Showing 21001 words to 24000 words out of 139785 words
Chapter 8 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
masa da kuka yana sake matse shi cikin jikinsa yana faɗin. "Daddy dan Allah kace su bari, Daddy zuciyata zata fashe sabida Rahama just free him , please Daddy ka taimaka..." Ganin yadda Imran ya shiga tashi hankali ne yasa Matawalle yi musu alama Akan su sakesa, nan da nan suka saki A Galadanci wanda ikon Allah ne kawai yake riƙe dashi da tuni ya haɗiyi zuciya saboda haushi. Kallansa ya ɗora kan Matawalle yana jin da yanzu fa shine da matsayin Matawalle a yanzu, da tuni shine kila zai bada order cewar a kamashi, amma dubi yadda Matawalle yasa aka yi masa cin mutuncin da be taɓa tsammani ba. Lallai mulki yana da matuƙar girma, ji yadda aka haɗu da ƴan sanda aka dizgashi a gaban yara. Ƙarasawa yai inda Rahama take, wacce aka watsawa ruwa ta dawo cikin hankalinta. Yana zuwa ya janyo mata hannu besaurari kowa ba ya nufi waje da ita. Motarsa ya buɗe ya cillata a baya sannan ya shiga ya zauna tare da jan motar da wani mugun speed ya.
Kallansa ya mayar kan D.p.o yana faɗin. "Kuna tuhumar ɗana da aikata mene?" D.p.o ya sunkuyar da kai yana faɗin. "Yallabai bamu san cewa yaronka bane, an kiramu ne akan rape case." Da mugun mamaki Matawalle yake kallan D.p.o kafin ya maida kallon kan Imran wanda gabaki ɗaya tunaninsa yana kan Rahma, yasan tabbas yau mai kwatarta a wajan A Galadanci sai Allah, rintse ido yai yaji mahaifinshi ya dafa masa shoulder cikin kulawa yake tambayarsa. "My son meye gaskiyya? Am so confused." Cikin takaici Imran yake faɗin. "Daddy babu macen da na taɓa kusanta, in fact bana sha'awar yin zina bare nayi. Daddy ko ina jin sha'awar mace a duniyar nan to Rahama ce, ko zan lalata mace zanyi raping Rahama Daddy, all my desire, my happiness, my life and my care yana wajan Rahama. Yarinyar nan sharri tai min, ban san kuma dalilinta na yi min hakan ba." Sanetor Matawalle ya sake dafo ɗan nashi cikin so da kulawa yace." Wacece kuma? Gaya min wacece ita da har ka bata waɗannan abubuwan?" Matawalle ya manta wace Rahama saboda sam bata gabanshi shi yasa tun a ranar da ya ganta a ɗakin Imran ɗin be sake sanyata cikin ransa ba. Ko yanzu ma da suka zo station ɗin be lura da ita ba har A Galadanci ya fita da ita. Kallansa Imran ya yi yana cije lips tare da jan numfashi yace. "Daddy ka manta Rahama? Please Daddy ka dena mantawa da ita saboda tana da muhimmanci a gurina." Cike da kulawa Matawalle yana shafar kansa yace. "Insha Allahu my son." Sannan ya maida kallansa ga D.o.p yana cewa. "Kaji dai yace be aikata ba, kuma nayarda Akan Bai aikata ba. Saboda Haka a rufe maganar zan bada 2 millions a bawa yarinyar karna sake naji an tada ita, idan Kuma ba Haka ba , zansa Ai min maganin yarinyar, karta sake kallan inda ɗana yake, D.p.o tell her." Cikin biyayya D.p.o ya amsawa da Matawalle, sannan ya kama shi suka nufi hanyar fita. Cikin motarsa yasa Imran suka zauna a baya sai D.s.s a passenger seat da driver, gaba da baya kuma securities ne cikin tasu motocin sannan Al-Amin a tashi shima, ana zuwa junction ya ɗauki hanyar gidan su, suma suka wuce.
Suna shiga layin Imran ya kurawa side ɗin gidan su Rahama ido, suna zuwa wajan gidan a lokacin suna jiran gate man ya buɗe musu gate ya sake kallan upstairs na gidan su Rahama, ji yake tamkar ya buɗe motar yaje gidan yaga a wane yanayi take, dan ya san A Galadanci ba zai taɓa maida ita school a wannan yanayin ba. Ji yai an riko masa hannu, ya juya yana kallan mahaifin nashi, "Tunanin me kakeyi? Ina tunanin an gama wannan maganar sai dai ka kiyaye gaba Haka kasan irin kalar mutanen da xaka riqa mu'amala dasu Imran." Numfashi yaja yana sake waigawa ya kalli gate ɗin su Rahama, dai-dai lokacin mai gadi ya buɗe musu suka shiga. "Ina so na huta ne Daddy." Cikin nuna soyayya Matawalle yace. "Alright Allah ya tashe mu lafiya." Buɗe musu motar akai Imran ya fita ya nufi apartment ɗinsa yana jin zuciyarsa na wani irin buguwa, tabbas Rahama na cikin tsaka mai wuya. Upstairs ya nufa, yana shiga ya nufi akwatinsa na sirri da babu wanda yasan dashi a cikin gidan, bottle ɗin beer ya ɗakko tare da zama ya buɗe, bakinsa ya kafa kawai ya fara tittilawa cikinsa yana jin wani irin mugun zafi a kirjinsa. Sai da ya shanye one bottle tas sannan ya faɗi a ƙasan rug, idanunsa a lumshe yana sauke numfashi a hankali, muryarsa cikin wani yanayi yake cewa. "Am so sorry R.. Please forgive me..." Hawaye ne suka shiga zirarowa daga cikin kyawawan idanunsa suna ɗiga a ƙasan rug....
#Asmy B Aliyu
#Hajja ce👈
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#A Galadanci
#Sanetor Matawalle
To be continued.... Next page
[11/12, 9:33 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
13
Kansa ne ya shiga wani irin juyawa duk da cewa idanunsa a rufe suke amman ji yake tamkar zai faɗo saboda wani irin jirin mugun nauyi da yai masa, ga wani irin jiri da yake ji tamkar wanda yai hajijiya. Yana nan ƙasa kan rug a kwance, damuwa tayi masa yawa, yana so yasan a wani hali Rahama ke ciki? Sai kawai ya dinga jin wani irin ƙamshi yana bugar masa cikin hancinshi, ido ya shiga ƙoƙarin buɗewa amma yaji ya kasa, gashi yaji sam zuciyarshi bata amince da wanda yake a cikin ɗakin ba. Ita kuwa Humaidah ganinsa a cikin wannan yanayin kaɗai ya bala'i faranta mata rai, cikin yauki kai kace yana kallanta ta isa inda yake baje, a gabansa ta tsugunna tana kallan kyakkyawar face ɗinshi da ta yi wani irin fayau sakamakon kuka da yayi. Yatsanta ta ɗora saman leashes ɗin girarsa tana wani irin shafata cike da salo. Bottle ɗin beer ɗin ƴa janyo tana karkaɗawa taji babu. Hannu Imran ya ɗaga dakyar tare da riƙe mata nata da take faman shafa masa gashin gira, cikin yanayin maye yake magana. "R.. Ki yafe min, ban san me yasa nake yin abinda zai janyo miki duka ba, ban san me yasa nake kasa ƙin shan beer ba duk kuwa da nasan bakya so, please ki yafe min." Ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya, a take kuma wani wahalallen bacci ya ɗauke shi. Kallan yadda yake furucin kawai Humaidah takeyi, yanayin yadda yake motsa lips nashi kaɗai yasa taji wani mugun feeling ɗinsa ya dirar mata, ƙasan zuciyarta kuwa so take tasan wacece wannan R ɗin da yake bawa hakuri? Tamkar tana tsoran ya buɗe ido ya ganta a kusa dashi, saurin kai lips nata tayi kan nashi ta sumbata tare da sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ji take kamar an cire mata wata ƙaya a cikin zuciyarta, lumshe ido tayi tare da kwanciya saman cikinsa tana jin wata irin nutsuwa. Da tasan kullum zata dinga shigowa ta sameshi cikin wannan yanayin tabbas da ba zatai fashin shigowa side nasa ba. Wai yau itace a jikin Imran Matawalle? Matashin saurayin da duk cikin faɗin duniya take masifar so, ta rasa me zatai dan taja hankalinsa gareta amma ta rasa, komai zatai bata burgeshi, Mommy kullum maganarta zata san yadda zatayi ya so ta amma har yanzu shiru. Haka Humaidah ta dinga jinta kamar wacce sukai aure dashi, sai sake mannewa take a jikinsa bata wani fargabar wani yazo ya ganta akanshi.
****
A ɓangaren A Galadanci kuwa, tunda ya ɗakko Rahama yake jin zuciyarsa na tafasa, yana jin yadda take kuka wanda kukan tana yinsa ne kawai dan tasan an kuma lalata duk wata alaƙarta da Imran, dan abinda Matawalle yaiwa Abbanta tasan ya sake dasa wutar tsanarsa a cikin rayuwarsa. Mai gadi yana buɗe musu gate A Galadanci yai parking tare da fitowa ya shaƙo wuyan Rahama, ido ta dinga zarowa jin yana neman rabata da numfashinta, suna shiga parlor ya hankaɗata gefe ta bugu da bayan kujera, nan da nan taji tana neman rasa wani sashe daga cikin tunaninta. Ummy ta fito daga kitchen dan taji shigowar motar maigidan, ganin Rahama rakuɓe a bayan kujera tana kuka yasa ta dafe kirji tana fito da idanuwa waje, cike da tashin hankali take tambayar. "Lafiya naganki a gida Rahama?" Cike da ƙunar rai Abubakar Galadanci yake magana. "Gwarake a cikin gidanki kika ganta, wai ni ya zanyi da shaiɗaniyar yarinyar nan ne Hafsat? Ya zanyi da fitinar yarinyar nan? Ina murna na kaita makaranta zata rabu da wannan tsinannan yaron ashe duk shirme nayi? Wallahi sam sunan da nai miki khuduba dashi be dace dake ba, kuna can kuna yawon iskancinku shine ƴan sanda suka kamaku ko?" Cikin kuka Rahama ta shiga girgiza kai tana faɗin. "Abba wallahi ba haka bane, ina s..." Bata ƙarasa ba ya isa inda take ya zabga mata mari. "Karki maidani wani shashasha dan ubanki, idan ba yawon iskanci ba taya zan ganki da da ɗan gidan matsiyacin can? Ina ma ace ban sanki ba Rahama, ina ma ace Ra'ees shine kawai gudan jini na a duniya da yanzu bansan wannan baƙin cikin da kike ƙunsa min ba." Ummy ya kalla wacce ke tsaya tama rasa abinda zata yi saboda tsabar ɓacin rai. Ji tai A Galadanci na cewa. "Hafsa ina san yanzu ki duba min gaban Rahama ki gani ta bashi virgin ɗin ko kuwa, idan har gurin akwai ɗan ragowa zanje na lallaɓa Farooq ya rufa mata asiri ya aureta, gobe idan Allah ya kaimu zan kaita hospital ai mata gwajin cutar nan, in babu zan dawo da auranta da Farooq ya dawo kwanaki uku, na gama magana." Yana gama magana ya haye sama.
Rahama kuwa babu maganar da ta ɗaga mata hankali irin ta cewa idan aka dawo daga gwaji nan da kwanaki uku za'a aura mata Farooq Galadanci. Ta sake fashewa da kuka tare da rarrafawa wajan Ummy, kafarta ta kamo tana kuka mai gigitarwa tana faɗin. "Ummy wallahi banyi zina ba na rantse da Allah Ummy, please forgive me bazan sake ba dan Allah ki bawa Abba hakuri ya barni naci gaba da karatu na dan Allah Um.." Wani marin ta sake ji a duka kumatunta wanda yasa ta saurin haɗiye maganar da takeyi. Ummy ta janyota kamar zatai kuka take faɗin. "Ki gaya min Rahama me kikeji a tare da Imran? Wane irin abu yake miki wanda tun kina ƙaramarki muke fama dake akanshi? Me yake baki Rahama tell me." Kuka kawai Rahama keyi, cikin sarƙewar murya take faɗin. "Ummy please dan Allah karku aura min Ya Farooq, wallahi Ummy ina san karatuna wallahi Allah ina yin karatu Ummy ku taimaka min." Fizgota tayi tana janta suka hau stairs, cikin tsakiyar ɗakinta ta hankaɗata tare da rufe ƙofar tasa mata key, idanun Ummy jawur ta kalli Rahama tana faɗin. "Oya cire pant ɗin." Rahama ta sake fashewa da kuka haka kawai taji tana jin muguwar kunyar Ummy ta ganta ba pant, duk da tasan mahaifiyarta ce babu wani abinda zata iya ɓoye mata, yanzu kam ji tayi bazata iya ba, ko Imran bataji kunyar yadda takeji yanzu ba. Ganin taki cirewa yasa Ummy sake yowa kanta tana cewa. "Kin cire kosai na falla miki mari? Ni zakiji kunyar nunawa jikinki? Ko kin manta matsayina a fannin lafiya? Naga wadanda suka fiki komai dan ubanki, dallah tashi nayi abinda aka sani ina da abinyi." Jikin Rahama ya shiga rawa, gani take tamkar tana cirewa Ummy zata gano abinda Imran yai mata, tana kuka ta zaro pant ɗin. Kan gado Ummy ta nuna mata tana cewa. "Kija skirt ɗinki sama ki kwanta, kika buɗewa wani katan banza ma bare ni da na haifeki." Kirjin Rahama yana bugawa ta rintsa ido tare da yin sama da skirt ɗin taje kan gadon ta kwanta, banda bawa Ummy hakuri babu abinda take yi. Sosai Ummy ta gama bincikar Rahama, ganin bata siyar da mutuncin ba yasa Ummy sauke wata muguwar ajiyar zuciya, dan sosai taji tsoran ace Rahama ta bawa wani ɗa namiji mutuncinta. "Amma kema kina shaye-sayen da yakeyi ko?" Ummy ta jefawa Rahama wannan tambayar bayan ta tabbatar da cewa virgin ce. "Ummy wallahi ban taɓa shan abun da ba halattace ba." Sauke numfashi Ummy tayi tana faɗin. "Amma me yasa kike biyewa Imran Matawalle? Shin ke bakya san kare martabar mahaifinki? Rahama me yasa kike biyewa yaron can? Mekike yi a cikin rayuwar sa?" Rahama na share hawaye ta sunkuyar da kai, ji take kamar zuciyarta zatayo waje tace. "Ummy ina san Imran, ban san meyasa hakan ba, the only thing kawai zuciyata tana bashi muhimmanci Ummy, kuma wallahi Ummy Imran mutumin kirki ne, shi kansa besan me yasa yake shan beer ba. Kema kiso Imran Matawalle Ummy, kinga maraya ne be taso tare da mahaifiyarsa ba." Wani mugun tsaki Ummy taja tare da wurgawa Rahama kallan banza tana faɗin."Kema rabaki zamuyi dashi, saboda kowane iyaye suna son ganin yaransu cikin mutane nagari, ke kuma kin rasa dawa zaki hurɗa sai da, mashayin giya, kuma ɗan gidan maƙiyinmu." Girgiza kai Rahama ta shiga yi, a rayuwarta bata san taji ana cewa Imran mashayi, duk lokacin da taji hakan tana jin tsanar wanda ya faɗa a cikin ranta, sai dai yanzu mahaifiyar ta ce ke ce masa haka, dole kuma tayi kokari wajen ganin bata tsaneta ba. Ficewa Ummy tai daga ɗakin, wajan Abba ta nufa wanda yana tsaye hannunsa da waya a jikin kunnansa taji yana cewa. "Hakane Hajja, abar auran nan cikin kwanaki uku kacal idan ba haka ba bansan ya zanyi da yarinyar nan ba." Daga can ɓangaren Hajja ke faɗin. "Toh shikenan zan yi kokari naga gobe ko jiba nazo Kano, kila idan tana ganin ido na ba zatayi wani abun ba." A Galadanci yace. "Shikenan Hajja sai kinzo, yanzu zan kira ɗan uwana shima na sanar dashi." Sukai sallama, duk da yaga Ummy a cikin ɗakin be kulata ba ya kira Alhaji Uthman Galadanci wato mahaifin Farooq Galadanci ya sanar dashi cewa a dawo da bikin nan da kwana uku, Alhaji Uthman ya tambayesa kome yasa? A Galadanci ya tabbatar masa da cewa yaron Matawalle ne yake san hure mata kunne. Nan da nan shima ya amince, sukai sallama kowa ya ajiye wayar. Kallan Ummy yai yace. "Kin dubu abinda na saki?" Tace. "Na duba komai kuma yana nan." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Auranta da Farooq nan da kwana uku, ina so kisa ido sosai akanta idan aka samu matsala kece." Kamar zatai masa magana sai kuma tai shiru dan taga a sama yake kiris yake jira kai masa gardama ya huce akan ka. Rahma kuwa da kyar ta miƙe, room ɗinta ta koma tana jin zuciyarta na tafasa, shin yanzu ya za'ai tasan halin da Imran ke ciki? Tunawa tayi da wayarta, cikin sauri ta miƙe, down stairs ta nufa ta ɗakko jakarta ƴar ƙarama da wayar ta ke ciki tai saurin komawa cikin dakinta, kiran Imran ta shiga yi bata shiga, shi kuma tun a lokacin da ta some a station ya jefar da ita be sani ba Al-Amin ya ɗauke masa ya kashe ta, be bashi ba ya manta ya wuce da ita gida. Gaba ɗaya ta sake shiga cikin damuwa, bacci ya gushe daga idanunta kwantawa gamida yin shiru tana tunanin makomarta.
********
Ana kiran sallar farko Imran Matawalle ya fara buɗe idanunsa, jin kamar mutum a jikinsa yasa shi kallan saman cikinsa, gashin attachment da yaji ne yasa shi saurin tureta yana buɗe idanuwa. Cikin sauri itama Humaidah ta miƙe, yanayin yadda taga yana kallanta ya sa zuciyarta tsinkewa, ta faraja da baya shi kuma sai kallan jikinsa yakeyi yace. "How dare you zaki shigo har cikin ɗakina? Tsabar ke ƴar iskaci akai na ma zaki kwanta?" Humaidah ta narke fuska, murya a sanyaye ta shiga yi masa magana. "Haba Imran meyasa kome zan maka baka appreciating ne? I saw you yesterday yadda ka shigo side ɗin na kana da buƙatar mai kwantar maka da hankali, that's why nazo kuma zuwa na ya yi amfani a yadda na ganka." Wani irin tsuka yayi tare da shaƙo wuyanta, a yadda yake jin ransa tsab zai iya ganin ya kaita lahira. "Ina ruwanki da Rayuwata ? Ko mutuwa kika ga zanyi ina ruwanki? Humaidah kin takurawa rayuwata, nace miki bana san alaƙarmu dole ne? Ko ce miki akai idan na rasa matar aure zan iya auranki ne? Leave my life Humaidah, ki barni kije kiyi rayuwarki idan ba haka ba.." Ya faɗa yana sake matse mata wuya ta fara kakarin mutuwa ya sake ta. "Get out of my room kafin na kasheki a gurin nan." Da gudu ta fice tana wani buga kafafuwa. Shi kuwa juyawa yai cikin fushi ya dinga cilli da pillows ɗin kan gadonshi. Wai me yasa ake masa kallan bad man ne? Me yasa kowace shaiɗaniya tazo da shaiɗancinta sai ta tunkaro shi? Wajan mirror ya nufa yana kallan kansa, gani yai be yi kala da wanda za'a cewa mutumin banza ba, banda wanda yasan yana shan giya, duk inda zai fita ya shiga ba za'a kirashi da mai shanta ba, amma ya rasa me yasa mata suke yi masa haka. Juyawa yai tare da fadawa kan gadonsa, Rahama ce ta faɗo masa a rai, yai saurin tashi tare da, zuge glass window yana hango gidan su Rahama, ko a wane hali take ciki oho. Koma menene shi ya janyo mata, da beje club ba da wannan abun ba zai faru ba bare har ta baro school taje inda yake. Rintsa ido ya yi yana cizon lips.
Rahama kuwa a dai dai wannan lokacin tana kan sallaya tana sallah, addu'a kawai take Allah ya kawo mata mafita da zata gujewa auran Farooq Galadanci dan bata jin ko ɗigon kaunarsa da aure, Imran Matawalle shine zaɓinta, mafarkinta kuma burinta, shi kaɗai ta mallakawa ranta, zuciyarta da kuma gangar jikinta. Hawaye take