Showing 96001 words to 99000 words out of 159513 words
Chapter 33 - YAR GARUWA COMPLETE.BY REAL SMASHER.-1.txt
dan tsaban tashin hankalin da yake ciki.
Idanunsa har sun soma chanja colour baya ga jinsu da yake suna masa zafi kamar an zuba masa chili a ciki,kansa ya kwantar a baya ganin hakan bai masa ba ya fice daga lambun yana nufan hanyan d'akin da KHUBRA ta zauna kafin b'acewanta,a hankali yasa hannu cikin aljihunsa ya fito da key en sannan ya bud'e k'ofan kamar wanda bashi da kuzari haka ya shiga had'e sa rufe k'ofan,d'akin yake bi da kallo duk tsayin lokacin nan d'akin bai yi k'uraba kamar dama can da mutum a ciki,komai tsaf a d'akin da alama dai BB na kula da d'akin,kwanciya yayi k'asa kan carfet kansa kuma ya d'orashi saman katifan,idanunsa da suka canja launi ya kulle har lokacin jinsa yake kamar ba shiba a fili ya furta
"Ya zama dole na d'auki mataki,idan ba hakaba komai zai iya faruwa....."
Kamar wacce aka cillo haka ta fad'o cikin parlor'n ko sallama bata iya yiba,akan BABA ZUWAIRA idanunta suka fara sauka da gudu ko ta fad'a jikinta,gaba d'aya kallon mamaki suka bita da shi ita ko kulawa da hakan bata yiba saboda yadda take a firgice sannan ga d'okin ganin BABA ZUWAIRA da suka had'e mata.
Dariya suka sa mata wanda ya jawo hankalinta garesu kallonsu tayi tana tsuke fuska kamar mai shirin yin kuka,MAMA dake zaune tana murmushi ta furta
"Ya isa haka nan kunga kada kusamin ita kuka kunsan dai hali ko?"
Like serious tayi maganan,dalili kenan sa yasa duka suka k'unshe baki amma duk da haka ba wai dainawa sukayi ba..
'Dan sakin fuska tayi sannan ta gaida MAMA da BABA ZUWAIRA dake ta faman shafa kanta tana murmushi..
Wuni guda cikin gidan amma sam basu ga BB ba,har suka tashi tafiya dan KHALEEL ma daya kawosu bai wani jimaba ya tafi sai yanzun da ya dawo d'aukansu,haka suka tafi basu sashi a idanun suba kuma cikinsu babu wanda ya tambaya yana ina..
********
Shiri sosai BB ya shiga yi cikin kwanakin ba tare da sanin kowaba dan ganin ya nemama kansa mafita kan abunda ke shirin faruwa da shi,a ganinsa hanya d'aya ce maganin wannan damuwan nasa.
Shigowarsa gidan kenan ya zube keys en a saman side drower had'e da wasu takardu,gefe kuma envelop ne sannan luggage daya gama zuba kaya cikinsu.
Tsayawa yayi yana kallon room en a hankali ya furta
"3 days to go...."
《《》》
Damuwa kam KHALEEL ya shigeta saboda rashin ganin aminin nasa duk kuma lokacin da zai je gidan sam baya ganinsa ko da ko zai wuni a gidan ba zai tab'a ganinsa ba,tun abun bai wani damunsa sosai har yazo abun na matuk'ar damunsa,waya kuwa ko da zai kwana yana kiransa bazai d'aukaba tun yana tura masa text har ya daina.
Yanzu'nma da yake zaune cikin parlor kiransa ya gama amma har ta k'araci kukanta ba'a d'aukaba,hak'uri ya bama kansa dan yasan ba d'aukan zaiyiba.
Yayi nisa cikin tunani UMMI da fitowarta kenan zata d'auka ruwa a fridge en k'asa ta ganshi zaune,kusa da shi ta isa sannan ta dafa shoulder ensa da yasa ya d'ago.
A hankali ya kalleta sannan ya k'irk'iro murmushi da bai kai har zuciba
"Lafiya kuwa SON kake....kwana biyu ina yawan ganinka cikin damuwa,kawai dai na kyaleka ne ko zaka yi hankalin sanarmin,amma shiru baka ce min komaiba na zuba maka ido naga iya gudun ruwanka ne kawai,me yasa kake sha'awar sama kanka damuwa?ko kuwa kana sha'awar wani ciwon ya kamaka ne?"
Kai ya girgiza mata,ajiyan zuciya yayi sannan a hankali ya furta
"Wallahi UMMI ni da KHALEED ne kwanakin nan sam na kasa gane inda ya dosa,idan na kirashi baya d'auka haka ko text na masa ma babu amsa,idan kuma naje gida nemansa bana samunsa,na rasa me yake damunsa da har ya kawo wannan chanjin a tsakanunmu cikin wad'annan kwanakin,na tambaya ko baya nan an cemin babu inda yaje yana garin, na rasa me yasa UMMI...."
Yanayin da yake magana ya nuna tabbas abun sosai yake damunsa.
"Tun tsahon wane lokaci hakan yake faruwa tsakaninku?"
UMMI ta tambaya idanunta kuma na kansa
'Dan d'age kansa yayi alaman tunani
"Ammmm!UMMI ina ganin kamar tun ranar dana miki tuni kan neman aurena da KHUBRA ne"
Shiru tayi tana tuna ranar da abunda ya faru tsawon watanni biyu kenan da faruwar hakan ai,yanayin da ya nuna har zuwa ficewarsa daga gidan,ita sai yanzunma ta sake yin wani hasashe kan hakan,d'an murmushi tayi sannan ta furta
"To Allah ya kyauta amma dai SON kabi komai a hankali kaji ko?Sannan ka tsananta addu'a kan abunda kake nema idan babu alkhairi a tsakaninka da abun cikin sauk'i ubangiji zai maka chanji mafi alkhairi kaji ko?...."
"To UMMINA na gode sosai,Allah ya barmin ke"
Kansa ta shafa tana murmushi
"Maza kaje ka kwanta kaji ko dare yayi,sannan kayi kuma addu'a kafin ka kwanta"
"To UMMI sai da safe"
Ya fad'a yana bin hanyan bedroom ensa,har ya b'acewa ganinta sannan ta juya tana girgiza kai alamar tausayi dan ta fuskanci abubuwa da dama na shirin faruwa
"Lallai ya zama dole na dage da addu'ah kan wannan rikitaccen al'amarin,Allah ya zab'a muku abunda yafi alkhairi baki d'ayanku......"
*2 DAY'S LEAP.*
Cab en ta parker a k'ofar gidan,cikin shiga ta alfarma kamar baturen daya fito daga k'asar amuruka jikin nan a murje kamar mai rayuwa cikin k'ank'ara,k'afarsa ya sako waje ko kafin ya k'arasa fitowa har cab driver'n ya gama fito masa da luggage's ensa dake bayan booth.
Sallamansa yayi sannan yaja luggage's en yana nufan get en gidan,kasancewar safiya ce sosai yasa ya tsaya a dai-dai k'aramar k'ofan knocking ya shiga yi saboda babu lallai ace mutanen gidan sun tashi a wannan lokacin..
Ya d'an jima tsaye kafin aka bud'e k'ofan,kallon tsoro game da mamaki BABA MAI GADI yake binsa da shi wanda yasa shi jaa da baya,murmushi mutumin yayi sannan ya shiga yana jaye da luggage's ensa,shi dai BABA gani yake kamar gamo yayi da wannan sanyin safiyar shi yasa ya kasa motsawa daga inda yake,wucewar mutumin kawai ya gani,faruwar hakan ke da wuya BABA ya shige d'akinsa,cikin seconds da basu fi 3-5 ba ya fito hannunsa d'auke da buta aiko da sauri ya fad'a toilet dake jikin d'akin nasa ta baya...
Kallon cikin gidan yake komai yana nan kamar yadda ya barshi sai dai gyara da gidan yake samu wanda ya hana shi tsufa,amma kam kamar yadda yake a wancan lokacin haka ya tarar da komai a mazauninsa..
Fitowansa kenan sanye da train suit da alama zai fita motsa jiki ne,shigowan mutumin yasa shi binsa da kallo tun daga nesa har ya dad'a matsowa kusa da shi kallonsa BB yake jikinsa duk ya saki saboda mutumin da yake gani gaba gare shi gani yake kamar mafarkin da ya saba ne yauma,murmushin da yayi masa ne yasa a hankali ya bud'e baki ya furta
"ABBA.............."
*~TEAM KHUBRA.~*
*_REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*©®2018*
*19/ʝųlყ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
*4⃣7⃣*
*M* urmushi ya sake yi masa da sauri kuma BB ya isa inda yake tsaye,hannu ABBA yasa ya jawo BB jikinsa,wani feeling's ne suka dinga sauka a cikin jikinsa wanda ya kasa bambance na mene ne a wannan lokacin,da k'yar BB ya iya komawa gefe sannan ya amshi luggage's dake hannun ABBA ya nufi hanyan komawa cikin gida.
A dai² lokacin MAMA,BABA ZUWAIRA,ASHNA da FATAHIYYA na kitchen kamar ko yaushe suna had'a break fast daya zama al'ada tun bayan barin su ZUHRA a gidan,duk safiya musamman idan akace weekends to tare suke shiga kitchen.
Karafniyarsu a kitchen en ne yasa BB yayi hanyan da sauri bayan ya ajiye luggage's en ABBA a gefe cikin parlor.
"MAMA zo kiga wani abun al'ajabi...."
Abunda ya fad'a kenan fuskarsa da matsanancin farin ciki,kamar zata tambayeshi kuma ta fasa,hannunta ta wanke sannan ta goge da duster dake saman k'ofa.
Fitowa tayi batayi maganaba,ba dan komaiba sai dan yadda taga fuskarsa a sake ba kamar sauran lokaciba da sam basa ganin sakin fuska daga gareshi baya ga haka kuma tasan abunda yake son nuna mata mai girma ne shi yasa tak'i yin maganar..
Tsaye yake ya juya baya hankalinsa nakan wani frame dake d'auke da photo'nsu dukansu sai dai babu HANEEF ajiki,a lokacin KHALEEFA ne k'arami.
Yanayin yadda yake tsaye ya juya baya ta kalla ita kam tasan ko daga mafarki ta tashi ba zata kasa gane shiba,jikinta a matuk'ar sanyaye taci gaba da matsowa,kaf jikinta rawa yake saboda bata gama gasgata zatontaba,ita kad'ai take fad'in
"Anya kuwa shi ne da gaske ko kuwa gizon da ya sabamin ne yauma.....to amma taya haka zai faru?.......idan har da gizo ne me yasa KHALEED zai kirani.....?"
Cikin wani salo ya juyo fuskarsa har lokacin cike da annuri daya gagara b'acewa daga samanta.
Still tayi a gurin bakinta bud'e saboda ganin mutumin da batayi tsammaniba a dai-dai lokacin da kuma bata tab'a tunanin faruwar hakan ba.
Hawaye ne suka shiga tsere akan fuskarta babu k'ak'k'autawa murya na rawa ta bud'e baki za tayi magana,da sauri ya d'aga mata hannu alaman bai son tace komai,daga haka ya juya tare da bin corridor,jikinta a sanyaye ta goge fuskarta sannan ta kalli BB dake tsaye yana murmushi,ta cikin idanunsa kana iya hango kyallin hawaye da yaketa k'ok'arin dannewa dan ganin baiyi kuka'nba.
Murmushi tayi masa itama lokacin da wasu hawayen suka sake biyo baya,da sauri tabi bayan ABBA daya riga ya shige,a bed room enta ta tarar da shi har lokacin yana tsaye bai zaunaba,k'arasowa tayi kanta a k'asa ta sark'e hannayenta,cikin wani irin murya mai cike da nadama da dana sanin abunda ta aikata a baya ta nufi inda yake,kan gwiwoyinta ta zube hannuna rik'e da k'afarsa,hawaye sai ambaliya suke a fuskar MAMA cikin kuka take fad'in
"Ka gafartamin abunda nayi maka tsayin wad'annan shekaru,duk da nasan ni mai laifi ce wanda bata cancanci hakan daga gare kaba,amma ba zan gusheba ina neman yafiyarka saboda abunda na aikata maka....Na yarda wallahi ko da mata uku zaka kawo bayana....bazan ce maka a'a ba,na amince...duk duniya bani da burin da ya wuce kace ka yafemin...."
Kukane yaci k'arfinta daya sata dole tayi shiru tana shashshek'ar kuka,hannu ya mik'a ya d'agota sai da ya goge mata fuskanta tukun yayi murmushi
"Indai har dan wannan ne to kisa a ranki na riga da na jima da yafe miki,fatan ubangiji ya yafe mana baki d'aya,nima kuma ina neman afuwarku na tafiya da nayi na barku tsayin wad'annan shekaru,na yanke hukunci cikin fushi..."
Murmushin tayi tana kallonsa sannan a hankali ta furta
"Duk laifi nane dana biyewa zuga da rud'in zamani,badan na biyewa son zuciyaba da duk haka bai faruba...."
"K'warai kuwa amma tunda yanzun kin gane laifinki komai ai ya wuce....ba kuma nason ki sake taso da wannan maganmaganara kinji ko....?"
'Dan mirmushi tayi hanunta akan fuskarsa take fad'in
"Har yanzun kana nan kamar yadda kake.....Zuciyarka mai kyauce da ba kowane ke da irinta ba,na godewa Allah daya bani miji irinka mai saurin yafiya da kuma tausayi,sannan kuma na godema mijina daya yafe min laifin da na aikata masa baka rik'e niba....."
Wasu hawayen ne suka kuma gangarowa,da sauri ya girgiza mata kai fuskarsa kuma ya d'an had'eta alama'n baya so.
Hannu tasa tayi saurin gogewa tana k'irk'irar murmushi
"Ina yarana suke sam banji alamunsu ba"
"Ka huta tukun kafin nan sai na kirawo maka su......"
"A'a bana son jin wannan magana sam...yanzun nake son ganin sanyin idaniyata maza a kiramin su,yanzun zan fito mu gana dasu"
Murmushi tayi
"An gama ranka shi dad'e..."
Tana fad'in haka tayi hanyan fita daga d'akin kuma tana waiwayensa.....
《《》》
Da sauri UMMI ta fito daga bedroom tana kiran KHUBRA da ZUHRA,Fitowa sukayi daga kitchen suna amsawa.
"Yawwa y'an albarka maza kuyi sauri ku shirya mana breakfast UNCLE yana hanya,yanzun ya kirani yake fad'amin ya kusa k'arasowa gida....UNCLE yayi mana zuwan bazata wollahi..."
"UMMI ai har mun jima da kammalawa ma"
Kallonsu tayi tana murmushi
"Da kyau y'an matana Allah yayi muku albarka"
Amsawa sukayi da ameen,kafun su juya wani kiran ya dad'a shigowa wayan dake hannunta,kallon wayan tayi da sauri kuma ta d'aga ganin MAMA ce,kafin tayi magana har ta rigata ko gaisawa ba suyiba ta ji MAMA'N tana fad'in
"UMMI'N YARA dan Allah ki turomin su ZUHRA yanzun KHALEEL ya kawosu...."
"To Allah dai yasa lafiya kike nemansu da wannan farar safiyar"
"Lafiya k'alau wallahi....ai da labari amma sai mun had'u...."
Yanda tayi magana ya tabbatar mata da abunda ta fad'a wani abune na farin ciki yake shirin faruwa koma ya faru.
"To Allah ya sadamu da alkhairi..."
Da sauri MAMA ta amsa da ameen tana y'ar dariya,ita dai UMMI sai mamaki take kome ya faru haka MAMA take neman yaran da wannan safiyar ohoooo,sai dai sun had'un kamar yadda ta fad'a taji koma mene...
"Kuna ina kuma.....?"
Da sauri suka lek'o daga kitchen
"Yawwa tunda kun gama maza kuzo ku shirya zaku je gidan MAMA..."
Tsalle sukayi suka rik'e juna kamar wad'anda suka jima basu jeba..
"Bari na tashi YAYA'NKU sai ya kaiku...saura idan kun shiga d'aki kada kuyi sauri ku fito kunji....kun dai san halinsa..."
Tsere suka shiga yi suna dariya,itama UMMI murmushi tayi tana binsu da kallon sha'awa..
*SOME HOUR'S LEFT.*
Suka shigo cikin parlor'n mutanen gidan gaba d'aya suna parlor,abun mamaki kamar ana wani taro na musamman,shigowa suka yi suna kalle-kalle sannan suka gaida MAMA dake zaune kusa da ABBA ta sha ado,idan ba wanda yasan MAMA ba a wannan lokacin babu tabbas ya ganeta saboda yanda ta koma kamar wata basarakiya..
Fuskarta cike da annuri take kallonsu
Kusa da ASHNA suka zauna cikin rad'a ZUHRA tace
"ASHNA bak'o mukayi ne kuma yau?"
Tana dariya tace
"Ke dillah ABBA ne ya dawofa baki gane shiba ne?"
Ido ta zaro tana fad'in
"ABBA fa kikace....dan Allah da gaske ko wasa?"
Hararar wasa tayi mata sannan ta dad'a sunkuyowa a hankali ta furta
"Banda abunki idan ba ABBA bane to wane zai zauna kusa da MAMA haka wanda ba muharraminta ba...."
"Ehhh to kumafa hakane...."
Bakinta a bud'e ta d'ago
"ABBA barka da dawowa"
Gaba d'aya parlor'n aka sa mata dariya,kallonsu tayi d'aya bayan d'aya tana sunk'e kai jikin KHUBRA dake mata dariya itama
"Sai da kika tambaya sannan kika gane ni kenan"
Dariya tayi bata iya yin maganaba,hannu ya bud'e mata a hankali kuwa ta mik'e ta nufi gurinsa,alama yayiwa KHUBRA da tazo saboda MAMA tayi masa bayaninta tun kafin ya ganta,sai dai kuma ganinta yasa shi jin wani abu game da itan,rungumesu yayi gaba d'aya ko sukayi luf a jikinsa dama ZUHRA ma ba bayaba ce gurin son jiki da ita da KHUBRA shi yasa amintar tasu tazo d'aya..
Nan a parlor suka shiririce ranar idan kaga sun motsa daga gurin to sallah zasuyi sai ko cin abinci abunda ke tashinsu kenan.
Wajejen bayan salla'n Asr motan su KHALEEL ta dad'a kunno kai,dan dama daya kawo su bai shigaba ya koma gida,sai yanzun da ABBA'NSA yasa shi kawosu shi da UMMI...
Anyi gaishe-gaishe UNCLE na shirin yin magana ABBA ya dakatar dashi ta hanyar yi masa inkiya..
Hira sosai ta yaushe rabo ake tsakaninsu duk wanda ya kallesu sai sun bashi sha'awa ganin yadda family biyu suka had'e kamar guda d'aya.
Sai dare suka shirya komawa gida,ZUHRA da KHUBRA na shirin bin UMMI ta daka tar dasu,gefe ta jasu saboda tana son yin magana da su
"Kunga yau ABBA ya dawo ko? to abunda nake so da ku,ku zauna kuyi masa wannan girke-girken naku shima kunji ko?....idan ya so bayan kun gama yi masa barka da dawowa da kaina zan dawo na d'aukeku kunji ko y'an albarka..."
Cike da murna ko dan dama kawai sunyi hakan ne dan kada ace sunyi ba dai-daba,sallama suka mata sannan suka juya..
UNCLE rik'e da hannun ABBA suma suna gefe UNCLE en ya furta
"Bansan dalilin da yasa kak'i yarda ayi maganar abunda ya faru ba.....ko mene ne ma'anar hanawan da kayi?"
"Uhmmm!kasan shi sha'ani irin wannan ba a buk'atar tado shi,sannan ba a buk'atar yaro ya sanshi saboda zai jima yana kallonka a matsayin mai laifi....Bayan hakama bana son yin