Header Ads
Showing 63001 words to 66000 words out of 139785 words

Chapter 22 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1003

Ads at the middle of Article

ido tana riƙe hannun Amaan Ka'oje. Ɗan zungurinta yai da gefen ƙafarsa ta kalleshi yai mata alamar be strong ta shiga rufe bakinta da hannayenta tana maida kukan da ya taho mata. "Aure kuma Imran? Kai dawa?" Imran da idanunsa ya fara lumshewa ga wani irin jiri yana ɗibarsa yake cewa. "Rahama Galadanci." Haba Hanan kawai ta saki kukanta a fili tana riƙe Amaan. Janyo hannunta yai suka fito daga bakin ƙofa, janyota yai yana kallan face nata da take ɓatawa da ruwan hawaye yace. "Hanan the only opportunity Kenan da zaki samu Imran Matawalle, malama ki ajiye duk wani banzan kishinki kije ki kwanta dashi ko babu komai kin rage zafi da ɗacin soyayyar da kike yi masa, tun yaushe muke nemansa bama ganinsa? Tunda gashi yanzu ya kawo kanshi nan this is your last chance Hanan babu ruwa na." Cikin kuka take faɗin. "Amaan na tsani Rahama." Amaan ya janye hannunsa daga cikin nata yana cewa. "Ke ta dama." Yana kaiwa nan yabar wajan ita kuma ta shiga room ɗin da Imran ke ciki. Tarar dashi tayi yana ta faman riƙe kai, da azama ta ƙarasa wajanshi ta riƙe masa shoulders tana masa kallon cikin ido.
Ƙoƙarin tashi yake yi tana maidashi idanunta sun ƙanƙance shi kuma beer ɗin ta fara rikita masa lissafi har ya fara ganin dishi -dishi, ya riko mata hannunta da karfi yana faɗin. "Kira Amaan ya kaini gida." Fuskarta ta kai kusa da tashi tana hura masa iskar cikin bakinta tana faɗin. "Kai nawa ne ni kaɗai Imran Matawalle, please don't stress yourself." Ta faɗa tana zare ɗankwalin kanta. Shi kuwa matse kujera kawai yake saboda yadda yaji brain ɗinsa tana neman hautsinewa, ya farajin wani sha'awa na taso masa ya kalli Hanan Asheer tare da damƙo mata gashi yake faɗin."Yauma desire pills kika samin ko? Why Ha... Han..an?" Ya ƙarasa saunding so collapse yana kuma riƙota da karfi. Wuyan rigarsa ta riƙo a hankali ta fara ɓalle botir ɗin ta zura hannu cikin rigarsa tana shafa kirjinsa, nan da nan Imran ya fara fita daga cikin hayyacinsa. "Na daɗe ina bibiyarka kana shareni Imran, me yasa baka gane inda zuciyata ta dosa? Ina so yau mu kasance tare ko zanyi alfahari da hakan nan gaba tunda kaje ka auri wannan little baby ɗin." Da wani irin fushi ya shaƙo mata wuya duk da wine ɗin ta fara tasiri gashi desire pills ɗin tana tado masa da tsantsar buƙata hakan bai hana yaji zafin kalmar baby da Hanan ta kira Rahama ba, yana wani irin huci ya turata gefe yana shirin miƙewa wayarsa ta fara ringing Hanan ta fizge, Gate man taga yai saving, kamar zatai picking sai kuma ta fasa tana ta kallan sunan. Cikin maye ya fara shirin karɓar wayar sai dai ya kasa, Hanan ta daga jiran tana faɗin. "Ya aka yi?" Rahama jin muryar mace yasa kirjinta bugawa tace, "Ina mai wayar?" Hanan tayi wani irin murmushi tare da cewa. "Ku har yanzu house wife bakwa gane cewar mazajenku idan suna gida sune naku idan sun fito waje na masu rabone, to ni yau dai hardani a rabonsa sai kuma ki jirashi ya dawo bye." Hanan ta katse tana jan tsaki. Hannu takai bayanta ta zuge zip gaba ɗaya rigar jikinta tayi ƙasa, daga ita sai bra da Pant ta nufi jikin I Matawalle. Al-Amin ne ya buɗe ƙofar yana cewa. "Wallahi Imran ko..." Chak ya tsaya yana ware eye's akan Hanan Asheer, ransa a ɓace ya shiga yana kallanta. "What are you doing Hanan? Kinsan waye kike shirin yiwa fyaɗe?" Hanan ta shiga girgiza kai hawaye ya cika idonta take faɗin. "Al-Amin karka hanani, karka cutar dani please ka barni naji ɗuminsa ko zuciyata zatai sanyi." Shaye da toka ya ɗago Imran yake cewa. "Bazai yiwu ba wallahi, idan har na bari kika aikata tabbas Imran zai tsaneni dan nasan dole yai bincike ace masa ina cikin club ɗin na."
Hanan tai saurin rungume Imran ta baya tana kuka tana roƙon Al-Amin akan ya bar mata Imran, cikin zafin rai ya shiga tureta yana cewa. "Bazai yiwu ba Hanan ki barni na kaishi gida, ki bari idan yana cikin hankalinsa sai ki buƙace shi amma ba a wannan yanayin ba." Al-Amin yaja Imran wanda yake masa wani irin riƙo da haka har suka bar cikin club ɗin, motar Imran ɗin ya buɗe ya saka shi a back seat yana tambayar sa. "Ina Rahaman take?" Cikin maye Imran Matawalle ya janyo hannun Al-Amin ya ɗora saitin heart nashi yana faɗin, "Albi." Ɗan tsaki Al-Amin ya saki yana ture masa hannun. "Giya ma dai batai ba wani lokacin, ana tambayarka inda matarka take kana wani nuna min zuciyarka, kasan tana ciki ka barota kazo za'ai maka fyade." Side din driver yaje ya zauna, motar ya kunna yana cewa. "Gidanka zan kaika da safe ka nemi inda ka kaita." Maigadi na ganin motar Imran ya buɗe da sauri, Al-Amin na shiga da motar mai gadi ya ƙarasa wajan yana cewa. "Au ina kuma mai gidan nawa?" Al-Amin ya nuna back seat yana cewa. "Jeka buɗe min ƙofar entrance na shigo dashi." Cikin jimami gate man ɗin ke faɗin. "Assha tun ɗazu hajia ke nemansa." Lokaci ɗaya Al-Amin ya juya yana kallan mai gadin yana cewa. "Rahama tana ciki?" Yace. "Eh tazo ta karɓi wayata tana ta kirashi, sai dai naga da gudu ta shiga ciki da alama kuka takeyi." Al-Amin yaja numfashi ya buɗe ya janyo Imran suka shiga dashi cikin parlorn shida mai gadi. Rahama ya kwalawa kira jin muryar Al-Amin yasa ta fitowa da gudu dan tayi zaton wani abun ne Ya samu Imran. Idanunta suka sauka akan Imran dake kan rug yana faman rike ciki sai kiran sunanta yake. "R please.. Please I want you... Hhhh.. Uhmm..!" Da gudu ta sakko daga stairs ɗin tana zuwa ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka. Ficewa Al-Amin yayi daga parlorn yaje ya shiga motar yabar gidan. Rahama dake jikin Imran kuka kawai take mai taɓa zuciya, yadda taji yana cafko nashanunta ga kuma B* ɗinsa kyam yasa ta tabbatar har yanzu be samu yadda yake so ba, ta ɗago fuskarsa tana kallansa yadda yake lumshe idanuwa, ta zura bakinta cikin nashi, aikuwa yai wa harshen ta wani irin cafka yana sake matseta a jikinsa. Da wani irin fushi ta fisge tunawa da muryar mace da taji a wayarsa, da gudu ta haye stairs tana sake fashewa da kuka, bakin ciki kamar zata mutu.


********
A Shirye suka fito zuwa parking lot kowannensu cikin shiga ta alfarma, Humaidah ta shiga apartment ɗin Imran tana dubawa ko suna nan taga wayam, fitowa tayi ranta a ɗan ɓace ta isa wajan mota Mommy ke tambayar ta, "Lafiya Humaidah?" Haɗe fuska tayi tana faɗin. "Ina so naga Imran ne kafin nabar ƙasar nan sai dai da alama ba a gidan nan suka kwana ba shida banzar yarinyar nan." Mommy ta tabe baki tana cewa. "Idan zaki shigo mu tafi to, ke idan muka bari Imran yazo gidan nan bamu tafi ba ina mai tabbatar miki da cewa sai ya hana, tsab zai ce ki bari ayi order." Humaidah ta shiga da sauri, "I Matawalle yana bani wahala Aunty." Daga bayansu sukaji ance. "Yana kan baki Aunty Humaidah tunda baya sanki." Duk suka kalleta Maheera ta kawar da kai tana faɗin. "Allah ya kai ku lafiya." Mommy ta haɗe rai take faɗin. "Ina da aikin da nake san bari idan na tafi, amman halinki ba zai bani damar baki ba." Maheera ta saki ɗan murmushi kawai batace komai ba har driver ya shiga yaja securitys suka bi bayansu zuwa airport. Basu wani jima ba jirginsu ya tashi a lokacin ne kuma hankalin Mommy ya kwanta.
***********


Ware idanuwa ya shiga yi yana karewa parlorn kallo, rug ɗin da yake kai a kwance ya kalla wanda ya sake tabbatar masa da cewar a gida yake. Rintsa idanuwa yai ya miƙe da yana jin kansa nayi masa nauyi ya nufi stairs. Tun daga bakin ƙofar shiga ɗakin da take ya fara jiyo sautin muryarta tana karatun Qurani, yanayin yadda muryarta ke rawa cikin shaukin karatun yasa Imran rintsa idanuwa, a hankali ya furta. "Sutarul Ma'idah." Har ya gane surar da take biyawa, ya kama handle zai buɗe wata zuciyar ta hanashi. Ɗayan ɗakin ya shiga yai wanka da alwala lokacin karfe 6:47am, wasu wando da riga yasa marasa nauyi masu tsananin santsi ya shimfiɗa praymat ya gabatar da sallah, a hankali ya ɗaga hannu yana addu'ar Allah ya barshi da Rahama yana santa soyayyar da bakinsa ba zai iya furtawa ba, yana addu'ar Allah ya kare masa ita ya kuma bashi damar kulawa da ita kamar yadda yai alƙawari. Ya tashi tsaye, wajan mirror ya nufa ya ɗauki turare yana fesawa tare da kallan face nashi lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai , a hankali ɗan mari kuncinsa yayi yana faɗin. "Why Imran? Bakajin magana kasan da sanin ka ɓatawa Rahama Galadanci rai." Ya sake marin ɗaya ɓarin "Imran baka kyauta ba, kaje ka bata hakuri." Ya faɗa yana jan dogon hancinsa. Juyawa yai ya fito kai tsaye ya murda ƙofar ɗakin ya shiga lokacin ita kuma tana ƙasa kwance cikin soofa ta takure kanta waje ɗaya. Sakkowa yai shima bayan ya tabbatar da cewa bata bedroom da toilet, yana hangota ya sauke ajiyar zuciya, sauka yai ya nufi inda take. Gaba ɗaya ya ɗago zai ɗorata saman kafarshi ta tureshi zuciyarta na wani irin bugawa. "Ni karka kuma taɓa ni, kaje can wajansu." Ta faɗa kuka na kwace mata. Fizgota ya sake yi ta faɗa jikinsa yai mata wata irin rungumar da bazata iya kwacewa ba, muryarsa so cool yake bata hakuri.....










#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Rahama Galadanci
#Imran Matawalle
#Hanan Asheer
#Humaidah
#Albi
#Haske writer's association
[11/23, 6:26 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...* (my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


29....


Ƙoƙarin fisge kanta take daga riqon da yai mata yana kwantar da murya cikin rarrashi da ban baki tamkar ba Imran Matawalle ba mai jiji da kai da wata irin izzah, sai gashi yau duka babu wannan girman kan da izzan, wai shine ke lankwasawa mace murya cikin rarrashi da ban baki, shi kansa ko nawa za'a bashi bai taɓa tunanin xai iya rarrashin mace har haka ba, musanman Rahama dake da kanananun shekaru sa'ar Maheera Matawalle, shi kansa yasan soyayyar Rahama tana bashi matuƙar wahala, yasan ya ɗebo ruwan dafa kansa na soyayya da ƙanƙanuwar yarinyya, gashi har da ma aurenta yayi, da gaskiar su Amaan Ka'oje ne da suke faɗar zata bashi ciwon kai saboda yarinta, ga manyyan mata nan a gari amma yaki. Tana kokarin fisgewa ta fusata shi sosai, ran mazan ya motsa ya daka mata wata irin muguwar tsawar da yasa ta natsu, lokaci ɗaya ya zare mata ido yana faɗin "Kiyi wanka ki sauko yanzu zamu fita bana son wannan silly drama naki." Ya faɗa yana cire hannayensa daga cikin jikinta. A fusace yabar mata ɗakin gamida buga ƙofar. Hannu tasa tana toshe kunnayenta hawaye na zubar mata, jikinta yayi sanyi sosai, yanayinsa kurum da ta kalla duk zafin kansa bazata bashi kanta ba wallahi, inhar zai zabi zaman aure da Humaida ta shirya rabuwa dashi na har abada. Jiki sabule ta nufi toilet tana kumbara kamar zata fashe. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya shiga neman sigari da abar kunnawa, dakyar ya samu kwali ɗaya cikin kayansa. Parlor ya koma ya zauna ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kunna ya fara zuka sosai. Kusan guda biyar ya sha a nan zaune a wurin babu abunda ke tashi a cikin parlorn sai warin sigari, still baiji zuciyarsa ta sauka daga zafin da take yi masa ba. Waya ya ciro ya kira Maheera Matawalle akan ta shirya masu breakfast mai sauqi, nan da minti talatin zasu shigo. Yana gamawa ya kira mai yi masa aikin furnitures ya fara zuba masa bala'i da masifa ta wayar yana faɗin. "Toh wallahi a yau yake son gidansa ya dawo normal Idan bazai iya ba ya faɗa masa ya samu wani. Hakuri ya fara bashi yana faɗin, "Insha Allahu a yau za'a gama komai. Katse wayar yayi yana jan dogon tsuka, lokaci-lokaci yana kallon stairs yaga ta inda zata ɓullo sai gashi har kusan mintuna ashirin yana zaune a parlorn, still bata fito ba, ya girgiza kai yana faɗin. "Da Humaida ce da yanzu na haɗa mata jini da majina wallahi." Ransa yaji yana ƙara ɓaci, miqewa yayi ya nufi stairs dai-dai lokacin Rahama ta fito daga nata ɗakin cikin Turkish abaya kalar light brown babu komai acikin fuskarta, babu powder babu kwalli fuskarta ta faɗa haka idonta ya zurma sabida kukan da ta kwana tana yi, sai wani sanyayen ƙanshi ke tashi a cikin jikinta. Zuciyarsa yaji tana dokawa da wani sabon yanayin da yakeji akanta, ta haɗe rai tabi ta gefensa a fusace ta nufi ƙofa bayan ta zabgawa wajan daya gama zuƙe-zuƙensa harara, shima haɗe ran yayi haka suka zauna a mota kowane fuska babu walwala, ta kallesa ta ƙara haɗe rai take faɗin. "A school zaka saukeni ina da lecture karfe 12 na rana." Shima cikin serious yake faɗin "A aje wannan karatun zuwa wani satin saboda sabon aure gareki yanzu baxan kara ɗaga maki ƙafa ba sai idan kina da test ko exams, lecture kuma ki hakura wani satin ki karbi note zan tayaki dubawa." Da haka ya haɗe rai ya mai da hankalinsa wurin tuki tamkar bashi yayi magana yanzu ba, zuciyarta na mugun tafasa take kallonsa, har suka isa Matawalle mention ran Rahama a ɓace yake. Yana gama parking ya ciro wayarsa ya kira Maheera, cikin minti biyar maheera ta ƙaraso cikin shiga ta alfarma, ta riqe hannunta sai rawa da farin ciki take yi mata. "Sannu da zuwa." Rahama ta amsa tana ƙwaƙwalo murmushin dole tana ɗorawa kan fuskarta. "Kije da ita part ɗina Mahee kuyi breakfast zanje clinic anjima zan dawo na kaiku wurin mai lalle da gyaran kai." Maheera tai saurin cewa "Muje part ɗin Mommy Yaaya." Zaiyi magana tayi saurin tarar numfashinsa tana faɗin. "Mommy sunje Dubai ita da Aunty Humee siyo kaya." Baice komai ba ya juya zuwa part ɗin Matawalle. Maheera ta ɗaga murya ta yadda zai jiyota tana faɗin. "Yaya naka abun breakfast ɗin fa?" "Zanyi tare da daddy." Ya faɗa batare da ya kalleta ba. Binsa kurum Rahama keyi da ido zuciyarta na wani irin tafasa, Maheera na riqe da hannunta suka nufi part ɗin Mommy ga ƴan aiki nan birjik sai hidimarsu suke, Maheera ta rasa inda zata sauke Rahama sabida farin ciki, lokaci ɗaya Allah ya saka mata soyayyar Rahama Galadanci a cikin ranta, "Yanzu dai Aunty Rahama mu shiga dinning area mu fara karin kumallo sai mu shiga ɗaki ki bani labarin tayaya ki ka sace min zuciyar Yayana bashi da wata magana da tunanin kowa sai naki, gaskiya kin dace sosai, ina son nima na samu miji irin Yayana wanda ya iya tattalin mace da nuna mata soyayya ko a gaban waye, kin ga yadda kuka burgeni kuwa? yadda ya ɗakkoki tamkar wata ƴar baby." Murmushi kawai Rahama tayi tana rufe idonta maganganun Maheera Matawalle na sakata jin wata irin kunya.
Yadda ya riqa faɗa yasa Daddy ya buɗe baki yana kallonsa, cikin takaici yake faɗin." Imran na tambayeka mana? Shin kudina ko naka?" Zai yi magana Matawalle ya ɗaga masa hannu. "Mu rufe wannan rigimar, kuma ka hakura da wannan gidan naka ku dawo ɗaya daga cikin gidajena ka zabi ɗaya ka zuba matanka a ciki, wannan da kake ciki yayi maka kaɗan." Lokaci ɗaya ya haɗe rai yana girgiza kai yana faɗin. "Kasan ra'ayina daddy bana son ƙaton gida, wannan ma ai yana da bedrooms da parlor biyu zan zauna a sama nida Rahama, ita kuma ta zauna a ƙasan ai daki biyu ne a kasa ga kuma parlor. Kitchen kuma da store suyi sharing." Jinjina kai kawai Matawalle yai yana cewa. "Shikenan idan hakan ka zaba, nidai adalci nakeso kayi." Shi dai Imran kin cewa komai yayi gaba ɗaya bashi da wani walwala, kawai tuno da ƴar rigimarsa yake da bai buɗe mata ido ba da yanzu kansa ya kusan rabewa gida biyu sabida rigimar ta. Kai tsaye clinic ya nufa sha biyu ya dawo ya ɗauke su ya kaisu wajen saloon da gyaran jiki, yana saukesu ya baiwa Maheera kuɗin, yanxu ma ko kallon Rahama bai yi ba jikinta yayi bala'in yin sanyi ganin yadda yake wani share ta. Suna fita ya figi motar da wani irin speed ganin yadda jikin Rahama yayi sanyi yasa Maheera tasan akwai matsala, "Kunyi faɗa ne da yayana ko Aunty Rahama?" Maheera ta tambaya cikin sanyi murya tana kallon Rahama, ta girgiza kai cikin sanyin murya take faɗin. "Kiyi hakuri dan Allah haka halinsa yake bai iya fushi ba yana da wuya yayi fushi, amman idan yayi kafin ya sauqo akwai wahala, mu shiga daga ciki zan baki satar amsa yadda zaki sauke masa wannan fushi dake kansa, karki wani damu tunda yana sonki ki zuba mulkinki yadda kikeso, saboda idan Yaya yana son abu baya iya jure wannan fushin na tsawon lokaci, yanzu idan kika bincika zuciyarsa ya damu da wannan fushin da yake yi dake." Maheera ta faɗa tana kallon Rahama da jikinta yayi wani irin sanyi, lokaci ɗaya hawaye suka cika idonta, tambayar kanta take ita meye laifinta aciki? itace ya kamata tayi fushi dashi amma ba shi ba, dan ita yayiwa laifi shine zai hau fushi da ita. Bazata canja ba kuwa inhar akan maganar Humaida ce...


********
Sai wuraren 4 Maheera ta kirasa tana sanar dashi an gama masu yazo ya ɗauke su. Haka Maheera sai yaba lallen jikin Rahama take yi wanda aka sirqa da ja da baki saɓanin Maheera da aka yiwa jaa kawai. Gefe Rahama ta koma ta kira Ihsaan a waya suka ɗan taɓa hira sukayi sallama har Ihsan na zolayarta da cewa yau amarci ya riqeta taki shigowa school. Murmushi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads