abubuwa da suka faru wanda a dai² wannan lokaci nake mai burin sanar daku GASKIYAR AL'AMARI'N da ya faru shekaru bakwai da suka faru"
Labarin yadda suka rabu da ABBA'NSU BB ta shiga badawa tun daga lokacin da suka fara samun sab'ani har zuwa lokacin da ya bar garin,da yadda suka had'a baki ita da HAJIYA LAURA kan cewa da mutane mutuwa yayi,duk dan gudun kada duniya ta zagesu,gaba d'ayan parlor'n sunyi shiru kowa da abunda ke damunsa da jin wannan al'amari mai matuk'ar rikitarwa da d'aure kai musammanma su BABA KHALEED da basu san da wannan labarinba,shiru mutanen parlor'n sukayi suna jiran jin me kuma zai dad'a fitowa daga bakin wani a gurin.


Shiru zuwa tsayin lokaci da haka taron ranar ya watse ba tare da wani ko wata sun sake furta wani abuba saboda zuciyoyinsu na cike da alhini.


Bayan tashinsu daga gurin BB tare da KHALEEL suka fice,basu zame ko inaba sai guarding inda suka zauna saman kujerun dake gurin,shiru na d'an lokaci sukama juna kowa na tunani duk da a gurinsu wannan maganar ta MAMA bata wani sasu jin shock kamar sauran mutanen dake parlor'nba kasancewar sun riga da sun san da ita,sai dai a wannan karon suna tunanin mafitane.


Bayan shud'ewar mintuna arba'in suna zaman kurame ba tare da wani yayi magana ba da sauri BB ya kalli KHALEEL
"Heyyy!MAN ka san me nake tunani kuwa?"


Kai KHALEEL ya kad'a masa


"Ina tunani ne akan b'acewar ABBANMU gaskiya inaji a jikina babu wanda yasan inda ABBA yake face ABBANKA"
Shiru duka sukayi suna kallon juna da sauri sukayi ihu had'e da k'ank'ame juna
"Tabbas!kayi gaskiya duk duniya ABBANA ne kad'ai zai iya sanin inda yake,amma me yasa bamu yi wannan tunaninba tun farko sai yanzun???"


"Wallahi dai kam MAN na manta ne tun farko,kuma kaima bakayi tunanin hakaba ko?"


"Sosaima kuwa sam tunanina bai kawomin haka ba shi yasama ban maka maganar ba"


Sai da suka jima a gurin suna shawaran yadda zasu fuskanci ABBAN KHALEEL idan ya diro k'asar tun bayan da ya bar k'asar shima akan wani project da yaje k'asar Singapore na tsawon shekaru uku wanda ya rage masa y'an watanni ya kammala.


"To amma MAN baka ganin gara tun yanzun mu tuntub'eshi da maganar,kaga idan suna tare nema zai iya convincing nasa su dawo tare ko kuwa me kace?"
BB yayi maganar had'e da kallon KHALEEL yana jiran jin me zai ce masa
"Ehh!kumafa shawaran da ka bayarma idan muka bishi hakan zaifi mana"


Sai da suka kammala shawaran sannan KHALEEL ya fiddo phone ensa yana dannawa alaman neman wani abu...


《《》》


Shigowarsa gidan zuciyarsa ta sake yin k'unci saboda tunawa da abunda ya faru kwanaki biyar da suka wuce,duk asuba anayin kiran sallah idan ya fice baya tab'a shigowa gidan sai bayan dare ya gama tsalawa alamar babu wanda zai san da zuwansa kenan yake shigowa.
Shigowarsa kenan kamar kullum yana k'ok'arin wucewa yaji an rik'o gefen rigarsa,da mugun fushi ya juyo dan ganin waye zai aikata masa haka.
LADIYO ce ta rik'e shi sai girgiza take alamar dake nuni da yau ba zaman lafiya kenan,fisgewa yayi tare da nunata da hannu,ba tare da yayi magana ba ya juya zai bar wajen,sake rik'oshi tayi cikin b'acin rai wanda yafi na farko yana juyowa ya d'auketa da mari.


Dafe kuncinta tayi tana kuma kallonsa,cikin kaushin murya had'e da sake nunata da hannu
"Ke dabbar wace duniyar ce da har zaki rik'e ni? ko kuwa kina tunanin nima baho ne irinki da zaki aikata abu kiyi tsammanin ban saniba
To bari kiji duk abunda kike aikatawa ina sane da halin da kike ciki,sai dai abu biyu zuwa uku zan fad'a miki
Na farko dai zan fara miki da Allah ya isa da har kike cin amanata kuma a haka kike tunanin ban saniba,kin munafurce ni sannan kin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads