Showing 12001 words to 15000 words out of 139785 words
Chapter 5 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
lau Rahama albishir nazo miki dashi." "Okay Ummy gani nan kuna ina?" "Muna nan admin block." Da sauri ta zare wayar daga kunne tana cewa Imran. "Ummy ce tana Admin jirana take." Imran ya riƙo hannunta ganin duk ta ruɗe yace. "R Galadanci easy, please don't stress yourself, kije nima zan ƙarasa hospital yanzu." Buɗewa tai zata fita ya riƙota, kallan cikin ido suka yiwa juna cike da shauki wanda basu ma san suna yinsa ba, Rahama ta katse su ta hanyar zare hannunta tace. "Sai ka dawo." Ta fita tare da rufe murfin ta nufi admin gurin Ummy, shi kuma ya wuce hospital ɗinsa cike da tunanin Rahma.
Tun kafin ta isa wajan take tunanin kome Ummy tazo yi oho? Allah yasa maganar da zata faranta mata rai za'ai mata. Ummy na jikin mota ganin Rahama yasa ta faɗaɗa fara'arta, suka rungume juna bayan ta isa wajan. Kallanta tayi cikin kulawa ganin yanayinta kamar wacce ke cikin ciwo, front seat suka zauna Ummy ke cewa. "Baki da lafiya ne?" Rahama tai saurin cewa, "No Mekika gani Ummy?" Tace, "Kamar kima cikin firgici, meke faruwa?" Murmushin yake Rahama tayi tana cewa. "Babu komai." Kafada ta daga "Idan kinsa akwai damuwa a zuciyarki ki gaya min, Rahma bakida wanda ya fini kidena ɓoye min damuwarki ko farin cikin ki." Sake yin murmushi Rahama tai tana nunawa Ummy ita fa babu abinda yake damunta, ta kawar da zancen ta hanyar cewa. "Menene surprised ɗin Ummy?" Fara'a ta saki tana faɗin, "Har zan wuce wajan aiki nace bari na biyo na gaya miki, Ra'is ya samu scholarship." Wani ihun daɗi Rahama tayi tana farin ciki tace, "Inyee Ra'is, Ummy ina ya samu?" Cike da dariya Ummy tace, "United States of America, jiya Abban ku yake sanar damu." Rahama ta sake sakin ihu tana yiwa ƙanin nata murna, "Wow! Ummy wallahi naji daɗi, ina yiwa Ra'is murna."
"Hope kema kina karatunki yadda ya kamata ko?" Rahama ta ce.
"Ina yi Ummy."
"Toh a kara maida hankali sosai, karatun da kika ɗakko bana wasa bane ki maida hankali sosai, bari na wuce gurin aiki."
"Insha Allahu Ummy thank you."
Ummy tai murmushi ta buɗe jakarta, dubu biyu ta zaro ta mikawa Rahama, ansa tayi tana godiya ta fito daga Ummy tana ɗaga mata hannu. Department ɗinsu ta wuce idanunta sun kasa goge hoton Imran, abinda ya faru tsakanin su da Suraaj tasan yanzu zai dena shiga harkarta tunda Imran ya gargaɗeshi. Koda suka hadu a lab Suraaj be kulata ba dan baya fatan wani abu ya kuma haɗa shi da Imran Matawalle bare yai masa wulakanci irin wanda yai masa yau.........
#Asmy B Aliyu
#Hajja ce👈
#Albi✍️
#Imran Matawalle
#Rahama A Galadanci
To be continued............. Next page.
[11/12, 9:32 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
*Free page 10*
Kusan kwana biyu kenan tana gwada lambar Imran bata shiga, ba ƙaramin kewarsa tai ba tamkar tayi hauka haka takeji na rashinsa, dan fushinsa na bala'in azabtar mata da zuciya. Suna zaune a hostel kasancewar week end ne babu lectures, bayan la'asar tana zaune kan sallaya, sallah ta idar tana ta danna waya ta rasa meke mata daɗi a duniya. Ihsan dake zaune gefen bed tana chat da wayar hannunta, ta ɗago tana kallon yadda Rahama tayi shiru gameda ƙurawa waje ɗaya ido, ta girgiza kai tana mamakin taurin rai irin na Rahama, yanzu har ace kamar Imran Matawalle da ƴan matan b.u.k suke haukan sonshi, ko wace so take ya kulata, amman wai itace zata dinga rejecting zuwa birthday party ɗinsa? Tabbas tasan harda rashin wayewa dake damun Rahama, ji tayi dama itace a matsayin da Rahama Abubakar ɗin take dashi a wajen Imran Matawalle, wallahi da sai ta juya b.u.k. dukanta. Ihsan taja dogon tsaki na karo babu adadi tare da gyaran murya tana wani haɗe rai tana faɗin.
"Duk wannan tunanin bazai fissheki ba wallahi Rahama, tunda bazaki yi attending birthday party dinsa ba ai shikenan, kina ji kina gani su Hanan Asheer zasu kwace maki shi, dan ina ji suna magana cikin gang ɗin su akan Hanan zatayi attending birthday party ɗin Imran Matawalle. kuma kinsan zuciyar Hanan babu Allah a cikinta." Da wani irin shock Rahama ke kallon Ihsan zuciyarta na bugawa, idanunta ta zaro waje. Ihsan ta ɗaga kafaɗa, da sauri Rahama ta shiga kiran layin Al'ameen. Wannan karon lambarsa ya shiga lokacin yana guest house ɗin Imran suna tsara yarda birthday party ɗin zai kasance shi da abokansu. Shi kuwa yana kwance cikin doguwar soofa idonsa a rufe yaki koda saka masu baki a maganar. Gaba ɗaya tunaninsa na akan Rahama, yana tunanin zai yi birthday party wannan shekarar tare da ita ba. amman ga mamakin sa Rahama ta buɗe baki tace bazata iya zuwaba, idan yace maganarta bata ɓata masa rai ba yayi karya. Yasan Rahama bata da wani buɗewa ido duk abunda ya ɗorata akai shi takeyi, yasan tun tana ƴar shekara goma rainon sa ce, amma meyasa yanzu zai ce tayi abu ta gujewa hakan? Tunda Rahama Galadanci ta fara jami'a bai taɓa fita da ita koda a bakin gate ba, saboda yasan tsaurin ido irin na mahaifinta, yasan duk inda zata taka ƙafa idonsa na kan ƴarsa duk saboda shi, kuma yana son kasancewarta cikin hostel ne kawai dan ya samu damar ganinta shi yasa bai taɓa bada ƙofar da za'a fahimci suna tare da ita ba. Imran yasan ko wanda mahaifinta ke biya duk ƙarshen wata, wanda yakesa ido akan lamurran Rahama Galadanci na cikin makarantar yana ninka masa kuɗin da Alhaji Abubakar Galadanci ke bashi duk gudun kar ya faɗa wanda har yau ɗin bai faɗa ba saboda girman alkhairin da Imran Matawalle keyi masa. A acan gefe kuma yana karɓar kuɗaɗen Alhaji Abubakar Galadanci yana masa karya akan Imran bai taɓa taka ƙafarsa cikin b.u.k ba da sunan zuwa wajen Rahama. Haka kuma Rahama bata taɓa saurayi acikin b.u.k ba, hakan yasa Abubakar Galadanci yake alfahari da Rahama a wannan fannin. Amaan Ka'oje yaja Iska a karo na babu adadi yana kallon Imran Matawalle yana faɗin.
"Kai yanzu saboda ita zakasa a fasa wannan phatyn ? wai ya kake zaunawa kana biyewa karamar yarinya sai abunda ta faɗa shi zakayi? Gaskiya ni wallahi dan haka bana kula ƙananan yara, kai ma ga manyyan ƴan mata nan wayayyu a cikin b.u.k ka zauna kana kula wata kwailar yarinya? nace kazo na haɗa ka da Hanan Asheer ƙanwar abokina ce, wallahi babyn nan tayi babu karya, amman duk kabi ka nacewa wannan yarinyar da ba class ɗin kaba." Imran ya buɗe ido a hankali ya ɗorasu akan Amaan ka'oje, karo na farko da tun zaman su a falon zaiyi magana wayar Al'ameen tayi ƙara, ya ware ido gamida kallon inda Al-Amin yake, da sauri yace.
"Kaga Rahama ta kira please ka ɗauka kaji." Imran ya faɗa zuciyarsa na tsananta bugawa, addu'a kawai yake a cikin ransa wannan karon Allah yasa Rahama ta amince zata karbi gayyatarsa. Lokaci ɗaya Amaan ka'oje ya haɗe rai gaba ɗaya wannan yarinyyar ce zata rusa masu duk wani plan da suka shirya yi, dan ya yiwa Hanan alkawarin haɗa su da Imran Matawalle akan zata kwanta gado ɗaya dashi. Yasan kuma muddin wannan yarinyyar tazo birthday party ɗin nan toh komai da suka shirya zai rushe. Dan idan Imran Matawalle yana gaban Rahama Galadanci mantawa yake da komai da kowa sai su kaɗai. Al-Amin ya girgiza kai yana sake maidawa Imran wayar alamar yaje ya amsa kawai. Hannu ya miqawa Al'ameen babu musu ya damka masa wayar lokacin wayar ta katse wani kiran ya sake kara shigowa. Ɗaga wayar yai da sassarfa ya nufi hanyar barin parlorn, da wani kallo Amaan ka'oje ya bisa, sosai yaji takaici da baiji me Imran ɗin zai faɗa a wayar ba.
"Yes go ahead." Muryar da bata taɓa tsammanin ji a wannan lokacin ba ta daki dodon kunnenta. Lumshe idonta tayi na kusan sakan biyar jin muryarsa kurum ya saukar mata da wani irin natsuwa, cikin shagwaba da muryar son tayi kuka take faɗin.
"Shine zaka wani kashe wayarka har na kwana biyu ko?" Hannunsa ɗaya ya saka cikin sumar kansa yana squeezing gashin. Shi kansa yasan dauriya kawai yake yi amma kwana biyu ɗin nan da baya jinta ba ƙaramin azabtuwa yayi ba. "Mekike yi yanzu?" Ya faɗa cike da kulawa. Ta turo baki tamkar yana ganinta tana faɗin. "Babu komai, dama ina son na faɗa maka cewa zanyi attending birthday party ɗin Naka, amman da sharaɗi." Wani irin murmushi ya dinga saki wanda tana jinsa har cikin zuciyarta. "Meye sharaɗin?" Cikin dakewar murya take faɗin. "Zanzo amma babu shan wani abun da duk zai iya saka mutum ya fita hankalinsa, nasan duk sanda zakayi irin wannan taron zaku kwana ne kuna shan beer ni kuma bana so." Ji yai sharaɗin nata yazo masa awani iri, zai yi magana kuma tayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa.
"Promise me bazaka sha komai ba Imran, please promise me ba za'a gayyoto min gayyar ƴan ta'adda da yan turowe ba." Cikin dakewa yace. "Naji, da daddare zan shigo na kawo maki kayan da zaki saka." Cikin sauri tace dashi. "No inada kayan da zan saka." Imran ya yakune fuska tamkar tana ganinsa yace. "Nasan baki san wane irin shiri nayiwa wannan birthday party ɗin nawa ba, kinsan kuwa kayan ki tun daga ƙasar Turkiya nayo miki oder ɗinsu? Kuma ni su nake so ki saka, na gama magana kuma." Zatayi magana ya datse kiran bai bari tace komai ba. Koda ya koma cikin parlorn mikawa Al'ameen wayarsa yayi ya kalli Amaan kao'je yana faɗin. "Banda oder ɗin duk wani kayan da kuka san zai sa maye, only drinks da snacks ya wadatar." Ya maida kallonsa wajan Al'ameen yana faɗin, "Banda gayyar matan banza, kuma ka faɗawa su Zak ba sai sunzo ba, zan tura masu kuɗi ta account suyi nasu hidimar a wani wurin nagode da dukkan soyayyarsu." Baki da ido suka buɗe suna kallon Imran Matawalle, cike da jin zafin sa Amaan Ka'oje ke faɗin. "A saboda me? Ya mun riga mun gama tsara komai kai kuma lokaci ɗaya kazo ka canja mana tsari?" Ya faɗa sounding so very harsh. Imran ya buɗe hannuwa gamida ɗage kafaɗa yana cewa. "A saboda Rahama bata so." Al'ameen ya girgiza kai cike da wani irin takaici, bai taɓa jin haushin Rahama Galadanci ba a dukkan tafiyar dake cikin rayuwarsu ita da Imran Matawalle ba irin wannan karon, saboda yanzu akanta ita kaɗai zai canja duka wasu abubuwan da ya sabayi duk shekara tare da Imran, cike da takaici yace. "Amman dai kasan su Rufy bazasuji daɗi ba ko?." Cikin ko in kula Imran yace. "Ni ba hanasu zuwa nai ba, dama ai kwashe-kwashen ku ne ba nawa ba, kawai abinda zan faɗa banda misbehaving a gaban Rahama." Yana gama faɗa ya kwashi wayoyinsa ya nufi hanyar barin parlorn da alamar bar masu gidan zaiyi duka, dama kuma can Amaan Ka'oje baya shiri da Rahama Galadanci sosai, Allah ya ɗora masa tsanarta a ransa ganin yadda Imran Matawalle yake bata muhimmanci fiye dasu da suka taso a tare tun suna yara, kuma dama baya shiga sabgar Rahama, itama haka duk cikin abokanin Imran tafi tsanar Amaan ka'oje saboda duk yafisu rawar kai. Al'ameen ne mutumin ta. Shima Al'ameen motarsa yaja yabar gidan. Amaan kawai suka bari, ya ɗaga waya ya kira Hanan Asheer yake bata labarin Rahama Galadanci zatazo fa kuma Imran ya soke duk wani shagalin kayan maye da za'a shigo dasu. Cike da takaici take faɗin. "Shikenan kawai mu haɗu a hotel akwai plan ɗin da zan shirya mana." Da fargaba Amaan yace. "Idan kuma Imran ya gano fa? Hanan karki saka rayuwarmu a matsala fa. Kin san taurin kan Imran." Cike da rashin tsoro tace. "Babu abunda zai iya kai dai kawai mu haɗu."
****************
Bayan isha'i tana kwance waya take da Farook Galadanci, sama-sama ta faɗa masa cewar bacci zatayi, anan yayi mata sallama ta harari wayar gamida murguɗa baki tana faɗin. "Wallahi ban taɓa ganin mai nacin tsiya a duniya ba irin Farook Galadanci, wallahi bana san surutunka." Wayar Imran ce ta shigo a wayarta, ta ɗaga ya faɗa mata ya shigo cikin makarantar su. Dogon hijab ta saka har ƙasa dama su biyu ne a ɗakin daga ita sai
Ihsan Galadima. Kuma itama Ihsan ta fita wajen saurayinta da yazo. Rahama ta rufe ɗakin ta nufi wajen Imran, har ta shiga motar ransa a mugun haɗe yake ta kallesa ta girgiza kai tana faɗin. "Mekuma ya faru?" Murya a kausashe taji yace "Dawa kike waya?" Ta zaro ido tana kallon yadda ya haɗe rai, gabanta ya shiga faɗuwa tana murza hannayenta. Cikin rawar murya take faɗin, "Deejah Galadanci ce." Ya girgiza kai cike da wani sabon ɓacin rai mai ɗauke da kishi yake faɗin. "Kedai kawai kice da Farook Galadanci." Ya faɗa da wani yanayi acikin muryarsa. Kansa ya kwantar jikin seat zuciyarsa na tsananin bugawa da wani irin kishinta wanda bai san yadda zai bayyana kalarsa ba, Rahama kuwa ta tsani ganin damuwa akan kyakkyawar fuskarsa. A hankali ta kwantar da kanta a kan kirjinsa tana jin yadda zuciyarsa take wani irin bugawa tamkar zata fito duka. Cikin raunin murya take faɗin.
"Am sorry nayi laifi bazan karaba." Hannunta ya lalubo ya damke cikin nasa, wani irin sanyi ke ratsa cikin hannayensu su duka biyu, haka lokaci ɗaya dukan su suka shiga wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, da wata irin murya yake faɗin. "Kema kiyi hakuri dan Allah, kuma nasan laifina ne naƙin baki damar kula kowane irin saurayi, saboda na riga da nasan yanzu kin kai har kinyi yawa da ya dace ki fara kulasu." Da sauri ta ɗago daga jikinsa tana yi masa wani irin kallo tare da turo baki, ya girgiza kai yana faɗin." Bance ki daina kula Farook Galadanci ba, amman ki san irin mu'amalar da zakiyi dashi, am very sure babban goronki na tafe Insha Allahu R Galadanci, fatana kawai shine, Allah yasa zaki iya ɗauke duka dawainiyyarsa." Lokaci ɗaya tasha toka ta wani haɗe rai tace. "Kanata faɗin min cewa babban goro zai zo gareni, wai waye shi? idan kuma ni bana sonsa fa?" Tayi maganar in a naughty way . Ya ɗage mata gira yana girgiza kai yana faɗin. "Am sure zaki sosa ma, dan nasan duk wanda zaki aura he is your favorite." Hannu ya kai back seat ya ɗauke mata wata ƙatuwar leda ya damka a hannunta yana faɗin. "Gakayan da zaki saka." Cikin turo baki tace dashi. "Toh ni wa zaiyi min make up?" Ya girgiza kai yana faɗin. "Kin san ni na tsani wannan kyale-kyalen, kawai only powder ya isar miki, da man baki. A hakama bakiga yadda kikai kyau ba, ni na fison mace a natural beauty ɗinta, bana son wannan kwaliyyar dan bai taɓa burgeni ba koda na minti ɗaya. So gobe zanxo na ɗaukeki." Ya faɗa yana kallon ta, yadda take yatsina fuska tace dashi. "Tare zamuje da Ihsan and magana na karshe banda masu ɗaukar hoto da ƴan media, kasan dai idan Abba ya gani zai kasheni ne kawai." Maganarta na ƙarshe ta bashi dariya yace mata. "Abba bazai ma kasheki ba." Wayarsa ce ta fara ringing, Rahama tana ɗaga idonta taga sunan dake yawo kan screen ɗin wayarsa zuciyarta tai wani irin baki, sunan Humaida ne ta haɗe rai sosai, shima kallon wayar kurum yake hannu ta kai zata kama handle ɗin ƙofar Imran yai sauri ya wani fisgota, lokaci ɗaya hawaye ya shiga wanke mata kyakkyawar fuskarta, baki ya buɗe yana kallonta yace. "Kuka kuma? Please meya faru?" Rahama ta shiga dukan kirjinsa tana faɗin. "Dama kuna waya da ita kenan? Gashi nan kayi saving lambarta. Please ni ka rabu dani na fita." Imran ya runtse idanunsa, ƙoƙarin kwace hannunta take daga rikon da yayi mata tana so ya cikata dan gabaki ɗaya ta haukace masa. Lokaci ɗaya taji ya daka mata wata shegiyar tsawa, hawaye na rolling akan fuskarta ta kalleshi. Baice mata komai ba, gani tai ya jawota duka zuwa jikinsa. Ajiyar zuciya ta shiga saukewa har kusan minti biyu suna a haka, ta zare daga jikinsa, bata kalleshi ba take faɗin. "Zan tafi ka buɗe min." Bai yi musu ba ya buɗe mata kofar ta fice daga motar ko waiwayensa bata yi ba. Tana shiga ɗaki ta kashe wayarta duka, bazata kuma kunna wayarta ba sai gobe da safe.
Kusan sha ɗaya na dare ya kira wayarta yaji ta a kashe, yasan fushi tayi. Bai wani damuba yana tare dasu Al'ameen duka suna guest house ɗinsa shima saboda Humaida yaji bazai iya komawa gida ba, gashi saboda nacinta yasa Rahama Galadanci tayi fushi dashi babu gaira babu dalili, hmmm wato mata dai iya masu sai Allah. Yai maganar cikin zuciyarshi. A parlorn yabar su Al'ameen ya nufi master bedroom ɗinsa, wanka yayi yai kwanciyarsa akan haɗaɗɗen royal bed ɗinsa kalar white da silver ajikinsa. Washegari duk acikin ƙunci take, duk da ta kunna wayarta bayan sallar asuba har kusan 12 Imran bai kirata ba, Ihsan na tsaye tana juya wata english gown ɗin da Rahama zata saka kalar blue sunyi matuƙar kyau, Imran na matuƙar son blue a rayuwarsa mai ratsin black a jiki, sai ɗan mayafin rigar, kayan sunyi mugun kyau dan Ihsan sai yaba gown ɗin take. Wasu shoe ta ciro a ledar wanda suka dace da rigar, Ihsan ta girgiza kai tana faɗin. "Ke ƴar kauyace wallahi A Galadanci, Yau yaci ace kin bawa Imran special gift wanda zai yi matuƙar farin ciki da hakan." Cikin ko in'kula Rahama tace. "Yo me zan bashi Ihsan? yana da komai fa, ko nace zan gwada bashi wani gift faɗa zaiyi min, ke baya ma bari naje na siya masa ko turarruka." Ihsan ta taɓe baki tana faɗin. "Ni ba irin wannan gift ɗin nake nufa ba, just ki bashi irin ɗan hot mouth to mouth kiss ɗin nan, I know Imran zai ji matuƙar daɗi." Cikin zabura Rahama ta zaro ido tana girgiza kai tana faɗin. "This