Showing 27001 words to 30000 words out of 139785 words
Chapter 10 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
kira taji ta a kashe. Gabanta ya shiga faduwa, kodai har yanxu Imran baya sonta? Idan haka ne ita kam ta shiga uku bata san inda zata saka rayuwarta taji daɗi ba. Dafe kansa yayi da yake jin tamkar zai bar jikinsa, maganganun Rahama suka shiga dawo masa akai, ransa yaji yana zafi zuciyarsa tana kuna wani irin bakin ciki yana taso masa tun daga ƙasan ransa. Yanzu kam babu abinda yake buƙata a yanzu irin ya samu kayan mayen da zasu fitar dashi daga cikin hankalinsa, ɗayar wayarsa ya ɗauka ya kira Amaan yana faɗin ya haɗo masa kayan maye masu zafi yanzun nan su haɗu a guest house ɗinsa. Tashi yayi da sauri ya shirya tare da ɗaukar car key ya fice daga gidan ransa a mugun ɓace. Har washe gari da aka saka Rahama a lalle wayar Imran a kasheta, Abbie da Mami da kuma Deejarh Galadanci sun iso kasancewar ta jirgi sukayi tafiyar. Nan kuma tun wajen ƙarfe goma na safe aka saka Rahama lalle a ɓangaren Hajja, zuwa lokacin wani irin zazzabi ya rufe Rahama wacce sai da aka yi mata allurai aka ɗora mata drip zuwa ƙarfe biyu na rana bata san wanda ke bisa kanta ba haka A Galadanci ya hana akaita asibiti tana can ɓangaren Hajja ta zuba tagumi ji take tamkar a fasa auren. Cikin yini ɗaya kacal Rahama tayi wani irin fita hankalinta. Sai bayan magriba dakyar Hajja ta samu ta sha fura da nono, wai itace gobe kamar yanzu ta zama matar Farook Galadanci, meyasa Imran ya karya mata zuciya? meyasa ya nuna mata kulawa idan har yasan babu soyayyarta a zuciyarsa meyasa yayi wasa da zuciyarta? Haske taga wayarta nayi, ganin mai kiran ta kauda idonta dan komai zai faru bazata ƙara ɗaga wayar Imran matawalle ba, ta amince zata auri Farook Galadanci, ta yadda zata zauna dashi a matsayin mijinta. Kusan kira goma Imran yai mata taki ta ɗaga. Ya kalli Al'ameen yana faɗin. "Akwai matsala dan taki ta ɗaga wayar gashi gobe ɗaurin aurenta taya zan zuba ido ta auri wani ina raye? No way.....!" Ya faɗa yana saka ƙafarsa yana tura centre table ɗin da ke tsakiyyar parlorn. "Nace a ɗauko min yaron nan a ɓatar min dashi kace a'a, dole nayi wannan plan ɗin da baka so ta haka kawai ne zan dakatar da wannan auren. Ni babu ruwana da komai duniya zata faɗa akai na inhar zan rayu da Rahama. Please ka kira min ita yanzu a wayarka." Al'ameen ya girgiza kai yana kallon Imran wanda tun jiya hankalin kowa a tashe yake kawai saboda Imran ɗin. "Kasan Allah wannan karon bazan saurareka ba Al'ameen get out of my face." Ya faɗa da ihun tsawa yana zubawa Al-Amin idanuwa. Ganin kiran Al'ameen yasa ta ɗauka. Cikin kwantar da murya yake faɗin, "Meyasa ina kiranki da wayar Imran bakya dauka?" Cikin wata irin murya take faɗin, "Mexan ce muku Al'ameen? bai faɗa maka ba munyi sallama dashi? Na sanar dashi mahaihifina zai aurar dani a gobe kamar haka na zama matar wani, toh me zan muku idan na ɗauki kiran?" Runtse ido Imran yayi yana jin maganganunta na taɓasa sabida a speaker yasa wayar. Al'ameen yayi gyaran murya yana cewa. "Bansani ba koke zaki iya tsayarda shi, kizo dan Allah Rahama dan ga Imran nan wai barin ƙasar zaiyi duk sabida aurenki, yana tunanin kamar kema kina son Farook Galadanci. Nidai nayi ƙoƙarin na fahimtar dashi yaki ya saurareni." Wani irin bugawa zuciyarta ta shiga yi tana cewa. "Kabashi wayar Al'ameen." Ta faɗa da wata irin murya. Kallan juna sukayi kafin Al-Amin ya ɗaga gira shi kuma da gudu ya nufi stairs, cikin nuna tashin hankali Al-Amin yace da ita. "Yaki karɓar Rahama please kiyi min taimako ɗaya zanxo yanzu na ɗaukeki a mota maybe idan ya ganki ya fasa tafiyar." Lokaci ɗaya ta fashe da kuka tana saukowa daga kan gado duk a hargitse take tana cewa, "Kazo ka daukeni Please Al'ameen ina son ingansa, idan ka ƙaraso ka kirani." Tasan zuwa wannan lokacin maigadi yana wurin sallah. Ɗakinsa zata fara zuwa neman makullin ƙaramar ƙofar dake baya. Hijab ɗin Hajja ta saka tabi ta cikin balcony sai sauri take zubawa ta damke wayarta wacce ta saka a silent. Dubawa ta shiga yi kusan makullai kala uku ta binciko ta fito dasu a hannunta haka ta rika gwada makullan har jikinta yayi sanyi dakyar ta samu na ƙofar ya buɗe. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta mai da ta rufe da makulin ta tafi dashi. Gudu ta farayi sosai gudun kar a biyota a baya, sai da takai ƙarshen layinsu ta tsaya tana mayar da numfashi. Kiran Al'ameen tayi tana faɗin yayi sauri tana ƙarshen layi, dan duk dauriya take sabida har yau akwai zazzabi ajikinta. Da wani irin speed ya ƙaraso wajen, gidan baya ta shiga ta zauna ta kwantar da kanta cikin seat hawaye taji suna cika a idonta, har suka hau titi babu mai magana acikin su har suka ƙarasa guest house ɗin Imran ta buɗe ta shiga cikin parlorn tana kwala masa kira. Tsayawa tayi cak tana maida numfashi, hangoshi tayi a tsaye ta yazuba hannayensa duka cikin aljihun wandonsa na jeans blue color. Da gudu taje ta rungume shi ta baya tare da fashewa da wani irin kuka mai cin rai. Kukanta yaji yana tabasa dan ko kaɗan baya son jin wannan kukan, Cikin shesshekar kuka take faɗin. "I was all alone imraan I'm completely alone..." Dawowa yayi gabanta yasa hannu yana ɗauke hawayen idonta a hankali yana cizon lips. Lokaci yayi da zai bayyanawa Rahama Abubakar Galadanci soyayyarsa, lokaci yayi da zai daina wahalar da zuciyarta da tashi. Zai bayyana mata abinda ta daɗe tana san ji daga gareshi, yau zai sanyayya zuciyarta da kalmar da be taɓa gayawa kowa ita ba, cikin wata irin hosky voice. "I love You." Ya faɗa yana subbatar goshinta zuwa hancinta, "I love You with all my life Rahama, ban taɓa son wani a duniya ba daga mahaifina sai ke, ina sonki R.. ina sonki R da dukkan zuciyata." Ya faɗa yana ɗora bakinsa akan nata, cikin wani irin salo ya fara kissing dinta da duka zuciya da gangar jikinsa. Wata irin gigicewa Rahama tayi, bata san lokacin da itama ta fara mayar masa da martani ba dan dama irin wannan ranar take jira. Jin kafafunta sun kasa daukarta yasa ya dauketa cak! ya nufi master bedroom ɗinsa cikin sassarfa still bakinsa na cikin nata yana yi masa wani irin sha tamkar zai canye bakin duka. A hankali yake blowing ko wace gaɓa ta jikinta cikin wani irin deep kisses wanda Rahama Galadanci bata taɓa karɓa ba a duk cikin rayuwarta. Gashi yau Imran Matawalle zai amshi budurcinta kuma tana jin bazata iya hanashi ba, dan da Farook Galadanci ya karɓi wannan budurcin da ta daɗe tana tattalawa, gara Imran ya karɓe dan dama shi ta tanadarwa duk iya shekerun nan. Ɗagowa yai ya zuba mata idanu da shanyayyun kwayar idan da suke ta wani irin lumshewa, hijab ɗin jikinta ya zare, ya miƙar da hannayenta ya zare mata rigar jikinta. A hankali yake bin na shanunta dake cikin farar bra da kallo kafin ya ɗora fuskarsa a tsakiyarsu yana sauke wani irin numfashi. Hannunsa ya ƙai ƙasa yana dauke skirt ɗin dake jikinta, ta janyo hannunta da kyar ta cusa su cikin sumar kansa tana janta cikin wata irin.........
Thank you#
Asmy b Aliyu#
Hajja ce#
Rahama galadanci#
Imran matawalle #
Farook galadanci#
Stop turned and find out...
Keep loving and supporting it...
[11/12, 9:33 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
16....
Da saurin Ummy ta hau stairs tana huci, ji take kamar zata mutu dan bakin ciki. Ummi na shiga ɗakin ta fisgota ta zuba mata wani gigitaccen mari wanda yasa ta nemi ganinta ta rasa na wucin gadi. "Wato duka kalaman da mahaifinki yayi maki babu wanda ya shiga a kunnen ki ko? Wato ma kin nuna mishi cewar shi ɗin banza ne barin gida zakiyi da gaske ko? Kinsa a ranki kin biyewa zuciyarki kawai barin gida zakiyi saboda ga Imran Matawalle ubanki ko Rahama?" Ummi ta faɗa cikin rawar murya tana dafa bango saboda shock. Rahama na hawaye tana girgizawa Ummi kai take faɗin, "Da ayimin aure da wanda bana kauna Ummi ƙara na bar maku gidan duka." Ummi kallonta kawai take, tamkar ba Rahama ke magana a gabanta ba, saboda idan wani ya faɗa mata Rahama zata iya faɗin haka zata iya ƙaryata hakan nan take. Cikin zafin rai Ummi ke magana. "Karuwancin zakije ku cigaba dayi dashi kenan? da gaske abinda idanunmu ya gane mana cikin wayar Farook shi ya faru dake a zahiri? kin sai da mutuncin ki wajan Imran Matawalle?" Ummi ta faɗa tana ƙoƙarin tare kwallar da zata xubo mata. Duk da Rahama tayi masu laifi mai girma wanda zaiyi wuya su manta hakan. Amman zubar hawayenta musamman ita dake matsayin uwa zai zama mata dafi a cikin rayuwar Rahama. Cikin kuka take faɗin, "Ban taɓa zina ba Ummi ki yarda da dani." Ummi ta girgixa kai tana sakin wani murmushin da babu nishaɗi a cikin sa. "Bazan yi maki baki ba Rahama, amman ki sani soyayyar Imran Matawalle a gareki sai ta zamar maki masifa da bala'i acikin rayuwarki, tunda kin zabi ki rayu dashi fiye damu dake matsayin iyayenki." Idan har tace kalaman Ummi basu girgizata ba tabbas tayi karya, haka bata da kalaman da zata fahimtar da Ummi a yanzu, maybe sai anan gaba. Jan bag ɗinta tayi tabar ɗakin Ummi na bin ta da ido har ta fita. Abbanta da Abbie da Hajja duka suna tsaye acikin falon buɗe baki Hajja tayi tana kallonta cike da sabon ɓacin rai take faɗin. "Auh an baki lasisin zuwa yawon iskanci kenan? zaki koma da jakar nan ko sai na kakkaryaki da hannu na ƴar banza mai baƙar zuciya." Hajja tayi maganar sounding so very angry. "Makaranta zan koma idan Abba da Ummi sun huce zan dawo." Rahama ta faɗa muryarta na karyewa haka hawaye na cika idonta lokaci ɗaya. "gidan ubanwa zaki dawo?." Abba ya faɗa a tsawace, "Ai na yafewa ɗan gidan Matawalle ke, wallahi bacin Hajja da take a matsayin uwa a gareni da ta hana na tsine maki albarka, da yau sai na tsine maki albarka Rahama, amman ko yanzu kije kiji shiga duniyar inda daɗi zaki gane, ki tafi kibar min gida bana son na ƙara ganin fuskarki acikin gidana." Abbie zaiyi magana da sauri Abba yabar falon itama Rahama juyawa tayi tabar falon tana jin yarda take tafiya tamkar bada qafafunta take taka kasa ba. Haka ta riqa ratsa maza wanda har sun halarci wurin ɗaurin aure tana jan dogon hijab ɗinta jikinta tana rufe rabin fuskarta. Tafiya kawai take ba tare da tasan inda zataje ba, wata zuciyar ke gaya mata kota koma ta hakura da soyayyar Imran Matawallen? Wata zuciyar kuma tana faɗa mata kiyi tafiyarki ki samu farin cikin ki, dan idan kina tare da iyayenki har abada bazaki taɓa samun farin ciki ba. Tasan yadda iyayenta ke tsananin kaunar ta, musamman ma Abbanta da kuma Hajja, fushi su na ɗan wani lokaci ne zasu sauko su nemeta. Adaidaita ta samu tace ya sauketa a b.u.k.
Kallonta Ihsan kurum takeyi ganin yadda ta shigo janye da katon akwati, rabonta da ita tun daren da aka kai Imran Matawalle station, sai dai suyi waya. "Ke lafiya?" Ihsan ta riƙeta tana kallon yanayinta, ganin tamkar bata cikin hankalinta yasa ta riko kafadunta. Zube gwiwoyinta tayi a ƙasa sai a lokacin hawaye suka samu nasarar zubowa cikin fuskarta. Ihsan duk ta rikice da yake itama shigowarta kenan ta gama lectures ɗin 10 to 12, duk ta zatama mutuwa aka yiwasu Rahama ɗin ganin tamkar bata cikin haya cinta. Hannayenta ta riqo tana tambayarta a rikice take faɗin. "Lafiya Rahama ko mutuwa aka yi muku ne?'' Wata irin runguma Rahama tayiwa Ihsan tana jin wani irin sabon ɓacin rai na lullube mata zuciyarta, ita kanta ba zata ce ga dalilin da yasata kukan ba, iyayenta gaba ɗaya sun tsaneta basa duba farin cikinta.Ihsan tayi rarrashi tayi juyin duniya Rahama ta faɗa mata damuwarta ta faɗa mata cewa ba komai gameda ƙarasawa wajan gado tayi kwanciyarta. Kafin la'asar wani mugun zazzabi ya rufeta tana ta kwanciya ita kuma Ihsan dama yau friday zataje gidan Auntynta weekend dan asalin su ƴan jahar Taraba ne, aure ya kawo Auntynta Kano. Sallama ta yiwa Rahama dake kwance har lokacin, wacce sallah ce kawai ke tada ita. Ihsan tayi tafiyar ta cike da jin haushin Rahamar na kin gaya mata damuwarta. Runtse idonta tayi sai lokacin ta tuno da wayarta, da sauri ta cirota cikin hand bag dinta, miss calls ta gani da yawa harda na Aunty Kausar, sai na Imran ashe wayar silent ta sakata. Dialling lambar Imran tayi tamkar jira yake ya ɗaga tana jin lokacin da ya saki wata irin nannauyar ajiyar zuciya. "Are You okay?" Ya faɗa can ƙasan makoshi, muryarsa kurum da taji ya tafiyar mata da kusan rabin damuwarta. Hawaye na tarar mata a ido, cikin rawar murya take faɗin, "Banda lafiya Imran ina hostel." Da sauri ya katseta yana faɗin, "Yaushe kika koma hostel?." Cikin kuka tace. "Abba ya koreni daga gidansa." Kalmar yaji wani iri bai taɓa tunanin Abubakar Galadanci zuciyarsa irin ta kafiran farko bace sai yau, duka-duka shekarun Rahama nawa da za'a koreta a gidan? "Kijira ni yanzu ina zuwa." Da haka ya katse wayar. Dama yana cikin asibitinsa. Dr Fahad ya kira a waya ya masa bayani cewar zai bar asibiti sai zuwa gobe koda yamma zai sakewa leqo wani uzuri ke gabansa yanzu ya kula da komai. Tun a hanya ya tsaya ya sayi alluran da yasan dole ta karɓesu da kuma maganunna sannan ya nufi makarantar b.u.k. Fuskarta kurum yake kallo yadda ta kumbura tayi sukutum, ransa yaji ya kara ɓaci da sauri ya ɓalle marfin motar ya fito ya buɗe mata front seat ta xauna ya mai da ƙofar ya rufe. Har yabar cikin makarantar fuskarta a rufe take. "Kashe kanki zakiyi ne?" Ya faɗa mata da murya marar amo. Ta ɗago tana kallonsa hawaye na cika a idon ta. Bai ƙara magana ba har suka isa gidansa. Ganin tana neman faɗuwa yasa shi dagata da dukkan karfinsa ya nufi entrance ɗin shiga gidan yana jin yarda jikinta ya ɗau wani mugun zafi. Kai tsaye master bedroom ya wuce daita ya kwantar kan lafiyayyan bed ɗinsa. Mota ya koma ya ɗakko ledojin takeaway da ta maganunna. Abinci ya kai mata da kansa ya cire mata dogon hijab ɗin dake jikinta yabi doguwar rigar dake jikinta da kallo marar nauyi, haka ƙamshin turarenta na wankan lalle sai hawar masa kai yakeyi, ya ɗauke kansa yana faɗin taci abinci ta gama ta karbi allura. Karba tayi baifi spoon biyar ba ta faɗa masa ta koshi. Haɗa alluran ya shiga yi cikin rawar murya take faɗin. "Nifa bana son allura, magani kawai zaka bani." Ya girgiza kai yana faɗin. "Idan baki karɓi injection ɗinnan ba xaxxabin nan bazai sauka ba." Yayi maganar sounding so cool. Tana ji tana gani yayi mata allura har guda biyu, ya kuma yi mata umurnin ta kwanta. Zama yayi cikin soofa yana danna waya shiru ya ziyarci ɗakin kowa da abunda ke cin zuciyarsa har kusan minti goma sha biyar sannan ta samu bacci. Imran ya rage mata sanyin ac da yaga yayi mata yawa, ya jamata duvert. Note yayi mata ya aje a kan bedside ya russuna ya subbaci goshinta. Da sassarfa yabar ɗakin gamida rufo mata ƙofar. Motarsa yaja yabar gidan, kai tsaye gidan su ya wuce zuwa lokacin an fara kiraye-kirayen sallar magrib. Kallon gate ɗin gidan su Rahama kurum yasa yaji wani sabon ɓacin rai yana dawo masa.
Dama a cikin gidan Matawalle akwai wani Ƙaton masallaci wanda mutanensa ke gabatar da sallar magrib da isha'i a cikinsa. Ganin motoci da yawa a cikin compound ɗin gidan nasu ya san mahaifinsa yana da baki yau. Ya hura iskar bakinsa dan yana son yaga mahaifinsa yanzu, kuma yasan zaiyi wuya ya bashi damar ganinsa. Sumar kansa ya shiga hargitsawa da hannun yanata zama a mota har aka kammala sallar ba tare da ya fito daga cikin motar ba. Yana ganin mahaifinsa ya fito tare da mutanensa suna binsa a baya ya yatsina fuska. fitowa yayi daga cikin motar da sassarfa ya cimma Dadynsa da yake ƙoƙarin shiga cikin babban falonsa na karɓar baki. Ganin tahowar Imran ya ɗan dakata har ya ƙaraso mutanen sa kuma cikin falon suka shige aka bar senator Matawalle a tsaye. Imran na zuwa ya wani rungume Daddyn nashi, murmushi Daddy yayi yana ɗan buga bayansa gamida ɗagosa. "Meya faru kuma my son?" Imran ya shafa kansa yana faɗin, magana zamuyi Daddy, kuma naga kanada baki." Matawalle ya jinjina kai, "Kaje kayi sallah magrib, bayan isha'i idan nagama da baƙin sai ka dawo" Zai yi magana Matawalle ya ɗaga masa hannu yana faɗin. "Idan mutum ya mutu sallah ce za'a fara tambayarsa, nasan bakayi sallah ba, Please kaje kayi tukunna." Matawalle ya faɗa yana barinsa a wajen. Kai tsaye part ɗinsa ya nufa ya rage kayan jikinsa wanka ya shige ya yi gameda ɗauro alwallah ya fito yayi sallah. Kai tsaye kitchen ya nufa dama yana da Kitchen acikin part ɗin nasa. Cikin mintuna ƙalilan ya haɗa bakin shayi mai zafi ya dawo cikin falon ya xauna yana juyasa a hankali, duk tunaninsa yana kan Rahama. Yana gama sha ya haɗa kayansa cikin ƴar ƙaramar trolley yaje ya kai mota. Ana fara kiran sallar isha'i ya nufi cikin masallaci, tare da shi akayi sallar isha'i. Gabaki ɗaya hankalinsa na kan mahaifinsa shima kuma Matawallen hankalinsa yana kan Imran ɗin yadda yaga yanayin Imran ɗin yasan yazo da magana mai muhimmanci, dan haka ana gama sallar yajashi har cikin part ɗinsa. Matawalle ya zauna a cikin kujerun da suka kawata falon yana kallon Imran ɗin cike