Header Ads
Showing 123001 words to 126000 words out of 139785 words

Chapter 42 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1022

Ads at the middle of Article

tana ɗaukar babyn. Komai bece mata ba ya fito daga ɗakin ya nufi ɗayan a lokacin ne ya kira Matawalle ya sanar dashi yadda sukai. "Kayi min dai dai my son, yake ya kwaɗa ƴar tashi." Imran ya dafe saitin heart nashi da yake jinta tana masa zafi yace. "Daddy ina so muyi magana dakai, yaushe zaka dawo Kano?" Matawalle ya numfasa. "Zan dawo but yanzu akwai wasu meeting da zamu zauna da president gobe da jibi, why not ka taho nan Abuja da babyn sai Mamah (amaryarshi.) ta dinga kulamana jaririyar? Kamar hakan zai fi tunda kaga ita babbace tafi Maheera sanin komai." Imran ya cije lips. "Daddy bana san baro Kano saboda Rahama still tana cikin tashin hankali." Matawalle yace. "Kai yanzu ina ruwanka da ita? Ko ka manta yanzu babu aure tsakaninku? Bana so kana damuwa Imran na dauka ma ko ka samu min wata surukar?" Ya faɗa sounding so funny. Kamar yace masa ai har yanzu matarshi ce, sai kuma yai shiru kawai. Salama sukayi ya ajiye wayar akan bed tare da rage kayan jikinsa ya shiga toilet. Sai wajan ƙarfe goma sha biyu na dare ya shirya zuwa asibiti da yake ba'a barin masu jinya mutum ɗaya aka lamunce ya kwana da marar lafiya a clinic ɗin, ya yiwa Maheera sallama ya tafi. Ummy ce a wajanta dama tuni Imran yace da Dr Fawwaz zai shigo amma baya son kowa yasan da zuwan nashi. Ta baya yabi ya shiga room ɗin bayan Dr Fawwaz yace Ummy ta ɗan basu waje......




(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Farooq Galadanci
#Team Albi
#Haske Writers Association...
[12/16, 7:25 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


52....


Ɗagota yai gabaki ɗaya zuwa jikinsa, bacci takeyi hannunta daure da drip ya mannata sosai a cikin kirjinsa da yake wani irin mugun bugawa. Tausayinta yakeji sosai ba kuma yaso yaga ta sanadinshi tana shiga cikin damuwa saboda Rahama bata cancancin haka ba, ta sadaukar da komai nata a baya saboda shi. Amma be dauke babyn saboda ya sanyata bakin ciki ba, yayi haka ne kawai dan ya nunawa Abubakar Galadanci cewa da Rahama kawai yake iko ba da sauran mutanen duniya ba. Zame mata ɗankwalin kanta yai ya shiga shafar lallausar sumar dake kwance a kanta yana jin wata irin sabuwar kaunarta tana huda jinin jikinsa. ALBI ..!" Ya faɗa a saitin kunnanta, sai dai bata san yanayi ba sakamakon allurar bacci da Dr Fawwaz yai mata dan ta samu nutsuwa ɗazu kukan da takeyi shine yake haddasa jininta ƙin sauka. Cikin nutsuwa ya maida ita kan gadon ya zura hannu cikin aljihu ya zaro wata small feeder ya buɗe, sunkuyawa yayi saitin ta ya buɗe kirjinta. Sai da zuciyarsa ta kusa tsinkewa lokacin da yaga sun wani kuma cika sunyi kyau gashi dama babu bra, wani irin feeling ya ringa fisgar Imran yayi matuƙar missing ɗinta, ya ɗora fuskarsa tare da rungumeta yana wani sauke ajiyar zuciya. Da kyar ya iya control ɗin jikinshi ya sa baki a hankali ya fara tsotsarsu ta yadda ruwan zai zo, aikuwa kamar jira ake a taɓasu ya tara Feeding bottle ɗin yana matsawa ruwan yana shiga, sai da ya samu ruwan nonon sannan ya gyara mata kwanciyarta ya rufe Feeder yasa cikin aljihu tare da sumbatar goshin Rahama yana jin tamkar ya tafi da ita. Yana fitowa shi kuma Dr Fawwaz ya shiga ciki ya buɗewa Ummy ta shigo yana cewa. "Yauwa muna sa ran Insha Allahu da ta farka komai zai dawo normal, Hajiya dan Allah idan wani abun ne bata so ayi gaggawar nisanta ta dashi, idan kuma abu take so har kuna da damar bata ku bata saboda idan jinin ya ci gaba da yi mata haka babu abinda zai hana brain dinta ya tabu, please Hajiya ƴarku tana cikin hatsari wallahi." Ummy ta kalli Rahama cike da tausayawa tana faman jinjina kai. Aikuwa zatayi da gaske wajan ganin Rahama ta samu sauki domin su biyu ne Allah ya bata idan ta rasa su Abba zai iya auro wata matar tazo tai ta haihuwa a barta da tagumi. Kujera ta janyo ta zauna kawai tana tunanin yadda zata ɓullowa lamarin. Yana zuwa gida ya tarar Maheera da babyn tana ta jijjigata sai ihu takeyi. Ya ciro feedar yana miƙawa Maheera yace ta bata, Maheera ta sauketa suka zauna tasa mata a baki yarinya ta kama da mugun sauri tana sha. "Yaya nima fa kaga na haɗa mata Nan ɗin wallahi taki sha." Imran ya shafa sumar kansa yace. "Kici gaba da bata zata dinga karɓa." Sosai tasha shi ganin ta koshi harta koma bacci yasa ya miƙe yana cewa. "Mahee ki kular min da ita, idan akwai wata matsalar let me know please." Tana kwantar da ita take faɗin. "Toh Yaya Allah ya tashe mu lafiya." Ya fice ya shiga ɗaya ɗakin su kuma suka kwanta. Tunda ta farka ta fara zubar da hawaye tana dafe kirjinta, Ummy dake kan sallaya idar da sallarta kenan ta asuba taji kukan Rahama, ƙarasawa tayi da sauri ta dafa goshinta tana yi mata sannu. "Mekikeji yanzu?" Rahama ta nunawa Ummy kirjinta murya a hankali kamar mai mura take cewa. "Ummy zafi suke min." Ummy ta ɗaga rigar tana kallan breast ɗin Rahama yadda sukayi wani irin burɗin-burɗin tana ta cije baki tare da juyar da kai side by side. "Kiyi hakuri Rahama taki ƙaddarar kenan, amman duk mahaifinki ne ya janyo miki wannan bala'in akan wani banzan ra'ayinsa, kinga da babyn tana nan ai da ta ɗan sha koyaya ne saboda yanzu ke zaki ta shan wahala." Da rawar murya take cewa. "Ummy Imran ɗin be dawo min da ita ba?" Taja numfashi ta sauke cike da tsananin damuwa tace. "Taya zai dawo da ita Rahama? Karki manta kema mahaifinki ke iko dake shi yasa shima ya rama, ni banga laifin Imran ba Abban ki shi yake zubar mana da mutunci." Hawaye na rolling saman face nata take cewa. "Ummy mutuwa zanyi, ni kaɗai nasan ya zuciyata keyi, ku yafe min Ummy. Ina san yiwa Abba biyayya hakan yasa na hakura da Imran ba dan na dena san shi ba Ummy, na hakura da Imran ne saboda farin cikin Abba ba wai dan zuciya ta naso ba, ina san yiwa Abba biyayya koda ace hakan shine silar barin numfashi na." Tayi maganar tari yana sarke mata da wani irin yanayi, kafin Ummy tace wani abu taga jini yana fitowa daga cikin bakin Rahama, hankalinta yai matuƙar tashi ta gigice ta shiga kwalawa nurses kira. Suna ganin halin da take ciki suka kira Dr Fawwaz domin shine babba a clinic ɗin bayan Imran. Da wani irin bala'e'en tashin hankali ya nemo lambar Imran wanda ke rungume da babynsa ya riƙeta Maheera tana sallah. A haukace ya kwantar da babyn ya fice daga cikin ɗakin da gudu, cikin tashin hankali ya dauki car key ɗinsa ko kaya bai canza ba sanye yake cikin tracksuit yaja motar da wani irin speed banda hasbunallahu wani'imal wakil babu abinda yake fitowa daga bakinsa, da yake gari yanzu ya fara wayewa babu wani motoci ko mutane a titin har ya isa clinic ɗin. Kai tsaye room ɗin ya shiga yaga yadda ake ƙoƙarin sanya mata oxygen. Abba da Hajja da Ummy duk suna tsaye hankali a tashe, da yake tunda akai sallar asuba Hajja ta kafawa Abba ƙahon zuƙa cewar dole sai ya kawota taga Rahama, suna hanya Ummy tai masa waya cewar Rahama na aman jini shi yasa suka riga Imran ɗin zuwa. Yana zuwa ya wani fizgota zuwa jikinshi yana girgiza kai idanunsa a runtse yake furta. "Rahama please... Please wake-up." Cike da ruɗewa ganin ya hana a sanya oxygen ɗin Dr Fawwaz ke cewa. "Oga kar a rasata gaba ɗaya, kayi hakuri ka bari a sanya mata because numfashinta yanata faman ɗaukewa." A haukace ya juya ya fizgo oxygen ɗin daga hannun nurse hannunsa yana rawa ya sanya mata yana kuma shafar gashinta. Dakyar suka samu Rahama ta dawo hankalinta ganin tana bacci yasa suka fito aka bar Imran zaune a kusa da ita. Shiga sukayi ciki Hajja ta fara kuka tana faɗin. "Allah sarki Rahama ubangiji ya tashi kafaɗunki ya baki lafiya, nayi miki alƙawarin duk abinda kike so indai ina da shi sai na miki, wannan yarinyar kinsha azaba daga cikin har haihuwar ba'a rangwanta miki ba." Abba ne ya haɗe rai bayan ya gama tabbatar da cewa Rahama na numfashi yake faɗin. "Ina jin dai Imran ka manta cewar yata yanzu ba muharramarka bace ko? Ya kamata ka sakar mata hannunta idan da halima kabamu room ɗin." Zuciyar Imran tai wani irin duhu ransa yai mugun ɓaci yana jin tamkar ya juyo ya nunawa Abubakar Galadanci cewar shi ɗin ɗan zamani ne. Sai dai ganin Rahama bazai barshi ba, kuma ko babu komai zuciyarshi har yanzu tana kan Rahama banda haka surukinsa ne amma da ya nuna masa shi ba irin mazan nan bane da za'a yiwa wulakanci ba. Ya tashi a hankali ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi kofa yaji Abba na cewa. "Kagaya min adadin kuɗin da yata taci tun zuwanta clinic ɗin nan zan biya." Imran har zai fita yaga ya dace yai magana shima, dan haka shaye da toka yake faɗin. "Ko na asibitin da aka fara kaita nasa aje a biya saboda dalilin cikina dake jikinta aka kaita, nan kuma da na kawota dama na baban babyn da ta haifa ne, so daga nan har lokacin da zata samu sauki tana ƙarƙashin kulawar Imran Matawalle." Yana kaiwa nan ya janyo ƙofar saboda ma yasan condition ɗin da Rahama ke ciki ne yasa yai a hankali amma da sai ya bugota yadda zasuji karar a brain ɗinsu. Motarsa ya shiga yana shirin tadawa yaga Ummy ta ƙaraso da gudu wajansa, ganin hawaye a face nata yasa yaji zuciyarshi ta wani buga ya buɗe ƙofar zai fito ta dakatar dashi tana cewa. "Kayi hakuri Imran karka hukunta zuciyar Rahama saboda halin mahaifinta. Dan Allah dan Annabi kayi min alfarmar kawo min babyn Mahaifiyarta ta shayar da ita, nonon sun fara yi mata ciwo gashi ta tabbatar min da cewa zuciyarta zafi take mata. Ka taimaka badan halin mu ba Imran, nayi maka alƙawarin Rahama nayin arba'in da kaina zan kawo maka ƴarka." Imran ya rintsa ido yana jin maganar Ummy na kashe masa jiki, ba tare da ya ɗago ba yace. "Shikenan Ummy yadda kikace haka zanyi." Ummy taji kamar ta rungume shi saboda farin ciki, share hawayen tayi tana cewa. "Nagode Imran Allah yai maka albarka." Ya amsa a cikin zuciyarsa, ta juya shi kuma ya ja motarsa yabar asibitin. Hajja ta kalli Abubakar Galadanci ranta a matuƙar ɓace tace. "Wai dan Allah Abubakar yaushe ka zama haka ne? Yaushe ka koma marar mutunci ban sani ba? Toh na gane saboda kaga mun goyi bayanka a lokacin da ka faɗi zaɓe ko? Ina ce duk shine yasa baka san ƴarka da wanda take so?" Abba yace "Hajja yaron nan fa ɗan shaye-shaye ne taya zan haɗa jini dashi?" Da mugun haushi Hajja tace. "Aikin banza aikin wofi jini na nawa ne baka son haɗawa dasu Abubakar? Jini daya wuce wanda jiya-jiyan nan Rahama ta sauke makashi sai kuma wanne jini ne baka san haɗawa? Yau ni naga masifa da bala'i da idanuwa na. Kayi nasarar raba auran nan kaji daɗi yanzu kuma wane bala'in kake nema na kasa gane manufarka." Abubakar Galadanci yai shiru jin yadda Hajja ke ta surfa masa faɗa. "Toh bari kaji na gaya maka ka fita harkar nan, Rahama dai tana gabanka ni zansa yaron ya dawo da jaririyar wajan uwata idan yaso sa dinga zuwa ganinta, kai kuma sai ka kwaɗa Rahama ka cinye tunda babu damar komawa ɗakinta." Abba yai shiru yana jin Hajja, ya kuma ji daɗi jin tace zata sa a dawowa da Rahama babyn ta ko babu komai yasan hankalinta zai kwanta za kuma ta yadda da duk wani tsari da zai kawo mata. Yana komawa gidan ya tarar dasu Mommy, Humaidah dasu Bassam sunzo ganin baby. Fuskarsa a sake ganin yadda suke mishi murna musamman Humaidah da ta kasa janye idanunta daga kanshi. "Yaya an samu ƙaruwa? Allah ya raya." Cewar Bassam da shima yanzu yayi wani tsaho yana jin kanshi kamar wani babba. Imran ya zabga masa harara Mommy na cewa. "Wannan yarinyar mun rasa da wa tayi kama, hasken dai na Mamanta ne." Kin magana yai kawai ya kalli Maheera yana cewa. "Ku shirya za'a maida ita wajan Mamanta." Maheera ta zaro ido ita ta dauka zata zauna da babyn ne har tasa an kwaso mata kayanta dake gida. Be jira jin komai ba ya haye sama, yana shiga ya faɗa kan gado yana faman rintse ido. Duka baya jin daɗin duniyar, halin da ya baro Rahama a ciki yafi komai bashi wahala yanajin kamar ya dawo da duk wani ciwo dake jikinta kanshi. Lokaci yayi da zai bayyana musu cewa har yanzu Rahama matarshi ce, lokaci ya yi da zai nuna musu cewa babu mai rabashi da ita sai Allah da ya haɗa zuciyarsu guri guda ba tare da sun shirya ba. Yanzu tsoranshi ɗaya shine Rahama zata yadda da duk abinda ya tsara mata har ta biyo shi ko kuwa? Dan yagama gane ta shirya tsab wajan ganin sun rabu kamar yadda Abbanta yake so. Ya rintsa ido lokacin da ya tuna sanda zai auri Humaidah tayi nadamar kin bin umarnin iyayenta a lokacin, yanzu kam yasan zata iya jure rashinsa dan ta nuna masa itama mai biyayya ce. "Ya Allah." Ya faɗa yana cusa yatsun hannunshi cikin sumarsa yana hautsinata. Tashi yai ya shiga toilet, wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani yadi da ɗinkin yai masa matuƙar kyau, ya sanya turaruka tare da ɗakko hula ya ɗora. Da sauri ya dinga sakkowa jin yadda babyn ke kuka kamar zata fasa musu gidan. Karɓarta yai yana kallansu yace su fito duk su wuce clinic ɗin tare. Haka suka tashi sukayi convoy. A reciption suka tarar da Ummy da Hajja Aunty Kausar, Hajiya Babba da Aunty Azeeza. Imran ya wuce room ɗin da Rahama ke ciki wacce nurse ke gyarawa drip ɗin da ya goce. Nuni ya yiwa nurse ɗin cewa ta fita, ya ƙarasa ciki ya zauna gefenta yana kallanta. A hankali ta buɗe idanunta da suka koma wasu iri saboda kuka, sau ɗaya ta kalleshi ta ɗauke kai. Hannunta ya kama wanda babu drip a jiki ga mamakinsa yaga ta zare hawaye na zirarowa ta gefen idanunta yaji duk babu daɗi yasa hannu yana share mata, murya a sanyaye yaji tana faɗin. "Bana so." Ya ware eye's yana kallanta da mugun mamaki....




(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Abubakar Galadanci
#Ummy
#Team Albi
#Haske Writers Association...
[12/16, 7:25 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




53.....


A hankali hawaye ke zuba daga cikin fuskarta tana jin xuciyarta nayi mata wani irin sabon ciwo, rungumota yayi duka jikinsa da murya can ciki yake faɗin. "Albi.." Ƙoƙarin fisge kanta take daga riqon da yayi mata, sai dai ko kaɗan bata da qarfin yin hakan, da wata irin murya take faɗin. "Zan iya rasa komai a duniyar nan amma banda babyna. Ka dawo min da babyna please." Ta faɗa tana dukan kirjinsa duk da cewar ba karfi jikin. Ya haɗe rai sosai yana kallonta yake faɗin. "Ki natsu idan kuma kina buƙatar na kara yi maki wani cikin toh zanyi idan kikayi arba'in koda acikin falon Alhaji Abubakar Galadanci ne." Sakin baki tayi tana kallonsa hawaye na xuba a fuskarta. Sai yanzu ma take ganin canji cikin fuskarsa, yayi ƙiba gamida haske ga wata uban kasumba da ya tara, waya ya ciro still tana cikin jikinsa ya kira Maheera Matawalle akan ta shigo da baby. Jin ya ambaci baby ne yasa tabar cikin jikinsa da sauri tana kallon ƙofar. Cikin few minutes Maheera ta shigo da babyn, hannu Rahama ta miƙa Idonta na cika da kwallah, karɓar babyn tayi gamida sakata cikin jikinta tana sumbatar ko'ina a cikin fuskarta da wata irin tsantsar soyayya irin ta uwa. Harɗe hannu yayi a kirjinsa yana kallonsu cike da sha'awa da wani irin sabuwar soyayyar su da yakeji a cikin zuciyarsa. Lokaci ɗaya kuma aka cika musu ɗakin, Hajja ta tsaya a gabanta tana faɗin. "Toh ki wanke nonon ki bata tasha ƴar baiwar Allah itama daga zuwa duniya taga bala'i." Ruwa aka kawo mata a roba kasa fito dashi tayi agaban Imran saboda yadda ya kura mata ido haka idonsa na kanta. Gira ya ɗage lokacin daya gano nufinta. Miqewa yayi tsaye ya kalli Ummi yana faɗin. "Idan akwai wata matsalar a kirani." Ya juya ya nufi ƙofar fita. Kusan cin karo sukayi da Abba, Abba lokaci ɗaya ya haɗe rai yana yi masa wani irin kallo. Sai da Abba ya wuce sa'annan Imran ya fita aransa yake faɗin. "Zaka ga Rashin kunya har cikin gidan ka, Allah ya nuna min ranar da sunyi arba'in lafiya." Ya faɗa yana shafa bayan kansa. Duk yarda Abba yaso a sallami Rahama daga clinic ɗin su koma gida hakan bai yuyuba, saboda Ummi tayi rantsuwa idan wani abu ya qara samun Rahama ta gama zaman aure dashi na har abada. Da yammah Imran ya dawo ya ɗauki little Aysha a ƙafadarsa, har lokacin Rahama kuma ko kallo bai isheta ba, haka ya karasa zamansa yai tafiyarsa. Yanayin da Rahama ta bullo dashi yadda take beherving akan wasu abubuwa yana tabasa sosai. Washe gari Mommy da Humaidah suka zo asibitin Rahama na ganin Humaidah ta wani haɗe rai sai lokacin ta tuna itama matar Imran ce kishi ya motsa, ashe shi yasa Imran bai taɓa nemanta ba har na tsawon wani lokaci saboda yana tare da wata matarsa tana bashi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads