Showing 57001 words to 60000 words out of 139785 words
Chapter 20 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
tana ciki." Jin cewa Umminta na nan yasa ta fara tafiya. Kai tsaye ta nufi entrance ɗin shiga cikin gidan. A cikin parlorn babu kowa sai masu aiki daketa gyaran gidan, kowa kallonta ya tsaya yi. Kai tsaye ta nufi stairs tana jin ƙafafunta na wani irin rawa. Bata tsaya ko'ina ba sai a ƙofar ɗakin Umminta, zuciyarta na harbawa tayi knocking har kusan minti biyu taji shiru hakan yasa ta ɗan tura ƙofar. Hango Umminta tayi kwance kan bed tana bacci. "Waye?" Taji an faɗa ba tare da Ummin ta bude idonta ba. Hawaye suka zubo mata lokaci ɗaya cikin rawar murya take faɗin. "Ummi Rahama ce." Da wani irin yanayi Ummi tayi saurin buɗe ido cikin second ɗaya kacal ta miƙe zaune tana kallon Rahama dake tsaye a gabanta. Ummi ta shiga girgiza kai tana faɗin. "Me kika zo yi mana?" Kasa daurewa Rahama tayi kawai ta nufi Ummi da gudu tamkar wata ƙaramar yarinya ta wani faɗa cikin jikinta gamida fashewa da wani irin kuka mai cin rai. "Kiyi hakuri-kiyi hakuri dan Allah Ummi, wallahi bazan iya rayuwa babu ku ba, Kune walwalata da duk wani jin daɗina duka. Ina jin tsoron rayuwar duniyar nan kar kusa tsinuwar Allah ta hau kaina akan fushin da kukeyi dani, nasan nayi maku laifi maigirma. Ummi kallon da kuke yi min yana ɗaga min hankali, yana rusa duk wani fatana a duniya, wallahi tallahi ban taɓa aikata zina ba, Ummi ko vedion da kuka gani a wayar Yaya Farook dan gujewa aurensa ne yasa na aikata haka, amma ba dan ina so ko shi Imran yana so ba." Ta ƙarasa maganar cikin shessheka lokaci ɗaya Ummi ta fisgota daga jikinta ta riqe mata shoulders tamkar zata ɓallasu, wani irin ɓacin rai take hangowa cikin idanun Ummi, "Yanzu akan wannan dalilin shi yasa kika buɗe jikin ki Imran Matawalle yayi yadda yaga dama dashi? Are you stupid? Taya zakiyi daraja a idanunsa ko bayan aurenku? kin cuci kanki wallahi kin tozarta rayuwarki, sannan zaki barwa ƴaƴanki abun faɗi, kuma har abada bazakiyi daraja a Idon Imran Matawalle ba, tunda har ya riga yaga tsaraicinki tun kafin aurenku. kibar namiji Inda yake komai son da yake yi maka da ya tuno da wannan ranar na cewa kin gama basa jikin ki tun atiti wallahi tallahi zaiji ya tsaneki idan ma bakiyi hankali ba ko bayan aurenku zai fara xargin kina bin wasu maxan sabida bakiyi musun basa jikin kiba tun a waje." Hawaye kawai ke xubar mata maganganun Umminta sun taɓata, haka sun karyar mata duka wani kwarin gwiwar da take dashi akan rayuwar aurenta da Imran Matawalle. Meyasa tayi wannan ganganci? meyasa ta yadda da khudubar da shaitan ya xauna yayi mata?kenan yanxu Imran kallon ballagaxa ƴar iska yake yi mata dan ya riga yagama sanin sirrin jikinta tun a titi? Tabbas idan ya auri Humaidah ta gama yawo, tasan bazai ƙara kallonta da daraja ba. "Ki tashi ki tafi Allah ya kyauta." Ummi ta miqe tsaye fuska babu walwala tana nuna mata ƙofa. Zubewa tayi agaban Ummi ta riqe kafafunta hawaye na xubar mata. Ummi ta runtse Ido haka kukan Rahama na karya mata zuciya. Addu'a kawai take Allah yasa Rahama ta hakura da Imran Matawalle sai kawai taji tana cewa. "Kiyi min addu'a a duk Inda xani taka ƙafata Ummi, addu'arki nake bukata saboda an ɗaura min aure da Imran Matawalle a jiya." Kalaman Rahama ba ƙaramin girgiza Ummi sukayi ba, sai ga Ummi ta xauna dabas akan bed tana kallon Rahama da wani irin tashin hankali da take hangowa cikin idanuwan Ummi. Sosai Ummi taji daɗin wannan auren aranta ko ba komai Allah ya kare mata ƴarta daga faɗawa halaka sai dai baxata nuna mata a fili ba xata kuma cigaba da yi mata addu'a a duk Inda take a matsayinta na uwa. Tun ranar da Rahama ta fice daga cikin gidan su walwalar Ummi da jin daɗin ta ya rage. Abba yasa duka sunyi blocking number ɗinta har ta Hajja ya karɓa yayi, haka yayi rantsuwa idan Ummi ta nemi Rahama xai datsa igiyar Ummi ta auren su. Kalaman Abba sun girgiza Ummi, sun kaɗata tana kaunar Rahama haka tana son aurenta sai dai a duk halin da Rahama ta tsinci kanta baxata daina yi mata addu'a ba a matsayinta na uwa. "Jeki kawai Allah ya bada xaman hakuri." Ummi ta faɗa tana kawar da fuskarta daga cikin ta Rahama dan kar Rahamar ta gano weakness ɗin Ummin akanta. "Zan roqi alfarma Ummi koda shine abu na ƙarshe da xan nema a wurinki Ummi. Dan Allah ki buɗe wayarki mu riqa magana koda xan riqa kiranki ne sau ɗaya a sati, hakan ma xanyi farin cikin jin muryarki please Ummi." Ta faɗa tana kallon reaction ɗin Ummi. Ummi ta girgiza kai batareda ta kalleta ba tana faɗin, "Kiyi hakuri banda wannan." Cizon lips tayi "Abba ya hana koh Ummi?" Rahama ta faɗa da rawar murya tana kallon Ummi, Rahama ta miqe tsaye ta nufi ƙofa tana faɗin "Nagode ma a hakan da kika sauraren, xanyi kokari na riqa xuwa asibiti muna gaisawa." Da haka ta fice daga ɗakin tana jin wani sabon kuka nazubo mata. Yadda yaga ta fito a rikice ne yasa ya balle marfin motar yayi mamakin data ɗauki lokaci bata fito ba ya ɗauka ko Abubakar Galadanci ya riqe ƴarsa kenan da ya kuduri aniyar wannan karon xai nuna masa bad side ɗin Imran Matawalle. Zai riqota ta fisge hannunta ta nufi front seat ta bude ta faɗa cikin motar ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, motar ya koma xai jawota tayi saurin fisgewa tuna kalaman Umminta kurum akan
Imran ɗin xai riqa yi mata kallon ballagaxa tun atiti ya gama ganin jikinta, A hankali ya ɗora kansa akan staring motar xuciyarsa na mugun tafasa, kukanta na mugun taɓasa. Motar yayiwa key da wani irin speed yabar layin idonsa sun kaɗa lokaci ɗaya ya canja kala jijiyoyin kansa suka fito sarari alamar ransa yayi mugun baci haka ya hau titi yana sharara mugun gudun da yasa Rahama ta tsaida kukan nata, cike da wani irin tsoro take kallonsa tana ganin yadda wasu ke binsa da xagi da bakaken kalamai amman Imran ko sauraren su bayayi dai-dai lokacin wani mai bara makaho da ɗan jagora suka kawo tsakiyyar titi, ganin da gaske cikinsu zai yi yasa Rahama ta runtse Ido gamida sakin wata irin kara, jikinta ba Inda baya rawa tana jin numfashinta na baraxanar ɗaukewa duka. Wani irin burki yaja ya kauce musu motar ta bugi wata transformer dake bakin hanya, lokaci ɗaya kuma transformer ɗin ta faɗi daga ma'ajiyarta. Mutane ne suka fara ihu da guje-guje Allah yaso babu wuta a transformer ɗin. Ya kalli gefen Rahama wacce ta dade da sumewa ko motsi batayi ga motar tana ta hayaki dakyar ya ɓalle marfin motar hannunsa da goshinsa yana fitar da jini sabida glass ɗin motar da ya fashe ya ɗan taɓasa. Ɗaukota yayi dukanta babu numfashi a tattare da ita, dandaxon mutane sun cika wurin. Wani shop dake gefen hanya nan ya shiga da ita aka shinfida musu wata ƙatuwar rug irin ta sallah. Murza cikin hannunta ya shiga yi agigice, jin bata numfashi hannusa duka biyu ya ɗora akan kirjinta yana ɗan dannawa. Mai shop ɗin ya taimaka masa ya basa bottle water YA buɗe, a fuskarta ya shiga shafa mata ruwan, wata irin ajiyar xuciya ta shiga sauqewa a hankali kuma ta shiga buɗe idonta. Wata irin runguma yayi mata xuciyarsa na tsananin bugawa bin wurin ta shiga yi da kallo zuciyarta na tsananin harbawa ta kalli Imran bakinta na rawa maganar da take kokarin yi ta kasa yi. "Are you owk?" Ya faɗa yana riqe da ita. "Ina motar?" Ta faɗa murya can ƙasa. Ya girgiza kansa yana faɗin, "Ki natsu dan Allah." Ya faɗa mata cikin kwantar da murya hannunsa tabi da kallo ganin jini haka ma goshinsa, ta rintsa ido. Waya ya kira yayi bayanin Inda yake, motoci biyu na gidan Matawalle suka xo dan tafiya da Imran ɗin, ya kwashe duka abubuwan amfaninsa dake cikin motar, duka a back seat suka xauna har lokacin Rahama na makale dashi jikinta gaba ɗaya ya saki ganin haka yasa shi ɗago kanta da sauri yana faɗin. "Idan kin san bazaki iya zama a school ba kawai mu koma gida." Da sauri ta girgiza masa kai, "Ina son na shiga school Imran kuma ko waya babu a hannuna tun ranar da daddy yasa aka ɗaukeni ban san inda suka ajemin ba, kuma ina son nayi magana da ihsan." Umarni Imran ya bayar akan su juya motocinsu zuwa Bayero University. Nan kuma ya ciro wayarsa ya kira Misbahu yana tambayarsa wayar Rahama. Da girmamawa yake faɗin ai tun a ranar ya baiwa maigirma Matawalle wayar, da haka ya katse kiran ya kira daddy kusan miss call biyu bai ɗaga ba. Motocin na tsayawa ta kai hannu xata buɗe handling ɗin motar ya riqeta yana kallon cikin idonta tare da cewa. "Anjima xan dawo muje gida." Maƙe kafaɗa tayi fuska babu walwala take faɗin. "A hostel xan xauna." Ya girgiza kai gamida riqo fuskarta cikin wani irin yanayi yake faɗin, "Kina matsayin matar tawa xan cigaba da barinki ki kwana a hostel? no way. Anjima xanxo mu koma gida." Zatayi magana yayi sauri ɗora yatsansa a saman bakinta gamida girgixa kansa yana faɗin. "Insha Allahu jibi xamu tare a namu gidan, kayan ne basu gama haɗawa ba, sannan kayanki duka dake hostel xamu kwashesu duka a yau." Ya haɗe fuskarsa da tata yana gogar hancinta gamida lumshe ido. Zaro Ido tayi tana kallon driver dake gaban motar, umarni yayiwa drivern akan ya fita, yana fita yasa remote dake control ɗin seat ɗin, ya kwantar da seat ɗin tayi ƙasa xata kwace kanta ya fisgota duka ya mata rumfa. Runtse ido tayi tana jin numfashinta na wani irin fita da sauri da sauri lokaci ɗaya taji yana yawo da hannunsa cikin rigar jikinta, bai saukar da hannun a ko'ina ba sai akan na shanunta, wata irin ajiyar xuciya ta sauke tana yi masa wani irin shanyayyen kallo, murxasu ya shiga yi cikin wani irin salo. Motsi da ƙafafunta ta shigayi ganin haka yasa shi haɗe bakinsa da nata ya shiga yana gigitata da possionate kisses ɗinsa masu wuyar misiltawa. Hannunta ya lalubo ya dora akan B* ɗinsa wacce tayi wani irin fitowa, gabanta na mugun faɗuwa ta jaye hannun da sauri tana sauke wani irin numfashi. B* ɗinsa ya ciro ya shiga goga mata ita a haukace, agigice ta kankamesa a lokacin ya ɗagata gamida komawa gefe yana sauke numfashi. Tabbas idan har bai kusanci Rahama acikin kwanakin nan ba komai zai iya faru dashi. Sai da suka samu natsuwa na kusan minti goma ya ɗago ta yana share hawayen idonta yaja dogon hancinta gamida sumbatar ɗan ƙaramin bakinta da sexy muryarsa yake faɗin. "I love you more than I love my self ALBI..." Ya qarasa da muryarsa da ta kashe duka jikin Rahama. Tana jin wani abu na sauka a pant ɗinta sai faman ciccijewa take saboda ita kaɗai tasan halin da take ciki. A hankali ya damƙa mata 10k acikin hannunta yana maida jikinsa bayan kujera, har ta fice daga cikin motar idonsa na kanta, remote yasa ya ɗaga seat ɗin, kwantar da kansa yayi cikin seat ɗin sosai gamida runtse idonsa hannunsa ɗaya na riqe da wandonsa. Kai tsaye gida ya koma wanka ya qarayi yayi dressing wajen da ya samu rauni. ya nufi part ɗin mahaifinsa duka yau da family ɗin Matawalle ke m breakfast dasu. Sannu Matawalle ya shiga yi masa yana jin tamkar ya dawo da raunin jikin ɗan nasa kanshi. Gyaran murya Imran yayi ya ɗan shafa kansa yana faɗin. "Daddy wayar Rahama tana bukatarta musamman ma sim card ɗin." Matawalle ya gyada kai yana faɗin. "Tana cikin master bedroom ɗina idan ka tashi kaje ka ɗaukar mata, sa'anann maganar hidimar bikinka da Humaidah shirye-shiryen me zakayi?" Ya wani yakune fuska lokaci ɗaya yana faɗin. "Daddy shirye-shiryen me xanyi? kawai a shafa fatiha that's all." Baki bude Mommy ke faɗin. "Sai kace wani bikin wasu ƴan iska?" Imran ya girgiza kai yana faɗin. "Nafi son na ƴan iskan ai dan bana bukatar party ko wani abun, idan kuma taji tana bukata tayi ita ɗaya amman ni baxanje ba." Humaidah ta kallesa da idonta da suka canja kala cikin rawar murya take faɗin. "A saboda ka auri wata waccan banxar shine bazaka ba?" A mugun haukace ya dawo gabanta ya shako mata wuya daman kuma cike yake da ita "Wacece banzar? Rahamana kike kira da banza?" Ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai, tari sosai Humaidah keyi salati Mommy ta soma yi tana faɗin. "Kashe ta zakayi ne Imran?." matawalle ne ya dakawa Imran ɗin tsawa yana faɗin. "A gabana kake kokarin kasheta don ubanka.?!" Matawalle ya faɗa so pissed up. Sakinta yayi a mugun fusace ya nufi ƙofa, lokaci ɗaya Humaidah ta fashe da kuka Mommy ta hau lallashinta. "Karki wani damu da barazanar sa Humee, aure ne baza'a fasa ba." Daddy ya qara baiwa Humaidah hakuri haka yace su shirya zuwa ita da Mommy su tafi Dubai ta hado kayan lefenta da furnitures ɗin da take bukata. Mommy ta saki murmushin samun nasara aranta take faɗin lallai malam mai tasiri maganinsa yayi masu rana batayi hasarar kudinta ba, ta gama da bakin Daddy saura wannan mai shegen taurin kan tsiyar. "Nagode sosai daddy Allah ya ƙara girma da arziki." Humaidah ta faɗa sounding so very happy, lokaci ɗaya Maheera Matawalle ta miqe tsaye ta nufi ƙofa, baki buɗe Mommy ke kallonta Daddy ya girgiza kai yana faɗin, "Wa kuma ya taɓo min Mamana?." Mommy ta girgiza kai tana faɗin "Ba an taɓa fav ɗinta ba, kasan duka gidan nan shine abun sonta da kaunarta." Mommy ta qarasa maganar cike da kishi bayan fitar Daddy mommy da Humaidah suma fita sukayi suka bar Maheera kawai a gida daman Imran yana fita clinic ya nufa ya tarar da ayyuka sosai dan haka bai samu kansa ba sai kusan karfe hudu da rabi, bai samu yin waya da Rahama ba sabida babu waya a hannunta, ya kira ta Ihsan kuma bata xuwa.
Ihsaan ta wani haɗe rai tana haɗa kayanta cikin rawar murya Rahama ke faɗin "Ina kuma zaki?'' Wani irin kallo Ihsaan ta shiga yi mata tana faɗin. "Canja ɗaki xanyi tunda bani da muhimmanci a wajen ki, komai naki ya canja Rahama tamkar bake ba. Nagaji to bazan iya wannan zaman dake ba." Tamkar jira Rahama keyi ai mata magana ta fashewa da ihsaan kuka mai taɓa xuciya. Baki Ihsaan ta saki tana kallonta haka lokaci ɗaya jikinta yayi mugun sanyi...
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida
#Ihsaan
#Haske Writer's Association
[11/21, 11:13 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya na MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
*Areewabook*
https://arewabooks.com/chapter?id=6362e614d52c9563f327d94f
27.....
Kuka kawai Rahama keyi irin kukan nan mai saka damuwa a cikin zuciyar wanda akeyi a gabansa, gabaki ɗaya Ihsan sai taji bata kyauta ba ta samu waje ta zauna tare da kwantar da kai tana cewa. "Gabaki ɗaya na kasa gane farin cikinki da walwalarki Rahama, ga rashin kwana a hostel, idan kuma na tambayeki matsalar da kike ciki kawai sai ki fashe min da kuka, a haka kike so muci gaba da zama a ɗaki ɗaya? Nasan soyayyarki da Imran Matawalle, sannan babu laifi nasan kaɗan daga cikin wasu habit nashi so tell me Rahama meke faruwa? Ni kawarki ce ban sani ba ko kinje kin samu sabbin kawaye shi yasa kike shareni." Cikin girgiza kai hawaye basu daina zirarowa daga idanunta ba take faɗin. "Nasani Ihsan kina hakurin zama dani, kiyi hakuri ki zauna a ɗakin nan dan Allah." Ta ƙarasa maganar tana shassheƙar kuka. "Naji zan zauna amma ki sanar dani meke faruwa?" Rahama ta sunkuyar da kai ta fara bawa Ihsan duk labarin abubuwan da suka faru tun daga zuwanta police station har auran da sukayi ita da Imran da kuma auran Humaidah da zai yi. Ai duk sai Ihsan taji abubuwan abai-bai, kallan Rahama kawai takeyi tana girgiza kai haushi kamar ya kasheta ta fara magana. "Lallai Rahama kinyi wauta, ni wallahi kin bani matuƙar mamaki ace kin guji su Abba saboda wani Imran, me yasa kike sanshi da yawa har haka Rahama? Kinsan butulcin namiji kuwa?" Wasu hawaye ne masu zafi suka zirarowa Rahama, ta riƙo hannayen Ihsan tana faɗin. "Na fara gani Ihsan tunda gashi Imran zai yi wani auran bayan ko tarewa banyi ba." Ita kanta Ihsan wani irin bakin ciki takeji, gabaki ɗaya taji Imran yana bata mugun haushi. "Yanzu wacce mafitar kika samawa kanki?" Shiru Rahama tayi ta kasa cewa komai, kiran Imran ne ya shigo wayar Ihsan dake kusa da Rahama a ajiye, Rahama tana gani taki ɗagawa, Ihsan ta ɗan sauke numfashi tace, "Haka nan zaki hakuri ki ɗauki wayar tunda yanzu kin zama matarsa dan nasan ke zai tambaya." Rahama ta hadiye wani abu mai zafi tana cewa. "Rabu dashi kawai." Ta faɗa tana sake fashewa da kuka, Ihsan ta cije lips tare da cewa. "Bazaki iya jurewa ba na sanki sarai Rahama indai akan Imran ne." Kira yai ta yi amma taki ɗagawa duk da cewa zuciyarta tana san jin muryarsa, ta daure sosai dan tana son yasan ya ɓata mata, ya kuma gane cewar auran Humaidah ba ƙaramin tada musu hankali zai yi ba dan ba zata taɓa yadda ya auri katuwar matar nan ba. Wayar ya sake kira, kallan Rahama tayi tare da cewa, "Kinki ɗagawa gashi nan yana ta kirana." Wani irin riko Rahama ta yiwa hannun Ihsan tana girgiza kai tana faɗin. "Please Ihsan kice masa har yanzu muna lecture." Kafaɗa Ihsan ta ɗaga tare da kara wayar a jikin kunnenta. "Ihsan ƙawarki tana lecture ne?." Cikin dauriya tace dashi. "Eh gaskiya dan har na taho basu fito ba.. Okay zan sanar da kai..." Dire wayar tayi tana kallan Rahama da ta haɗe hannayenta biyu ta ɗora haɓarta tana tunani. "Yace wai idan kun fito na sanar