Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 139785 words

Chapter 34 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1016

Ads at the middle of Article

sake zaro ido tana dafe kirji. "Haka nace kace? Ni duk kasa bazan kuma zuwa na kallesu ba." Tana maganar tana turo baki tare da yatsina fuska tana wani kawar da kai gefe. Yayi dariya har haƙoransa suna bayyana, kamo fuskarta yai tai saurin rintsa ido tana lasar leɓenta da harshe, kallanta yake cike da wani irin so yana faɗin. "Su Aunty Kausar ne kawai bazaki iya haɗa ido dasu ba? Ko harda Daddy wanda shi har tukuici ya bamu ni dake?" Da sauri ta buɗe ido tana zaro su baki buɗe tace. "Kace masa mene?" Imran ya sake sakin dariya ganin duk ta birkice masa yana janyota yake faɗin. "Nace Daddy kin bani farin ciki jiya da daddare, yace mu zabi ƙasashen da zamuje honeymoon." A kunyace ta shigar da kanta cikin kirjinsa tana faɗin. "Wayyo Allah na ni dai baka kyauta min ba." Sake rungumeta yai yana cewa. "Kinsan babban jin daɗin Albi?" Girgiza masa kai tayi ba tare da ta dago sun haɗa ido ba, Imran yace. "Bazan faɗa miki ba sai kin bani tukuici." A hankali ta ɗago tare da sumbatar kuncinsa tace. "Gashi nan na baka gaya min." Imran ya ɗaga girarsa yana kamo gashinta da tai parking ɗin yace. "No ba wannan ba gaskiya, ki bani abun ji.. Wow wasan nan so awesome baby." Haɗe rai tayi dan yana gama faɗa taji gurin ya sake ɗaurewa ta girgiza masa kai kawai tana cewa. "Kawai bar maganar ba sai ka gaya min ba." Cikin da yake a shafe ya shafa yana faɗin. "Haba Albi karkice min ke raguwa ce, I swear na yanzu bazai kai na jiya ba, please dear bari kiji ma." Ya fara ƙoƙarin ɗage mata mini skert ɗin, cikin tashin hankali da ruɗewa Rahama ta fara hawaye tana bashi hakuri. Rintsa ido kawai yai saboda yadda yakejin wani iri a jikinsa, shi gaba ɗaya ma ji yake tamkar be taɓayi ba. "Okay na bari muje kici abinci." Tashi sukai ya kama hannunta suka nufi dining bayan ya ɗauki basket ɗin, saman table ya ajiye sannan ya matso da ita sosai jikinsa suka sakko down stairs, kitchen suka shiga ya ɗakko plate da spoon sai cup sannan suka koma up stairs ya zauna akan kujerar dining ɗin tare da janyota, kan ƙafarsa ya ɗorata sannan ya buɗe warmers ɗin, funkaso ne da yayi matuƙar kyau anyi masa miyar gyaɗa da tasha naman rago, ya buɗe flask ɗin wanda shi kuma kunun madara ne sai ƙamshi yake tasha. A cup ɗaya ya zuba musu sannan ya fara feeding ɗinta, yana bata itama tana bashi har sai da suka ƙoshi sannan yajata suka koma cikin sofa. Langaɓe kai tayi tana shafa lallausan quarter millions ɗin fuskarshi, baki a ture tana yamutsa girarta take cewa. "Ni bazaka gaya min abinda Daddy yace ba ko?" Imran yai murmushi yana riƙo ƙugunta idanunsa akan fuskarta ganin yadda take shirin yi masa rigima yake cewa. "Zan baki but sai na sake ɗanɗanawa idan kin yadda dan naga kina san jin saƙon Daddy." Cike da shagwaɓa tana wani bubbuga jikinta a nashi tana faɗin. "Ni dai dan Allah kayi hakuri idan ba so kake kasa na mutu ba." Idanuwa ya ɗaga yana faɗin. "Bazaki mutu ba Albi na, Insha Allahu sai kinyiwa Mah takwara, first born ɗin mu ina son baby girl." Rahama tasha toka tana turo baki. "Cewa akai maka zan haihu?" Tayi maganar tana shirin sauka daga jikinsa, ya riƙe ta sosai yana cewa. "Toh bazaki haifa min baby's ba?" Ɗaga kai tayi cikin gaskiyarta sai yace. "Fine Albi tunda bazaki haifa min ba Humaidah ta haifa m..." Ai be ƙarasa ba ta wani tureshi ranta a mugun ɓace, bakinta na rawa take faɗin. "Ai daman nasan kana san kayarka sai kaje kaita mata cikin tana haihuwa, idan ta tashi ta haifi dubu karewa." Ta shiga fisge jikinta Imran yai saurin ɗagata gabaki ɗayanta ya nufi master bedroom tana cewa. "Ba abinda zaka min, ni ka rabudani bazan sake baka jikina ba." Kin sakinta yai har suka hau kan bed ya manna ta cikin jikinsa yana sumbatar fatar wuyanta zuwa tsakiyar kirjinta. Nan da nan jikinta ya fara rawa, tsigar gashin ta suka fara miƙewa, tuni ta fara mantawa da rigimar da take masa tana mayar masa da martanin saƙon da yake isarwa cikin magudanar jininta. Shi kuwa cikin ransa wata sassanyar kaunartace take sake shigar masa rai, yana addu'ar Allah ya bashi ƴaƴa daga cikin jikinta, yana so yaga Rahama ta haifa masa yara, yana sha'awar ya gansa da ƴaƴa kamar guda biyar ace kuma duk nashi ne, yana fatan Allah ya bashi badan halinsa ba. Gabaki ɗaya ya tattaro ta zuwa saman cikinsa yana ɗage mini skirt ɗin jikinta, jikinsa rawa kawai yakeyi babu abinda yake buƙata irin yajisa a jikinta saboda zuciyarshi har wani girgizawa takeyi musamman idan ya tuno daran jiya. "Albi please ki barni na kasance tare dake, ki dena haramta min abinda yake halak a gareni. Albi idan ba'a gurinki ba a wajan waye zanyi abinda nayi daren jiya? Ke nakeso, ke kaɗai zuciyata ta yarda tayi amfani da ita, zo gareni ki ƙarasa mallake duk wani gurbi da yai saura a jikina, don't say anything my love." Yana kaiwa nan taji an fama mata ɗinkin gurin. Wani irin ƙara ta saki tare da ƙanƙameshi taja kuka tana bashi hakuri, ina Imran Matawalle yayi nisan da hankali zai iya taro shi har yaji kuken da ake yi masa. Cikin wani gigitaccen yanayi ya maida ita saman jikinsa yana sake sumbatar duk inda bakinsa yai karo dashi a jikinta. Tun tana jin wata gigitacciyar azaba da wani irin birkitaccen zafi har ta denaji ya koma kuma tana matuƙar jin wata nutsuwa a cikin zuciyarta, ta dinga rirriƙeshi yai azamar sanya bakinsa cikin nata, bai bartaba sai da ya tabbatar da ita kanta ta samu nutsuwa sannan shima ya samu tashi tare da sakar mata wani narkakken kiss a tsakiyar kirjinta. Gefe ya koma yana sauke numfashi hannunsa ɗaya riƙe da nata ya wani damƙeshi kamar ance za'a fisge masa ita. Juyawa yai yana yi mata wani irin kallo yaji ta bashi tausayi, shi kuma gaba ɗaya idan har ya samu ya kasance tare da ita mantawa yake da wani ƙananun shekarunta da rashin wayewar da batayi ba akan sha'anin. Ya dafe goshinsa da ɗaya hannun yana wani rintsa ido kafin ya juya ya matsa kusa da ita ya rungumeta yana faɗin "Sorry Albi am out of control nima bansan haka nake ba daga jiya zuwa yau ne, you're so sweet to me, I love you Albi so much and I'm so glad you are mine, Ina sanki fiye da yadda bakina zai iya furta miki yadda nake jinki a zuciyata." Bata kalleshi ba tasa hannunta ta ƙanƙame nashi daya rungumeta, jin irin yadda take riƙe shi ne ya tabbatar masa da cewa itama tana cikin love. Ya ɗagota gabaki ɗaya ya kifata a jikinsa yana shafar tsakiyar bayanta, magana yake mata cikin hosky voice nashi idanunta a rufe tayi luf da ita kamar wata mage. "Daddy ya min alƙawari yadda kika bani farin ciki zaije wajan Abba ya nemar miki gafararsa." Da wani irin sauri Rahama ta ɗago kai ta zubawa Imran idanunta masu kamar na cat waɗanda suke sake jefa duk wani ɗa namijin daya haɗa ido da ita cikin soyayyarta. "Are you sure Albi?" Imran yasa lips ɗinsa sama da ƙasa ya matso breast ɗinta ta rintsa ido yana faɗin. "Am very sure." Da wani irin farin ciki ta faɗa cikin jikinsa tana murna, ta ɗago tare da kamo fuskarsa takai bakinsa saman goshinsa ta sumbata tana sake kwantar da kanta saman kirjinsa take faɗin. "Millions thanks to Daddy, Wayyo Allah na ALBI bakiji zuciya ta ba, bakiji farin cikin da nake ciki ba." Imran ya shiga shafa lallausan gashinta da yake fitar da wani irin ƙamshi. Kanta ya ɗago jin kamar hawaye suna sauka a fatar ƙirjinsa, kamar jira take ya ɗago mata da fuska kawai ta fashe da kuka yace. "Menene kuma?" Rahama ta shiga juya kai tana faɗin. "Amma Abbana zai hakura kuwa?" Da mamaki Imran ɗin yake cewa. "Why not?" Rahama ta sake fashewa da kuka cikin shasheka take faɗin. "Abba na yana da wahalar sakkowa, ina tsoran kar garin gyarawa a sake ɓatawa ina tsoro Imran." Ta ƙarasa maganar tana maida kanta cikin kirjinsa. "Za'ai nasara Insha Allahu, kedai kici gaba da addu'ar nan taki sai kiga ta sanadin wannan auran namu sun shirya sun dena gabar da sukeyi." Jinjina kai ta shiga yi tana faɗin. "Insha Allahu." Daga haka ya sake ja musu duvert suka ƙanƙame junansu, babu daɗewa bacci ya ɗauke su dukansu.


******


Humaidah ce zauna gefen gado tana faman kuka, da kyar aka samu aljanunta suka tafi bayan sun ɗauki alwashin sai sun raba auran Imran da Rahama tunda har basa bawa Humaidah farin ciki, yanzu da aka samu suka tafi ne Mommy ta dawo da ita cikin bedroom, cikin ɗar-ɗar da ita Mommy ke faɗin. "Bari nasa a kawo miki breakfast kiyi." Da wata irin murya Humaidah ke faɗin. "Banaci Aunty." Shiru Mommyn tayi tana kallan yadda take zubar da hawaye, cikin lallashi take cewa. "Dan Allah Humaidah kiyi shiru, ni wallahi da zakiji ta shawarata da kinbar Imran ɗin nan saboda gabaki ɗaya ba ajinki bane, keda kike da manyan maza me zakici da wannan yaron? Dan Allah Humaidah ki kyaleshi hakan nan." Cije lips Humaidah tayi tana jin tamkar ta shaƙo wuyan Mommy, cike da masifa take cewa."Idan kin gaji da taimakamin ki kyaleni, kinsan yadda zuciya ta takeyi akan Imran Matawalle? Kinsan yadda nake tsammanin son mu kasance nidashi? Idan bazaki iya taimaka min ba kawai ki kyaleni Aunty." Tana kaiwa nan ta zari mayafinta ta fice, mota ta shiga cikin tashin hankali ta shiga kiran Sooraj. Taita ringing ba'ai peeking ba Humaidah ta zunduma wani ihu tana dukan sitarin motar. Cikin matse kafafuwa ta nemo lambar Yak tace gatanan zuwa wajansa, fatanta kawai ya yarda su kasance da juna dan wani lokacin Yak bashi da mutunci tsab zai iya disgata gashi ita kuma tana da bukatar zuwa inda za'a rage mata zafi. Tun a parlorn gidan nasa ta dire jakar da mayafinta kai tsaye ta nufi upstairs tana zuwa ta murɗa handle ɗin master bedroom ɗinsa, idanunta ne sukai tozali da shi kwance da wasu kirɓa-kirɓan mata huɗu kan bed, kirjinta yai wani irin bugawa suka haɗa ido dashi ta zabga masa harara tare da cewa. "Ashe kana da wasu dan wulakanci kasa nazo?" Bata jira cewarsa ba kawai ta juya a fusace ta dauki jakarta da mayafin ta fito, Sooraj ne yaja mata tangari a wajan wasu mazan, da ya dauki wayar ta da bata kalli wannan takaicin ba. Kai tsaye gida ta wuce tana jin wani irin azababban ciwon kai......


(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300




#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida Makarfi
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/6, 1:56 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




43......




Senator Matawalle ne yake sakkowa daga stairs yana gyara babbar rigar jikinsa, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda ash color anyi mata aiki daya dace da mai ita, bayansa Mommy ce tana ta faman kashe murya, so take ya bata wani filinsa daya siya za'a yi masa gidan mai shine take son kwacewa tayi gurin event. Har suka kusan fitowa daga apartment ɗin Matawalle bece zai bata ba, sai ma maganar tafiyar su Imran honeymoon da yake yi cewar ace a farayi musu shiri. Cikin ranta sai kwashewa Imran albarka takeyi tana wani shan toka. Sai da ya riƙe murfin motar da aka buɗe masa ya kalli drivern yana cewa. "Kafin mu wuce ina san ganin Abubakar Galadanci." Da wani irin mamaki drivern ke kallan Matawalle har ya zauna akan kujera Mommy tace. "Wane kuma Abubakar Galadanci kake nema Alhaji?" Cike da rashin damuwa yake faɗin. "Sirikina mana Hajiya, ko kuma nace dake maƙocina sannan abokin adawa ta." Mommy ta wani zaro ido tana dafe kirji, ita kuwa yau meyake samunta da komai babu sa'a a cikinsa? Yau Matawalle ne ke cewa A Galadanci sirikinsa, mutumin da ko sunansa baya san yaji ankira. Zuciyarta na rawa take cewa. "Me zakai masa?" Sai da yai murmushi wannan lokacin kafin yace. "Sasanci zanje domin daughter in-law ɗita tana matuƙar farantawa yaro na, duk abinda kikaji Imran ya yaba to tabbas anyi masa yadda ya kamata." Jikin Mommy ne ya fara rawa, ganin kamar zata faɗi ne yasa tai saurin juyawa ta nufi apartment ɗinta tana jin tamkar zata zunduma ihu. "Muje." Cewar Matawalle yana bawa drivern umarni. Gabaki ɗaya sauran masu kula dashi suma suka shiga motocinsu gate man ya buɗe musu suka fito. Horn drivern Matawalle yai a wajan gate ɗin gidan A Galadanci, gate man ya ɗan leƙo ta ƙaramar ƙofa, ganin motocin Matawalle ya matuƙar tayar masa da hankali, ko kafin ma ya fito securities ɗin Matawalle sun mamaye ƙofar gidan da cikin ƙarama ƙofar. Fitowa Matawalle yai da ƙafafunsa ya shiga gidan A Galadanci, tunda neman sulhu yake yi dole ne a ajiye duk wani iko da tinƙaho da yake kansa, yana kallan gate man ɗin yake cewa. "Ina mai gidan?" Cikin rawar jiki yace "Yana ciki." Matawalle ya kalleshi yana faɗin "Ayi min sallama dashi." Da sauri maigadin ya juya yana ta tunanin abinda ya kawo Matawalle gidan. Ƙofar parlorn yaje yayi knocking, mai aikin Ummy ta fito riƙe da mopper ta buɗe, ganin maigadi yasa tace. "Meya faru?" Kamar wani munafiki ya juya bayansa yana kallan gate cikin ƙasa da murya yake cewa. "Alhaji ake kira." Tace "Amma bayace maka duk wanda yazo yau ace baya gida ba? Kasan dai ba lafiya gareshi ba." Sai a lokacin ya tuna da gargaɗin A Galadanci na cewa duk wanda yazo nemansa ace baya gida. Gashi yana tsoran ya koma yacewa Matawalle wani abu yadda yaga sojoji da ƴan sandan nan sun zagaye gidan. Ummy ce take sakkowa daga stairs hango su tsaye a bakin ƙofa yasa ta shan mamaki tana faɗin. "Ya akai duk kukai cirko-cirko a bakin ƙofa? Lafiya dai ko?" Mai aikin ta ɗan yi baya tana faɗin. "Wai Matawalle ne yake sallama da Alhaji." Koda Ummy taji sunan sai da kirjinta ya wani irin bugawa, babu abinda ya faɗo mata sai ƴarta Rahama, zuciyarta ke sanar da ita wani mummunan abu ya sameta, da kyar ta iya cewa. "Yana ina?" gate man yace "Hajiya suna ƙofar gida, umarni yake jira sai ya shigo." Juyawa tayi tana kallan upstairs tunani kawai take ta yadda zataje ta sanar da mijin nata zuwan makocinsa. Tana gudun sanar dashi abinda zai sake tada masa hawan jininsa dan yanzu an samu ya dawo normal. "Ado kaje kace bacci yakeyi baya jin daɗi." Ummy ta faɗa masa haka tana yin hanyar kitchen. Dakyar ya juya yaje ya sanar da Matawalle abinda Ummy ta faɗa, jin-jina kai kawai Matawalle yai tare da karɓar lambar A Galadanci a wajan maigadin sukai masa sallama Matawalle yasa aka bashi 10k ya shiga mota driver yaja suka bar unguwar. Ummy ta ɗakko madarar shanun da aka gama dafa masa ta nufi upstairs Abba na kishingiɗe yana danna waya taje ta ajiye masa gefenshi itama ta zauna tana ɗan hadiye yawu tana faɗin. "Matawalle ne yazo nemanka amma nace a gaya masa cewar bazaka samu fitowa ba. Cike da tsantsar mamaki Abba ke faɗin. "Mezanyi masa? Zuwa yai ya sanar dani mutuwarta na fito jana'iza ko kuwa me yazo yi min? Gara da baki gaya mun ba dan za'a iya yin abinda bai dace ba." Wayarsa ce ta hau kadawa tana neman agajin mai ita, ya ɗan yi tsaki yana faɗin. "Daga kunna wayar sai kira?." Ganin new number yasa ɗan jan tsaki yana maida wayar gefensa. "Ka ɗaga mana kaji menene?" Ummy ta faɗa tana miƙa masa madarar da ta zuba masa a cikin cup. "Kika bibiya ƴan neman taimako ne, wallahi yanzu bana san abinda zai dinga ɓata min rai." Ya faɗa yana karɓar cup ɗin yakai bakinsa bayan yayi basmala, haka wayar ta karaci yi yaki ɗauka.
********


A hankali tabi upstairs ɗin da kallo tasan yana nan saboda duk motocinsa suna a parking lot, zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi ta shige ɗaki tana cilli da handbag ɗin hannunta tare da faɗawa kan gado. Meya kaita narkar kayan mata masu zafi bayan tasan wanda ta aura ba kaunarta yake yi ba? Haka ta dinga jin ɓacin rai tana wurgi da pillows ɗin kan gadonta. Taje ta janyo beer ɗin da tayiwa mugun boyo ta buɗe ɗaya tare da kafa kai ta fara tilawa cikinta duk da cewar tayi mata karfi tafi karfin kanta amma sai da tashi dan tasan ita kaɗai ce abar da zata kawar da tunaninta akan komai. Tana so tayi nadamar auran Imran wani ɓari a zuciyarta yana sake ƙawata mata girma da kuma matsayin auransa, batada buri a yanzu irin ta samu ci koma nawaye cewa zatai na Imran ko koda zata samu ɗan guntun so a wajanshi. Wani irin wahalallan bacci ne yai gaba da ita hawaye na zirarowa ta gefen idanta. Ka rasa meke jefamu cikin bala'i bayan Allah da, kanshi yace idan kaga mai kyau daga gareni ne, idan kuma kaga saɓanin wannan to ka bincika kanka, gashi dai Humaidah yanzu a kwance take batada masaniyar zata kuma farkawa ko kuwa daga wannan kwanciyar tayi ta har abada? Ta manta da mutuwa wacce tana kan kowa bata ware yaro ko babba ba, mai kuɗi ko talaka ba, tsoho ko matashi duk bata ware ba kowa sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa. Ta kanta ruwan giya shine abu na karshe da ya shiga bakinta ya sauka a cikinta. Ta samu bacci bayan ta kwanta cikin zuciyarta babu komai sai yadda zata samu wani ya biya mata buƙatarta. A haka take neman rahama? A haka take saka ran shiga aljanna? Tayi taƙama da kyawun da Allah yai mata ta bi ruɗin zuciyarta shaiɗan ya buga mata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads