Showing 24001 words to 27000 words out of 139785 words
Chapter 9 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
tare da kai goshinta tayi sujud tana kuka tana rokon Allah ya bata Imran koda kuwa duniya zata juya mata baya. Har aka kira asubahi ta tashi tayi sannan ta sake zama tanaci gaba da addu'arta. Wajan karfe shida taji muryar Abbanta a ƙasa yana cewa ta fito. Bata sauya komai ba dama hijjab ne a jikinta ta ɗauki jakarta da waya ta sakko. "Abba ina kwana?" Yai mata banza yana jin haushin gaisuwar, jiki a sabule ta juya gurin Ummy tana gaisheta the same thing da yadda Abba yai mata haka Ummy ma. Hawaye suka ziraro mata Abba yace ta wuce su tafi. Suna fitowa Rahama ta ga motar Al-Amin zai shiga gidan su Imran, ji tayi kamar ta kirashi ta tambayeshi ina Imran ɗin? Sai dai babu dama dan Abba kiris yake ta kuma yin wani abun ya kaita lahira.
Suna zuwa hospital Abba ya kaita wajan gwajin HIV sam bataji komai ba saboda tasan ita ba ƴar iska bace. Akai gwaji ya tabbatar da Rahama bata da ita, nan ma hankalin Abba ya kwanta sai dai yanzu bashi da buri irin yaga ya kaita ɗakin miji, yasan hankalinsa sai yafi kwanciya akan cewar tana zaune a gida. Kai tsaye gida ya mayar da ita sannan ya fito ya nufi wajan aikinsa...
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce 👈
#Rahama Galadanci
#Imran Matawalle
To be continued..... Next page
[11/12, 9:33 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
14....
Ayinin ranar asibiti yayi sa sabida akwai aiki sosai da zai yi, haka kuma yayiwa mata biyu tiyata, bai samu kansa ba sai la'asar. Kai tsaye gida ya nufa, kana kallon idonsa kasan cewar ya gaji, haka yana jin matukar yunwa. Wanka ya farayi ya haɗe sallar azahar da la'asar lokaci ɗaya. Waya yayi da yaron dake kula da part ɗinsa yace ya shiga cikin gida ya karɓo masa abinci, dole ce kawai zata sakashi cin abinci Mommy dan ya gaji da yawon cin abincin bisa titi saboda kwata-kwata baya jin wani daɗin sa. baifi minti goma ba mai masa hidima ya shigo da katon tray kusan abinci kala huɗu ya jero aciki sanin halin uban gidan nasa, ya ɗauki wanda zai iya ci ya mayar da sauran. Sai yanzu ya tuno da wayarsa wacce Al-ameen ya kawo masa, itama yana shiga hospital bai ƙarabi takan wayar ba a kashe yabarta. Yanzu kam yana son ya kira Rahama yaji halin da take ciki dan yinin ranar tana manne a cikin zuciya da ruhinsa. Wayar da yake kiranta da ita tana cikin mota da brifecases ɗinsa dan bata ma da wannan layin na wayarsa wanda yake hannunsa yanzu, dan kusan lambobin ma'aikatan sane ajikin wayar. Wayar tana da muhimmanci a wajensa shi yasa da wuya ya kashe ta. Waya ya ɗaga ya kira Musbahu mai masa hidima, cikin minti biyu kuwa ya bayyana a falon cike da girmamawa, car key Imran ya miƙa masa yana faɗin ya ɗakko masa brifecases ɗinsa da wayarsa a mota. Ya karɓa ya juya yabar falon dan cika umurnin Imran Matawalle. Anan cikin falon ya koma ya kwanta cikin soofa yana jin tamkar zazzabi zai rufeshi sabida gajiyar da yayi. Musbahu na kawo masa wayar ya kunnata tare da kiran layin Rahama, ga mamakinsa lambar Rahaman a kashe take kuma duka layukanta. Tunani ya farayi Allah yasa ba karɓe wayar akayi ba, bari ya barshi zuwa anjima zai kara gwada kiranta ya gani, Idan har bai sametaba a wannan lokacin yasan akwai matsala. bari yai bacci nan da zuwa magariba idan ya tashi zai ƙara kiranta, yau dai bashi da ra'ayin taɓa komai na kayan maye da haka ya manna pillow cikin fuskarsa sai da ya tabbatar ya kashe wayoyinsa gamida murzawa ƙofar falon key ya kure sanyin a.c sosai, bai daɗe ba kuwa ya samu bacci.
Tun safe take ta zama a ɗaki kiran da ta yiwa Imran yafi sau hamsin amma a kashe. Cikin awanni ƙalilan tayi wani irin rama dan tun safe babu abunda ke cikinta sai ruwan lipton, ji tayi komai na duniyar nan nayi mata kuncin. Bayan la'asar ta riƙa jin dirar motoci a cikin gidan nasu, gabanta yayi wani irin faɗuwa wanda bata taɓa jin kalarsa ba, ji tayi tamkar anyi mata dole da san ganin ko suwaye, ta yaye labulen window ta leƙa idonta suka hango mata Hajja da wasu mata biyu wanda take ganin fuskar Mamin su Farook Galadanci, daga bayansu ta hango fuskar Farook Galadanci wanda ya koma gefe yana amsa waya, kallo ɗaya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar farin ciki. Sake hango manyyan akwatuna na alfarma taga Hajja tasa ana fitowa dasu daga cikin wata ƙatuwar jeep ɗin da suka zoda ita. Nan take zuciyarta ta bata cewar kayan lefenta ne. Wani irin rawa kafafunta suka shiga yi mata. A hankali ta shiga jada baya tana girgiza kai hawaye na rolling akan kyakkyawar face ɗinta. Daɓas ta zauna akan marbles tana girgiza kai tamkar zatayi hauka haka take ji dan komai ganinsa take tamkar a mafarki. "Ya Rabbi kasa mafarki nakeyi.!" Ta faɗa tana fashewa da wani irin mahaukacin kuka mai cin rai. "Please Imran where are you?" Ta faɗa da wata irin murya, ta haɗe kai da gwiwa ta shiga rera kuka, yanzu kam ta tabbatar ba mafarki takeyi ba, tabbas da gaske Abbanta auren dole zaiyi mata. "Allah ka ɗauki raina kafin zuwan wannan rana." Gabaki ɗaya bata jin zata iya rayuwar aure da wani idan ba Imran Matawalle ba. Turo ƙofar ɗakin da take ciki akayi, lokaci ɗaya ta daga kai tana kallon kofar still hawaye na zubar mata. Aunty Kausar ce ƙanwar mahaifiyarta baki ta buɗe tana kallon Rahama ta girgiza kai ta karaso cikin ɗakin gamida zama gefen bed tare da jawota jikinta tana faɗin. "Daɗina dake Rahama sam baki da hankali, wallahi kurciya na yawo saman kanki. Yanzu dama duk irin nasihar da nayi maki akan kiyi wanka ki canja kaya kafin baki su shigo bakijiba? kalli kanki dan Allah, haka kikeso Farook ɗin yazo ya ganki?" Aunty Kausar ta ɗaure fuska ta kalleta tana faɗin," Oya tashi minti goma na baki kiyi wanka ki fito ina nan ina jiranki." Ganin yadda ta sha toka tasan Aunty Kausar bata ɗaukar raini haka kuma ana tsoronta shi yasa ta tashi tabi umurninta ta nufi toilet. Da wani irin kallo Aunty Kausar ɗin ta bita tana faɗin," Stupid girl." Tana shiga cikin toilet taji wani irin kuka yazo mata, da sauri ta rufe bakinta. Tafi minti biyar a haka dakyar ta miƙe tsaye ta cire kayan dake jikinta ta zuba su cikin basket, watsa ruwa kawai tayi batareda ta saka sabulu ba, ina ruwanta da wani sabulu ba dai yace yaji yagani ba? Toh wallahi Farook Galadanci sai yayi da nasanin auranta, dan sai ta fito masa da ainahin true color ɗinta. Koda ta fito daga wanka fuska babu wani walwala still Aunty Kausar tana zaune a ɗakin tana jiranta har ta fitar mata da kayan da zata saka. lece ne ɗan kasar sinigal mai ratsin baki da ja acikinsa da aka kawata da wasu irin flowers, ɗinkin riga da skirt ne Ummi ta ɗinka mata shi bata taɓa saka su ba kwata-kwata, dan kayan basu wuce wata ɗaya da yinsu ba, tareda Ummy ta ɗinka da nata lece ɗin kalar Orange da baki ita kuma nata baki da ja. Kayan kawai ta saka ta saka mayafin kayan baki buɗe Aunty Kausar take kallonta tace. "Ahaka zaki fita babu powder babu turare? Wai ke wace irin macce ce.?" Ta faɗa tana daka mata tsawa. Zata fara murza ido Aunty Kausar tace. "Idan kika yarda kika fara min wannan kukan naki wallahi jikin ki zai gaya maki, dan ko a gaban Farook sai na jibgeki, kuma kinga na jibgi banza, bari na gaya miki ni ba irin Aunty (Ummy) bace da kika raina. Ki dawo nan gaban madubi ki gyara wannan fuskar taki ki saka turare ko kyayi daraja." Ta faɗa tana daka mata tsawa rai a mugun ɓace da nuna babu wargi. Cikin wani irin yanayi Rahama ta ƙarasa gaban mirror dressing ta shiga murza powder. Bayan ta gama ta zizarawa fararen idanunta kwalli, turare kala biyu ta saka duka Aunty Kausar na tsaye tana kallonta. Bayan ta gama tajuya tana kallonta Aunty Kausar wacce ta ɗan saki murmushi ganin wani irin mugun kyau da taga tayi. Lokaci ɗaya kuma ta daure fuskarta tare da ɗan jan kunnenta tana cewa. "Idan muka fita kikayi wani abu da zai bada fuskar cewa bakya son auren nan wallahi ranki zai ɓaci." Ta saki kunnen nata ta riƙe hannunta suka bar ɗakin. Hango Hajja tayi a ƙasan ƙaton rug an shirya mata kayan cin abinci akai tana ci cike da natsuwa da jin daɗi, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin farin ciki. Acan cikin dining area Farook Galadanci ne da small Mommy's ɗinsa suma suna cin abincin su cikin nishaɗi, da alamar har sunyi sallolin dake kansu kasancewar tafiyar mota ne bata jirgi ba. Kallonta Farook Galadanci kurum yake yi yadda tayi masa wani mugun kyau, gashi tayi wani irin cika lokaci ɗaya komai na halittar jikinta ya canja, sakamakon ya daɗe ba ganta ba. Wani irin yawu ya haɗiya lokaci ɗaya ya rufe idonsa yana hango kwanaki uku kacal da zai mallaki wannan jikin duka. Da sauri ta cire hannunta daga cikin na Aunty Kausar ta nufi Hajja da gudu kuka nazuwar mata, wani irin runguma ta yiwa Hajja, kuka mai cin rai ta fara yi, baki buɗe Hajja ke kallonta tana cewa, "Duk murnar auren ne haka kuma harda wani kukan farin ciki Rahama? Toh ma wai mekike yiwa sauri kuma? kwanaki uku ne kawai ya rage fa." Da wani irin yanayi Rahama ta ɗago tana goge hawayen idonta ta buɗe baki zata faɗawa Hajja bata son aurenta da Farook Galadanci idonta suka haɗu cikin na Aunty Kausar dake zaune cikin falon tayi mugun haɗe rai, lokaci ɗaya Rahama ta haɗiye maganar da take shirin faɗawa Hajjan tuno gargaɗin da Aunty Kausar tayi mata a ɗaki. Hajja ta kalleta tana faɗin ƴar uwarki sai gobe zata ƙaraso ita da iyayen nata, ta kira wayarki a kashe, dama kuma ɗaurin aure kawai za'ayi anan, shagulgulan biki duka a gidan Usman za'ayi su idan angama sai akai ki gidan ki tunda dama a can Abujan zaki zauna, karatun ki kuma ban san ya zaiyi dashi ba yawo da gantali akan hanya ya sameku keda mijin naki, kullum kuna kan hanyar Abuja zuwa Kano, ni dai babu ruwana idan aka sanƙameku a hanya, dan wannan shegen karatun da ina da iko dana dakatar dashi, toh amma ya na iya Usman da Abubakar da Farook duk suna bayan karatun nan. Ni wallahi babban abun damuwata shine, babu wata ƙibar amarci da zakiyi." Kallon Hajja kawai take dan batama fahimtar abinda take faɗa, duka tunaninta yana kan yadda zata tsayarda wannan auren koda shine abu na karshe da zata gabatar acikin rayuwarta. Da ladabi ta shiga gaishe da small Mommy's ɗin Farook, ganin irin kallon da Farook keyi mata mai cike da shauki yasa ta sulalewa tabar falon ta koma room ɗin ta. Kwanciya tayi akan bed ɗinta ta shiga raira kuka, turo ƙofar ɗakin nata akayi. Harɗe hannayensa yayi akan kirjinsa yana kallonta. Gyaran murya yayi, tashi tayi zaune tana yi masa wani irin kallo. Ya saki murmushi yana faɗin, "Da alama bakya farin ciki da wannan auren ko?" A tsawace take faɗin. "Akan me zanyi farin ciki dashi? Ni yaushe ma nace ina sonka Yaya Farook? Kamanta alƙawarin da kai min na cewar zaka dakatar da auran?" Ƙarasowa tayi gabansa cike da masifa da bala'i take faɗin. "Wannan kaɗai yasa naji na ƙara jin haushinka, kuma bana sonka bana kaunarka dan ban taɓa sonka ba wallahi." Farooq ya ɗage kafaɗa yana faɗin. "Ai na daɗe da fahimtar haka Rahama, tunda dai ni ina sonki ai baki da matsala." Cike da haushi tace. "Ai kuwa aurena zai zame maka bala'i da masifa a cikin rayuwarka Farook Galadanci, dan sai na tarwatsa dukkan wani farin cikinka, dan haka ina shawartarka akan ka hakura da wannan soyayyar da kake yi min kar ta zame maka danasani mai yawa a cikin rayuwar ka." Idanunsa ne suka kada sukayi ja, lokaci ɗaya kuma ya fisgota zuwa jikinsa ya matseta acikin kirjinsa, ji tayi tamkar zai rabata da rabin jikinta, taji yana cewa. "Ke wacece da zaki tsayar da soyayyar da nake yi maki Rahama?" Ya faɗa a tsawace, bata taɓa ganinsa a haka ba, ya shiga girgiza kai yana faɗin. "Ke baki isa ki tsayar da wannan auren namu ba, haka baki isa ki tsayar da soyayyar da nake yi maki ba ya kamata kisan da wannan Rahama Abubakar Galadanci, idan kuma zaki gwada, toh ga fili ga mai doki." Ya faɗa yana turata da karfi. A tsorace ta dafa bango tana binsa da wani irin kallo har ya fice daga cikin dakin. Ihu ta shiga yi tana sake fashewa da kuka. Da dukkan karfinta ta shiga hargitsa kayan ɗakin duka, kwanciya tayi a tsakiyyar rug ta shiga juya kanta side by side tamkar mai aljannu, numfashinta taji yana wani irin katsewa tana cikin wannan hali aka turo ƙofar ɗakin, da sauri Ummi ta nufeta tana kiran sunanta, ɗagota tayi taga bata motsi gabanta ya faɗi. Hannunta ta ɗora akasan hancinta, da sauri ta ajeta ruwa ta gani akan bedside ta ɗakko ta shiga goga mata cikin fuskarta. Wata irin doguwar ajiyar zuciya Rahama ta sauke. Ummi ta kirata cikin wata irin muryar a hankali ta soma buɗe ido ganin Ummi yasa tayi ƙoƙarin miƙewa zaune take, da sauri ta taimaka mata , hawaye na zubar mata bakinta na rawa Ummi ta girgiza kai tana karewa ɗakin kallo take faɗin. "Meke damunki?" Ummi ta faɗa tana kallonta hawaye na zubar mata take faɗin, "Ummi bana son Yah Farook me yasa dole sai shi! haka zaki zuba ido Abba yayi min auren dole?" Numfashi Ummy ta sauke tana cewa. "Amman dai kin san babu abunda zaisa auren nan ya fasu, meye na wahalar da kai Rahama? Ai gara ayi auren ko hakan zaisa ki dawo cikin hankalin ki. Ki tashi kiyi sallar magrib ki fito Kausar na nemanki." Da haka Ummi tabar mata ɗakin. Har bayan sallar magrib Imran wayarsa a kashe ko miqewa tsaye bata iyayi sabida rabonta da abinci tun safe kiran Aunty Kausar ya shigo a wayarta, ɗauka tayi taji Aunty Kausar ɗin nayi mata masifa, aje wayar tayi ta fito. A ƙaramin falon Ummi ta sameta, wani kallo Aunty Kausar ta rika yi mata har ta ƙarasa ta zauna akan rug ta saukar da kanta kasa hawaye na cika idon ta. Wani cup Aunty Kausar ta miƙa mata fuska babu walwala, babu musu ta karɓa takai bakinta, maltina ce da madara rabi kawai tasha ta sauke cup da rawar murya take faɗin. "Na koshi." Wani kallo ta rinqa yi mata tana cewa. "Kibar ganin zakiyi aure Rahama, ba wani babban aikina bane na tashi na zaneki kin san halina." Dakyar Rahama ta kafa baki ta shanye. "Ki saurareni da kyau, daga yanzun nan abubuwan dake cikin fridge na falon nan sune ruwan shanki na kwana uku, maganin sanyi ne, dama kuma kin saba sha ba sai nayi maki bayanin suba, sannan daga yanzu har zuwa ranar da za'a ɗaura maki aure tare zamu riqa kwana dake
A dayan ɗakin Aunty (Ummy)." Daman kuma Kausar ɗin ba aure gareta ba, mijinta ya daɗe da rasuwa haka bata taɓa haihuwa ba tana zaune a gidan Hajiya Yaya wacce itace yayarsu Ummi dukansu, haka kuma tamkar itace mahaifiyarsu. Babu abinda yafi ɗaga mata hankali sai na ɗaki ɗaya zata riƙa kwana da Aunty Kausar, "Kije ki dauko duk abunda kike buƙata ki dawo nan." Babu musu Rahama ta miqe tsaye tana jin yadda kafafunta ke wani irin rawa. Tana shiga ɗakinta ta murzawa ƙofar ta key da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga typing ta turawa Imran. Tana ta zama har akayi isha'i sanin halin na cin Aunty Kausar yasa ta shiga wanka ta saka kayan barci masu nauyi tayi sallah ta ɗauki abubuwan da xata buƙata ta nufi ɗakin da Aunty Kausar ta sauka dake kasa. Aunty Kausar ce ta debo mata tuwo da miya wanda yaji naman kaza tace ta canye tabata plate ɗin. "Aikin sa batacin tuwo fa, kin manta ne kawai, a samu wani abun abata." Ummi ta faɗa tana kallon Kausar. "Mekike so a dafa maki?" Murya can ciki tace, "Bari naje na dafa indomie." Da haka ta nufi Kitchen, tana shiga tsaye tayi kawai acikin Kitchen.
*******
Sai da ya rama duka sallolin dake bisa kansa, dan sosai yai baccin, sai kusan karfe 9 na dare sannan ya kunna wayarsa yana so ya kira Rahama. Ai kuwa da sakonta ya faracin karo dashi ya wani haɗe fuska yana bin sakon da kallo tamkar bai fahimci meke cikin sakon ba. Yaushe suka fara irin wannan wasan da Rahama? kar tasa zuciyarsa ta buga, wane irin aure kuma ana zaune ƙalau? Wani irin murmushi ya saki wanda baya tattare da nishaɗi, kiran wayar yayi bata ɗaga ba haka ya ƙara kira lokacin tana cikin dafa indomie. Ganin kiransa yasa ta ɗaga wayar da sauri gamida kashe gas ɗin duka. ƙofar Kitchen ta baya ta fita zuwa cikin balcony ganin babu motar Abbanta yasa ta sauke ajiyar zuciya. "Rahamaaa.." Ya Faɗi cikakken sunanta a can ciki-ciki. Kuka kawai ta fashe masa dashi tana rufe bakinta kar ajita take cewa. "Imran Abba aure zai yi min da Yah Farook nan da jibi daurin aure." Imran ya cije lips na sama cike da dakewa yace. "Duk a sabida wannan dalilin zaki ɗaga hankalinki?" Ya faɗa in I don't care manner, da alamar zancen bai ratsashi ba. Ta buɗe ido tana faɗin. "Da gaske nake maka Imran." Ya sake cije lips "Allah ya nuna mana lokaci lafiya." Ya faɗa yana kashe wayarsa duka. Wayar tabi da kallo lokaci ɗaya tana